Showing 87001 words to 90000 words out of 118783 words
a gidan, amma tana shakkar kar Mum taqi yarda dan yadda suka yarda da Jameelaa abun har abun mamaki.
Amma ta ayyana ma ran ta ko ba zasu yarda da ita ba sai ta faɗa masu abubuwan da take gani kuma da wanda akai a gaban idon ta.
Jameelaa ce ta sha kwalliya tana zaune gefen ta Humairah ce kwance ta na wasa irin na yara, Kulu ce ta shiga da sallama ta durqusa kamar yanda take yi mata tace,
"Barka da hutawa uwar d'aki na,"
"Barka dai, ya aka yi?"
"Dama na gama aikina ne nace bari na zo na nemi izinin ki ina son naje na gaida su hajiya, na kwan biyu ban ji labarin mutan gida ba"
"Ki gaishe su,"
Magana take cikin isa da taqama ita a dole mai gida da mai aikin ta. Kulu ce ta tashi ta sanya hijabin ta dake hannun ta ta dan yi wa Humairah wasa sannan ta tafi.
Koda taje gidan Mum ta tarar bata nan, zama tayi suka sha hira da mai aikin Mum taci abinci tayi sallah ta dan kwanta, bata jima da fara bacci ba Mum ta dawo, mai aikin gidan ta sanar da ita, bari suka yi sai da taci abinci ta yi wanka, ta fito parlour sannan Kulu taje suka gaisa tace,
"Hajiya dama tin ɗazu nazo ai ni na ma manta yau ranar aiki ce, ina tafe da wata muhimmiyar magana ne Hajiya ina fatan ko baki yarda dani ba zaki yi bincike akai, saboda ki gano gaskiyar lamarin"
"Ikon Allah ! wannan wacce iriyar magana ce mai mahimmanci haka? Ina sauraron ki Kulu,"
"Yauwaa Hajiya.... dama magana ce akan Uwar d'akina Jameelaah da uban d'aki na Ummaru, a gaskiya Hajiya zaman nasu na kasa gane irin shi, yaron nan yana iya qoqarin shi na kyautata ma iyalin shi daga kan ci da sha sutura, lafiyar su, da komai na su da idona ya gani, amma matar shi bata da godewa Allah, kwanaki munje gidan mahaifiyar ta, ana zaune ana hira, sai kawai suka ban Humairah wai na je waje na yi mata wasa, ina fita na tsaya tsakar gida, ina jin suna tattaunawa akan Uwar zata kai ta gidan boka, sannan jiya abinda ya faru ya ban mamaki kuma ya sa ni zargi kala-kala, yarinyar nan tin da ta fita da safe sai dare ta dawo, ta dawo da wani irin salo na makirci, saboda kar Ummaru ya tambayi ina taje, qiri-qiri bata damu ko zan gani ba, bayan ya juya baya ta fara dariyar mugunta harda tsalle, ni ina zargin ma fa ko tana bin wasu maz......"
"Dan girman Allah dakata anan kulu, haba kulu da girman ki, da hankalin ki, kike aibata yarinya mai nutsuwa da hankali irin Jameelaah? Taya zaki zayyana waɗannan abubuwa a kan Jameelaa? Sannan har ki yi zargin tana bin wasu mazan bayan Umar mijin ta? Gaskiya ban ji daɗin wannan maganar ba,"
"Hajiya dama ai ba magana ce mai daɗi ba, magana ce ta kiyi bincike akan abinda na sanar da ke yanzu, ni dama ai bance ki amince da magana ta ba a tashi ɗaya ba tare da kin yi bincike ba, ki bincika ki gani, innai qarya a magana ta sai ki d'au mummunan matakin qazafi akaina na amince, soyayyar ku a raina ta daban ce, ba zan bari Ummar ya cutu ba ina ji kuma ina gani inshaa Allahu,"
"To kulu zan yi bincike akai, yanzu ki koma gida kar ta neme ki na gode,"
"Ta san na zo nan dan da izinin ta na zo nan, yana daga cikin laifukan ta shine satar fita, daya fice ta sa qafa ta fice itama,"
"To yayi haka kulu, zan bincika na gode,"
Dubu ɗaya ta bata tace ta hau abin hawa ta koma gida, godiya tayi ta koma.
La'asar ake kira lokacin da ta isa gida ta tarar da Jameelaa bata gidan, ta kuma tabbata bata fita ba sai da ta tabbatar Umar ya ci abinci ya koma, kad'a kai tayi ta faɗa kitchen dan ɗora abincin dare, ta sake gyara inda aka b'ata.
Jameelaa ce ke ta bulayin neman layin da aka kaita jiya, in an shiga layi ta ce ba nan ba, har suka shiga wani layin da ke kusa dana bokan nata, yana zaune cikin abokai ana zuqe-zuqen kayan maye, shi sigari yake ta busawa, yana hango ta cikin adaidaita sahu ya sunkuyar da kai, sai da suka wuce ya bi ta siririyar hanyar ya d'iba da gudu zuwa gida, shagon shi ya maida kamar na boka, yana tsaka da saka rigar bokan cin shi ya ji ana buga qofar, surkulle ya fara yi, yana faɗin a jira shi, yana gamawa da 'yar matumbura.
Sai da ya shirya tsaf ya zauna sannan yace a shiga, shiga ta yi tana ta washe baki ta zauna tace,
"Ta kan tsamiya ta taimaki boka, boka na zo godiya ne, aiki yayi kyau, shine nace dole na zo na kawo gaisuwa ta musamman"
"Tiiirrrrr, sirrrrr, firrrr, bucaaaaa, kin kyautaaa, kin kyautaaa, hakan yayi daidaiiii, Ta kan tsamiya na jin ki, kuma itama ta ji daɗi,"
"Boka sai dai akwai wani hanzari da nake tafe dashi a yanzu, jiya da kyar yarinya ta ta farka daga baccin nan na karya sihiri, dan saida muka je asibiti aka ce mana maganin bacci ta sha,"
Dan zazzare ido yayi sannan yace,
"Kar ki damuuu, ai su likitoci basu so a ce basu iya aikin su baaaa shine kawai, amma maganin karya sihiri na baku dika, kuma ya karye, sai dai akwai matsala aikin Uwar mijin ki bai yi ba, sai an......."
Wayar ta ce ta katse masu hanzari, janyo jakar ta tayi ta duba, no Mum ta gani nan ta nuna masa, ya yi mata izinin d'agawa sai kace wayar shi haka ta bi umarnin shi ta d'aga,bayan gaishe-gaishe ne Mum tace,
"Jameelaa lafiya kuke kuwa? Rabon ki da zuwa gidannan har na manta, ko a waya baki kira a gaisa in ba ni na kira ki ba, ko akwai wata matsalar ne ki sanar da ni?"
Sai da ta gama rashin kunya da baki da ido sannan tace,
"Ni ba komai kawai 'yan zuwan ne basu zo ba, amma dik sanda na so zuwa zan zo"
Tirqashi ! Mum ce ta miqe tsaye sakamakon saurarar kalaman Jameelaa da tayi, lallai maganar Kulu akwai qamshin gaskiya aciki,
"Jameelaa lafiyar ki kuwa kike yi min magana a haka?"
"Qalaou nake ni yanzu bana nan na dan fita unguwa in anjima munyi magana,"
Kit ta kashe wayar,
"Kinji me nake fada makiiii,aikin ta bai yi baaa, sai an sake aiki akan ta, ki tube a yi maki aiki,ki tubeeee, tubeeee, tubeeee"
Ai jiki na rawa Jameelaa ta tube, kallon da ya ke binta da shi ne ya fara tsorata ta, gashi yau bashi da maganin da zai sanya mata, dan haka ya hau borin qarya yana faduwa yana miqewa, shi a dole aljanu ne suka zo,
"Lale maraba da zuwan ku na Nijer, maraba maraba, yauma ta dawo a yi mata aiki, a raba ta da Uwar mijiiiii, ta dawo a yi mata mai sauqiiiii"
Nan ya fara da fesa mata ruwa kamar jiya, daga nan ya fara shafe mata ruwan daya fesa mata, tin tana daurewa har ya fara bata wani yanayi a jikin ta, (kun san dai mutuniyar ku, ba sai anyi ta dogon bayani ba😂) nan da nan cikin sauqi ya same ta, ita da ake ma aiki sai ta dawo tana aiki, nan suka samu suka gama lalacewar su, ta gyara jikin ta tsaf ta tashi,
"Dama irin wannan ne aikin? Aini jiya baka sanar dani ba, ga mallakar miji na samu, yau kuwa ina fatan na samu ta uwar miji, aikin ka akwai biyan buqata ta kowanne fanni,"
Kudi ta laluba ta damqa masa, ta goye Humairah ta fita, a gaskiya ba qaramin nutsuwa ya samu da ita ba, da da yanda zaiyi kullum tana zuwa ai shi bai da case.
"Ki daina bani kudiiii bana soooo, bana soooo, aje su cannnn Ta kan tsamiya zata daukaaaa, ki dawo gobeee sai kinyi wata kina zuwa kafin aikin ki yayi kyau, shi irin sihirin nan na dindindin yana buqatar ayi wata ana yin shi, in ya kama jiki har abada ne, sai kin mutu aljanin dake baki kariya zai rabu dakeeee,"
"Lallai da na zama mai sa'a na mallaki umar da iyayen shi har mutuwa ta,da kuwa na mallaka maka dukiya kaima mai tarin yawa,na yi maka alqawari dik abinda na samu zan raba uku na baka kashi ɗaya,"
"Bana son kudiiii, bana soooo, bana soooo, sai dai ki kawo na yankan Takan tsamiya,"
"Shi ɗin dai za a Kawo babban boka mai babban aiki, bari na koma ni kar a neme ni a ga shiru na gode bokan duniya, Ta kan tsamiya ta taimaki babban boka"
Nan ta fice tana murna, aikin akwai daɗi kuma akwai biyan buqata.
(Wannan shi ake cewa tsafi gaskiyar me shi)
Yau ma sai magrib ta koma gida Umar bai koma gida ba, kulu na kula da dik abinda take yi, wanka ta fesa mai kyau kamar ba abinda ya faru, ta sha kwalliya sosai koda Umar ya dawo ya ganta wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar shi, Humairah ma an mata gayu sai qamshi take zabgawa.
Ɗauke take da Humairah ta je yi masa Oyoyo, dikkan su ya haɗa ya d'aga su sai dariya suke yi gaba ɗayan su, kafin daga baya ya ajiye su ya amshi Humairah yana yi mata wasa, ita kuma Jameelah sai ta amshi jakar shi suka shige ciki.
'Kaiiii da na san da wannan boka tin asali da na je, da Umar ya dad'e ashe mallake a hannuna, rashin sani ya fi dare hudu, ba zan kuwa wasa da dama ta ba, sai na ci gaba da zuwa na wata ɗayan nan cirr, na samu a mallakan shi na har abada'
Abinci ta zuba masa ya fara ci ya yi masa daɗi sosai abincin amma ba halin yayi santi tinda ba ita ta dafa ba, in yayi santi sai tace yana yabon girkin wata bayan ita ba tai masa ba da kan ta.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya daga baya ma idan zata fita yawon ta sai ta aje ma Kulu Humairah ta fice, dan kar a asirin ta ya tonu sai take raba qafa, taje gidan su sannan ta wuce, ko in ta dawo daga wajen bokan ta je gidan nasu.
************************
Umar na duba marasa lafiya ya bar wayar shi a Office, koda ya koma ya tarar da missed calls da yawa,No Umaimah ce sai ta Mum, yana cikin dubawa Umaimah ta sake kira.
"Assalamu alaikum, sweet sis,"
"Uncle Umar wa'alaikumussalam,albishirin ka"
"Sapnah me kike nufi da uncle? Kar ki faɗan umaimah na ta haihu sai yanzu ake sanar da ni?"
"Kwarai da gaske Umaimah ta haihu lafiya mun samu mace tin da ta fara naquda nake ta kiran ka ba ka daga ba ai, Mum ma nan sai kiran ka take yi shiru baka ɗauka ba, so kaga kenan ba laifin mu bane"
"Haka ne baku da laifi me muka?"
"Mace muka samu,"
"Masha Allah,Allah ya raya mana, gani nan zuwa na gama abunda nake yi dama kuna ina?"
"Muna gida a gida ta haihu,"
"Ok sai nazo to,"
Tattara wayoyin shi yayi ya rufe office sai gidan su Umaimah.
Murna ta hana shi rufe baki yana matuqar qaunar qanwar shi sosai, gashi ta haifa masu yarinya,Humairah ta samu abokiyar wasa.
Jameelaa ya kira ya sanar da ita yace ta kira ta yi wa Umaimah barka.
Cikin murna kuwa ta kira qawar ta ta, daga wayar Sapnah tayi dan Umaimah na bacci.
"Qawata qanwa ta kuma maman Baby barka... barka.. barka, kin sauka qalaou?"
"Lafiya qlou ta sauka, kina magana da Sapnah ne,"
"Mtsssss me ye naki na amsa wayar mutane ke kuma karere, ke kenan ba zaki zauna gidan yayar ki da kika zo ba sai kin je gidan Umaimah, salon ki kwacewa mutane maza ko? An tsufa gidan tsoho ana neman wajen sakad'a d'uwais ba a samu ba shine ake bin mazan mutane, to kurwar mazan mu kur ba ki isa samun mazauni a zuciyar mijina ba, ni nafi qarfin ki bari kiji na faɗa maki tun yanzu dan ki san na san menene qudirin ki akan Umar d'ina, aikin banzaaa kawai ko da boka kike yawo akan ki baki isa mallake min miji ba,duk ki gama asire-asiren naki munafuka kawai, in ba rashin imani ba har yarinya qarama kike yiwa asiri? To ta Allah ba taki ba,kuma kin kai qarshen iskanci da asiri tinda kin taɓa ni "
"Keee malama dakata min! Sapnah ce fa kike magana da ita ba wata ba ni me na yi maki?"
"Zaki ga me kika min in na zo gidan, zaki ga hauka ganin idon ki,"
Sapnah riqe wayar tayi a hannu hawaye na zuba mata cikin tsananin takaici, tinda take ba wanda ya taɓa yi mata rashin mutunci irin haka, harda zargin tana asiri? Akan me zatai asiri bayan tana da Allah.
"Me ya faru kike kuka? Ke da wa?"
Aunty Hauwaa da Mum ke mata wannan tambayar, bata iya amsa su ba ta aje wayar Umaimah ta fita daga gidan gaba ɗaya, wayar Aunty Hauwa ta ɗauka, ta ga sunan Jameelaa shine last call da aka dauka.
"Ikon Allah ! Mummy kiran Jameelaa ta d'aga fa take kuka, ko me ya faru kuma sai Allah,"
umar yaga shigar ta gidan Ishaaq tana kuka amma bai san dalili ba, ko me ya same ta kuma oho? Sai ya ji ranshi na masa zafi dan ganin kukan ta, amma son ganin umaimah da babyn da aka haifa masu yafi yawa a ran ranshi dan haka sai ya fita ya nufi gidan Umaimah.
Mum na ɗauke da jaririyar ya shiga nan suka fara yi wa juna barka,
"Ina Umaimahr?"
"Tana d'aki bacci take an yi mata wanka, taci abinci sai kuma ta b'ingire da bacci"
"Allah sarki ina maqale matan mijin ta yake naga ban gan shi ba?"
"Yana kasuwa, ana ta kiran su shi da yayan nashi ba su d'aga ba, sunje store fidda kaya"
"Allah sarki na riga shi ganin baby, sai yazo na san ya dame mu akan ba a sanar da shi ba.....Mum me ya faru naga Sapnah ta fita tana kuka?"
"Ka gan mu muma tambayar da muke wa kan mu kenan, ana zaune lafiya lafiya, ta na sanar ma da mutane haihuwar sannan tana amsa wayar Umaimah sai matar ka ta kira sukai magana shine ta aje ta fita tana kuka"
"Subhanallahi ! to me ya faru? Me tace mata? Bari dai naje na ji daga bakin Sapnah me aka yi mata"
Basu babyn yayi ya fita zuwa gidan Ishaaq, ya na zuwa sai ya hau buga gate, ya dad'e yana bugawa kafin Sapnah ta leqa idon ta yayi mugun ja hancin ta ma haka, tana ganin shi ta sake fashewa da kuka, da sauri ya qarasa gaban gate ɗin, ya durqusa kamar yanda tayi,
"Sapnah dan Allah ki sanar dani me ya sa ki kuka? Kin dai san dik wanda aka haɗa da Allah an gama komai ko? Ki fad'an meke zuciyar ki tsakanin ki da Allah,"
Zayyana masa komai daya faru ita da Jameelaah tayi, sannan ta qara da cewa,
"Yah Umar tabbas na san zuciyata ta kamu da son ka, kuma ban san sanda hakan ta faru ba, na tabbata saboda kyawawan halayen ka ne ya sanya, amma na hakura na danne a raina ban taɓa yunqurin kai kaina wajen ka ba, dik da a baya na so yin hakan, sai na ga bai kamata ina mace nai ta cusa kaina wajen ka ba na hakura, dan ko no da kace na baka ina sane na hana ka,kawai shine matar ka zata zargeni da yi maka asiri, shirka fa kenan? Akan namiji sai na sab'awa Allah na?"
Kuka ta sake fashewa da shi Umar kuwa ji yayi wata iriyar soyayyar Sapnah mai tsafta na fizge shi, kallon ta kawai yake yi bai ma san me zai ce mata ba a wannan yanayin da ya shiga wanda shi kan shi bai san da wanne suna zai kira shi ba, abinda kawai ya sani shine ba zai taɓa bari Sapnah ta kub'uce mashi ba.
"Kutum......bur......ubancan kayyasa, yau za a mutu a unguwar nan me nake gani haka?"
Ashar din da suka ji ne ya sanya su juyawa gaba ɗayan su a tare sannan suka miqe daga durquson da suka yi, tin kan adaidaita sahun ya tsaya ta dira, kan Humaira kuwa ya buge da qarfen adaidaita sahun, kuka ta fasa mai qarfi da gigicewa, amma Jameelaa ko a jikin ta,
Umar ne ya tafi da sauri zai amshi Humairah, Jameelaa ta hankada shi baya,
"Kar ka kuskura ka taba mu maci amana, ashe kana nan ma sanda nake mata magana tana nuna min bata san meke faruwa ba, kuna nan kuna cin amana ta, yau sai an mutu, dan uwar ki fito nan munafuka kike b'uya a bayan mijina,"
Nan da nan kuwa 'yan gulma suka taru ana kallon su, faɗa ba sabon abu bane a wajen Jameelaah dan kuwa sanda tana lungun su har da maza yi take yi, 'yan kallo kuwa ta gan su kala-kala waɗannan tsirarun ba za su hana ta ci wa Umar da Sapnah mutunci ba,shi kuwa Umar kunya dik ta gama baibaye shi,Sapnah kuma kuka ba baki, ita a duniya tafi son ai ta hira ana darawa ta tsani faɗa da tashin hankali.
Umaimah data tashi a bacci ce tace,
"Mum hayaniya nake ji a waje, kamar ana faɗa,"
"Faɗa kuma? Wanne irin faɗa anan unguwar taku?"
"Nima dai abun ya ban mamaki, dan bamu saba jin hayaniya haka ba,"
Nan dai Aunty Hauwa ta aje Muhammad ta sa mayafi ta fita, tana ganin abinda ke faruwa ta koma ta kira Mum, kunyar duniya ta gama kama Mum, jin irin ruwan ashar da rashin mutuncin da Jameelaa ke saukewa Umar da Sapnah, har da kiran su Mazinata.
Saphan nata aikin kuka, dan ita kam cin fuska an gama yi mata shi.
"Jameelaa muje ciki ayi maganar a ciki saboda kinga mutane na ta kallon ki mutuncin mu kike zubarwa anan fa,"
Tankad'a Mum tai sai da ta fadi qasa warwas irin fad'uwar nan ta bazata, sannan ta nuna ta da yatsa tace,
"Ku har wani mutnci gare ku, d'anki na waje yana zina da wata kuna ciki a zaune yana nan yana cin amana ta, amma kike maganar mutunci, wanne mutunci ya rage maku kuma?"
Sapnah ce ta yi saurin d'aga Mum daga qasa, Umar kuwa fuskar