Showing 102001 words to 105000 words out of 118783 words
na koyar dake abinda ya dace mai kyau, ki yafe min, ki yafe min Jameelaah,"
Jameelaah rungume Ramai tayi sukai ta kokawa, har Bukar ya koma da saqon kayan yin awara ajewa yayi ya isa ya zauna yana tambayar waɗannan kayan fa masu tarin yawa daga ina? Nan Ramai ta masa bayani shima ta nemi yafiyar shi, suka yafe wa juna.
"Mama (sunan da suka koma kiran Ramai dashi kenan) ni ina da shawara fa, tinda kin iya girki, mai zai hana ki samu ki dinga yin dambun naman kaza ana siyarwa? A irin robobin nan, a kafa waje anan qofar gidan, tinda kan hanya ne, za a yi kasuwa, sosai"
"Kuma kacewani abu fa Bukariri, bari mahifin ku ya shigo ayi maganar in shawara ta tsaya ni da kai na zan dinga yi,"
Kallon Jameelaah tayi ta ji me zata ce akan hakan amma taji shiru, Jameelaah na can duniyar tinani, ta langwab'e kai gefe hawaye na zubar mata, fatan ta kawai Umar ya maida ta gidan shi.
**********************
An d'aura Auren Sapnah da Umar akan sadaki nera dubu ɗari, ba wata hidimar biki da akai in ba wuni da iyayen su suka yi ba, Umaimah da Aunty Hauwaa da Mum sun tsara zasu ɗauki nauyin yi ma ango da amarya walimah bayan an kai amarya gidan ta kamar yanda islam ya tsara, sun gama qayyade iya adadin mutanen da zasu gayyata, sun gayyaci kala-kalan mutane guda hamsin, a babban wani hall za a haɗu duk a yi walimar.
Sun riga sun yi order na abincin da za a ci a sha, sannan da takeaway da mutane zasu tafi da shi.
Ishaaq da Haroon tare da Daddy sun sake ma matan su kuɗi dan cika burin su, dan haka ba zama sun zama busy, hakan ya sa Sapnah damuwa ainun, tana cikin matsanancin buqayar lallashi a wajen Aunty Hauwaa da Umaimah, dan kuwa Umaimah qawar ta ce sosai, sun shaqu matuqa.
Daga ita sai Safiyya a d'akin, tana ta kukan rabuwa da iyaye da 'yan uwan ta, Maman ta ta shiga ta same ta kwance saman cinyar Safiyya suna ta kuka.
"Ikon Allah ! kuna nan kuna ta kuka ga qawayen ku can a d'akin ku kun baro su kun dawo d'akin Abban ku, wa ya fada maku aure mutuwa ne? Ai ranar farin ciki ce yau, addu'ar neman alkhairin dake cikin shi da neman kariya daga sharrin dake ciki zaki tayi a zuciyar ki amma ba kuka ba, dan ban ga me kukan zai qara maki ko ya rage maki ba, ke kuma da kika zauna kike taya ta kin kai ma mutanen da nace ki kai masu abinci abincin?"
"Eh na kai Ummaah, Ummah kukan kewa muke yi ai, yanzu in ta tafi ba zan dinga ganin ta ba akai-akai,"
"Ban son shashanci, da ɗin akai-akai kike ganin ta? Ina makaranta take yi da a can wani waje, daga baya ta koma wajen Jidda, to yanzun ma in ta koma gidan ta ba wani abu bane sabo in kin so ganin ta zaki je can,"
"Taso kin ji ta gidan Ummaah, daina kuka, ke dai ki riqe biyayyar aure, bana jin ki ta kowanne fanni,saboda na san baki da dama wajen iya girki, kwalliya, iya tsara kalamai masu daɗi, shagwava kuwa har ta saidawa kina bayarwa, ga shi wajen qamshi a gaskiya ke din abar yabawa ce mutum baya gajiya da shaqar qamshin jikin ki, kina da tattali baki da almubazzaranci, dai-dai misali kina da tsoron Allah da ibada, Sapnah ko ta wanne bangare za a lissafa Kyakkyawan hali kin mallaka, to me ne ne abin kuka? Kuka ya kama wadda bata da dik waɗannan abubuwan da na lissafa amma ba ke ba, share hawayen ki, zuwa qarfe biyar za a zo a kai ki d'akin ki kinji? Dan Allah kar ki bani kunya, kar ki kunyata zuri'ar mu, Allah ya yi maki albarka, ya baku zuri'a d'ayyiba saliha mumina, Allah ka saɓa halayen su, in yayi fushi ke ki sauka,in kinyi fushi shi ya sauka, Allah ya kare ku daga sharrin zamani da rud'in duniya, Allah ya kare ku daga sharrin shaid'an kin ji? Taso maza kije wajen qawayen ki, dan ke suka zo ba dan kowa ba, ba daɗi ki bar su su kaɗai ki dawo nan ki tare"
Share hawayen ta tayi suka jera da Umman nasu tana riqe a jikin Umman suka fita, wasu yan uwan su suna ta tsokanar ta akan shagwab'ar ta tayi yawa ko Safiyyah dake qarama bata shagwab'a sai ita, sake lafewa tayi jikin Ummaan nasu, tare da boye kan ta.
Daf za su shiga d'akin su suka ji qawayen su na ta hira, wata Ameerah na magana,
"Dik irin kurin Sapnah ace bikin ta ko dinner babu, ba wanai casu ba party, a gaskiya wannan yawa ne, ba aji"
Safiyyah ce ta bude qofar cikin fushi zata yi magana Sapnah ta hana ta, nan da nan kuwa ta kafe ta da ido, ranta ya ɓaci, ta danne ɓacin ranta,
"Kar ki ce komai Safiyyah, dik kuri na ban taɓa yi wa kowa qarya ba, na godewa Allah ina da surutu na sani amma ban taɓa cewa kowa komai akan aure bama balle nai qaryar za a cashe a bikina, gobe ki zo hall.......... ki ga me za ai inshaa Allahu, ina gayyatar kowa a cikin ku dan ganin me zai wakana goben,"
Nan da nan kuwa qawayen su sukai ma Ameerah caaa, har wadan da da ace bata zo ba suna da niyyar topa albarkacin bakin su, amma ganin an kama Ameerah ya sa sukai lif suka wayance.
Zama Sapnah tayi ta takure, tana jin su bata tanka ba, Safiyyah dataji daɗin amsar da Sapnah ta bayar ta ware sai hira da qawayen su take yi.
Umar ke ta kiran ta amma taqi d'agawa, dan sai take jin wani haushin shi dan zai raba ta da iyayen ta da kowa nata, sai take ganin hakan a matsayin son kai.
Message ya tura mata ta whatsapp, da kwalliyar da yayi, lokacin daurin aure, murmushi ne ya k'wace mata, dan kuwa ya tafi da numfashin ta, Itama tura masa nata tayi, ya maido mata da qatuwar heart,
~kiyi magana mana babes, ki faɗan yanda kike ji a yanzu, na matsu lokacin kawo ki gare ni yayi, na matsu na nuna maki tsantsar qaunar dake danqare a ruhi na, ina son ki Mrs Umar~
Zaro ido tayi waje fall hawaye, lallai ma Umar dinnan mugu ne, wato ya matsu akai ta ya gwada mata muguntar daya tanadar mata dai, banza tayi da message ɗin ta ci gaba da share hawayen ta, qirjin ta na bugawa da qarfi a dik second ɗin dake qarato da kaita d'akin mijin ta.
Kiran sallar la'asar ne ya tada su, wasu kuma suka zauna saboda basu yin sallah, wasu basu tashi ba saboda kar su goge kwalliya, wasu kuma da alwalar su, Aunty hauwaa ce tayi sallama ta shiga d'akin, Sapnah na ganin ta ta kwab'e baki irin na shagwab'ar nan ta miqa mata hannayen ta, kamar wadda za a ɗauka, aunty hauwaa da sauri ta isa gare ta ta fara lallashin ta.
"Taso muje kiyi sallah,"
D'akin Abban su suka shiga, ruwane zundum mai qamshi sosai da lalle aka cika kwamin wanka da shi, (lallen jiqawa ake a tace sai a zuba a ruwan wanka ko bayan anyi wanka sai a wanke jiki da zallan ruwan lallen saboda fata tai santsi da haske).
Kayan ta aunty Hauwaa ta fara taya ta cirewa bayan ta mata bayani tayi wanka kafin tayi alwala, tayi sallah su shirya ta ita da Umaimah.
Bata musa ba dan ko ta musa ba kyale ta zasu yi ba, taji daɗin ruwan d'umin kuwa sosai, ya dauke mata gajiyar da tayi sai da ta jiqu da ruwan lallen nan qamshin turarukan suka ratsa ta, sannan Aunty Hauwa ta d'akko irin garwashin nan na leda ta turara ta da kayan qamshi,ta bata farin musk mai kyau ta shafa a HQ, ta shafa mata alimun a hammata kadan, bakin ta kuwa sai da tayi brush,wanke da mouth wash ta qara da fesa mouth freshner, sannan ta bata kaninfarin guda ɗaya ta tauna, tai ta yamutsa fuska kuwa wai da yaji, Aunty hauwaa bata kula ta ba ta ci gaba da gyara qanwar ta ta ko ta wanne kusurwa bata bar wani datti ko kafar wari a jikin ta ba, gashin ta kan shi sai da ya sha turaren wuta dana gashi, sannan ta gyara mata shi ta d'aure mata.
Wasu fitinannun kaya Aunty Hauwaa ta deb'o ta bawa Sapnah ta saka riga ne da wando, rigar qarama sosai ta manne da cikin ta, hannun bra gare ta, sai wando iya cinya, kalar baby pink, sai ta bata wani skirt dogo mai faɗi sosai har qasa yake ja, da wata riga mai shara-shara itama mai dogon hannu da mannewa a jiki tace tayi sallah sannan suyi kwalliya.
Bayan sunyi sallah dika Umaimah ta gama shayar da Ummee, ta je ta tsara mata kwalliya mai kyau,irin simple din nan,nan da nan kuwa ta qara yin kyau, ga turaruka masu kyau da tsada da suka feshe ta da su(inma baki da mai tsada amarya ko ɗan d'ure mai daɗin qamshi da sanyin qamshi asanya abinki, iya kud'in ka iya shagalin ka kar dai a yi tsami)
Laffaya kalar baby pink mai ratsin baqi da golden a jiki kamar kayan dake jikin ta suka naɗa mata, takalmanta da qaramar jakar hannun ta golden ta riqe, sai abun hannu kowanne hannu an sa masa awarwaro na zinare, da kudin sadakin ta da wanda Abban ta ya bayar Aunty Hauwaa ta siyo mata a d'azun, kukan murna taji na son ya zo mata, sai qoqarin maidawa take yi kar ta b'ata kwalliyar ta,
"Kika sake kika min kuka saii na make qeyar ki"
Dariya suka yi tayi dikan su sannan suka raka ta waje inda motocin kai amarya ke tsaye ana jiran ta, a wuce da ita gidan mijin ta abin son ta, dik yanda ta so ta riqe hawayen ta kasawa tayi, ganin qoqarin da take na kar tai kuka kadai sai da yasanya mutane kuka suma, Aunty Hauwaa har sai da Umaimh ta riqe ta saboda kuka take sosai na tausayawa qanwar ta, zata shiga sabuwar rayuwa,rayuwar da ta qunshi komai da komai a cikin ta, abinda ka zata da wanda ba ka zata ba shi zaka gani a ciki,abinda kake son gani da wanda baka son gani duk zaka tarar a cikin ta.
*Cassssssss ni dai a radu ina lab'e ko kowa ya kai amarya ya tafi ni gidan nika kwanci yau sai an ci kaza da ni😂*
[09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 44:
'Yan kai amarya dai jama'a a gidan suka sami ango shi ya yi masu iso zuwa cikin gidan, sai dariya kuwa ake yi masa ana qusqus,shi kuwa ko a jikin shi, ganin haka mutane suka yi ta fita suna komawa mota tinda sun ga gida kuma sun sanya albarka zaman me za su yi? Sai fatan alkhairi da suke yi wa Sapnah da Umar ɗin , Safiyyah sai kuka take da zata tafi, Sapnah ma tsabar kukan da ta sha kan ta sai sarawa yake yi bayan tafiyar kowa Umar ya shiga ya same ta tana ta tsiyayar da hawaye, jingina yayi da gefen gadon da take zaune, ya kafe ta da ido, cikin yanayi na tsokana ya furta,
"Ohhhh Allah na, daɗi na da aure yana sa dik wani mara kunya mai surutu yayi ladab,who could have thought wai Sapnah zatai laushi ta yi irin wannan kukan kamar wadda akai wa auren dole? Ah ah ah..... na manta fa, maybe auren dole aka yi mata bata so na wayyooo...abin tausayi ni Umar ..... gaskiya Umar in ka barta ta kwana a gidan ka baka kyauta ba, ya kamata ka maida baiwar Allahn nan wajen Umman ta,...ko dai wajen Aunty Hauwaa zan maida ki?"
Tinda ya fara maganar tayi d'if dan ta samu damar jin me yake faɗa da kyau, jin tambayar da yayi mata ne ya sa ta kallon shi, suna haɗa ido kuwa ta zabga masa harara, idon nan kamar zai faɗi qasa, bakin kuwa kamar zai tsinke saboda murgud'a shi da take yi.
"Dawa kike?"
"Da kai nake"
Ta faɗa muryar ta sam bata wani fita sosai, amma yaji me tace sarai,
"Kayyaa... na zaci tsiwar taki ta hayaqa ashe iya gida ta tsaya ba a zo da ita gidan miji ba, da ki faɗa mana kice dani kike da qarfi ki ga ya zan maida ke yan zunnan"
Shiru tayi dan bata son dik wani abu da zai sa Umar ya kusance ta a yau, a matuqar tsorace take da shi.
Sai takalar ta yake yi ita ko ta yi masa banza, daga baya ya fara da cire mata mayafi, nan fa ta qanqame qammm, Umar yayi yayi ya cire ya kasa tabdi jam, ashe bayan surutu Sapnah gwanace wajen qarfi, saki yayi kar yaji kunya, yarinya sai shegen qarfi kamar wadda ake taya wa?
"Ina zuwa be a gud girl please yanzu zanje na dawo, na san me yasa kike b'ata rai, ba kiji qamshin mutuniyar taki ba ne ko ? wato kaza, bari na je na siyo na kawo kazar amarci, harda kud'in siyan baki zan had'o miki,"
B'are baki tayi ta fashe da kuka wai Umar me ya maida ita ne, sai wani tsokanar ta yake yi, tama gama gane ina ya dosa da kalaman shi, son auren take yake nufi ko kuma qin auren take yi kenan oho, sai yayi tufka ya warware.
Rungume ta yayi tsam a jikin shi yana shafa bayan ta, tin tana kukan har ta fara sauke ajiyar zuciya, qamshin junan su kawai suke shaqa, Umar ji yake gaba ɗaya sai a hankali, in bai samu yanda yake so ba akwai matsala, dole ya samu had'in kan Sapnah yau, tin da yayi auren farko ya fara kusantar Jameelaah bai taba nesa da matar shi ba sai da Jameelaan ta fara iya shegen ta, da sauri ya sake qanqame Sapnah, zuciyar shi na bugawa da qarfin gaske.
'Jameelaah, Ya Allah ka sa wannan ba halin su ɗaya ba, Ya Allah ka sa halin ta yanda yake a fili na b'oye yafi shi kyau,'
In Sapnah ta kasance irin Jameelaah zuciyar shi bugawa zata yi, a da ya zaci ba zai sake son wata sama da Jameelaah ba amma a yanzu ji yake ba kamar Sapnah a zuciyar shi dik duniya, d'aga ta yayi daga riqon da ya yi mata yace,
"Tashi kiyi alwala muyi sallah dan gode ma ubangijin da ya mallaka mana juna mu, mu roqe shi daya yi mana albarka, ya sa mutuwa ce zata rabamu"
Babu musu ta miqe cikin dishewar murya ta ce masa,
"Ina da alwala"
"Anyaaa kuwa Sapnah? Fadi gaskiya anya bata karye ba?"
Dukan wasa ta kai masa a qirjin shi, ya riqe hannun ta a wajen yana shafawa da hannun ta,
"Ouchhh,hannun ki na da zafi fa, kar ki karyan haqarqari fa, bari naje nai alwala ki jira ni"
Zama tayi tana murmushi haka Umar yake dama, yes ta san yana da magana kamar yanda take da magana, dik da Umaimah tace da ita yake sakewa yayi surutu mai tsaho haka, amma bata taɓa zaton ya zama mai shegen tsokana irin wannan ba.
Shimfid'a masu abin sallah tayi ta gyara laffayar ta ta rufe jikin ta sosai, ya jima sosai dan sai da yayi brush ya sake gyaggyarawa ya fita, sallah sukai raka'a biyu sannan ya yi masu addu'a, ya dafa kan ta ya karanto addu'ar da tazo a sunnah ango na yi wa amaryar shi, sannan ya ce,
"Taho muyi hira mu rage lokaci, dan yau daren namu zai yi tsaho"
Sanya ta yayi a tsakanin qafafun shi, ya fara da yi mata tambayoyin da suka shafi addini, tana amsa masa dai-dai gwargwado, a zaton shi a iya boko ta k'ware kawai, ashe ta bangaren islam ma ba laifi,sauraron ta yake tayi, tana zuba masa bayani akan tambayar da ya yi mata na yanda ake wankan tsarki, ta haɗe dikkan kala-kalan wanka da ake a islam tana yi masa bayani da banbancin su, Umar yayi kasaqeee da kunne yana sauraron ta.
"Da kyau, ba zan boye maki ba wasu abubuwan ma yanzu na san su, Allah ya yi miki albarka, zadakillahul ilm wa taufiq wa fatahallahu alaiki"
"Ameen ya zaujissalih"
"Iyyeee lallai ne yarinyar nan da gaske kina so na, soyayya ta ta rufe maki ido gaskiya ke da kike cika baki in kin zo ko kallo na baza ki yi ba jibe ki yanzu kwance a jikina, kin wani qanqame ni"
Da sauri ta d'aga shi ta koma can saman gado tana dariya, tare da rufe fuskar ta,
Tashi yayi ya je Allah ya bashi sa'a ya k'wance laffayarta ta sama, adon da tayi ne ya bayyana, tare da wani irin qamshi mai sanyi ya bugi hancin shi qoqarin Karb'a take yi, ya kai hannun shi wuyan ta wani iri ta ji a jikin ta, sai da ta rintse ido hannu ya sa ya cire band din da aka d'aure mata gashi da shi, nan da nan gashin ta mai madaidaicin tsaho ya bazu a kafad'ar ta, d'aga kai tayi ta kalle shi, bata taba ganin shi a wannan yanayin ba, zama yayi daf da ita, yana qare mata kallo, cikin bushewar lips dan tsoro ta zaro harshe ta tsotsi lips din ta, Umar ji yayi kamar da gayya tayi hakan, bai bata lokaci ba wajen kai nashi bakin zuwa nata.....
Yana cikin jagwalgwala mata kwalliyar ta da Umaimah ta bata lokaci wajen tsarawa, aka kira sallar magrib, hamdala tayi a cikin ran ta, dan kuwa ta gama zata ta shiga hannu kenan.
Bata tashi sanin me Umar ya mata ba sai da ya daga ta zai je masjid taga daga ita sai dan qaramin wandon rigar dake jikin ta, gashin ta dik ya yamutse saboda saka hannun shi daya dinga yi, jikin ta tini ya ɗauki rawa ta ja mayafin ta ta ruje jikin da shi, Umar dariya yayi ta qasan maqoshin shi, dan magana ba zata samu ba a wannan yanayin da yake ciki.
Sai da ta tabbata ya tafi sannan ta sake watsa ruwa ta sanya turarukan wanka da ta gani a toilet ɗin, tasan aikin aunty Hauwa da Umaimah ne, murmushi tayi ta masu addu'a a