Showing 48001 words to 51000 words out of 118783 words
baje mata basirar kan shi jiya a jikin ta zai same tane yau cikin farin ciki, dan kuwa ta yaba ta koka sosai saboda haduwar tashi ta yi mata,amma kuma me yasa yau ta tashi fuskar ta babu annuri sam.
Gyaran murya yayi ya taɓa ta, ganin haka Haroon ya tashi da plate ɗin shi yayi d'aki, Ishaq bai tsaida shi ba dan yana buqayar jin meke damin matar shi.
"Meke damun ki ne Baby? Dan Allah kar ki min qarya ki sanar dani ko mene ne, inshaa Allahu na maki alqawarin sama maki mafita akai,"
Sauke ajiyar zuciya tayi ta kalle shi, hawaye ya zubo mata a kuncin ta,ta sa hannu ta share, sannan ta miqe ta ce masa,
"Muje ciki na faɗa maka,"
Kamar raqumi ta riqe masa akala haka suka shiga ciki.Sai da suka zauna a bakin gado, kan ta a qasa tace masa,
"Dan Allah da son Annabi Ishaq ka yafe min dik abinda na yi maka wanda ka sani da wanda baka sani ba, ka tausaya min ka yafe min na san bana kyauta maka a gidan nan, amma inshaa Allahu daga yau zan gyara rayuwa ta, zan sake sabon zubin alkhairi a zaman mu,"
Bata bayyana masa laifin ta bane saboda ita zina zunubi ne tsakanin bawa da ubangijin shi, wajen Allah zata maida hankali ta yi ta neman gafara da afuwa har ya yafe mata,sannan ta gujewa duk wani abu da zai sa ta komawa wannan zunubin,ta kuma gyara tsakanin ta da Allah,neman yafiyar mijin nata kuma zata yi shi ne saboda ta cutar da rayuwar auren su ta yanda idan har ta faɗa masa ainahin mai ya faru to duk son da yake yi mata zai tafi,idan kuma be daina son ta ba to za su yi ta zama da zargi ne da tsana da jin haushin ta har abada wannan tabon ba zai taɓa gogewa ba a ran shi, madadin ta gyara sai ta b'ata wataqila ya qara nesanta da ita, ko ya qara aure ya kuma sanar da kishiyar ta me ta aikata abun ya zama abun gori a yi ta yaɗa maganar har yara da jikoki,wataqila ta dalilin nisantar ta da zai yi ta koma ruwa. To rufewar ba tare da ta bayyana asalin laifin nata ba ya na da nashi amfanin.
Ji yayi kamar ranar ya fara ganin ta, wani irin kyau ya ga ta qara yi masa sai ya ga qima girma da darajar ta ta qaru a idanun sa duk da bai san me ta aikata ba, saboda wanda yake neman gafara irin haka tabbas ya san ya yi laifi kuma a shirye yake da ya gyara laifin nasa,cikin murya mai nuna farin ciki ya ce mata,
"Na yafe maki kome ki ka yi min a tsahon zaman mu da ke Hauwaa komai girman shi indai zaki kasance cikin farin ciki na yafe maki, murmushin ki kawai nake son gani a yanzu,"
Ai kuwa murmushi ta fara yi na tsantsar farin ciki tare da share hawayen dake zuba mata, can ta sake saka fuskar tausayi ta na so ta yi magana ya riga ta da cewa,
"Subhanallah menene kuma?"
"Dan Allah ina son ka siyo min hijabbai dan ban da hijabi babba ko ɗaya, in zamu tafi su nake son sanyawa,"
Wata raruma ya kai mata yana sumbatarta ta ko ta ina ya na dariyar farin ciki, sakin ta yayi ya ɗauki key ɗin mota dan bai ga ta zama ba sai ya je shagon su ya buɗe sabbin hijaban da suka shigo da su, ya dakko mata iya yanda zata buqata hankalin shi zai kwanta,sai kiran shi take amma ya fita yana ta doka murmushi, murmushin da ya sa ta murmusawa itama.
Haroon ne ya fito dan aje plate ɗin shi da ya gama cin abicin safe da shi ya na ajiyewa zai fito suka haɗa ido Hauwaa, sai taji kunya da nauyin sake haɗa ido dashi, shi kuwa sauyin da ya gani a tare da ita ne kawai ya sanya shi kasa ci gaba da kafe ta da ido,a hankali ya ce mata,
"Godiya muke da abinci mai daɗi Aunty Hauwaa,"
Da sauri ta zube a kan guiwowon ta, ta fara hawayen nadama da kunyar abinda ta aikata masa a baya.
"Haroon dan Allah ka yafe min na san....."
"Shiiiii ya isa Aunty Hauwaa tashi dan Allah, tashi da sauri kafin wani ya gan ki a haka ya zaci wani abu ne na daban, ni Haroon na yafe maki ki ɗauka komai bai faru ba na goge shi a kwanya ta da zuciya ta, kema ina fatan zaki manta da komai ki riqe Allah kiji tsoron shi iyakar iyawar ki kuma ki bi mijin ki ki yi masa biyayya,"
"Nayi nadama Haroon, na tuba nabi Allah nabi ma'aiki, "
"Yauwaa Aunty naa, yanzu ki zauna kafin Yah ya dawo, kema ki fara shirya kayan tafiyar ku, ki je ni kuma zan je na dakko takardar da jiya na kasa bacci sai da na rubuta ta,wato takardar list ɗin kayan danake son a sanya a lefen matata"
Murmushi suka yi wa juna a hankali ta fara sakewa da shi, d'aki ya je ya d'akko mata list ya miqa mata, sai ta hau dubawa ta ga ya rubuta kusan komai da komai da ya kamata da kuma wanda shi yake so a sanya wa matar shi a lefen nata.
Ishaaq ne ya dawo da ledoji manya masu ɗauke da tambarin shagon su da adireshin shagon, hijabs ne manya da dogayen riguna da qananan hijabs din su, da socks sai niqab, ya baje mata su a gaban ta dariyar farin ciki ta dinga yi, ta na godiya da yi masa addu'a.
Wata leda ya d'akko sarqoqi ne a ciki guda uku, masu ɗauke da abin hannu harda sarqar qafa da zobunan su da d'ankunne daga india suke shigo da irin su.
Murna ta farayi sosai ta dinga godiya sabanin da kome zai aje mata a wulaqance take kallon shi, tinda ya gaza a gado, raini ne sosai a tsakanin su.
"Ni fa gaskiya sai an cinye abincin can, in baku cinye ba ba za ai tafiyar nan ba,"
"Tabbb ai bari ka ji daga can ma gaba mukai yaro, ba dan ka qi ba ma ai da tare da kai zamu je ka haɗa lefen ka da kan ka mu kuma mu sha honeymoon din mu da bamu yi ba ada"
Rufe fuska Hauwaa tayi ta shige d'aki tana dariya dan kuwa yanzu kunyar su take ji gaba ɗayan su kwarai da gaske, ta na tafiya Ishaq ya rungume Haroon yana murna da farin ciki tare da yi masa godiya, cikin washe baki ya ce,
"Wai qanina me ka keso na yi maka ne dan kaji daɗi kaima a duniya?"
"Ka auramin Umaimah, ka zauna da matar ka lafiya cikin so da qauna, shikenan ka biya ni,"
"Ka kuwa samu, auren ka za a yi shagali na gani na faɗa inshaa Allahu"
Haroon ne ya kai su filin jirgi bai bar wajen ba sai da jirgin su ya tashi ya koma gida cike da godiyar Allah, nan ya kira Umaimah sukai ta hirar soyayya tana ta mamakin shi, kamar ba Haroon da ta sani ba, dik sai yana bata tsoro ma wani lokacin idan ya yi magana, irin su ne ustazan da idan ka aure su ka ke shan soyayya kamar a turai.
*Tooooo ayi hakuri da wanga zuwa gobe mu leqa mutan india mu ga soyayya🙊😂*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 22:
Jirgin su na sauka a airport ɗin dake babban birnin Delhi ta india aka zo ɗaukan su a motar hotel ɗin da zasu zauna a ciki,Ishaq ya shiryawa wannan tafiya da gaske, dan haka suna gamawa da filin jirgin drivern ya loda kayan su cikin mota sai ya ɗauki hanyar hotel ɗin nasu mai suna Cartel palace wanda ke cikin garin na Delhi.
Waje ne mai kyau da ban sha'awa, iya kudin ka iya shagalin ka,daki ne madaidaici wanda ya qumshi kayan more rayuwa, Ishaaq na aje kayan shi ya sumbaci goshin ta ya fita sai tambayar shi take yi ina zashi amma sauri yake ya je ya kammala komai sannan ya nutsu ya sha amarcin da bai sha ba ada.
Kallon wajen ta tsaya yi taɓa wancan ta gama ta duba wancan haka tai tayi sai da ta kashe qyayar idon ta sannan ta yi shirin wanka, wanka tai sosai da ruwa mai zafi, ta gasa jikin ta da kyau dan ba qaramin tsami ya yi mata ba, toilete ɗin ya tsaru sosai dan haka bata san iya lokacin da ta ɗauka ba wajen gyara jikin ta da kayayyakin wanka da na gashi, sai duba sunayen abubuwan take yi dan tana sha'awar itama ta siya ta dinga gyara jikin ta dan mijin ta ya ji daɗi shima.
Wata rigar bacci ta saka mai musulmin kyau kalar kore, kun dai san Hauwaa wajen sanya qananan kaya oganniya ce dama, dan haka zan taqaita maku ince sai wanda ya ga wannan riga kawai.
Yunwa take ji amma tana tinanin ya zata yi tai magana akawo mata abincin ita bata taɓa zuwa hotel ba dan haka bata san ya ake yi ba, tinanin yanda ta gani ana yi a film tayi, dan haka kawai ta dauki salular d'akin ta danna kira, da turancin su irin na indiawa suka tambaye ta ko zasu iya taimakon ta da wani abu?
Kafin tayi magana aka qwanqwasa qofar d'akin ajiye wayar tayi ta sanya hijab domin buɗe qofar dan taga waye, tana bud'ewa taga ma'aikatan hotel din ɗauke da abinci kala-kala an turo a teburin da suke aza abinci na qarfe, matsawa ta yi suka shiga ciki suka ajiye mata, 'yan mata ne kyawawa sun saka kaya irin na indians amma kala ɗaya sun nannad'e gashin kan su sun sanya qarshen a cikin wata baqar hula hakan da ta gani ne ya bata tabbacin wannan shine uniform ɗin su kowacce da sunan ta rubuce a wani golden qarfe a gaban mayafin ta.
Murmushi suka yi mata tare da yi mata barka da zuwa hotel din Cartel palace, ajiye abincin sukai sannan suka fita.
'Ishaq'
Shine abinda zuciyarta ta raya mata dan ta tabbata shine zai bada umarnin a yi mata hakan tunda ita bata yi magana a kawo ba, bud'e abincin ta fara yi yawun ta na tsinkewa, abinci ne kala-kala masu tsinka yawu,sai juice kala uku, da babban bowl mai dauke da fuit salad, fruits din ciki wasu ma bata taba ganin irin su ba, sai shayi a wani qaramin kofi,murmushi ta yi dan kuwa da a gida ne ai sai ta kandama shi a babban kofi ta sha ta koshi.
Zama tayi akan kujerar da ke kusa da table ɗin da suka aje mata abincin, ta dauki bowl din fruit salad ta hau sha, sai da taji ta kusan qoshi ta ajiye ta tattab'a sauran abincin hamdala tayi ta jingina bayan ta a kujerar tare da lumshe ido ta ce,
"Wannan itace irin rayuwar danake mafarki kullum, da na tsaya zan zalunci kaina na kai kai na da kai na wuta da mugayen ayyuka na"
A haka bacci mai daɗi ya ɗauke ta, ta ko duqunqune kan ta saboda sanyin ACn dake ratsa ta.
Ishaaq sai da ya gama auna kayan shi zuwa gida Nija ya tabbatar komai ya kammala, sannan ya fara neman inda zai samu ɗan maganin da zai yi amfani da shi a daren duk da ma ya ga dare ya yi sosai an kusa kiran sallar asuba, kafin gobe ya je ga likita.
Wani ba'indiye ne mai kamala ya zo wucewa ta gaban shi, sai yaji kawai bari ya tambye shi wataqila ya san inda zai samu irin magungunan, da harshen turanci ya fara yi masa magana dan yawan zuwan da yake yi qasar be sa ya iya yaren su ba, sai dai da alama turancin ba'indiyen ba sosai bane, sai da Ishaq yayi da gaske sannan mutumin ya gane me yake nufi, dan kuwa qarshe ta kurame ya yi masa.
Yana ko ganowa ya washe baki, ya fara yi masa yare, Ishaaq dai kad'a kai kawai yake yanda yaga sukan yi da kai suma idan suna magana.
Jan Ishaaq yayi suka hau adaidaita sahun irin nasu suka isa wata kasuwa, wasu shagunan ma dik an rufe su saboda gabatowar asuba, wani babban shago suka shiga sai da Ishaaq yaji kunya dan ganin magungunan gyara na maza da mata birjik, mutumin yana gama nuna masa waje ya yi haramar tafiya, Ishaq ya bi shi ya ɗauki kuɗi irin nasu ya ba ma mutumin, amma yaqi Karb'a, can nesa da shagon Ishaq yaga mutumin ya nufa, da alama ko ya san wajen sosai ko dama a ta nan ɗin yake.
Yaron shagon ne ya nufo shi yana masa bayani yana nuna masa kayan wajen, A Ishaaq bai ce ba saboda jin nauyin magungunan, hamdala ya yi da Allah ya sa a wata qasar ya zo siyan irin maganin nan da kan shi ba a Nigeria ba,nan take ya dinga mamakin abokin shi da ya bashi maganin da ya sha rannan yanzu haka suke zuwa shaguna ana ganin su suna siyan waɗannan abubuwan? ganin yanda Ishaq ya yi gum ya na nuna alamun jin kunya ne ya sanya wani babba a cikin su ya taso, ya fara yi wa Ishaq bayani da turanci nan da nan suka fara ciniki Ishaq ya deb'i na ɗiba ya bar na bari, ba shi da burin da ya wuce ya kyautata mu'amalar auren shi da Hauwaa dan haka dole ya jure ya daure ya ajiye kunya a gefe a take a wajen ya sha wasu ya kora da ruwa.
Ishaq sai huɗu da rabi na dare ya koma Hotel ɗin nasu, a hankali ya bude qofar, dubawa yayi saman gadon bai ganta ba, cann saman kujera ya gan ta kwanukan abincin da ya sa akawo mata kan ya fita a barbaje a gaban ta alamar taci ta yi nak.
Murmushi yayi ya isa gaban ta ya rufe ta da bargo sannan ya yi waya dan a zo a ɗauke kwanukan sannan a taho masa da Tea da chips, dan kuwa shima yunwar yake ji sosai tinda ya fita bai ci abincin kirki ba, ba a jima ba kuwa namiji ɗaya da mace suka je.
Dik a qofa Ishaaq ya bar su suka tsaya, shi yayi ta miqa masu kayan, ya amshi wanda suka kai masa ya koma ciki.
Sai da ya sha tea ya qoshi da chips sannan ya sha ruwa ya shige toilet, wanka yayi sosai,yayi brush shima harda shinshina bakin yayi tayi ta hanyar hura iska a hannun shi ya shaqa, sannan ya dawo ya b'oye kayan da ya siyo a jakar shi, ya ɗauki na bacci ya saka.
Turarukan shi masu tsada da qamshi ya fesa, jin kan shi ya ke kamar ba shi ba,yana jin shi kamar wani sabon angon da ya yi sabuwar amarya dal a leda,duqawa yayi ya fara sosa mata kuncin ta a hankali tare da fad'in,
"Sleeping beauty a tashi haka, a tashi a yi sallah, dan na san da kyar in kinyi isha'i ki ka b'ingire,"
Bude ido tayi a hankali suka sakar ma juna murmushi, kunya kunya nauyi nauyi da wani irin sabon feelings ke mamaye da su, tashi tayi dan shiga toilet dan kuwa tana buqatar sake wanke baki tunda ta sha bacci, Ishaaq kuwa qoqari yake ya manna ta da qirjin shi, zamewa tayi da gudu ta faɗa band'akin da murmushi ya bi ta, ya zauna zaman jiran ta, daga baya ya bi bayan ta, alwala suka yi bayan ta gama brush suka koma.
"Ka dad'e gaskiya baby, ina fatan ka gama komai kamar yanda ka tsara?"
"Na kammala komai na waje kin san dake mun gama siyan komai dama amfanin zuwan dan mutum ya ga yanda komai zai tafi kamar yanda yake so ne, sannan ya sake duba quality ɗin abinda ya siya kar sai an kawo ka ga ba abinda ka siya ba aka baka,tooo yanzu tunda na gama da waje sauran aikin ciki ko?"
Murmushi suka yi wa juna sannan ta dan harare shi, tace,
"Ka yi tafiyar ka ka barni ni kaɗai ina ta jiran ka,ba dan munyi sauran sallolin mu a jirgi ba ai da tini ina zaune da salloli akai banyi ba, na rasa gabas ni kuma na kasa tambayar su,"
"Sorry my dear, muyi sallah lokaci na wucewa amma da kin sani kin yi sallar a haka saboda gudun fitar lokaci ballantana a harka ta addini ba a kunya ko jin nauyi, ga lokacin sallar asuba ma ya gabato mu jira mu yi kawai saboda kar mu makara"
Bayan sun yi sallah suka ɗora da nafila,dan kuwa Hauwaa har yanzu ji take kamar tana tattare da tarin zunubai domin bawa bai da tabbas akan ko Allah ya karb'i tuban shi, sai dai kawai ka kiyaye aikata sab'on ka kuma tsananta wajen neman gafarar Allah, sannan kayi wa Allah kyakkyawan zato.
Suna idarwa suka zauna suna addu'o'i lokacin asuba na yi suka maida sallar asubahi suna idarwa Ishaaq ya ja ta zuwa jikin shi, ya fara aika mata da saqon da yake ɗauke dashi, Hauwaa tashi tayi ta gudu zuwa kan gadon su, a tsakiyar gadon ta zauna, tare da cire jallabiyar da ta yi sallah da ita, rigar baccin da ta sanya ta bayyana, kafe shi tayi da ido da kallon so da qauna tare da shauqin son kasancewa da shi, har na samu kujera na make kawai naga duhu ya bayyana, sai hasken fitilar gefen gadon mai kalar ja, kun san idon nawa sai da gilashi kuma na manta shi a Nijaaaa, dan haka kawai na kulle idona na hau bacci, nabar Hauwaa amarya da Ishaaq tsohon hango su amarce.
Washe gari Hauwaa tashi tayi da wani irin annashuwa da annurin fuska haka ma Ishaaq, bai taba zaton rayuwar aure na da daɗi irin haka ba, bai qi ya dawwama a tare da Hauwaa ba a yanayin da suka kasance da asubar ba har qarshen rayuwar shi.
Sai wani nan nan suke da junan su, yanzu Hauwaa in Ishaaq ya ga Alif yace Baa ce itama hakan take kawai a wajen ta,sai da suka sha bacci suka qoshi sannan suka tashi suka yi wanka suka yi azahar suka fita kasuwa.
Shopping ɗin lefe Haroon da Umaimah suka fara yi basu suka gama komai ba sai sha ɗaya na dare suka koma hotel