Showing 57001 words to 60000 words out of 118783 words
same shi zaune itama sai ta buɗe ta zauna bakin nan an cuno shi gaba kamar cokali, ganin haka sai yaji kamar yace ta koma anjima ya dawo ɗaukan ta,amma inaa bazai iya ba.
Tada motar yayi yana tinanin yanda yau zai lallab'a ta ko ya sha jaraba.
Ko da suka isa gida ma haka tai ta turo baki, kuɗi ya zaro dubu uku ya miqa mata ya ce,
"Ga sauran canjin katifa a sa a susu,"
Washe baki tayi nan tafara yi masa shagwab'a,shi kuma ya yi ta bata hakuri kamar ya yi mata laifi, duk abin alkhairin da ya yi mata da iyayen ta bata san ta buɗe baki ta yi godiya ba qarshe ma sai da ya bata cin hancin dubu uku ta baje baki ta na yi masa bayanin kud'ad'en da take tara wa,in ta saka wannan dubu ukun da ya bata tana lissafi ta sa ya kusan dubu talatin da wani abu kenan, Umar yayi mamakin yanda aka yi kud'in ya kai haka amma sai ya basar, sam bai taɓa kula da ɗauke-d'auken da take yi masa ba,tsabar iya taku wajen sibaren na bayye, in ta ɗauka baya taɓa gane ta zara.
***********************
Jameelaa fa yau kwanan ta biyu tana naquda a tsaitsaye dik ta fige tayi zuru zuru tsabar wahala, sai zuwa duba ta ake yi kamar wadda ta riga ta haihun, kowa hankalin shi ya tashi da yanayin da take ciki cikin ya yi girma da yawa gashi haihuwar fari, umar ya kasa ya tsare da shi ake yin komai watarana idan yaga ta na shan wahala zama yake yi ya yi ta kuka kamar ba likita ba,a rana ta uku ne midwife ɗin da Mum ta roqa a asibitin su tazo duba Jameelah anan ne ta yi masu albishir ɗin ta kusan haihuwa inshaa Allahu, ai kuwa nan ta sa Umar dole ya fita, dik da yaso ayi komai da shi tinda shi likitan mata ne, raunin sa akan Jameelan ne ya sanya Mum saka baki a lamarin dan haka ganin Mum na wajen ya sa yaji nauyi ya fita ɗin kamar yanda aka buqata, Mum ma a parlour ta zauna duk da cewa itama cikakkiyar Nurse ce amma ta kasa shiga, ta gan su sau ɗaya a halin da bai kamata ta gan su ba dan haka ba zata sake maimaita wannan gangancin ba ,Ramai kuwa tunda ta zo gidan take ta doka tagumi daga wannan bangaren zuwa wancan , ta kasa ta tsare tace ba mai kai mata yarinya asibiti, ta sha gani a layin su in an kai mace asibiti suna dawowa da qorafe-qorafen midwifes, musamman akan farke ma mata gaban su da suke ba tausayi dan su huta da jiran mai haihuwa, ba zata yarda Jameelaa ta rasa jarin ta ba ah atoh, ranar Mum taga jahilci tsabar shi a waje Ramai, dan kuwa dik bayanin da ake wa Ramai baya shiga kunnen ta, har mamaki ta dinga yi a ranta ta na ayyana ashe dama jahila ce mahaifiyar Jameelaa ,tinda har wa'azi ta yi mata akan maganganun da ta dinga furtawa dik akan haihuwar amma ko ratsa ta basu yi ba.
Suna nan zaune suka ji ihun Jameelaa tare da kukan Baby mai qarfi ya daki kunnuwan su a lokaci ɗaya ,nan take Umar ya zube dan yin sujjadar godiya ga Allah.
Yana dagowa kuwa ya afka dakin, Jameelaa na kwance...
*My FiFul barka-barka Jamcy kala ta haihu*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 24:
Zuwan su ke da wuya Jameelaah taga motocin kai amarya na qoqarin tafiya kuma idan ta fita ba zata samu shiga ba dan babu mai jiran ta tinda basu san da ita ba, kwab'e fuska tayi zata yi kuka, Umar kuwa na ganin motocin sun tafi ya kalli Jameelah ya ga zata yi masa kuka sai ya juya motar shi suka bi bayan motocin kai amarya, ai kuwa cike da murna ta zabaro masa wuya ta manna masa kiss a kuncin shi, murmushi yayi dan ganin ya burge ta.
"My love akwai ki da rigima,sai ki dinga abu kamar wata yarinyar goye,"
"Ni ce me rigima kooo?"
Ta faɗi hakan cike da shagwab'a,a wajen Umar hakan ma wani abun burge wa ne daga wajen Jameelar shi, sai ya ga ta qara yi mishi kyau, kad'a kai yayi ya d'age hannayen shi daga kan motar tare da zaro ido waje ya ce,
"Nii na isa nace dake nake?"
Dariya suka yi atare suna ta hirar su gwanin sha'awa ,Umar kuwa ya qi barin ko wacce mota ta shiga tsakanin motar su da ta ɗaukan amarya, a ran shi kuwa yana ta ayyana,
' Yau dai ga yayan kwabo an samu a gari da shi za a kai qanwar shi d'akin miji.'
Ko da suka isa qarfe shida na yamma yayi, cike da kid'a sauran motocin suka tsaya aka buɗe kowa ta fito,amma motar da amarya ke ciki ba a kunna kid'a ba dan kuwa tace bata so, albarkar aure take nema ba tab'ewar shi ba.
Sai da aka fara shigar da ita wajen aunty Hauwaa aka gabatar da ita tare da yi masu nasiha akan zaman tare da hakuri da juna,a nan 'yan uwan Mum da Dad suka miqa ta amana wajen Aunty Hauwaa, Aunty Hauwaa kuwa wadda bakin ta yaqi rufuwa saboda murna sai maimaita fad'in,
"Na Karb'a, na Karb'a da babban hannu,da hannu bibbiyu ya Allah ka taya ni riqewa da gaskiya da amana," take yi.
"Ameen ya Allah," mutanen wajen suka amsa.
Nan aka rankaya har aunty Hauwaan zuwa gidan Amarya,Amarya Umaimah kuwa na cikin mayafi tana kuka Jameelaah ta kutsa cikin mutane ta na so ta isa wajen ta ganin ta ɗauke da ciki ya sa mutane suka dinga bata waje, dan kuwa har wani sake turo shi gaba take yi,dangin Mum da basu san ta bane suka fara kallon isa da mallaka irin na Jameelaa.
Wata daga qannen Daddy ce tace ai matar Umar ce wannan,nan wasu suka washe baki aka hau gaggaisawa, wasu kuma suka d'aure fuska, a ganin farko suka gano bata da mutunci, gaida su ta hau yi tare da qoqarin durqusawa amma suka hana ta, a cewar su sun yafe durquson, bata kusa da Umaimah suka yi aka qarasa shigewa da ita gidan na ta,
Karatun qur'anin da aka saka ne tin kwana da kwanaki ke ta tashi, dan kuwa Haroon da Ishaaq sun ce gidan na buqatar karatun da wasu addu'o'in ma duba da cewar gidan yayi shekara da shemaru a rufe ba a san meke zaune a ciki ba.
Jameelaah sai walqita ido take yi dan ganin ta inda zata ga abokan ango sun bayyana tana ta washe baki,Umaimah ce ta ja ta kusa da ita sosai ta yi mata rad'a,
"Ya jikin Baba? Mum tace bai ji daɗi ba? Ya naki jikin,"
"Da sauqi dika sai da na tabbatar likita ya kula da shi na taho,yanzu ke ba lokacin tambaya bane banga angwayen ba fa Ina suke ne?"
"Ni ina zan sani? Ki daina yi min maganar angwaye gabana faɗuwa yake yi,"
Dariyar yaqe tayi kawai ta ci gaba da zaro idanuwa waje,cikin ran ta ta ce,
'Akan me zan daina zancen angwaye in basu wa zai bamu kud'in siyan baki gashi na ji an ce masu kuɗi ne? Kenan zuwa na ya tashi a banza?'
Qawayen su na islamiyya ne suka iso, suna ta yafito Jameelaah dan an ce kar ai hayaniya tinda an saka karatun qur'ani,sai dai an rage volume sosai, ta na ganin su ta ɗauke kai ta qi zuwa,kallon marasa hankali ma take yi musu dan kuwa a ganin ta ta kere musu nesa ba kusa ba amma suke abu kamar makafi,ganin ta qi kula su ne ya sanya suma suka ɗauke kai suka share ta.
Zama suka yi suka yi da'ira a tsakiyar parlourn, nan da nan suka fara karanta qur'ani daga bakunan su cikin suratul Rahman, basu tsaya ba sai da suka yi shafi biyu, sannan qanwar Hauwaa mai suna Safnah ta fara yin addu'u'o'i masu matuqar ratsa zuqata saboda da hausa take yin su, tana nema wa ango da amarya zaman lafiya da kwanciyar hankali, da zuri'a d'ayyiba,sannan Safiyya ta amshe itama ta fara zubo kalar nata addu'o'in kusan kowa dai a wajen sai da ya yi masu addu'a sai abun ya basu sha'awa su kan su,Jameelaa ta kula sun maida gidan kai amaryar islamiyya, ana zuwa kan ta tace,
"Allah ya bada zaman lafiya ya kawo qazantar daki,"
Ta ja baki ta gume shi gum dan ita bata ga amfanin waɗannan abubuwan ba gidan kai amarya an maida shi kamar wata islamiyya meye hakan?ai kyawun ta a baza masu kid'a irin na soyayyar nan me ratsa zuciya amma sun wani tsaya karatu kamar qauyawa ta na can ta na zancen zuci bata ma san kowa a wajen ya bi ta da kallo ba, saboda a qalla kowa yayi addu'ar da tafi haka balle ita babbar qawar amarya, kiraye-kirayen sallar magrib aka fara yi, nan 'yan uwa da qawayen Umaimah su kai ta yi mata Allah ya sanya alkhairi suka hau fita dan tafiya gida ,sai d'akin ya zama daga Jameelaa sai Safnah da Safiyya da kuma amaryar, Umaimah ta ɗan saba da su dan tin da aka fara bikin sun haɗu ya fi sau biyu dan haka da ta ga zasu fita sai tace da su,
"Dan Allah kar ku barni ni ɗaya mana,"
Cannn dai Safiyya tace bari muje muyi sallah zamu dawo in mijin ki bai shigo ba kenan, dariya suke tayi qasa-qasa dan sun shirya guduwa ne dama.
Safiyya ce ta fara fita sai da Safna zata fita ta gane wayo suke son yi mata, da gudu Safnah ta amshe mayafin ta ta fita tana dariya, riga da skirt ne jikin ta sun amshi jikin ta sosai saboda safna akwai ta da diri mai kyau, ɗan acuci mazan ta da ta yi da gashin ta mai uban yawa ba tsaho ya qarawa d'aurin d'ankwalin ta kyau, tafe take tana ɗan gudu tana dariya suka ci karo da Umar dake jingine a bakin motar shi ya b'ata rai ganin yanda 'Yan matan wajen ke ta kallon shi suna qusqus, yana nan kafe kamar an kafa shi yana jiran hajiyar tashi ta fito su tafi,dan kuwa tunda ta shiga yake zaman jiran ta sallah kawai yayi ya dawo ,a tsayen yake ta azkar din shi.
Bata kula da tsaiwar shi a wajen ba sai ji tayi ta bangaje mutum, da sauri ta juya dan bashi hakuri, sai taga yana yi mata kama da Umaimah sosai, sai ta rage dariyar da take yi tace,
"Dan Allah kai Yayan umaimah ne?"
Cikin d'aure fuska Umar ya ce mata,
"Eh ni yayan ta ne meye?"
Sai kawai ta ja mayafin ta da ya zame tin a gidan Umaimah ta qarasa yafe jikin ta da shi sannan tace,
"Ga qanwar ka can tana yi ma mutane kuka dan an kawo ta gidan miji bayan ita tace tana so,ka shiga ka bata hakuri ko taa sako maka matar ka, dan kuwa tana can ta qanqame ta ta hana ta fita,"
Kawai sai ya fara dariya ya san halin Umaimah sarai da shagwab'a, girgiza kai kawai yayi ya na dariyar shima can qasan ran shi kuwa tausayin qanwar tashi ne fal ran shi a hankali ya ce,
"Yanzu in banda abinki baiwar Allah ina ni ina shiga gidan surukai? Zata fito ne na san Jameelaah da ta gaza hakuri zata mata wayo ta gudo,"
"Ashe ma baka san Umaimah ba har yanzu, a iya ganin da na mata na gano wayo ne da ita itama,ko yanzu da kyar na kwaci kai na plan muka haɗa na guduwa amma Safiyya na fita ta gano mu ta damqe ni da kyar na kwace na gudo,"
Daga haka fa Safnah da Umar sukai ta hira, daga baya tace ta shiga ciki bata yi sallah ba sai watarana.
A cikin hirar su ne ya ji cewar ita ɗin qanwar matar wan mijin Umaimah ce sun zo bikin ne suma, amma tana makaranta a Zari'a tana karantar mass com.
Umar yana tsaye yana ta murmushin hirar su da Safnah Jameelaa ta fito, lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar isha'i ranta a mugun b'ace ta taddashi,ba ango ba abokan ango ba alamar ma za ta ga ango a wannan lokacin,sam ba haka suke biki ba su a cikin gari,ta yaya za a kawo maka amarya tin biyar na yamma har takwas na dare amma baka zo ba to sai yaushe za ka zo?
(An yi karatun qur'ani ta ce su qauyawa ne amma an zo bangaren kuɗi ta ce su ba haka suke yi ba a cikin gari,komai dama akwai lokaci na musamman da aka qirqire shi)
Ga wata muguwar yunwa da take ji har ta na jin kamar za ta yi amai saboda rabon ta da abincin kirki tin safe, sai uban ruwa da tai ta d'irka da Lacasera.
"Muje gida"
Ta ce masa ta na hura hanci ta na b'ata rai kamar zata kai masa duka, umar kuwa da sauri ya kalle ta ya ce,
"Gida ko asibiti?"
"Ni ka kai ni dik inda zan samu abinci yunwa nake ji marowatan banza kawai ku tara mutane amma ko wannan shegiya shinkafa babu balle mutum ya saka ran samun nama ko wani abu makamancin hakan,"
Ta qarasa maganar cikin datse haqorin ta dan haka baiji me ta ce ba, kawai dai ya ga tana b'ata rai ta zauna a kujerar me zaman banza (as she is) ta na qunquni.
Gidan Mum ya ɗauki hanya zai kai ta ya san a can za ta ci abinci kuma ko Allah ya sanya alkhairi ta yi musu duba da cewar tinda aka fara bikin bata je ba, bata yi masa musa ba amma ta d'aure fuskar nan kamar hadari, suna isa suka tarar da gate a bude yake, sa kan motar yayi ciki ya parker suka shiga riqe yake da jakar ta da abun ruwan ta dan kuwa ta yi gaba a yunwace take, suna shiga kowa ya bisu da kallo, cikin sauri ta zauna yaraf tana maida numfashi, ganin kallon da ake yi mata ne ya sa ta wayance ta ce,
"Yau na ga shagwab'ar Autan Mum, Mum Kinga yanda Umaimah ta dinga kuka kuwa tana qanqame ni dik jikina ciwo yake yi sosai, ga yunwa da nake ji, da kyar na k'waci kaina na taho,"
Dariya sosai wasu suka hau yi ana maida zance kowa na fad'in abinda ya gani da abinda ya faru, wata daga cikin qannen Mum ce tace,
"Ai gwanda kukan ta akan naki fa Jameelahh ke da ki kai ta kuka kamar zaki shid'e sanda za a kawo ki?"
Rufe fuska ta yi alamar wai kunya take ji, Mum ce ta shigar mata tace,
"Kinga rabu da su taso muje ki ci abincin ki kin ji 'yar albarkan Mum,"
Da kyar ta bi bayan Mum ita a dole wai kunya take ji, kitchen suka je da Mum sai da ta zaɓi abinci tsabar gashi nan kala-kala anan kitchen ɗin aka zuba mata taci ta yi nak,sannan tace zata wuce asibiti daga nan ta ga Baban ta a kunyace tace,
"Mum yah Umar fa shima yunwa yake ji bai ci abinci ba tun da safe da muka baro gida,"
Murmushi Mum tayi tace,
"Ai muna parlour ana hirar nan ya shiga ya d'iba ya wuce d'aki, bari na zuba maki ki kai asibitin ki gaida mai jiki idan kun je gobe inshaa Allahu zan shigo, sai na duba shi,"
"Allah ya kaimu Mum, ai da kin bari naje gida na yi masu girki tinda naga kamar akwai baqi sosai kar na kwashe kuma yazo bai isa ba,"
Mum bata kula ta ba ta ci gaba da ɗebar mata abincin dan kuwa tana cike da fara'a da jin daɗin samun suruka mai kirki a ran ta,haka ta loda ma Jameelaa abinci,naman da ta zuba mata kuwa kala-kala, akwai na rago, na sa, dana kaza, sannan da miyar masa da aka yi da kayan ciki na rago, Jameelaa tunani take yi yanda zata rage abincin taje da shi gida, saboda ba sai tayi girki ba washegari,in ta sa a fridge sai ta dumama masu kawai su ci, (wannan zarmewa taki na ban mamaki Jameelaa, komai akai maki na gaba kike hangowa, Allah ya shirya ki).
Mum kamar ta shiga ran ta sai ta d'ebi wani a leda ta saka mata tace,
"Kar ki manta da wannan da kunje gida ki sa a fridge,kin ji ko? gobe da safe kin huta da girki,"
"Mum dik kin kwashe mana ai, mun gode to Allah ya qara girma, ba dan kin matsa ba ma ba zan Karb'a ba, amma tinda kin matsa bari na Karb'a abinda babba ya hango yaro ba zai hango ba,"
Mum shiru dai tayi amma ita yaushe ta matsa? Sai da Umar ya taya ta d'iban abincin suka fito za su tafi sai sallama take yi wa mutane, Mum ke ma matan wajen bayani mahaifin ta ne ba lafiya yana asibiti, nan suka fara yi mata ya mai jiki, dan da sun zaci iskanci ne ya sa tin da aka fara bikin bata halarta ba.
A hanya sai tinani take yi shin ko bayan tafiyar su Haroon yaje da abokai an ba Umaimah kud'in siyan bakin ko yaya oho?
Haka suka isa asibiti Baba ya farka ba ko na abinci suna nan zaune, Ramai da ta je dan kwana da shi tana sane taqi badawa a siyo, saboda so take surukin nata ya ga tsananin babun da suke ciki,
Ai kuwa Umar daya ga haka sai yaga bai kyauta ba sam, shi yana cikin yalwa da iyalin shi wadda take 'yar su ce amma iyayen ta na cikin matsatsin rayuwa.
Alqawarin sauya masu wannan rayuwar da ya gani da abinda Allah ya hore masa ya dauka a ran shi.
***********************
Umaimah na ganin ba kowa kuma magrib da isha'i sun wuce ta bata yi ba, kawai sai ta tashi ta rufe d'akin da key ta shiga band'akin dake cikin d'akin ta yi alwala, band'akin ya haɗu sosai dan bata zaci ma zata samu kamar hakan ba,gashi komai tsaf a jere, ga kayan wanka da gani daga waje aka kawo su saboda haɗuwar su kawai ta isa ta sanar da mutum hakan,kayan wanke baki ta hango kala-kala masu kyau ai kuwa bata b'ata lokaci ba wajen wanke bakin ta tsaff sannan ta fita.
Sallah ta yi tana addu'a taji ana murd'a qofar,