Showing 33001 words to 36000 words out of 118783 words
kwadayin rahamar shi Allah zai baki aljanna dan ya yi ma wanda ya yi kwadayin rahamar shi alqawarin samun rahamar,"
"Kai ka san wannan ni dai na gaji ehe, nace na gaji a dau mataki akan wannan muguwar rayuwar da muke ciki ko kuma na dauka da kaina,habaa sai kace akan mu talauci ya ƙare?"
Juyawa ta yi dan ta yiwa Jameelaah magana taga wayam ba ita ba labarin ta,haka tai ta masifa tana gwada layin Jameelaah da 'yar qwabirar wayar ta amma ana yi mata turanci, soke wayar ta yi tana fadin zasu gamu ne goben.
Hanyar asibiti ya ɗauka da su, dan kuwa a yau zai kaita a dau jinin ta a gwada ta in result ya fito ya ga lafiya take to a washegari zasu koma gidan su, dan kuwa komai na more rayuwa an zuba a gidan su kawai yake jira .........
*Allah ya kaimu goben muji meye sakamakon gwajin jinin da za a yi wa Jamcy baby, shin makaranta Umar ya kyauta kuwa da zai je ayi gwajin jini bayan Jameelaa bata da masaniyar me za ayi?*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 16:
Ana gama d'iban jinin ta ya ce wa masu gwajin su yi mashi gwajin da suka yi magana za a yi akan wannan jinin yau zai je ya dawo,daga nan parking space suka wuce suka shiga motar su ya ajiye ta a gida, ta yi masa tambaya gwajin me za a yi mata yafi sau a qirga amma bai bata amsa ba, qarshe sai ce mata ya yi gwajin malaria ya kai ta a yi mata,mamaki take ta yi dan dai bata ce masa bata da lafiya ba ita rabon ta da ciwo ma musamman wanda zai kwantar da ita har ta manta, daya ga bata yarda da shi ba sai ya kama hannun ta yace.
"My love tinanin me ki ke yi ne haka? Ko baki yarda da abinda na faɗa maki bane?"
"Kawai ina mamaki ne Yah Umar akan gwajin da ka kawo ni a yi min naga ni dai lafiya ta qalaou,"
"Kin san yanda nake matuqar son ki ba zan so ki shiga cikin lissafin masu malaria na duniya ba a shekarar nan da za mu shiga, ko baki da masaniyar yanda malaria ke kisa ne kuma duk shekara ana tara data na iya adadin mutanen da ke ɗauke da cutar malaria na duniya? Qungiyar Wold health organization na fitar da wannan qididdiga duk shekara ki bincika zaki tabbatar da hakan,Baby dik abinda zai zama barazana ga rayuwar ki inshaa Allahu in ina da iko zan kawar da shi tun kafin ya riske ki, yanzu yayin mace-mace ake yi saboda wannan mummunan ciwo na malaria dan haka dole na kula dake,"
Jameelah ta ji daɗin kalaman shi sosai, saboda irin wannan kulawar da ya ke bata tana qara sanya mata hakuri da juriya akan qin kusantar ta da bai ba har na tsawon wannan lokacin,amma a qashin gaskiya ta fara gajiya akan rashin kulawar aure da yake bata,ita ai ba dutse bace in shi dutse ne, tana wanan tinanin ta ji buɗe qofar motar shi ya fita, nan ko bata san yana ta yi mata magana ba ma,itama fita ta yi suka shiga gidan a tare,cikin sauri ya juya ya gaishe da Mum da ke zaune a parlour ta na kallo,tambayar shi ta yi,
"Saurin me ka ke yi haka Umar?"
"Mum ina son naje na amso wani abu ne, yanzu nan zan dawo da yardar Allah akwai wani abu ne?"
"No ba wata damuwa dama ina son na sanar da kai ne ko zaku bar komawar ku gidan ku sai ranar juma'a ɗin anan mai zuwa? Saboda akwai gyare-gyare da nake son na yi wa Jameelaah, domin so nake ku koma gidan ku kamar ranar aka yi auren ku, tabbas kun yi min biyayya dole ne nima na kyautata maku, fatana Allah ya yi muku albarka, ya baku masu yi maku biyayya fiye da yanda kuka yi min,ba kowanne ɗa bane zai yi abinda kuka yi, na sani ban kyauta ba dokar da na sanya maku ta yi tsauri, sai gashi kun bani mamaki har bayan kammala karatun ka Umar kuna riqe da kan ku kuna jiran umarni na da amincewa ta,ko da ace kun saɓawa doka ta ba ku yi laifi ba, amma riqe alqawarin da ka yi ya qaramin ganin qimar ka da son ka da kuma son na ga na qara kyautata maku dika a matsayina na uwa a gare ku,"
"Muuuummm, zaki sa na yi hawaye amma na farin ciki, na ji daɗin addu'ar ki sosai a gare mu Allah ya amsa, bari na yi sauri na dawo ana jirana"
Kyab'e baki Jameelah ta yi ta wuce d'aki,cikin ranta ta na ayyana yanda zata muzgunawa Mum a duk sanda ta samu dama itama dan kuwa wannan ba qaramin zalunci aka aikata mata ba, mum kuwa ta zaci tsabar kunya ce ta hana ta tsayuwa a wajen ta gudu d'aki sai ta yi murmushi ta maida hankalin ta akan Umar ta ce masa,
"To sai ka dawo,"
Da hanzari ya koma asibitin, sai da ya tsaya ya yi sallar Isha'i a masallacin da ke cikin asibitin sannan ya qarasa lab din, ana miqa masa result ɗin ya damqe shi tare da yin godiya mai yawa ya fita yana yi musu sai da safe.
Zaune yake a mazaunin driver ya kasa buɗe takardar saboda fargaba,da kyar ya samu ya buɗe sakamakon da ya gani ya yi matuqar sanyaya zuciyar shi, wata hamdala ya dinga saukewa, sannan ya hau tasbihi ga Allah cikin farin ciki ya ke fad'in,
"Na yafe ma dik wanda ya yi maki fyaden nan tinda bai goga maki ciwon da zaki haramta a gareni ba, na yafe masa duniya da lahira, na yafe masa duniya da lahira, na yafe masa,"
Nannad'e takardar yayi ya yagata ya zubar, shopping yaje ya yi wa Jameelah na kayan kwalama sosai da kayayyakin shafawa da turaruka masu kyau da tsada, sannan ya yi ma Mum da Umaimah siyayya suma, Dad ma ya sai mashi turarukan da yasan yana so.
Gida ya wuce cikin farin ciki lokacin kowa yayi bacci banda Jameelaa, idon ta biyu ta na ta tinanin ina Umar ya shiga gashi har ta yi wanka ta shirya cikin kayan bacci jikin nan ta mulke shi da lotion mai gyara fata gashin ta ya sha gyara sai sheqi yake,sweet ce mai qamshi a bakin ta ta na ta tsotsa saboda tun tana gida ta tsani wani ya ji warin bakin ta balle kuma Umar da take mugun so.
Da kaya niqi-niqi ya shiga gidan, d'akin Umaimah ya leqa ya ajiye mata ledar ta a gefen gadon ta, sannan ya aje na Mum a d'akin ta itama, dan kuwa bata d'akin ta na d'akin Dad,duk abinda yake yi akan idon Jameelaah yake aikatawa, tsaki taja mai qarfi sannan ta ce,
"Dik bari mu koma sabon gidan mu za ku sha bakin mamaki ko ganin shi sai ya yi maku wahala, komai wai sai an yi raba dai-dai da ku, sai kace mijin su aikin banza,"
Ta na nan ta na surutu da baƙin ciki ya koma parlourn bata sani ba sai jin muryar shi tayi ya na fad'in,
"My love ke da wa ki ke magana? To ayi hakuri indai ni ne gani na dawo, muje ciki ko?"
Washe baki ta yi tare da amsar leda ɗaya dake hannun shi suka shiga d'akin su,suna shiga ya baje kayan a gaban ta tare da d'aga ta tsaye, ya manna ta da qirjin shi, cikin farin ciki ya ce,
"Love na amso sakamakon gwajin da aka yi maki kin samu nasara baki dauke da ciwon qa.....mammmamalaria,"
Cikin sauri ya sauya akalar maganar tashi kallo ta bishi da shi dan son gano me yake boyewa,idon shi tsilli-tsilli kamar na munafukin da aka turke ya na tsaka da gulma, sakin ta ya yi da sauri ya fara d'aga rigunan bacci dogaye biyu daya siyo mata masu mugun kyau, chocolates da sweets gasu nan barbaje a qasa, nan da nan kuwa uwar kwad'ayin ta basar itama kamar yanda ya yi ta hau duba kayan da ya kawo mata, wata leda ya janye gefe idon ta na sauka akan ledar ta miqa hannu da sauri ta ɗauke ta na dariya,
"Wannan turarukan na waye?"
"Na Dad ne gobe zan bashi tinda sunyi bacci yanzu,"
Ranta bai so ba sam duba da yanda ta ga ya yi wa Mum da Umaimah ma siyayyar amma ta maze ta ce,
"Ohhhh d'a da daɗi kaga ka sai ma Dad turare dan neman albarkar shi, Allah ka ban iko na kammala karatun nan na samu makarantar gaba da sakandire na gama ta nima na fara aiki na dinga sai ma iyayena abubuwan more rayuwa ko zan dinga samun lada kamar yanda ka ke samu a koda yaushe ,gaskiya Yah Umar in mutum na zaune da kai sai ya iya abubuwan alkhairi kala-kala,"
Ya ji daɗin yabon da ta yi masa, amma kuma sai ya ji bai kyauta ba da bai sai ma mahaifan ta komai ba, shi ya sai abubuwa ma nashi iyayen amma baya tunawa da nata sam,wayancewa yayi ya ce,
"Ai wannan ma harda Baba na siyo, nafi son na bashi da kaina ne, saboda ya samin albarka,"
Kauda kai tayi ta murgud'a baki, taso ya kawo ledar da ya kaiwa Mum d'akin ta dan ta samu na daukar ma Ramai, amma ba komai zata fanshe ne a wani wajen watarana.
Godiya ta yi ta masa har sai da ya rufe mata baki da nashi su Jameelaah an samu abin nema, ai kuwa ta qanqame shi ta hau shafa sassan jikin shi, Umar ya jiqu matuqa da salon Jameelaah, da kyar yake fidda numfashi tsabar yanda ta kannad'e shi kamar an ce mata guduwa zai yi.
Ganin yanda ta kai qirjin ta saman fuskar shi ne ya sanya shi saurin janye ta a jikin shi, yana neman iska dan ya shaqa, hawa saman gado yayi ya kwanta ya yi shiru ya na qoqarin daidaita kanshi,Jameelah kuwa tana nan kwance a aqasan carpet tana maida nata numfashin cike da matsanancin takaici, wannan wace irin rayuwa ce suna zaune gida ɗaya daki ɗaya da mijin ta amma saboda wata dokar banza ba zasu iya jiyar da junan su daɗin zaman aure ba, wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mata.
Umar idon shi lumshe suke yana sauke numfashi a hankali, gaskiya hakurin shi ya qare ba zai iya bari har juma'a ba kafin ya keb'e da matar shi inaaa ba zai iya ba hakurin shi ya qare, ya ma yi qoqari ai,a da fargaba da tsoron kamuwa da ciwon qanjamau na tsaida shi tare da dokar Mum ta ya bari ya kammala karatu,to a yanzu menene ke tsaida shi kuma? Babu komai, dan haka gaskiya gobe zai sama wa kan shi da matar shi mafita.
Jameelaah a nan ta fara yin bacci Umar ya yi bakam kamar wanda yayi bacci, sai cikin dare ya tashi ya je d'akin Mum din shi ya duba keys ɗin gidan su ya zari biyu ya fice, d'akin su ya koma ya kwanta.
Da safe Jameelaah ta gama dik wani shirye-shiryen tafiya gida yau za a kai amarya, daga yau an gama biki, Mum ta bata kuɗi mai ɗan yawa da atampa da sabulai na wanka da wanki da babban ledar omo ta ce ta kaima Ramai, daf zata fita ta hanyar kitchen Mum ta bita, dan bata son surukar ta ta taci gaba da satar abinci, dan haka tace
"Jameelah bari na d'eba maki ɗan dankalin nan ki kaiwa Maman ki, ki ce ina gaida ta"
Cikin kame-kamen ko dai an gano ta ne ta tsaya cak, sai zaro idon ta da yasha kwalliya take waje.
Tana nan tsaye mum ta ɗebar mata dik wani abu data ga ya dace ta bata, Drivern dake kaisu makaranta shi ya kai ta, Umar yace tayi gaba taje gidan su, in ya gama abinda yake zai je ya ɗauke ta ya kai ta gidan amaryar.
Koda sika isa gidan ta tarar da gidan cike yake ana ta hada-hadar biki, masu biki na nan na ta hidimar su gefe ɗaya masu sana'ar abinci na kullum na nan basu fasa ba, dan kuwa Ramai ma tayi nata yana can qofar gida ana ta saidawa, lungun shaqe yake da mutane kala-kala, can daga nesa ta hango yaran gidan nasu wasu na wasa wasu na zaune kawai suna kallon masu shige da fice, sai ta kira su ta sa suka d'ibar mata kaya suka nufi cikin gidan da shi, sai wani shan qamshi take yi ita a dole driver ne ya kawo ta, ga kaya nan niqi-niqi ta kawo gidan su, ai kuwa ta yaqi 'yan matan dake zaune a waje ana ta budiri da samari,nan da nan suka hau gaishe ta suna haɗa baki wajen fad'in,
"Jameelaah kin iso kenan, sannu da zuwa.....Jameelaa sannu da zuwa.....jameelaa tare zamu tafi gidan amarya anjima...."
Sai da suka gama surutan su ta d'aga masu hannu ta ce,
"Sannun ku,"
Ta yi shigewar ta cikin gidan su ta bar su nan tsaye baki sake, ai kuwa samarin wajen me za suyi in ba dariya ba, nan aka dinga yi ma matan da Jameelaa ta wulaqanta dariya, tin suna iya kare kan su har suka kasa.
Ramai na ganin an fara shiga da kaya ta hau gud'a tana yiwa Jameelah kirari har sai da ta shige d'aki tana wani nuna Kyankyamin zama a dakin,cikin yatsina fuska ta ce,
"Ramai ina kud'in ledar d'akin dana baki ne dan Allah?"
"Na cinye dan uban ki,ke bari ki ji fa ba yanda za ai na saka ledar d'aki anan wajen dik a lalace, in kina son in kin zo ki zauna a waje me kyau na sanar dake ki sa mijin ki ya kama mana haya amma kin qi, kamar ke ɗaya kike son hutun"
Shiru tayi dan ba ta son su ja maganar ta yi nisa, Ramai ta kasa ganewa so take sai sun koma gidan su zata fara baza mulki son ran ta,tafi Ramai son ta gyara su su fito tsaf dan kuwa ta jima ta na yanka wa qawayen ta na makaranta qaryar iyayen ta masu azziqi ne, tinda gaba ɗaya yaran masu hannu da shuni take tare da su a makaranta a yanzu.
Kayan da ta zo da su Ramai ke ta fitowa da su tana gani tana murna, kuɗi Jameelaah ta qirga dubu uku ta bata sannan ta sake qirga dubu uku tace na baban tane wannan, sannan ta aje ma Bukar dubu daya.
Turaruka biyu ta bawa Ramai tace na Baban tane, Ramai dik amsa tayi tana ta godiya,a ranta kuwa ta na fad'in,
'Shashasha an faɗa maki kowa soko ne irin ki? taya ma zan bawa baban ku wannan turarukan masu tsada? ai saidawa zan yi na manne kud'in, tinda shi ko an bashi ba wani amfani yake da su ba, kullum ana fama da man babur da na keke yaushe yake da lokacin fesa turare irin wannan?'
Waya ta tsinkayo Jameelah na yi da Umar,
"Na'am Kana waje? Ka manta sai qarfe shida na yamma nace maka za a kai amarya?......k to gani nan zuwa,"
Jakar ta ta buɗe ta fesa turarukan ta masu qamshi, ta sake shafa hoda ta saka janbaki sannan ta jefa sweet mai qamshi a bakin ta ta yi saurin tattaunewa ta shanye, Jameelaah ta qara gogewa ta yi kyau sosai ta iya gayu na musamman saboda zama da yaran masu kuɗi,ta zama cikakkiyar budurwa 'yar sha takwas, jakar ta ta ɗauka ta yi ma Ramai sallama Ramai sai jinjina kyau irin na d'iyar ta ta take yi kamar ba ita ta haife ta ba.
A mota ta gan shi zaune ya sha gayu da manyan kaya, ya yi kyau ainun matan layin su da 'yan biki kamar su janyo shi tsakiyar su tsabar yanda suke kallon shi duk ya qosa Jameelah ta fito su bar wajen, wanda suka san Mijin tane sai gulma suke yi suna fad'in, 'kyau da kyau an haɗu',wanda basu sani ba kuma sai suka hau tambayar waye shi, har ta zo qofa ta tina bata ma Mamalo magana ba ma tunda ta shiga gidan, da sauri ta koma ta ce mata Umar yazo zasu fita, in za a kai amarya zata zo.
Da wani irin taku ta fita kamar wata matar wani qusan a gwamnati sai wani hura hanci take yi,nan da nan kuwa ido ya koma kan ta har ta kusa isa wajen Umar ɗin da ya fita dan buɗe mata motar, ta na ganin haka ta sakar masa murmushi shima ya mayar mata, da ta shiga motar sai ya rufe ya zagaya ya shiga shima sallama ya yi ma samarin wajen sannan ya ja suka fice daga layin, wani ihun daɗi ta sake tana ta dariya,umar cikin murmushi ya kalle ta ya ce,
"Lafiya ki ke wannan ihun haka?"
"Yah Umar ka gama biyana yau, ka gama kashe gayun layin mu yau, kaga yanda kowa ke kallon mu,ka gama min komai Yah Umar,me kake so a duniyar nan na baka ko na yi maka dan kuwa ka fiddani kunya a lungun mu yau, kaiiii wani abu sai ma anjima a wajen kai amarya malam, har wasu kayan nazo da su dan sake kashe kala,"
Rage gudun motar shi yayi ya kalle ta ya ce mata,
"Kin tabbata komai nake so zaki yi min? Kuma kin yi alqawari?"
"Sosai ma na yi alqawari, in dai abun da ka ke so a waje na bai saɓawa addini ba zan yi maka shi, sab'on Allah ne kawai ba zan ba akan ka Yah Umar, amma indai ni Jameela ina da iko akan abu tambayi zan yi maka ko meye,"
"Kina ma da shi muje ki gani, zan faɗa maki me nake so,"
Wata hanya ya ɗauka da su wadda ta kula hanyar asibitin su ne da suka je rannan, me kuma za su sake yi a asibitin, tsoro ne ya kama ta kar dai allura za a sake yi mata yau ma a deb'i jinin ta?.....
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 17:
A k'ofar gidan nasu mai matuqar kyau da ɗaukan hankali ya ajiye motar shi,har ya buɗe mata qofar motar bata sani ba saboda yanda ta saki baki ta na kallon fasalin