Showing 54001 words to 57000 words out of 118783 words

Chapter 19 - MAZAUNA GIDA COMPLETE By HAERMEEBRAEH.txt

26 Oct 2025

641

ce,

"Ni dai gaskiya ka bar tsokana ta bana so ba wani ciki da nake da shi ni, likitocin nan shegiyar qarya gare su, Jameelaaah nan haka rannan tace min wai ina abu kamar me ciki, ko kuma dai itama har ta zama likitan da gaske kamar yanda tace min, dama haka ake yi daga fara boko sai mutum ya zama likita?"

Dariya Sadeeq yayi sosai, sannan ya juya da ita suna fuskantar junan su ya ce,

"Likita bincikawa yayi ya tabbatar da samuwar cikin naki Jameelaa kuwa kinga tana da ciki itama, in taga wadda sukai anko kuwa kin ga ai dole ta gane ba wai dan ita ɗin ta zama likita bane, zama likita ba abu bane mai sauqi ba dan ina nufin ba zata iya zama likitan ba ko da anan gaba ne kin fahimta?"

Kad'a kai tayi,sannan ta saka kan ta a qirjin shi ta ce,

"Ni kunya ma nake ji, yanzu su Lantai sai kawai su ji ina da ciki?"

"Ke ce ai baki sani ba, wancan maganin da ta aiko kina sha tace na shawara ne, ai maganin masu ciki ne yana qara lfy,"

"Wayyoo Allah na na shiga uku na, da gaske kake yi Masoyi? Kenan likitan yayi gaskiya daya ce cikina wata uku yanzu? Tinda dai tin kwanaki da nai rashin lafiyar nan da tazo ta ganni take kawon maganin nan ina sha,"

Sadeeq dariya ya dinga yi saboda shi a duniya yarintar Mamalon nashi na tafiya da shi, haka ya dinga kwasar ta yana shan dariyar wautar ta.

**********************



Gidan dake manne da na su Ishaaq ya sha gyara iri daya ne sak dana Ishaaq, nan Haroon zai zauna da Umaimah, Ishaaq bai taɓa nuna ma Haroon cikin gidan ba, dan kuwa Haroon bai ma san mallakin su bane, tin da suka dawo Unguwar yau shekara sama da goma bai taɓa ganin wani ya shiga gidan ba, shi kuwa Ishaaq bai taɓa gangancin barin Haroon ya gan shi ya shiga gidan ba,dan baya son mallaka ma matashi mara aure gida ba tare da iyali ba, tinda aka fara auren su Haroon ke son a nuna masa inda zai zauna da iyalin shi amma yana jin nauyin ya tambayi yayan nashi, daya tambayi Hauwaa sai tace itama bata sani ba tana dariya kawai, sai tace masa ya jira yayan shi zai nun masa in lokaci yayi.

Sai gyara gidan ake yi ana sabunta abubuwa Haroon ya zaci maqocin nasu yana son dawowa ne shi yasa ake gyare-gyare,dake ana hidimar bikin shi ma sai bai wani damu da sanin abinda masu gidan ke ciki ba, hankalin shi na kan bikin shi,ya tabbata dai tunda yayan nashi ya ce ya na da gidan da zai zauna da matar shi kar ya damu to fa akwai ɗin yayan sa bai taba bashi kunya ba, ya tsaya masa a kan abubuwa da dama na rayuwar shi.

Abokan shi na makaranta da Islamiyya sun hallara anyi walima, suma su umaimah ana can ana walima kafin a gama mata suje d'akko masa amaryar shi.

Wayar shi ce ta fara ruri, dubawa yayi yaga sunan yayan shi.

"Yayan ango kayi wuyar gani,"

"Gaskiya kam, ai dole tinda qanina yace shima auren nan yake so,  ka shigo gidan nan na maqotan mu ina ciki,"

Buɗe baki Haroon yayi ya na tunanin lallai yayan shi akwai cusa kai ba kwarjini, daga fara gyara gida har ya yi abota da masu gida har ya shige?

"Hello kana jina kuwa,"

"Ehhh... ehh ina jin ka, me kake yi a gidan mutane?"

"In ka shigo zaka gani,"

Murmushi Ishaq yayi kawai dan kuwa ya san zai sha mamakin ganin gidan, ta ciki komai iri ɗaya ne dana shi ta fannin tsarin gini, kuma shi ya zuba kayan d'aki da komai, dan islam bai ce dole dangin  amarya ne za suyi kayan d'aki ba,dan haka duk yanda iyayen Umaimah suka so su yi kayan d'aki sai Yah Ishaq ya hana, ya nemi alfarma wajen Dad akan a barshi ya yi komai saboda qanin nashi shi kaɗai yake da shi Allah ya hore masa dukiya dan haka hakan da zai yi ya san zai faranta ran ɗan uwan nashi, da kyar dai ya samu Dad ya amince ya yi komai.

Gate d'in Haroon ya ja ya bude ya shiga da kyar dan shi wannan irin gate mai jan wahalar buɗe wa yake bashi, gate ɗin gidan Yah Ishaq mai qofa biyu ne, baki ya bude dan mamaki a lokacin da ya yi arba da asalin cikin gidan,ganin gidan ya yi sak irin na Yah Ishaq a hankali yake shiga gidan, karatun qur'ani ke tashi a ciki,Ishaaq na bakin qofar shiga cikin gidan yana ma Haroon dariya, cikin buɗe hannayen shi dika da farin ciki ya ce wa Haroon,

"Supriseeee" 

Keys ɗin gidan ya kad'a ma Haroon da ya isa baki sake ya na kallon ikon Allah,cikin dariya Ishaq ya ce masa,

"Riqe nan ango ga gidan Amarya nan, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka,"

"Dama kai ne ka kunna karatu jiya da dare nake zaton ko masu gidan ne suka dawo?"

Dariya Ishaaq yayi ya damqa masa keys ya fice ya bar shi cikin ta'ajibi, ba inda haroon bai leqa ba a gidan tsabar daɗi da murna bai san hawaye na bin kuncin shi ba sai da yaji gishirin su a bakin shi, zama yayi a kujera riqe da remote yana kallon makka tare da sauraran qur'anin dake fita daga bakin Shaik alfasee, kuka sosai ya saki, Yayan shi ya zama uwa ya zama uba a gare shi, ba shi da wanda ya fishi a rayuwar shi, Allah bai ɗauke iyayen su ba sai da ya masa arziqin ɗan uwa mai riqo da zumunci fiye da abin duniya.

"Ya Allah ka farantawa ɗan uwana, ka qara masa arziqi mara yankewa, ya Allah ka bashi zuri'a mumina saliha,"

"Ameen 'yar budurwa me kuka, shin ko kaine amaryar ne banda labari? Sai ka tashi dan kuwa ga shi can an tafi d'akko amarya, na leqo na ga ko akwai abinda za a sake gyarawa kawai na gan ka zaune ka na kuka,"

In ji cewar Hauwaa da ta shiga a daidai wannan lokacin da Haroon ke kuka da addu'a, kallon ta ya yi ya na share hawayen shi ya ce,

"Yanzu dama har da ke aka yi min rufa-rufa dama wannan gidan namu ne? kullum nake cewa maqotan nan namu ba zasu shiga gidan ba sai aljanu sun gama samun muhalli, rana tsaka a d'aga su azo ana fama da matsalolin jinnu ashe namu ne,"

"Naka ne dai, kai ne mallakin gidan ai,tin kafin muyi aure ya siye filin dika biyun, sai da ya tabbata ya gama gin muka baro na haya muka dawo wancan aka kulle wannan yanzu da lokacin shiga yayi ba gashi za a shiga ba? Komai lokaci ne dashi ai dama a rayuwar nan, yanzu ka tashi na san ba wani jimawa za ai ba amarya zata iso, qannena biyu Safna da Safiyya ma sun zo za aje dasu d'akko ta,"

"Masha Allah na tafi nima na shirya dan tarbar amarya ta,"

"Ina zaka je? Kayan ka na can d'akin ai, ko baka kula zubin ginin mu ɗaya bane, Yayan ka ya tattaro maka komai ɗazu ai,"

"A gaishe da yaya wato ya ma sallame ni, ni ban taɓa ganin ango irina ba ana ta hidimta min ba tare da na sani ba,"

Hauwaa duba ko ina tai taga tsaf yake ba abinda zata gyara, dan haka ta fita tana ta godewa Allah, in zuciyar bawa babu tunanin sabawa Allah a cikin ta sai bawa ya ji ta wasai,sai ka ji ka baka da abin boyewa daga duniya har lahira, sai kaji ka kamar wani leda dan rashin nauyi.

**********************


A can asibiti kuwa tinda Jameelaa taga an fiddo Baban ta qafa ta sha gyaran likita bokan turai, Baban ta ma bacci yake yi ta saka borin sai an kai ta gidan Mum an kai amarya da ita, dan kuwa ba zata bari a karbi kudin siyen baki ba ita ba.

Dik yanda Umar ya so nuna mata ba komai ba sai taje ba qi tayi, daga qarshe yace ma Bukar ya zauna zai kaita ya je gida ya d'akko Ramai, sai su dawo tare, shi ya kula da Baban yanzu kan su dawo..........


*Wacce addu'a zaku ma Jamee, akan kudin siyan bakin nan data sawa ido kamar bakin ta za a siya...kar ku manta fa bata je bikin ba amma zata je dan kud'in siyan baki?*
😂😂😂😂😂😂😂😂
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻   MAZAUNA GIDA  💅🏻













WRITTEN BY HAERMEEBRAERH










PAGE 25:








Ko da ta koma gidan ta direct parlour ta shiga ta zauna a kan kujerar da ke kallon duk mai shiga da fita, tagumi ta zabga ta na ta tunanin yanda zata tara kuɗi Itama ayi suna mai qayatarwa idan ta haihu, har Sadeeq ya shiga gidan bata sani ba, a gaban ta ya tsugunna tare da qare mata kallo cikin yanayin damuwa ya ga fuskar ta,to meye ke damun Fateen nashi ne ko dai watace ta b'ata mata rai? Cikin yanayi na kulawa ya ce,

"My Teemaa meke damun kine har na shigo baki kula da dawowa ta ba?"

A dan tsorace ta kalle shi sannan ta yi ajiyar zuciya, tura baki tayi gaba ta maida kan ta dayan bangaren bata kula shi ba,cikin damuwa kuwa Sadeeq ya ce,

"Subhanallahi me aka yi maki ne fateena? Ni dai in dai ni na b'ata maki rai ki yafe ni sannan ki sanar dani laifi na saboda na kiyaye gaba, ko kuma Baban Jameelaan ne wani abu ya same shi?"

"Ina fa ! Ba abinda ya same shi kuma ni ba wanda ya b'ata min rai kawai so nake tinda sallah ta gabato mutane na ga sun fara kawo ɗinkunan su, wannan ɗinkin da za ka yi na shekarar nan ka dage ka tara kuɗi sosai, sannan albashin ka na makarantar boko in an baka muna rage wani abu mai yawa a ciki, a samu babban asusu ko ka kai banki ka ajiye, kaii ni koma ya za ai kawai ka tara kuɗi mai yawa kafn na haihu, dan kuwa ina son inna haihu ayi suna mai ban mamaki, sunan da tinda ake aurar da yaran layin mu su haihu ba a taba irin shi ba,"

Baki sake yake kallon ta sanda take masa wannan bayanin me kama da wadda aljanu suka taɓa ko suka bawa shawara,tashi yayi daga durquson daya yi kamar wani me neman gafara, cikin qanqance ido ya ce wa Mamalo,

"Ke da wa kuka tattauna kuka yi wannan shawarar?"

Yanda ya yi magana cikin d'aure fuska itama haka ta mayar masa da amsa cikin daure tata fuskar ta ce,

"Ni ban yi shawara da kowa ba, wato ka maida ni mara wayon da sai nayi shawara da wani sannan zan faɗi abinda nake so a yi min da suna na?"

"Hummmmm Allah to ya hore mana abinda zamu yi sunan idan kin haihu lafiya,"

"Ameen Allah ai yana taimkon wanda ya taimaki kan shi ne"

Ta fada a sanda ta ke tashi dan shigewa d'akin su, a gaskiya ta gaji da zama Jameelaah na fin ta a komai na rayuwa, bayan layin su ɗaya kuma gidan su ɗaya, wannn karon ko bashi zataci sai taci itama an buga suna na ban mamaki.

Sadeeq yana zaune yana mamakin sauyawar Mamalo cikin qanqanin lokaci, qarshe mamakin sa ya kau da ya tuna cewa da dikkan alama Jameeelaa ta zigo masa ita ne dan ba haka matar shi take ba, ba tun yau ba  ya kula da yanda Jameelaah ke taka mahimmiyar rawar dake gurɓata tunanin Mamalon shi, dan dik abinda Mamalo tayi mara kyau in aka bincika sai an gano da sa hannun Jameelaah a ciki,in ko haka ne zuwan ta wajen Jameelaah ya zo qarshe,dan ba zai dinga gini ana rusa masa ba, dama ba wata cikakkiyar tarbiyya gare ta ba lallab'a wa yake yi ta dalilin soyayyar da take masa ne yasa take jin maganar sa, sai yake amfani da hakan yake bata tarbiyya mai kyau da inganci musamman yanzu da take ɗauke da gudan jinin shi,dan haka dole ya sa ido kar yazo yana tufka wata na warware wa.

Kitchen ya shiga ya dau abincin shi, dan ko arziqin a kai masa ma yau bai samu ba.

***********************






Yau aka sallami Malam Jameel mahaifin Jameelaa daga asbiti yaji sauqi sosai qafa tawarke sai abinda ba arasa ba, tin da safen dama Umar ya ɗauki Bukar suka fita basu dawo ba sai yamma,lokacin da aka sallame su ɗin kenan,bakin Bukar yaqi rufuwa da alama akwai abinda yake son faɗa amma ya kasa,Ramai da Jameelaah ko sun yi tambayar duniya ya qi magana har sun gaji sun kyale shi, Umar kuwa sai kallon shi yake yi yana kad'a masa kai, da dikkan alamu akwai wata a qasa amma za su barsu idan ta yi wari sun ji.

Sun gama kwashe komai nasu da suka yi kwanciyar asibitin da shi suka yi sallama da maqotan su da ke asibitin Ramai na gaba ita da Jameelah suna hira Umar da Malam Jameel na baya Bukar kuwa har ya isa gaban mota ya ajiye kayan su kawai yake jira su tafi, bayan sun shiga Umar ya tada mota suka kama tafiya,sai Malam Jameel yaga ba hanyar gidan su aka ɗauka ba,sai kallon wajen yake yi yana son ya tambaya, amma yasan surukin nashi bazai yi wani abu dan cutar da su ba da alama wani wajen za su biya kafin ya kai su gida, dan haka ya ja bakin shi yayi shiru,Hajiya Ramai kuwa ta gaza hakuri dan kuwa gaba ɗaya bata gane hanyar da aka dosa ba sam dan haka sai ta ce,

"Ni fa ban gane nan hanyar ba, ohhh ni Ramatu Kano kenan tinjimin bajimin gari, Kano ta dabo timbin giwa jalla babbar husa, wato wani wajen dik girman ka a Kano har ka mace baza ka san da shi ba, nan kuma inane muke tafiya?"

Bukar ne ya kalli Ramai dake ta zuba ya kwashe da dariya sannan ya ce mata,

"Gidan Yanka kan mutane zamu je Ramai,"

"A kul nakuma ji dan Uban ka, dika-dika shekara ta arba'in da 'yan kai, ban shirya ma mutuwa ba sai na mori alatun duniyar nan nima"

Cike da jin kunyar kalaman ta Malam Jameel ya yi tsaki ya kauda kai,Jameelah ce ta ce,

"Balle kuma ni dana fara jin daɗin rayuwa ta ba, wataqila dai akwai inda zai kai mu,"

"To gamu mun iso sai kowa ya fito,"

"Mun iso ina?"

"Gidan ku da zaku dawo da zama, in yaso Mama gobe sai kuje ku deb'o kayan ku da kuke da buqata a can tsohon gidan, za akawo mota ta kai ku ku kwaso, wanda baku so zaku iya kyautarwa, dan kuwa daidai gwargwado an saka abubuwan buqatar ku anan ɗin, nan gidan mallakin mahaifi na ne wanda ya mallaka min shi a jiya dana roqe shi, dik da ba wani girma ne da shi ba ina fatan zai ishe ku, nan daki biyu ne da parlour sai kitchen da madafin gargajiya,  dan Allah da son Annabi ba dan ni ba domin Allah Baba kar kace komai, kawai kamin addu'a ka sanya min albrka, shikenan ka biya ni kai uba ne a waje na baka buqatar yi min godiya sai dai addu'a da sanya albarka,"

Malam Jameel hawayen farin ciki ne ya ɓalle masa, Ramai kuwa zubewa tayi a qasan wajen ta hau zabga godiya, Umar har kunya yaji ta kama shi dan kuwa abun nata yayi yawa.

"Ku shiga ciki ina zuwa,"

Kafin ya gama rufe baki ta kai hannu ta amshe keys ɗin gidan a hannun Umar ɗin, Baban su Jameelaaah kuwa gaba ɗaya kunyar duniya ta gama baibaye shi akan abinda Ramai ke ta yi kamar dama tana jiran hakan ta same su.

Budewa sukai suka shiga wata uwar gud'a suka ji an rafka, Malam Jameel na ji ya san daga ina ta fito, kad'a kai yayi ya kalli Umar ya ce,

"Ummaru Allah ya saka maku da mafificin alkhairi kai da iyayen ka, gaskiya ba dan roqon da kayi min ba da ba zan amshi kyautar nan mai girma ba,akwai kunyar ka mai yawa a ido na na san halayen d'iyata da naka sun sha bam-bam ta ko ina, amma a haka ka hakura kake zaune da ita cikin so da qauna,Ummaru ba abinda zan ce maka sai dai nace Allah ya yi maka albarka,ya haɗa ka da alkhairi a rayuwar ka a dik inda yake, ya nesanta ka da sharri a dik inda yake, muna godiya kwarai da gaske, kuma ka sanar dani sanda ake samun mahaifin ka agari sai naje na miqa godiya ta, kyauta irin wannan ta wuci saqo"

"Baba ni ne da godiya ni da aka yi ma kyautar mutum, dik soyayya irin ta iyaye da yaran su kuka hakura kuka auramin Jameelaa ai komai nai ban biya ba,kuma bana jin zan iya biya ba,"

Wani irin nauyi kafadun Baban Jameelaa suka yi sai yaji matsananciyar kunyar Umar ta kama shi, sun aura masa yarinya wadda ba kintsattsiya ba amma shi godiya ma yake musu, share k'wallar data gangaro masayayi yace,

"To bismillah muje ciki,"

"Ai Baba da ka turo ta kawai mun wuce gida kaga magrib tayi,bai kamata muna yawo da magrib ba musamman dake tayi nauyin nan,"

Sosa kai yayi daya kula dame ya faɗa nan take ya juyar da kan shi yana murmushin jin kunya, Baban ma murmushi yayi sannan ya shige gidan dan kiran gimbiyar.

Sai santin wajen suke yi tinda yau sune har da parlour nasu na kansu mai dauke da kujeru, ga carpet blue dark irin na gidan Jameelah kujerun kuma light blue, labulayen ma kalar dark blue kamar carpet ɗin sai qaramar TV ta bango dakin su Baban an saka gado da katifa da ledar daki, sai kitchen ɗin da aka saka risho da kananzir a cikk sai indomie k'wali ɗaya da kayan shayi, da sabbin tukwane a kwali shikenan, d'aki d'ayan kuma katifa ce babba sai leda, murna suka dinga yi kamar wanda aka ma albishir da gidan gwamna,ko da Baban Jameelah ya sanar da ita ta shirya mijin ta na waje yana jiran ta su wuce sai ta hau turje-turje ta na fad'in,

"Haba Baba ka bari ayi isha'i mana,"

"Nace ki wuce yana jiran ki ko? Me zaki yi mana in kin zauna ɗin?"

Cike da zumburar baki ta shuri takalman ta tafice, Ramai na ta sa mata albrka.

A mota ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login