Showing 114001 words to 117000 words out of 118783 words
da ta ga wucewar su ta juya a guje zuwa d'akin ta tana kuka, d'akin ta ta shige ta faɗa gado tana ta zubar da hawayen tausayawa kan su.
Abu da Mero sun tausaya mata sosai, yaran ma kowa sai ya koma wani sukuku saboda ganin Jameelaah a cikin damuwa, Jameelaah ta taimaki darayuwar su, miji ya zama abin so agare su yanzu, mijin su na da lokacin su dana yaran su, ga shi yanzu har shagon kekuna gare shi arziqi ya bunqasa sai godiyar Allah, abinci ya wadatu, tsafta ta wadatu a gidan, ga uwa uba tarbiyya, dan ta tsaya tsayin daka dan ganin yaran sun kaucewa rayuwa irin wadda tayi a baya, soyayyar da yaran suke yi mata wata ran har kishi iyayen su suke yi.
Sun sani zai yi wahala kuma ta sake fita cin abincin, dan haka suka dakko mazubin Tsalha suka zuba mata nata, sannan Abu ta shiga d'akin nata ta ajiye mata sannan ta zauna a gefen gadon Jameelahn ta dafa bayan ta cike da tausayawa ta ce,
"Auntyn yara dan Allah ki daina kuka haka, komai yayi farko zai yi qarshe,duniya dama ta gaji haka, komai kayi a rayuwa kamar jifa ne, in yayi sama dik nisan dad'ewar da yayi a saman zai fad'o qasa, ko ya fad'o maka dai-dai yanda ka jefa, ko ya fad'o maka a tarwatse, ki godewa Allah a kan ni'imomin daya yi maki, dik da irin mugunyar rayuwar da ki kai a baya amma bai bari kin wulaqanta ba, muma ga shi kin taimaka mana da tarbiyyar yaran mu, tinda ke kika san maganin irin halin da matasan yanzu suke fuskan ta,wanda ba dan zuwan ki ba da yaran mu sun lalace, Allah ya taimake mu yanzu ga shi yara bakwai muka kai d'akin miji lafiya, ga mahaifin su yanzu yanda ya sauya dik ke za a godewa akan hakan, ko dan haka bai kamata ki sanya kan ki cikin qunci da damuwa ba, dan Allah ki warware ki fito, mu sha iskar duniya mu warwasa abun mu yanda muka saba,in ma bazaki ci abincin ba yanzu zuwa anjima kunci ke da Baban Hajjo kuna ci kuna soyayya abun ku,"
Cike da jin kunya ta rufe idon ta sannan ta yi murmushi ta share hawayen ta tace,
"Ni ba zan ci da shi ba da ku zan ci,"
"Gulmamma nan nan ba tare kuke ci ana kaiwa juna a baki ba, ana kalaman qauna, ai ina sane da yanda kike susuta mana ɗan tsohon mijin mu, amma karki damu, muma dik mun koya yanzu duk abinda muka ga kina yi mai kyau yana yabawa muma yi muke koda bai yaba mana kamar yanda yake maki ba a qalla yana nuna mana jin daɗin sa,"
Dariya sosai Jameelaah take tintsirawa cike kuma da jin nauyin Abu, ashe komai suke yi akan idon su ake yin shi.
Abu taji dadin yanda Jameelaah ta saki ranta,dan haka tare suka ci abincin su, suna ci gaba da tsokanar ta, tana ta faɗin dan Allah su bari, yara na ji fa.
Koda Tsalha ya dawo sai da yayi wanka ya ci abinci, sannan suna hutawar su ta faɗa masa komai da ya faru da rana, ya ji tausayin ta sosai sannan daga baya ya lallashe ta yayi mata alqawarin har da shi za a je a bawa Umar hakuri, kuskure ba wanda ya wuce ya aikata shi ai, Allah na san bayin shi masu neman tuba da masu yafiya idan an nemi tuban su.
Im fada maku gaskiya dana ga tsalhan ku ban gane hyi ba fa, Tsalha har wani ja ja ja ja yake yi, gemun nan ya tsaya carrr, kumatun ya bayyana, daga lob'awar da yayi, jikin shi kamar ba nashi ba, ya koma mijin yarinya, shima ya zama saurayi abun shi yana ta dangwalar romon dimokuraɗiyyar soyayya abinshi.
*********************
Bayan Ummee wato Umaimah ta haifi Ibraheem Khaleel ❤️sai Shukrah wadda take shayarwa a yanzu,Aunty Hauwaa kuma bayan Muhammad ta sake haifiar Saifullah.
Sadeeq da amaryar shi wadda yake ji da ita a yanzu kamar k'wai, suna da d'iya mai suna Fateemaah wato (Mamalo) dan shi da Mamalo ma ya ke kiran ta, Matar shi ta san ko me zatai da wahala ya so ta kamar Mamalo, dan haka take kyautata ma Fateen nasu, yana jin daɗin hakan kuwa sosai.
************************
"Washhh Allah na gaji Mama akwai dan abin kaiwa bakin salati kuwa? Yunwa nake ji kamar naci babu, na so na leqa shago na karb'i dambun nama kanna tafi amma da yake ina sauri sai na manta,"
"Da dikkan alama yau ma ba ai nasara ba kenan ko Bukar?"
"Kamar kullum kuwa Mama, har yanzu ban samu aikin ba, na rasa meke damun qasata Nijeria, wai a ce ka gama karatu, da k'yar da sid'in goshi, sannan aikin ma da k'yar da sid'in goshi za ka samu ba wani tanadi da gwamnati ta yi wa matasa dan ganin sun samu aikin yi da zarar sun kammala karatun su da kyakkyawan sakamako,yanzu ki duba fa Mama mu da muka kashe lokacin mu, jikin mu, da dik wani arziqin mu bama samun aikin, sai waɗan da zasu jera sati basu je lecture bama, ko jarabawar gama sakandiren ma siyan ta suka yi, sune suna zauna a AC za a kai masu takardar aiki har gida, aikin ma haka za suna zuwan shi sanda suka ga dama, in ba su ga dama ba suyi wa mutum aiki ba dai-dai ba, kayi magana su zage ka, kaiii subhanallahi, talaka na cikin izayar rayuwa Mama, gwanda ma ni ai ban cika shekara ina neman aikin ba, ga wasu abokai na da suka rigani fara makaranta suka rigani gamawa su fa mama akwai masu shekara biyu uku a cikin su ba aiki, in ka nemi sana'a a dinga yi maka kallon jahili bayan da kwalin ka mai kyau na degree, in ka zauna ba aiki k'wandala ta gagare ka, in kai sata a garqame ka, ya ilahi ina talaka zai sa ranshi ne ?"
"Oohhh an tab'o me baki yau, yau da gwamnati taji wannan sharhi da sun baka aiki Bukar kowa ya huta,"
Dariya yayi, sannan ya ja kwanon data kai masa abinci ya fara ci yana ci gaba da surutai,
"Ni kin san ma me nake tunani Mama? Aikin nan aje neman shi zan yi, na kama sana'ar nan tamu na bunqasa ta, ko ina ana kai dambun nan ana siyarwa ta haka ne masu sari da siyan ɗaya za su qaru, in da rabon na samu aiki shikenan, in babu ban dai zauna da jahilci ba ko? To godiya ta tabbata ga Allah"
"Baki abun magana kenan Bukariri Allah to ya sanya albarka, mahaifin ka da Malam Tsalha kaga suma Allah ya bud'a yanzu shagunan keke gare su,mahakurci mawadaci aka ce, sana'a maganin rashin aikin office"
Kamar yanda ya tsara haka ya gabatar, Bukar na sa hannu a sana'ar dambun nama Allah yasake sanyawa abun nasu albarka da nasibi, yanzu da wahala kaje unguwa a kano baka ji ana da shago ko wajen da ake bada sarin dambun naman su ba, in an samu riba sai su kasa ta uku, Jameelaah na da kashi ɗaya su kuma kashi biyu, da ita suke baiwa Kashi biyun ta ce su yafi cancanta da su riqe kashi biyu ba ita ba.
**********************
Umar ne zaune a farfajiyar gidan shi riqe da jarida kasancewar yau weekend ne ba aiki, Sapnah na zaune a gefen shi tana b'are masu lemo shi da Humairah itama tana sha.
"Wajen nan qwari sun yi yawa Ammi duk sai cizona suke yi,"
Cike da shagwab'a take yin maganar, kallon ta Sapnah tayi sannan tace,
"Ki shiga ciki mana kin damen da surutu tin ɗazu, kin saka ɗan qaramin wando da yar riga to tsoron ki suke ji da bazasu cije ki ba? Yanzu ga jarabawar JSSCE din ku ta gabato, ya kamata ki maida hankali wajen yin karatu ba wasa ba, in kin ga ina zaune ba abinda nake yi kema ki bi waje ki zauna,ni ɗin nan na sha gaya maki da kwali na na digiri digirgir yarinya,aiki ne dai naqi yi, saboda ina son zama na kula da iyali na,"
Humairah tashi tayi ta rungume Sapnah, tare da manna mata kiss a kuncin ta sannan ta shige ciki tana faɗin,
"Na wuce ciki ni dai tinda dai kin kore ni, karatu kuwa zan baki mamaki Ammi zaki yi alfahari dani watarana,"
"Haka nake so ai dama na sha mamakin sannan ko a yanzu ina alfahari dake Allah ya yi maki albarka,"
"Ameeen Ammin Humairah,kema Allah ya yi maki albarka"
Umar ne ke ta murmushi baya gajiya da jin hirar Sapnah da Humairah, a can qasan ran shi kuma yana jin haushin Jameelaah da taurin kai ya hana ta zuwa ta nemi qafarar shi ta roqe shi ya bata Humairah dan itama ta saba da ita haka, shi kuwa yayi alqawarin in ba ita ta zo ta nemi a bata Humairah ba ba zai taɓa kaita wajen ta ba da kan shi.
"Tinanin me kake yi haka Zauj?"
Ya buɗe baki zai yi magana kenan, aka buɗe qaramar qofar gate ɗin gidan nasu aka ziro qafa, qurawa qafar ido Umar da Sapnah suka yi dan ganin wanene zai shigo, ko a ina Umar yaga wannan qafar tabbas zai gane qafar da ya sha yi wa tausa da hannayen shi ce, qafar da ya sha shafa mata mai da hannayen shi ce qafar da...................
*Casssssss anayi ina jin nice, ana bari ina yin😢*
[09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏼 *MAZAUNA GIDA* 💅🏼
*WRITTEN BY HAERMEEBRAERH*
Page 50:
Ajiye jaridar hannun shi ya yi ya miqe tsaye Sapnah da ke riqe da lemon da ta bare masa ta bi qafafun da yake kallo da idanun ta,Jameelaah ce ta shiga sanye da atampa riga da zani sai mayafin daya yi kala da kayan jikin nata, haka ma takalmi da purse ɗin ta iri ɗaya ne, kamala da kwarjini tare da nutsuwa sun bayyana a fuskar ta, lallai dik kyaun mutum in baida kamala bai gama cika mutum ba, yanzu ne Jameelaah take cikkkiyar kyakkyawar.
Sapnah ce ta tashi ta je gare ta fuskar ta ɗauke da murmushi mai qayatarwa, ta kama hannun ta tana mata sannu da zuwa, ciki ta shigar da ita, sai da ta zauna suka gaisa sannan Jameelah tace mata,
"Ni da maigidana muka zo yana waje,"
"Ahhh shi ne baki yi magana ba, bawan Allah ya na can waje a tsaye ai da kun shigo tare duk gida ne ai"
Zuwa ta yi tayi ma Umar bayani haka nan sai yaji dik wani haushin ta da yake ji ya kau a ran shi, gaba ɗaya yanda yaso ya yi mata rashi mutunci ya farfaɗa mata maganganu marasa daɗi a dik sanda ta zo wajen shi sai ya ji ko kallon banza ba zai iya yi mata ba.
Shigar da Tsalha ya yi cikin gidan, Tsalha zama ya yi kusa da matar shi sai ta miqa masa lemon da aka tsiyaya mata,cike da tsokana Sapnah tace,
"Ohhhh Maman Humairah wato soyayya daɗi ko, ai gashi zan zuba masa nashi shima,"
"Ammin Humairah baki da dama, wato har yanzu baki bar surutu ba ya huta shima ko?"
Dariya suka yi dikan su harda Umar, Umar kuwa sai kallon Jameelaah yake yi Tsalha ma na kula da kallon da yake ma matar shi,nan da nan kishin 'yan mazan jiya ya motsa,sai ya yi gyaran murya ya fara magana dan suyi suyi abinda ya kawo su su bar gidan,
"To da farko dai dalilin zuwan mu shi ne, mun zo ne dan mu bada hakuri akan abubuwan da suka faru a baya,ba sai an maimaita su ba a yanzu,na san duk irin abubuwan da Amaryata Jameelah ta aikata maka marasa daɗi a baya,gamu mun zo tana mai neman gafara akan su, ina fatan zaka dubi girman Allah ka yafe mata su,mun sani dika Allah baya barin haqqin wani akan wani, koda Allah ya yafe mata kaima tana da buqatar ka tausaya mata ka yafe mata,"
Umar dake kallon yanda take tsiyayar da hawaye ne ya ji jikin shi ya yi sanyi, sai ya ji me yasa ya ɗauki wannan tsahon lokacin bai yafe mata ba ? saboda ko ba komai Jameelaah ta so shi kuma shima ya so ta, ya daukake ta a rayuwar shi, ya girmamata a lokacin da dik bata cancanci hakan ba, me zai hana ya yafe mata a yanzu da ta zama mutuniyar kirki, har ta buɗe baki za ta yi magana Umar ya riga ta da faɗin,
"Na yafe mata Allah ya yafe mana baki ɗayan mu,dama ita rayuwa ana son mutum in ya yi laifi ya nemi yafiya, shi kuma wanda akai wa laifin ya yafe, shine cikar mutuntaka, dan haka na yafe mata dik abin da ta yi min wanda na sani da wanda ban sani ba, nayi hakan ne kuma domin Allah, ina fatan nima Allah ya yafe min,"
Jameelaah ce ke ta shasshekar kukan farin ciki, abubuwan da ta aikata masu muni a baya na ta dawo mata a kwanya da zuciyar ta, kallon gidan ta sake yi taga yanda aka sauya komai, arziqi ya haura na da, Sapnah ce ta miqe ta tafi d'akin Humairah,tana tafiya Jameelaah ta buɗe baki tace,
"Na gode Abban Humairah, Allah ya qara girma da daukaka, kaima Allah ya sanya ka farin ciki fiye da yanda ka sanya ni a da da kuma yau, na gode na gode,"
"Ba komai ya wuce,ina fatan nima ki yafe min in akwai abinda na taɓa yi maki da ya b'ata ran ki,"
"Ba ka min komai ba Yah Umar innace ga abinda ka yi min yau mara daɗi na maka qazafi, baka rage ni da komai ba, ka bani dikkan kulawa da girmamawa tare da cikakkiyar soyayya, ni ce nai fatali da komai, in ma yi kamin wani abun ko menene shi na yafe maka, Allah ya yafe mana baki ɗaya,"
"Ameen ya Allah, sai kuma maganar Humairah ga ta can dik sanda suka samu hutu inshaa Allahu zata dinga zuwa, ko kuma da weekends, zata zo har ku saba da juna inshaa Allahu,"
"Muna godiya malam Umar nima kaga ka koya min wasu darussan na zaman duniya, Allah ya albarkaci rayuwar iyalin ka, muna godiya sosai,"
"Babu komai, nima na gode"
Nan Sapnah ta shigo da Humairah da ta dame ta da tambayar ina zasu je? Sapnah taqi sanar da ita ta dai ce ta saka kaya sosai ta sanya mayafi ko hijabi, dan haka sanye take cikin riga da skirt na leshi, ta ɗora hijabi a saman su sai zaro ido take yi taga suprise ɗin da aka ce zata gani, su na zuwa parlour taga Jameelaah, cike da murna ta isa gaban ta ta rungume ta, Uwa Uwa ce😍 itan ma rungume ta tayi, tana shafa bayan ta, baki yaqi rufuwa, daga baya Humairah cike da jin kunya ta zauna a qasa, ta gaida su suka amsa, Jameelaah na shafa kan ta tace,
"Lallai Humairah kema girman jiki gare ki kamar ni,"
Dariya sukai banda Humairah da ba ta so ana ce mata yar lukuta,tinda a iya shekarun ta jikin ta babba ne,dan har bra take sawa a yanzu.
Turo baki tayi tana kallon Umar, alama ce ta ta kai qarar Jameelah wajen shi,
"Yi hakuri Daddy's girl wasa na ke yi maki, to jikin ki kamar na Abban ki,"
Murna ta fara yi, dan kuwa har yanzu Umar kowa ya san shi da suka sake haɗuwa yanzu ba zai ce ya sauya ba, sai dai ma a ce ya qara kyau da haiba.
Murna sosai Humairah tayi bayan sun taba hira Tsalha ya ceto su fa zasu tafi,
"Habaa ku dan qara zama mana, ga abinci can ya kusan yi," Inji Sapnah da ta yi maganar har cikin ran ta, dan kuwa ba qaramin daɗin samun wannan daidaito a tsakanin Umar da Jameelah ta yi ba ko dan Hunairahn ta ta samu farin ciki mai d'orewa.
"Ahhh ba komai kar ku damu, 'yan uwana nacan na jiran mu muci abinci, dan kuwa na ce masu ba jimawa zamuyi ba."
Tsalha yaji daɗin maganar ta sosai, saboda ko ba komai zuwan ta gidan shi ya sauya daga gidan qazamai ya koma na masu tsafta, tarbiyya ta wadatu, shi kan shi dik wata furfura da wani rama dik sun zama labari, yi 'yar qiba mai ban sha'awa yayi haske, ba wanda ya damu da furfurar shi, saboda kyaun da ya yi.
Umar kuwa d'aki ya shiga ya sanya kaya sosai, ya deb'i wasu shaddoji guda biyu masu tsadar gaske, da turaruka biyu, sai hula ɗaya takalmi ɗaya ya saka tashi hular ya ɗauki makullin mota sannan ya fita yace suje ya sauke su a gida daga nan yaga wajen da suke da zama ma.
Ai kuwa basu yi masa musa ba dan yanda Umar yayi magana ba damar musu n ma gashi yayi gaba ya bar su baya alamar su yake jira, sai da suka fita Sapnah ta fito itama ɗauke da ledar ta a hannu, kayan kwalliya ne da turaruka sai wani sabulun wanka da body scrub da skin oil sai hair oil da hair mask duk na kamfanin HAMIBRAH BEAUTY PALACE kaya ne dake gyara fata kuma basa saka bleaching sai dai suyi maganin quraje da qesbi, sannan gashi ya yi kyau ya yi tsawo ya yi daɗin maintaining.
Jameelaah tayi ta godiya kamar ba zata daina ba Sapnah har taji kunya ma ta kama ta, sanda zasu tafi Umar yace Humairah ta shiga daga nan sai su dawo tare.
Cike da murna kuwa tashige kusa da Jameelaah suka wuce.
Har gidan ya kaisu kuwa ya jira dan saida Jameelaah da Humairah suka shiga ciki sannan Umar ya baiwa Tsalha kayan daya d'akko masa, Umar na ganin alamun Tsalha zai qi Karb'a ne ya yi saurin riga shi yin magana ya ce,
"Don Allah kar ka qi Karb'a, ga shi nan a yi ma matan gidan kwalliya, yanzu ni da ku ai mun zama daya inshaa Allhu,"
"Kaiii amma na gode, ba dan ka roqe ni ba da sai nace ka bar su, daga zuwa neman gafara sai a had'o mu da irin wannan kab'akin arziqin haka?"
"Alamu ne na an yafe maku kenan ai,"
Dariya suka yi, Tsalha ya shiga gidan shi a dakin Jameelaah ya aje kayan sannan ya ma matan shi izinin su sa Hijabi su gaisa da Umar, a soron gidan suka tsaya suka gaggaisa,bayan sun koma cikin gida