Showing 108001 words to 111000 words out of 118783 words
dik abinnan da ake yi tinda ta sha lullubi ta zauna aka ci abinci da ita ta koma ta zauna a d'akin dake hall ɗin bata sake fita ba saboda zazzaɓi take ji sosai, kanta take ta murzawa a hankali saboda a tunanin ta hakan zai rage mata zafin ciwon da take ji,Umaimah ce ta shiga ganin halin da Sapnah take ciki ne ya sanya ta cewa,
"Lafiya kike kuwa Adda Sapnah?"
"Dan Allah ni kar ki wani kira ni wata Adda na yafe maki ki kira ni da Sapnah ta habaa,ni kaina ne yake ciwo kuma cinyoyina da nan wajen zafi suke yi min"
Murmushi Umaimah tayi lallai Yah Umar ba hakuri jiya-jiya daga kai masa mata har ya gama komai kamar wani wanda yake jira? Ai ya dan d'aga qafa a gama walimar ma mana a basu waje.
"Sannu bari na duba jaka ta na ga ko akwai maganin ciwon kai, bana rasawa dana Ulcer, sai ki sha magani, sannan na haɗa maki ruwan zafi ki zauna inshaa Allahu zaki ji sauqi sosai"
Haka kuwa aka yi sanda sika gama mutane dik an tattafi,sauran 'yan uwa na jiki sosai a hall ɗin.
Material ne a jikin ta mai laushi mai kyau an yi masa ɗinkin riga da skirt na zamani, ya yi mata kyau sosai, Umaimah sai yaba mata take yi, suna cikin hira Haroon ya iso tafiya dasu Aunty Hauwaa, tayi iya qoqarin ta na ganin ta danne hawayen ta amma inaa,aunty hauwaa sai lallashin ta take yi, daga baya ta hakura suka wuce, ko da Umar ya maida ita gida itama abun ya qayatar da ita dan kuwa gidan ya sha gyara sai qamshi ke tashi, bayan Umar ya fita Sapnah ko ina sai da taleqa taga yanda iyayen ta suka kashe mata kudi, tana tsaka da yi masu fatan alkhairi wayar ta ta ɗauki ringing takiran Umman su ta gani amsawa ta yi suka yi ta waya, sapnah kuwa sai wani shagwab'a take yi ,Safiyya ce ta amshe wayar tace,
"Ohhhh da alama mijin ki ya fita shi yasa kika tina da mu ko? Jiya tinda kika tafi ko flashing ba a yi mana ba ai se yanzu da muka kira zaki wani ishi mutane da narke murya"
Umman su ce ta ɗan daki kafad'ar ta, tayi dariya,Sapnah kam lumshe ido tayi sanda ta tina abubuwan da suka faru daga jiyan zuwa yau a ckin qanqanin lokaci,
"Ba zaki gane ba, ki samu kizo kiga abin alkhairin da na samu jiya, yaushe zaki zo?"
Kafin Safiyya tayi deciding amsar da zata bata har ta kashe wayar, sakamakon wani abu da taji ya ratsa jikin ta, ba komai bane face hannayen Umar, lumshe idanun ta tayi dan bata san sanda ya shiga gidan ba,sai kawai ta jinginar da kanta a qirjin shi,ya sa hannu biyu ya zagaye ta, yana sunsunar wuyan ta, dake fidda qamshi mai sanyi da daɗi,
"Barka da dawowa Zaujissalih,"
"Barkan ki da gida mar'atussalihah, sorry na bar ki ke ɗaya da kewa ta ko?"
"Ba komai yanzu ma waya muka gama da Safiyya da Ummana"
"Umman ki ko Ummn mu?"
Juyawa tayi tana kallon shi, sai taga ashe yafi kyau in ana kusa da shi daf da daf haka,
"Ya da kallo ko kin qyasa ne?"
Kwacewa tayi ta hau inda-indan daukan wani abun, ba komai a wajen da zata ɗauka, d'aki tawuce da sauri-sauri tana dariya, yaushe ta zamame kunya haka ne? Iya sanin ta bata d'agawa kowa qafa, kuma magana ba a biyan ta bashi sai ta maida.
"Kinyi dai-dai da kika shigo inda nake son kawo ki, kaiii yarinyar nan gaskiya na yi sa'a, na gama mallake ta"
Pillo ta wurga masa ya kama, ya isa gaban ta ya zauna a qasa, ya ɗora kan shi a cinyar ta, tsintar kanta tayi da shafa kan shi a hankali,a shagwab'e Umar yace mata,
"Wanka nake so,"
"OK bari na haɗa maka ruwa,"
"Ah ah ni kimin wanka,"
Buɗe baki tayi tana qoqarin magana ta ma rasa me zata ce masa wannan wanne irin sabon salo ne kuma? kawai sai ta ture kan shi ta wuce wajen haɗa masa ruwan, Umar da gaske yake dan haka ya cire kayan shi, yayi shirin wanka, tana qoqarin fita ta gama haɗa masa ruwan ya tare bakin qofar kallon ta yake da wani irin kallo ita kuma tana kad'a masa kai alamar kar ya yi mata abinda yake shirin yi.
"Ah ah please Zauj kar ka min haka ni nayi wanka ɗazu kuma banda lafiya, jikina ciwo yake min dan Allah kar ka sa na jiqe kayi hakuri, ba zan iya wanka da babban namiji kamar ka ba,"
"Ouchhhh, nine babban namijin? Habaa na zaci a irin surutan ki da wayewar ki kin san ana ma miji wanka, anyways in baki sani ba zan koya maki yanda ake ma miji wanka, qarin ilimi ne, ba sai kin biya ni da komai ba, in kin matsa sai kin biya kin biya anjima, yanzu wanka kawai zaki taya ni, in ma bazaki taya ni ba ki jira ni tsoro nake ji,"
Ya langwab'e kai ya yi ya turo baki irin na shagwab'ar nan, dariya ya bata sosai, tana dariya taji anyi sama da ita, sai cikin kwamin wanka, da kayan jikin ta da komai ya sata a ciki,tana jin ta cikin ruwa ta kuwa bare baki tin qarfin ta ta fara kuka, shima shiga yayi, ya rungume ta, tana ta dukan qirjin shi, harda su yaqushi, sai qara yake amma yaqi sakin ta, daga qarshe ya fara cire mata kayan dake jikin ta, suka fara wanka, ban dai san ya akai ba sai ganin Sapnah nayi ana kyalkyala dariya.
Kafin sati ɗaya sun zama abu guda,Sapnah ta aje kunya ta fara qoqarin maida mijin ta nata, kafin sanda zai zama nasu, dan bata taɓa sa ma ran ta mijin da zata aura zai zama nata ita ɗaya ba, tinda Allah bai halicci maza dan mace ɗaya ba.
Shaquwar su har abun mamaki,kowa ya gan su zai iya rantsuwa sun yi shekaru da aure, saboda shaquwa.
************************
Sana'ar dambun naman kaji ta kan kama, dan kuwa mutanen unguwar da ma wasu unguwanni suna zuwa siya har da masu sari, abun yafi qarfin Ramai ita ɗaya, sai suka buɗe shagon qofar gidan, guda biyu suna sana'ar a ciki, Jameelaah ta ɗauki ma'aikata biyu suke kula da wajen, dik da ta san Umar yayi aure, bata d'aga wa kan ta hankali ba, ko ta sakawa kan ta damuwa, dan a yanzu ko ita kan ta kunyar sake haɗa ido da Umar take yi, ko zata mutu dan son shi ta haramtawa kan ta Umar, Allah ya raya masu d'iyar su, ko da yaushe ne in ta girma zata neme ta, amma dik da haka in kewar su ta kama ta tana shiga d'akin ta tayi kuka ta godewa Allah.
Baban ta da Ramai suna matuqar tausaya mata a yanzun, amma sai ta nuna masu she is Ok, zata iya rayuwa ba Umar, kome ya faru ita ta jawa kan ta, ko batai abinda tayi ba in Allah ya nufa bazata koma gidan umar ba bayan sun rabu ba yanda zata yi, Allah ya zab'a mata abinda yafi dacewa a rayuwar ta.
*Bayan shekara Uku*
Humairah ba inda bata takawa, ga dan neman surutu a wajen yarinyar,a yanzu ta koma wajen Sapnah da zama Ammi ma take kiran ta da shi, umar kuwa Abbu, in ta fara surutu kamar kanyar da bata da daɗi, Umar yakan ce in batai ba ai sai an tambayi wace maman ta, tinda Sapanh ma haka take da surutun.
Har yanzu Sapnah ba ta samu rabo ba, ta damu sosai da hakan kuwa, Umar kuwa a koda yaushe yana kwantar mata da hankali, suna samun taimakon likitocin da suke zuwa wajen su neman magani, Mum tace su kwantar da hankalin su komai lokaci ne.
Humairah ce cikin kwalliyar atampa sun yi anko ita da Sapnah, sun yi kyau sosai Umar ya fito yana gyara hular dake kan shi sai qamshi suke bugawa dikan su yawo zai kai su su sha ice cream daga nan yaje da su gidan Zoo, Humairah taga Lion, ita a kayan namun dawa ta riqe shi sosai saboda kallon Cartoon ɗin Simba.
Sun fita da la'asar sakaliya, sai goshin magrib suka kama hanyar gida, a titi an tsaida su suna mota Sapnah taga dambun nama a roba sai ta kira mai saidawar wani da ya fita kusa da mai dambun naman ya karɓe ya siye, aiko ta dinga masifa can tayi shiru kamar zata yi kuka dan haushi, ganin haka Umar ya kira mai saidawar yaji a ina ake yi suje ya sai mata, kwatance ya masa na inda yake sari, jin kwatancen yayi sak na gidan su Jameelaah, nan da nan ya b'ata rai.
Sapnah da Humairah suna ta murna za a je a sai masu dambun nama, suka ji yace,
"Ba inda zamu je, gida zamu wuce in munje kinyi ki ci,"
Bata fuska tayi ta fara kukan shagwab'a ita da Humairah, wata uwar tsawa ya daka masu, nan da nan kuwa Humairah ta b'are baki da kukan gaske, dik yanda Sapnah ta so tayi shiru qi tayi, shi kuwa bai kula su ba har suka isa gida, da kyar ta d'aga ta ta kai ta ciki, sai kurma ihu take tana kiran dambun nama zata ci, a hasale Umar ya shiga d'akin ya wanke ta da mari sai da yatsun shi suka fita a saman fuskar yarinyar.
Cikn fushi mai tsanani Sapnah ta juyo da shi, tare da miqa mashi nata kuncin akan ya mare ta itama,
"Nace ka mare ni nima, tinda ni na fara cewa ina so, akan me baka bamu abinda muke so ba zaka dinga fushi bamu san dalilin fushin ka ba kuma, ka sanar damu mana cikin lumana, kace inna dawo zan yi ba shikenan ba me tayi maka?"
"Ba zaku ci dambun naman ba, na san daga inda ya fito, kuma ban da ra'ayin sake huld'a da su har abada"
Shiruuu Sapnah tayi dan gano ainahin me ya sanya shi fushi, zuciyar ta ke kai kawo akan yi masa magana akan fushin da yake da Jameelaa, wata zuciyar tana kar ki so ma, ai ba ke kk haɗa su ba da, sannan ba ke kika raba su ba..............
*Shin ya kamata Sapnah ta shiga wannan batu kuwa?*
[09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏼 *MAZAUNA GIDA* 💅🏼
*WRITTEN BY HAERMEEBRAERH*
Page 48:
Bayan sun idar da sallah ne taga ya d'akko irin qur'anin nan me falle falle ya na karatu irin na zaure, sai da ya gama yayi azkar, sannan yaran suka dinga zuwa bakin qofar d'akin ta suna gaida shi, a ciki-ciki yake amsawa,matan ma haka suka bi suka gaida shi suka koma tsakar gida ya fita ya kama qugu Yana muzurai yace,
"Kuna ina?"
Cikin hanzari kowa ya fito suka tsugunna, sai da ya gama qare masu kallo sannan yace,
"Wato dan rashin mutunci ni d'ayane a d'akin ko? Ita ba zaku gaida itaba? Ko haka na koya maku qin gaida na gaba da ku?ku kuma saboda ɗan banzan kishi ne ya hana ku tambayar ya Amarya ta ta kwana Ko kuma wanne iskanci?"
Uwar gidan ce da ake kira da Baba Abu tace,
"Ba fa zaka zo ka samu a gaba da yaran ka damu ka mana kud'in goro ba ehe,amarya ka nuna mana kalar ta balle ma mu san ya ta kwana? Yaran ka dai da basu gaida ta ba ka sa su fara amma banda mu can mata"
"Abu ki kiyayen in ina magana ke ce mace ta farko da zata fara mayarmin ko? Ranki zai baci,"
"Bacin rai na nawa kuma? Wanne kalar bacin ranka ne ban gani ba, shiru shiru ai ba a ce maka tsoro bane kawai gudun magana ne, in Mero na tsoron ka ni kam bana tsoron ka, munga jiya munga yau tare da kai, ka cud'eni na cud'e ka dan haka na daina raga maka"
"Kika cud'eni a gidan uban wa? In ba jiya ba ina na san ana cud'ar miji? Gaku nan ba abinda kuka iya sai baqar qazanta da shegen kishin tsiya, ku kuma me kuka tsaya saurara zaku wuce kuje makaranta ko sai na b'alla yaro,"
"Ka b'alla ka gyara,"
"Abu ki fa kiyaye ni,"
Gaban ta ya je ya daga hannu zai zabga mata mari, da sauri Jameelaah dake tsaye jikin labulen d'akinta ta fita ta riqe hannun shi,
"Dan Allah kar kayi haka tunda Annabi yake bai taɓa d'aga hannun shi akan matan shi ba da sunan duka,to kai me yasa zaka d'agawa matan ka hannu? Kamar ba da Annabin Rahama naga kana koyi ba? Habaa, kenan nima nan gaba dukana zaka dinga yi?"
Gaba daya qamewa yaran da matan suka yi, ji sukai Mero ta fashe da kuka, kowa kuma sai ya maida kallon shi kan ta,
"Allah sai ya saka mana, dama an shirya mana kora da hali ne kawai, in ba haka ba ina kai ina auro mace kamar wnnan? Dibe ta ka gani irin wannan sai a talabijin muke ganin irin ta, amma zaka had'amu kishi da ita, nidai ba zan taɓa yafe maka ba, ke Zara'u muje ki dama koko kowa ya sha ya wuce makaranta, na sake faɗa ban yafe ba,"
Cike da kuka da shan majina ta bar wajen, yaran da suka mallaki hankalin kan su dariya suka dinga yi har da kama ciki, tabbas Jameelaah ta firgita su da kyau da haɗuwar ta, amma Abu ko gezau bata nuna tsoratar ta a fili ba dan ta san Jameelaah tun bata kai haka ba,girma kawai da kyau ta qara akan sanin da ta yi mata,sannan kuma taurin zuciya gare ta, shi yasa ko faɗa sukai da Tsalha ko Mero sai dai su buga su barta, inda yake sata ta yi laushi ɗaya ne, wato dik sanda yace ta tafi gidan su yanzu zata nutsu.
Jameelaah bata kula su ba fatan ta ta saita lamarin gidan, dan kuwa tabbas sai yanzu ta tabbatar da qazantar dake gidan sune mu'assasin ta, qazantar su har abin kallo ne.
Jikin su fari fat kamar bai taba ganin mai ba, in ko ya taba wataqila tin na jarirantaka ne, ga kayan jikin su ba mai gane asalin wace kala ne? Ita dai Mero da ganin ta kyakkyawar mace ce, dan dik yaran ta da ita suke kama, kuma kyawawa ne, Abu ma ba laifi, black beauty ce, amma dik ba a gane kamannin su, datti da qazanta sun cinye kyan.
'Ina da qaton aiki a gabana ashe'
(Kun ji Jameelah ta koma 'yar agaji)
Shiru-shiru ba wadda ta kai masu abin karyawa a gidan, fita Tsalha yayi sai da ya jima ya dawo ɗauke da madara da milo sugar da lipton a aljihun babbar rigar shi, ya shiga madafi da kan shi ya kwaso ruwan zafi a flask ɗin Jameelah, ya wuce d'aki yana jin Abu na masifar an taɓa mata ruwa bata yafe ba, amma gudun kar ya b'atawa Jameelaah sai rai bai kula ta ba, a ran shi ya ayyana,
'Lallai matan nan wato sun samu dama ta yanzu, da wa ta isa ina magana tana mayarwa ko faɗan kishin su zasuyi sai bana nan, amma shine yau suke maida magana a gaba na harda furtan ba su yafe ba, lallai zan d'au mataki mai girma akan ku'
Har Jameelaah ta gama haɗa tea bai sani ba yana ta tunani,a hankali tace masa,
"Tinanin me kake yi haka? Haba Baban Hajjo kar ka na sawa ranka damuwa, in kana damuwa wani ciwon ya kama min kai ya zan yi da rai na?"
Sai ta fara hawayen gulma, nan kuwa dik hawayn takaicin rayuwar da take ciki ne, dama kuma kukan na kusa, ganin hawayen ta ne ya sa ya kid'ime ya rude, ya janye tea ɗin gefe ya fara lallashin ta yana shafa bayan ta, jin ta take kamar wata jaririya saboda yanda yake yi mata, shiru ta farayi a hankali sannan ta miqa masa tea again ta deb'o kayan gara ta aje masa da dambun naman da ta ga an saka a ciki nan kuwa ya washe baki yana murna ci ya farayi sai yaga ita bata ci, ya kalle ta sosai can kuma sai ya ci gaba da ci, dan shi akan abin da zai ci baya wasa, sai da ya qoshi yaga dai bata ci komai ba, sai a sannan ya kula ma ma shi kadai ta hadawa tea ɗin,cikin nuna kulawa yace mata,
"Wai kam Jameelaah me ya faru ne? Naga baki haɗa wa kan ki shayin ba,sannan bakici komai ba kuma, lafiya kike kuwa?"
"Lafiya nake sai tsoron wani abu ɗaya danqaren a zuciya ta,"
Cikin tsananin damuwa ya isa gaban ta ya jata jikin shi, ya dora kan ta a cinyar shi yana shafa bayan ta yace,
"Jameelaah me kike tsoro haka da zai hana ki cin abinci, ni da kika ganni nan bana wasa da abinci, dan haka bana son kema kina wasa da abinci, meke damun ki sanar dani inshaa Allahu zan yi maki maganin shi, indai bai fi qarfina ba,"
Kuka ta fara yi mara sauti,nan da nan Tsalha ya sake rikicewa yace,
"Subhanallahi, me kike jin tsoro haka tashi ki nuna min shi, inna kashewa ne a kashe yanzu nan"
D'aga ta yayi ya haura da ita saman gado ya na dube dube, hannun shi ta kama ta manna da qirjin ta tana ci gaba da zubda hawaye.
"Amarya ta dan Allah ki sanar dani abinda kike so,"
"Inna fada maka ma na san ba lallai kamin shi ba, shi yasa nake jin tsoro,"
"Ya Allahu ya rahamanu, dan Allah karki ce na sake ki ba zan iya ci gaba da rayuwa babu ke ba, daga jiya zuwa yau na san daɗin aure a rayuwa ta, in kika barni ina zan saka raina?"
Sai ga Tsalha na matsar kwalla, ganin haka yasa Jameelaah, kwantar da jikin ta a nashi, musamman qirjin ta da ta kula yana maita.
Ajiyar zuciya ya sauke mai qarfi,cikin shagwab'a tace,
"Ba zan taba cewa ka saken ba ni, ba kuma na fata mu rabu har abada, ni da kai mutuwa ce zata rabamu in Allah ya yarda, ina son ka Baban Hajjo, ko ba komai ka rufa ma rayuwa ta asiri da ka aureni ka killace ni a gidan ka,"
"To indai kina so na haka me zai sa kiji tsoron sanar dani abinda zai hana ki cin abinci ya sanya min ke kuka?"
"Dama....immm... damaa.. gamee daa..., immm ɗazu abinda na gani