Showing 69001 words to 72000 words out of 118783 words

Chapter 24 - MAZAUNA GIDA COMPLETE By HAERMEEBRAEH.txt

26 Oct 2025

630

kune idon gari, kin san kayan da ake yayi kawai ki siyo min a kai ɗinkin,"

"To shike nan zan dinga rubuta komai aka siya na ajiye saboda ki ga nawa aka kashe kuma a ina aka kashe su, zan ajiye a waje na dan kar lissafi ya b'ata watarana, inshaa Allah sai dai ki ji na aiko maki telana ya gwada ki,"

"Na gode sosai qawar rufin asiri,"

"In Allah ya kaimu ki ka haihu lafiya kuwa har qawaye na 'yan gayu sai na gayyata dan in d'aga darajar ki kema a wajen matan lungun mu, zaki ga yanda sunan ki kema zai yi aji ya zama abin bada labari a unguwar mu baki ɗayan ta,"

Mamalo cikin washe baki ta hau godiya,bayan sun yi sallama Jameelaa ta buga tsaki ta ce,

"Ke dai za ai suna me kyau yarinya amma ai ke kan ki kin san ba zan bari ayi wanda zai fi nawa ba ko? Tin da ba hauka nake yi ba,"

Umar ne ya shiga parlourn ya zauna gefen Jameelaah tare da fadin,

"Ke da wa kike magana kuma?"

"Ba kowa tasbihi nake yi,"

"My love kina burgeni gaskiya, kina da yawan ibada da tsoron Allah, Allah dai ya qaramin qaunarki,"

"Ameeen Abban Humairah,"

"Dan Allah ina son zani asibiti gobe, naga tana yawan kuka naje naji meke damun ta,"

"Subhanallahi haka kawai take kuka ko sai an taba wani wajen?"

Kame-kame ta fara yi dan ganin yanda Umar ya rud'e, ta rasa ma me zata ce masa, daga baya ta ce,

"Ina jin kunne ke yi mata ciwo ko kuma ciki kasan shi ke rud'a yara, ana zaune qalaou in ta rikice da kuka rasa inda zan saka raina na ke yi,"

"Ehh gaskiya ya kamata ki kaita asibiti, goben zan aje ku sai na wuce, in kin gama ki min waya sai na zo na ɗauke ku,"

"Habaaa kana kula da marasa lafiya zan taso ka? Ka bari kawai zamu dawo nan nan da asibiti ka aje mu kawai kaje zamu dawo, inna dawo zan maka waya na sanar da kai,"

"To shike nan Allah ya kaimu,"

"Ameen ya Allah"

Har aka sha ruwa Umar bai ga Humairah ta yi kuka ba, na d'aga hankalin da za a ce bata da lafiya, haka dai ya bar maganar yayi tinanin wataqila da baya nan tayi kukan har Jameelaan tayi tinanin ko kunne ke damun ta, bari ya barsu suje saboda kwanciyar hankalin su baki ɗaya.

Da sassafe kuwa suka shirya dan  kar ta samu layi a cewar ta,ai kuwa qarfe 8 a asibiti ta yi musu, yana fita ta wuce ta je ATM ta cire kuɗin siyayyar ta tass ta koma asibitin dan cin lokaci, sai da taga likitan yara aka duba su ba abinda ke damun yarinyar aka haɗa su da paracitamol in case in tayi kuka jikin yayi zafi, tinda tace in tana kuka jikin ta har zafi yake yi sai a bata.

Godiya tayi ta fita sai kasuwa, siyayya ta yi tayi na dik abinda ya dace, harda su sarqa da dan kunne da abun hannu, takalma da jaka, abubuwan da zasu raba abikin sunan dik sai da ta siya, ta wuce wajen telan ta ta bada ɗinki tace ya yi ɗinki dai-dai nata amma ya rage ta sama saboda Mamalo bata kai ta girman qirji ba.

Sai da ta cake masa kud'in ɗinki sannan ta tafi tsohon gidan su ta je ta kai wa Lantai sauran kayan ajiya, tace na Mamalo ne in suna ya zo dasu za ai amfani ta aje mata bata son Mamalo ta san tayi mata wannan siyayyar.

Ai kuwa Lantai ta dinga sa mata albarka tana godiya sai addu'a take Allah ya bar masu qawancen su har aljannah.

Sai da ta kammala komai ta koma gida ana kiran azahar lokacin da ta isa,sannan ta ɗauki waya ta kira Mamalo ta yi mata bayanin komai, Mamalo harda kuka dan farin ciki a ganin ta bata da masoyi yanzu sama da Jameelaa.

Suna yin sallama ta kashe ta kwanta a gefen Humairah da ta yi baccin wuya dan kuwa yarinyar tayi kuka har ta gaji tayi bacci, tinda suka fita bata samu ta shayar da ita ba,sai da suka dawo din tana waya tana bata mama, har bacci yayi gaba da ita.

"Mamalo kin gama cin gudummawar ki na suna a wannan wahalar dana sha, ko a nawa ban wahala haka ba,"

A haka suka yi ta shirye-shiryen suna a boye, daga wannan lokacin Mamalo kuwa dik maqotan ta samu take ta ɗan shiga a gaisa, wai a nata shirmen a haka za a saba har a ɗan samu su yi mata wani abu idan ta haihu (kamar aje su tayi, da can ba ai zumunci dan Allah ba sai dan a bata abun suna, hummmm).

Bayan kwana uku da kammala siyayyar komai da suke da buqata Mamalo ta tashi da naquda, naqudar ta zo mata da sauqi sosai dan kuwa bata dad'e tana yi ba Sadeeq ya kai ta asibiti suna shiga d'akin haihuwa da mintoci Mamalo ta haifi yaron ta mai matuqar kama da mahaifin shi, sai dai wani babban abun tashin hankalin Mamalo bata haifi yaron nan a raye ba, dan kuwa ko kuka bai yi ba da aka haife shi, ai kuwa tana farfadowa daga azabar haihuwa ta dinga washe baki tana a miqo mata abinda ta haifa ta gani, kowa a wajen shiru yayi,

Midwifes ɗin da suka amshi haihuwar Mamalo ita da wata a d'akin sune suka mata bayanin komawa da ɗan ta yayi, wata qara ta saki ta hau jijjiga idanun ta suka qaqqafe, a guje suka fita dan kiran Dr. Jariri kuwa na hannun Mahaifin shi wanda ke ta kuka saboda rasa babyn shi da yayi, ga kuma halin da Fateeman shi ke ciki.

Likita ne ya shige dan duba Mamalo, ko wanne taimako daya dace a bata an bata, sai dai inaaa shi alqawarin Allah in ya cika ba mai hanawa, kowacce mai rai zata dandani d'aci na mutuwa, Mamalo ta koma ga mahaliccin ta sakamakon kid'imewa da ta yi dan jin ɗan ta bai zo da rai ba, komai dawo mata yayi a lokacin ta hau tinanin kuskuren data tafka na amsar bashi mai yawa gashi yaro ya mutu kuma bata sanar da ko da mijin ta bane abinda ta aikata,wanda aka amshi bashin domin shi ko qamshin duniyar ma bai shaqa ba ya koma, hakan ne ya sa zuciyar ta bugawa ta bi bayan ɗan nata.

Sadeeq kuwa qaramin hauka ya hau yi masu a asibitin, da kyar aka samu ya nutsu, ya zauna a qasa ya dafe kan shi ya dinga rusa kuka, tabbas yayi rashi, yayi babban rashin abar son shi, ba zai taba samun kamar Fateen shi ba.

Da kyar ya iya ɗaukan waya ya kira Malam Buba mahaifin Mamalo ya sanar da shi rasuwar Mamalo da abinda ta haifa, Malam Buba  shima kid'imewa yayi 'yar tashi guda ɗaya tilo yanzu ta zam babu, Lantai kuwa da ya sanar mata suma ta dinga yi.

Mahaifan Sadeeq sun samu halartar gidan su Mamalo sun miqa ta'aziyyar su ga iyayen ta,Sadeeq kuwa baya imm baya imm imm yanzu da ya zauna tinanin irin rayuwar jin daɗin da suka gudanar a gidan su yake yi shi da Fateen shi.

Jameelaa bata tashi jin rasuwar Mamalo ba sai washegari, kuka ta dinga yi tana kumawa cikin ranta tana fad'in

'Na shiga uku ni Jameelaa na lalace na d'akkowa kaina jaraba da bala'i, yau ya zanyi da bashin waɗannan bayin Allah dana amso ba tare da sanin kowa ba? Ga shi ba wanda ya san ma na amso mata sai mu ya mu kawai balle na kafa shaida, dan Allah Mamalo ki tashi na san baki mutu ba, wayyooo Allah na ta mutu ta barni da bala'i,'

Mutane sai riqe ta ake yi sanda ta shiga gidan ta tabbatar da gaske Mamalo mutuwa ta yi, wasu sun zaci tsabar shaquwar dake tsakanin su ce ta janyo ta shiga halin damuwar da take ciki, nan kuwa ba su san me ke cikin ran ta ba na damuwar inda zata samu dubu ɗari biyu ta biya bashin da suka ɗauka take yi.

Umaimah ma ta samu zuwa gaisuwar rasuwar Mamalo, mutane sun samu zuwa sosai saboda abun ya girgiza kowa, maqotan ta sai yabon ta suke yi, suna tina yanda take shiga a 'yan kwanakin, (dik da basu san abinda ke kai ta ba amma sun bada shaida mai kyau akan ta)

Bayan sallah qarama da sati ɗaya Qawayen Jameelaa suka fara doka waya suna tambayar ya suka ji shiru, qarya ta zabga masu da cewar har yanzu qawar ta ta bata haihu ba, ko da ta kashe wayar tinani ta dinga yi ko sata zatai a wajen Umar ne ta biya su? To ta yaya zata saci har dubu ɗari biyu bai gane ba? Ko da da take sata ma qananan sata take yi ba manya haka ba.

Dik wani irin tashin hankali Jameelaa ta shige shi a wannan lokacin,kayan sawar da aka d'inka aka kawo mata a ranar ta fara cigiyar masu siya, haka kuwa aka dinga yi mata tayin walaqanci, a haka ta saida kayan wajen dubu hamsin banda kud'in ɗinki da ta bayar wajen dubu arba'in, kuka kuwa Jameela ta dinga yi wanda ta rasa mai lallashi.

Wanka tayi ta fita ta bar Humairah wajen Kulu Umar ma bai san zata fita ba, gidan su Mamalo ta je, da sallama ta shiga suka gaisa da kowa ta nufi d'akin Lantai,Lantai na zaune ta zabga tagumi tana tinanin d'iyar ta hawaye sirara na bin kuncin ta, dan kuwa bata san sanda zata ji sanyin wannan rasuwa a ranta ba, 'yarta ta kenan guda ɗaya bayan sun gaisa da Jameelaah a mutunce ne Jameelahn ta ce,

"Lantai ki kara hakuri kin ji?hakurin dai zamuyi baki ɗaya dole, Allah dai ya jiqan ta,"

"Ameen Jameelaah ba abinda zan ce maki sai godiya, kin gwada min soyayyar da kike wa Mamalo domin Allah ce, Allah ya albarkaci rayuwar auren ki kema,"

"Ameenn Lantai......immmm.... damaaa.... na zo ne akan kayan dana kawo kwanaki, dama a gaskiyar magana bashi muka ci ni da ita, dan a fita suna lafiya kar a ji kunya, yanzu na zo na amsa na sai da su ko da ba su kai kud'in dana siye su ba na haɗa da kud'in wajena na biya masu kuɗi kud'in su, yanzu dik sauran kud'in ni zan cika na biya gashi banda ko sisi, tinda abunnan ya faru hanyoyin samuna suka toshe gaba ɗaya kamar an datse min su, ko nera dubu Abban Humairah bai sake bani ba"

Cike da bacin rai Lantai ta kalli Jameelah ta ce,

"Kan uban can ! auuuu ina yabon ki sallah zaki kasa alwala Jameelah? Ina ganin Mamalo bata da masoyi sama dake ashe har yanzu halin ki na nan na son abun duniya? Yarinyar ma ta mutu amma ba zaki bar ta ta huta ba?"

Wani irin tashin hankali ne ya rikitowa Jameelah ta ji kamar zata zaga dan tsabar damuwar da take ciki, cikin fitar numfashi sama-sama ta ce,

"Ba haka bane Lantai da gaske bashi muka ci wajen qawaye na ni da marigayiya yanzu haka sai waya suke yi min nayi qarya nace bata haihu ba, dan Allah ki rufan asiri ki ban naje na siyar na haɗa dana hannu na na rage wata asarar,ki barni naji da biyan sauran kudin, in baki biya bashin bane ma zata wahala a qabari, dan kuwa tana cikin azaba dan akwai bashin mutane akan....."

Gaffff naji qarar duka ya sauka a bakin Jameelah, ai kuwa Jameelaah ta buɗe murya tun qarfinta ta zunduma uban ihu ta dafe bakin ta da ya fashe, tana kallon Lantai a tsorace, Lantai kuwa cikin tsananin fushi da bacin rai ta ke nuna Jameelaa da yatsa ta ce,

"In kika kuskura kika sake kira wa yarinya ta azaba a qabari na rantse sai kin kwashe haqoran ki a qasa, dan uwar ki tashi ki bar nan, ki kira kotin qoli ta amsar maki kayan matsiyaciya wadda bata san mene ne mutunci ba,"

Qofar dakin Lantai kuwa nan da nan aka taru ana son jin me ya faru, Jameelaah kuwa sai tayi gum da bakin ta dan tasan tonuwar asirin Mamalo tonuwar nata asirin ne, Lantai ma ba zata so wannan labarin ya fita ba itama, tankad'a Jameelaa waje ta yi, daga dakin ta, sannan ta ce,

"Kar ki bari idona ya sake shiga naki mara mutunci, ki bar nan gidan ko na qarasa maki abinda na fara dan kuwa sai na cire maki haqori"

Jameelaah ba baki sai ido haka ta d'au jakarta ta fita a qofar gidan ta sai ruwa ta wanke bakin ta dake fidda jini ta yi gida.

Ita dai yau ta shiga uku ina zata nemo dubu ɗari da goma ta biya bashi? Ko wajen Mum zata ta roqa ne? Ko zuwa zata yi ta kai dubu arba'in wajen malamai su juya mata da kan Umar ya mata kyautar wannan maqudan kuɗin a dare ɗaya, ko kuma yau zuwa za ta yi ta sha maganin mata da ake cewa gida ko mota ko kyautar kujerar makka wataqila idan Umar ya gigice zai yi mata kyautar da zata wanke mata takaicin bashin da suka gingimo ba mai biya????


*A cikin shawarwarin nan da take yi, wanne ne kuka zaba?*

*Ina ma masoyan Mamalo ta'aziyya rasuwar takuyi hakuri, haka labarin yazo, na san ba za kuji daɗi ba amin afuwa*
[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻












WRITTEN BY HAERMEEBRAERH








PAGE 30:










Zaune take ta saka sarqar da Umar ya bata ta zinare a gaba  tana ta kallo, tinani take yi ko saidawa za ta yi ne ta fidda kud'in mutane dan rufuwar asirin ta, dik da dama ba son komawa makaranta take yi ba balle a gano maqaryaciya ce ita,dan kuwa  in ta bari magana ta fita ajin ta ya zube a wajen kowa da take huld'a da shi a makarantar,ko a wajen qawayen ma bata isa magana ba sai dai su rabu, dan ba su son harkar qaranta su.

Kukan Humairah ne ya dawo da ita daga dogon tinanin da ta tafi, can ta hango ta gefen gado da dikkan alama fad'uwa tayi, sai tsala ihu take yi kuwa kamar zata tsaga gidan, Kulu ce ta shiga dakin tana tambayar lafiya? Ita kanta kulu ta kula da yanda gaba ɗaya yarinyar bata samun isasshiyar kulawa daga wajen mahaifiyar ta sam.

Kuka Jameelaah ta fashe da shi dama ta kai iya wuya wajen quluwa da shiga damuwa, a gigice kulu tace,

"Subhanallahi uwar d'aki na me ya same ki haka ki ke kuka? Me ya same ta itama naga gefen kan ta yayi ja kamar ta bige? kawo ta nan na gani,"

Kuka kawai suke tsalawa daga Jameelahn har jinjirar ta, ji take ko zata sanar wa Umar me ya faru ne dan ya biya kuɗin a huta, amma ba zata so ya gane ta amshi bashi da sunan Humairah ba ba zai ji daɗi ba tinda komai ya yi iya yin sa dan yaga ya wadata su da duk abinda suke da buqata,cikin kuka Jameelah tace,

"Dan Allah Kulu kin san inda ake saida gwal?"

Kallon ta kulu tayi da mamaki tace,

"Eh na sani, amma uwar d'aki na me zai kai ki saida kadarar ki?"

"Ba ruwan ki ni dai kawai ki nuna min muje yanzu kafin Abban ta ya dawo muje mu dawo,"

"Ai kuwa sai dai ki bari ya dawo yaci abinci ya koma, sannan muje dan kuwa ya kusan dawowa,"

Wasu hawaye ne masu zafi suka sake zuba mata, tabbas ta dakkowa kan ta masifa har da bala'i, amma kuma ta san wannan bala'in da take ciki dik Mamalo ce ta jefa ta a cikin shi, da ta sani da bata amsar mata bashin ba, gashi komai nata ya tsaya cak bata samun ko sisi tunda ta karb'i bashin har lokacin mutuwar Mamalon ita da Umar a rana sai ya bata 5k, wataran ma aje kuɗi yake masu yawa yace in tana so ta d'iba ta yi hidimar gaban ta,amma yanzu ko ɗari biyar bata haɗa su tinda abunnan ya faru baya barin sisi ma a gidan dika,hanyoyin samun ta sun qare tasss, rarar 30k data samu a sunan Humairah da ta san haka zai faru data adana bata kashe a banza ba, a qallah ai da ta d'aga dubu saba'in yanzu gashi ɗan abinda ya rage a ciki take ta kuɗin mota shiga can fita can duk dan ta rufawa kan ta asiri.

Har Umar ya shiga parlourn bata sani ba tana nan zaune tana tinanin da ba mafita, sallama yayi ta yi kafin daga baya ta tsorata ta miqe tsaye tana amsawa.

"Ya akayi ne? My love kwana biyu na kula kamar baki cikin nutsuwar ki me ye matsalar ki ne? Faɗa min na yi maki maganin ta,dan kin san ni a duniya bana son na gan ki cikin damuwa ko ya ya ne ba tare da na kawo maki qarshen ta ba"

Hawaye ne ke qoqarin zuba mata ta danne, ba zata yi subul da baka ba, dole ta rufe magana har sai taje ta saida sarqa, in kuɗi bai cika ba ta roqa ya cika mata.

"Ba komai kawai na gaji da zaman gidan ne, anjima ina son zuwa gida na gaida Mamana, wataqila naji daɗi,"

"Indai wannan ne kar ki damu, bari na ci abinci muje na ajiye ku,"

Bai jira me zata ce ba ya fita parlour ya zauna kan dinning din su madaidaici mai kyau na glass ya fara zubawa kan shi abinci, sauri tayi ta shirya, ba komai indai zata samu ya aminta ta fitan ai tayi satar hanya suje su siyar su koma gidan nasu sai yaje can ya ɗauke ta.

Tana gama shiryawa ta d'ebi kayan Humairah ta kaiwa kulu dan ta sauya mata, shiryawa sukai sika karkashe kayan wuta da fitilu na gidan (a dinga kulawa nan gaba kadan sanyi za a shiga, a saba da kashe kayan wuta kan a bar gida, Allah ya kare)

Keys din shi ya koma d'aki ya ɗauko suka fita suka shiga mota sai gidan Hajiya Ramai, sarqar da d'ankunne na maqale a jakar ta, har da abun qafar dika ta d'akko.

A qofar gida ya ajiye su ya ce in ya dawo ɗaukan su ya gaida Maman ta kafin nan ma Baba ya dawo.

A qofar gidan suka maqale sai da suka daidaici ya tafi suka fita a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login