Showing 39001 words to 42000 words out of 118783 words
take.
"Ke lafiya na gan ki kwance haka? Ince dai ba wata matsalar bace,"
Tana magana tana harar Umar kamar ta na zargin shi da ci mata zalin 'ya.
Da sauri kuwa ya buɗe baki dan kare kan shi, amma Jameelaa ta katse shi ta hanyar cewa,
"Wuce kaje ka qarasa abinda kake yi,"
"To"
Yace ya na dauk'ar da kai ƙasa,dan kuwa ya so ya kare kan shi wajen surukar ta shi,
"Ramai na faɗa maki kar ki dinga shiga lamarin mu, ina ruwan ki zaki na tuhumar shi kamar ya maki sata? Ni ba abinda ya yi min kaina ke ciwo, kuma Ramai yaushe yaushe muka dawo gidannan, amma kusan kullum sai kin zo,"
Juyawa ta yi tana murgud'a baki da fari da ido, ranta a mugun bace,
"Dan uban ki da ba na zuwan zaki samu maganin da zaki maida mijin naki haka? Ko uban ki ban taɓa nemawa maganin mallaka ba sai ke,saboda uban naki bai tara abinda zan mallake shin ba, ya ji da talaucin shi ma, kin samu ina kawo maki ne bari na koma da wanda na zo naga ɗan iskan da zai na kawo maki,"
Da sauri Jameelaa ta cafke hannun Ramai ta kwanta a jikin ta, tana dariya ta ce,
"Habaaa Ramai na, kin san idan bana jin daɗi dama haka nake masifa, dan Allah ki yi hakuri kawo na gani,"
"'Yar kwal uba kai, hanni zaki nunawa kin yi kud'in da ba zan zo gidan ki ba? Innai niyya ke kan ki sai na mallake ki naga ta tsiya,"
"Haba Ramaiinaaa bai kai na haka ba, muga wannan miqo min na fara amfani da shi, kin san shi da yawan ibada, sai abun ya damqe shi anjima kuma ki ji ya fara lalacewa,"
"Matsalar da malam (malamin dhibbu) yace kenan yana fama da ita akan wannan tattauran mijin naki, shi bai da aiki sai karya masa sihiri, ina kyautata zaton fa wannan biyayyar da yake maki ba wai naganin kaɗai ke aiki ba dan dai kawai yana son ki ne, amma ba dan sihirin mu ya kama shi da kyau ba,"
"Koh?"
"K'warai kuwa, yanzu dai kawon abinci na ci na ɗan sha jusi na tafi sannan ki ɗan haɗan kayan abinci, na gida ya kusan qarewa,"
"Ramaiii hooo,ba wani qarewa wannan uban abincin da kika kwasa shekaran jiya ne za a ce ya kusan qarewa? Ai na san zai kai ku sati ma aci a wadace,ke dai kawai ki ce sai kin sake diban wani,"
" 'Yannema mai kan kwando je ki deb'o kawai bar tone-tone"
"Yah Umarr ! Yah Umarr !"
"Na'am my love,"
"Dan Allah zuba mana abincin nan yunwaa nake ji,kaga ga Mamana ma tazo,"
"Na gama zubawa ma, dama naga kuna ta hira ne shi yasa ban yi magana ba,"
Da sauri ya tafi yaje ya kawo abincin a babban faranti da lemu da cups da dik wani abu da zasu buqata dai ya ajiye masu ya koma kitchen, a tsaye ya cinye nashi ya dau jaka dan komawa bakin aikin shi, kuɗi masu ɗan kauri ya miqawa Ramai, Jameelaa ta amshe ta raka shi, a hanyar dawowa ta rage wani ta soke, Ramai da tinda suka fita take leqen ta, ta kasa hango wajen saboda window irin na glass ɗin nan ne kuma rufe yake da labule jibga jibga ga kujera ta rufe ta dai-dai wajen ta kasa janyewa, ido ya sha hayaqin dafa wake da shinkafa ba wani gani take sosai ba, k'wafa ta yi ta ce,
'Zaki ci uban ki ne, ba dai ni ke kawo maganin ba, har aban abu ki wafce? Naga shegen da zai dinga maki wahala kina samu kina ci ke ɗaya,'
Jameelaa ce ta shigo ranta b'ace dan ma kar Ramai tai maganar abinda ya faru ɗazu, aiko batai maganar ba abinci suka ci sukai nak, sannan Jameelaa ta shiga kitchen dan debarwa Ramai kayan abinci, sai da ta loda mata sosai sannan ta kira ta dan ta ɗauka, ita kam tace ba zata iya d'ibar kaya ba a gajiye ta ke.
Ramai kuwa haka ta shiga dan tsabar kwad'ayi ta kwashe komai da aka d'iba domin ta, ta tsare mai napep ta shige sai gida.
Jameelaa bacci ta kwanta tayi, sai da ta farka ta yi sallah gaba daya wato ta haɗe Azahar da la'asar dika sannan ta yi wanka ta shiga maqotan ta ta samu garwashin wuta ta turare gidan da mix din turaren wuta da maganin mallaka da aka kawo mata,ba a jima ba kuwa Umar ya dawo.
Da ganin shi ka san a gajiye yake wanka ya shiga yayi sannan ya fito, kan shi yake ji yana juya masa, dan haka ya zauna ya dafe kan nashi, nauyi ya masa kamar an d6ora masa abu mai nauyi, tasbihi yake tayi ga Allah, yana istigifari, tare da hailala da hauqala, nan take ya ji ya fara jin sauqin jirin da yake gani.
Zama tayi kusa da shi tana ta nazarin yanayin shi.
"Yaushe ka dawo? Naga ma har kayi wanka,"
"Ban wani jima ba da dawowa ba na shigo na ji ki shiru,kawai sai na shiga na watsa ruwa na ɗan zauna na huta,"
Shagwab'a ta fara yi tare da d'alewa cinyar shi, ta zagaye hannayen ta a wuyan sa sannan ta manna qirjin ta dake rud'ar da shi a fuskar shi tare da kukan shagwaba,
"My love menene shin me ki ke so?"
"Ni gaskiya yau bana son ayi girkin dare a gidan nan,sha'awar naman rago nake irin gasasshen nan da ka ke siyo min da freshyo sai fruits,"
"To bari kuka dan dai wannan kawai? tashi ki sa kaya muje a siyo,"
Tsalle tayi ta qara faɗa masa gaba ɗaya a jikin shi kyakkyawar runguma ta samu a wajen shi, sai da suka dan taba soyayyar su sannan taje ta saka kaya suka fice, yawo ta sa yayi tayi da su tana shaqar iska, magrib ta wuce amma bata ji su koma gida ba daga nan su yi can, sai da ta sa Umar kashe kuɗi sosai,har yana tinanin anya za a samu kud'in su kai shi qarshen wata kafin wani albashin ma kuwa?
Bayan magrib liss suka koma gida, bata b'ata lokaci ba wajen baje kayan a nan parlour, ta fara cin na ci,tana ware na iyayen ta, da nasu da alwala ya zo ya tsaya a gaban ta yana tambayar tayi alwala ne ta kalle shi tare da harara
"Yanzu fa muka dawo, habaa ai ka bari ma na dan ci na qoshi tinda ka san yunwa nake ji,"
"Nayi sallah ta kenan tinda ba zaki zo muyi jam'i ki samu ladan bin liman nima na samu ba,"
"Yi taka sallar ni na haɗa da isha'i"
Kad'a kai yayi ya je ya tada sallar shi, cikin sujjadar qarshe yake roqon Allah daya sa jameelaa kar ta sauya daga kyakkyawa zuwa mummuna,dan ya fara ganin wasu halayen da sam bai taba sanin tana da su ba.
Da weekend ya so yaje ya gaida Mum amma sai yaji gaba ɗaya baya son shiga gidan nasu, ba wai iyayen nashi ne bai son gani ba ah ah gidan nasu ne kawai yake jin qiwar zuwa.
Suna zaune suna shan soyayyar su, dan Jameelaa ba abinda ta fi so irin ya zauna yana wasa da ita, tare da yi mata irin soyayyar da ta saba da ita tin asali.
Wayar shi ke ta ringing, amma bai gani ba saboda ta sa masa wayar a silent, tana ganin wayar na haske taqi yi masa magana, cikin dabara ta haye cinyoyin shi ta kwanta a jikin shi ta leqa wayar, sunan Mum ta gani a jiki, hannu ta sa zata sake tura wayar qasan kujera suka hada ido da shi, sai ta wayance ta d'akko ta miqa masa.
Karawa yayi a kunne bayan ya amsa, sallamar Mum ya amsa tare da gaida ita.
"Ok Mum inshaa Allah zan zo anjima, ko yanzu zasu zo?........ok to ga ni nan zuwa"
Kashe wayar yayi, da hanzari ya miqe yana murna,
"Kin san me? Maneman auren Umaimahn ki ce zasu zo, shine Mum ke kirana ya kamata naje ayi komai dani,"
Dan yatsina fuska tayi, sannan tace,
"Kuma zuwa za ka yi ɗin?"
Dan haɗe fuska yayi ya kalle ta da alamar ban gane ba? Wayancewa tayi ta fara kame-kame sannan tace,
"Nima gaskiya sai kaje da ni, dan kuwa ba za a yi maganar auren qawata kuma qanwata ba bana nan,"
D'aga ta ya yi sannan ya saki fuska ya ce,
"Muje maza mu shirya ana jiran mu,"
A tare sukai wanka suka shirya, cikin jallabiyya kalar blue wadda ta sha aiki ya saka wandon rigar, turaruka masu qamshi ya sanya, itama doguwar riga ce a jikin ta, dark blue, mai ratsin pink a jiki, ta yafa mayafin rigar tare da sanya takalmi mai tsini kalar pink da jakar shi suka fita zuwa gidan su Umar.
Koda suka isa an gama komai sun tadda kayan saka rana da Daddy da Mum tare da Umaimahn suna ta hirar bikin Umaimah, shigar su ce ta sa suka maida hankali kan su, Mum cike da jin nauyin su ta gyara zama.
Dad ne ya fara yi masu barka da zuwa, Umaimah ta tafi da sauri ta rungume Jameelaah ta ce,
"Gaskiya nayi kewar ki sosai, da alama ke kam hankalin ki kwance yake, ji har wata qiba ki kai sati biyu kawai da tafiya,"
Wank irin haushin Umaimah ne ya kama Jameelah cikin ranta take fad'in,
'Ji dalla yanda ta wani cukuikuye ni kamar ta samu flour tana curawa,mtsssww'
Yaqe ta yi mata suka samu waje suka zauna, suna gaida iyayen nasu.
Bayan gaishe gaishe ne Daddy ya yi masu bayanin sanya ranar auren Umaimah da aka yi watanni biyar masu zuwa da Haroon,Jameelah ce ta ce,
"Dama na san malamin nan na son ta, itama kuma tana son shi, amma dana tambayi yarinyar nan sai ta musa min,"
Rufe fuska Umaimah tayi ta tafi d'akin ta tana dariya, Jameelaa na nan a zaune taqi tashi, sab'anin da da take nuna jin kunyar Iyayen mijin bata son zama da su su dad'e a waje ɗaya,yanzu kuwa idon ta fess akan su, Allah Allah take ya tashi su wuce ta gaji da zama a gidan.
Sun kula da sauyawar ta ta amma basu ɗauke ta ta wata mummunan hanya ba, a zaton su shaquwa ce ta ke tasiri a tsakanin ma'auratan.
Message ta masa akan su wuce ta gaji kuma kanta na ciwo, sai ya mayar mata da ta ɗan jira kaɗan sai su tafi, aiko nan da nan ta b'ata rai, Umaimah na can d'akin ta tana jiran Jameelah ta je su ɗan yi hirar yaushe gamo amma ba ita ba alamar ta,shirun da taji yayi yawa ne ya sa ta leqa ta ce mata,
"Qawata muje ciki mana ki sha labari, naji ance anyi bikin mamalo ko?"
Wani kallo tai ma Umaimahn sheqeqe,sannan ta ce mata,
"Lallai Umaimah baki da kunya, ni kike ce wa qawar ki? Ko kin manta ni matar Yah Umar ce yanzu? Dole yanzu suna na ya sauya a bakin ki, sannan ni kaina ma ciwo yake yi so nake mu tafi gida,"
Kowa a wajen har Umar kallon ta yake cike da mamaki, me ya same ta ne haka? Jameelaa mai kunya da hankali tare da sanin ya kamata ita ke magana kamar wata babbar mata mara tarbiyya,
Umar ne zai yi magana, Mum ta kula da bacin ran shi, nan da nan ta tari numfashin shi ta ce,
"Subhanallahi ! ciwon kai kuma Jameelah? Ya kamata kam ki sha magani ki kwanta ki huta, Umar tashi maza ka kaita gida, ka kula da matar ka sosai,"
Bai musa ba kuwa ya amsa mata da toh, kafin ya miqe Jameelaa ta tashi ta saɓa jaka a kafad'a ta kai qofa? Ba magana ba komai balle ta yi wa surukan nata sallama.
Har suka isa gida ba wanda yayi magana, suna shiga ta fara cire kayan ta a parlour Umar yayi yayi dan ya ɗauke kai akan abinda take yi da gayya dan jan ra'ayinsa amma ya kasa jin idon shi yake yi kamar an manna a jikin ta, sai da ta gama cire komai tsaf na jikin ta sannan ta d'ebi kayan a hannu ta shige d'aki, kamar raqumi da akala haka ya bi bayan ta har ciki, bata ce masa ci kan ka ba ta sake fita dan shiga d'akin shi tayi wanka, dan nan ne kaɗai ke da band'aki a cikin d'akunan dika,manna ta yayi da jikin qofar bayan ya mayar ya rufe qofar, na so na ga me zai mata dan tana buqatar a zane ta ta dawo hayyacin ta haka na fita ina ta murna dan kuwa abinda tai ta cancanci a hukunta ta.
Na kai awa ɗaya a waje ina jiran na ji kukan Jameelaah abun mamaki sai kawai na ga sun fito riqe da junan su suna ta sheqa dariya, ta na dukan shi cikin sigar wasa cizon yatsa na na yi na bar gidan gaba ɗaya ba zan iya kallon abin duka ba sanda ba.
**********************
Haroon kuwa hankalin shi ya kwanta da aka bashi Umaimah, dan haka yanzu ya maida hankali kan karatun shi da kuma kasuwancin shi, sai chatting da waya da Umaimah da yake yi a koda yaushe dan sake kafa gwamnatin sa a wajen ta, kusan kullum suna tare da junan su a waya, hirar su rabi bata wuce akan qara mata junan su ilimin addini, rabi kuma ta soyayya.
Yah Ishaaq ne ya dawo daga kasuwa tare da Haroon, suna cin abincin dare Ishaaq ke sanar da su za shi india dan saro wasu kayan.
Hauwaa ce ta kalle shi cikin ɗauki tace,
"Dan Allah kaje dani, ina son india sosai,"
"Kin dai san me kike tare da shi a yanzu ko? Kina ɗauke da ciki na wata ɗaya zan ɗauke ki tafiya wata qasa? Ba inda zaki je gaskiya,"
Haroon bai ce komai ba yana ta kallon su, tayi magiyar tayi roqon amma shiru ya qi yarda daga qarshe tana hawaye ta bar wajen.
"Yah dan Allah ina son na maka wata magana a matsayina na qanin ka amma ina tsoro da tinanin ya zaka d'auki magana ta,dan Allah ka fahimci abinda zan sanar da kai, kar ka min mummunar fahimta, sannan ka gyara abinda zan maka magana akai, ba tare da ka bi diddigin ya akai na sani ba,"
"Haroon wannan bayani naka ya sa naji mutuwar jiki,me nake aikatawa mara kyau haka?"
"Yah a gaskiyar magana ina son shawartar ka ne dama akan matar ka, mace na da matuqar rauni, mace tana da son a tattala ta, tana son ta zama dik inda take mijin ta na nan, yana bata soyayya da kulawa tare da girmamawa, Yah na san zaka ce me Hauwaa ta rasa? Komai tana ci ta sha ta sanya tayi ma wani ma, amma a gaskiyar magana ta rasa soyayyar ka, ba ina nufin baka son ta ba, a iya sani na bayan ni Hauwaa ce mafi soyuwa a gare ka, amma baka bata soyayyar da ke ɗauke cikin ran ka, in zan iya faɗan wannan kalmar ba tare da kaji haushi ba ina nufin u ar not romantic, gaba daya baka nuna mata kai ɗin dan soyayya ne, ba irin gifts ɗin nan na masoya tsakanin ka da ita, ba wata soyayya, kuma kwanaki na ji tana magana a waya akan baka biya mata buqata sosai, i am sorry to say amma kaga wannan babbar matsala ce da zata iya jefa ta neman wasu mazan musamman tinda baka nan, kuma baka tafiye-tafiye da ita,kuma Hauwaa mace ce da take very sensitive, abu kadan yana tasiri a ran ta me kyau ko mara kyau,"
Shiru Ishaq yayi cike da jin kunya yau wai qanin shi ke nuna masa me ya kamata yayi,
"Me kake ganin ya dace nayi mata yanzu Haroon?"
"Naji daɗi da ka fahimce ni, ina roqon Allah daya baka ikon sake siyan soyayyar ta da yarda ta a karo na biyu a rayuwar auren ku, shawara ta na farko shine ka je da ita wannan tafiyar, amma kai suprising ɗin ta, in yaso sanda zaka faɗa mata sai kace ka ce bazaka da ita bane yau dan kar ta rusa maka plan ne dama, ka dai lallashe ta in yaso in kun je su ta can ba ruwan su suna saida magungunan maza da na matan ma dika sai ka siya abun ka, sannan ka daure ka ɗan dinga ɗan wasanni da ita da zuwa wajen shaqatawa haka,"
"Lallai ba banza ba kake so a yi maka aure yaro ba abinda baka sani ba, na gode to na gode sosai, Allah ya yi maka albarka, gaskiya naji daɗin shawarwarin ka a gareni,ina godiya sosai qanina, ina godiyar yanda ka zauna ka bani shawara sosai wanda ba kowa ne zai iya ban shawarar yanda zan zauna da iyalina lafiya irin haka ba,"
"Yah ai kaima abin a gode maka ne ba dika mutane ke son a nuna masu gazawar su ba musamman ta ɓangaren rashin qarfi a wajen mu'amalar auratayya,sai ka ga namiji har na miji amma a d'aki babu fus, mata suyi ta haƙuri da shi, yana gani kamar shi ya gama yi masu komai dan ya mallaka masu dukiya,"
Haka dai sukai ta tattaunawa a kan matsalar ma'aurata Haroon na ci gaba da wayar ma da yayan shi kai a harkar aure a musulunci.
*********************
A qofar gidan Mamalo umar ya aje Jameelaa, glass din idon ta ta cire tana kallon gidan cike da d'agun kai...................
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 18:
Babu inda Hauwaa bata duba ba a gidan amma bata ga Haroon ba,babu ma alamar yana cikin gidan,cike da takaici ta koma parlour ta zauna, wayar ta ta kunna ta nemo No Haroon ɗin ta hau kira, tayi ringing yafi a qirga amma bai d'aga ba.
Har ta cire ran zai ɗauka ta ji sallamar shi,cikin muryar bacci,
"Ina kaje?"
"Ke meye naki na nema na a wannan lokacin?"
"Ina son sanin inda kake ne, saboda yayan ka ya kirani ya ce na kula da kai,"
"Jariri ne ni? Ai ba jariri bane ni da za a ce ki kula da ni, ke in ba dan tsaurin ido ba da kuma kina auren yayana har kin kai wadda zata kula dani? Ke koda kin girmen ma, ni namiji ne da ace kina da halin kirki ni zan kula da ke amma ba ke za ki kula da ni ba, zan kashe wayata kar ki sake kirana dan ban ga abinda zan yi maki