Showing 78001 words to 81000 words out of 118783 words

Chapter 27 - MAZAUNA GIDA COMPLETE By HAERMEEBRAEH.txt

26 Oct 2025

626

tsoron Allah, maza masu kuɗi kuna sakewa matan ku su ci arziqin ku, matan ku sune abokan rayuwar ku, masu tara haram ma dan matan su suji daɗi da yaran su suke yi balle kai me tara halal? K akashe kud'in ka ta halal ka more rayuwar duniya da lahira, dan in ka kashe ma mace kud'in ka wallahi at the end kai zaka mora dan kai za ai wa qunshi, kitso, siyan kayan kwalliya, siyan turare, yi ma yaran ka siyayya, rage maka cefane mata muna da tausayi, rashin ganewar ku ne maza yasa kuke mana dik abinda kuke so mara kyau wai dan tsare gida , ka sake zuciyar ka ma mace kaga yanda zata maida kai ɗan lele, sai dai in kaga mace na mugun abu to yar uwar Jameelaa ce,kuma Ramai ita ce maman ta,sannan mata masu karb'ar kuɗi a wajen mazan su dan mazan sun sauke buqatar su ta sha'awa a wajen su su sani da su da karuwai na kan titi 'yan gudu ibinin (Good evening) basu da banbanci.

Washe gari Jameelaa ta yi ma Ramai waya akan ta aika Bukar ai kuwa kamar wanda take jira, ta katse wayar ta yi wa Baban Jameelaa qarya da cewa,

"Malam Jameelaa ke kira na naji Humairah na ta tsala kuka, wai sun rasa me ke damun ta magani anyi har na asibiti, shine nace bari naje na gwada na gida,"

Ko d'ago kai Malam Jameel bai yi ba ya ci gaba da yankan farcen hannun sa ya ce,

"Yaushe kika zama mai bada maganin gargajiya banda labari Ramai? Da alama kin manta da wayar ki ana iya jiyo qarar mai magana dake tsabar qure mata sauti da ku kai , to ba inda zaki je ki aika Bukar kamar yanda tace ko kuma ki fita ba da izini na ba kamar yanda kika saba,dana gama yanke farce na zan fita anjima zan aiko a kawo cefane, na ga kamar kayan miya sun qare"

Cikin jin haushin shi ta amsa da,

"A had'o da nama dai ah toh,"

"Inshaa Allahu za a had'o da shi kuma a daina yi wa jika ta qaryar ciwo irin wannan bana so,"


"Anyi din"

Ta furta a hankali,

"Na'am magana ki ke?"

"Ince me?😏"

Murmushi yayi ya ajiye rezar a saman window ya fita, ya kula har yanzu matar tashi na da halin yara, ji yanda take wani kumbura dan ya yi mata faɗa kuma ya hana ta fita.

Bata da zaɓin daya wuce na ta aika Bukar ɗin, dan haka ta faɗa d'akin ta dan ta dan jira ya kammala shirin makaranta ta sanar da shi,in an tashi daga makaranta ya je ya ji meye kiran Jameelaan,

Tana nan zaune bacci ya kwashe ta sai zabga munshari take yi Bukar kuwa da yaga tana bacci ya wuce makaranta abun shi, kamar wadda aka maka wa duka haka ta miqe ta hau kiran Bukar, jin shiru ya sa ta sanya mayafi ta rufe gidan ta sa kai zata je gidan Jameelaah da kan ta.

Surutu take ta yi ita ɗaya a hanya, akan bari tai sauri ta koma kan wancan jarababben ya koma yaga bata gida,fakam fakam fakam take tafiya cikin sauri,har ta yi nisa sosai tana tafiya amma babu abin hawa, kamar daga sama taji an kwashe ta an watsar a qasa a gefen hanya, wasu matasa ne a kan babur sun yo goyon biyu su na ta yi mata magana dan ba horn a babur ɗin nasu ga qarar babur ga ihun da suke mata amma tana can tana tinanin gidan Jameelaa me za a samu ya sa bata ji su ba har sai da suka iso suka rasa yanda za su yi su kauce mata, qarshe dai suka kwasa ta a saman hanya.

A kan qafar ta ta hagu Ramai ta cake ai kuwa nan take ta samu tsagewar qashi,tini ta zube a wajen sumammiya, mutane an taru a kan ta wanda suka buge ta kuwa sun gudu abin su.

An duba ta tsaf ba a samu waya ko wani abu da zai nuna daga ina take ba, sabuwar unguwa suke balle a ce wani ya san ta, qafa tayi tsami ta fara kumbura mutane sai video ake yi mata, wasu sun fara rubutun qarya akan videon ta da pictures da suka ɗauka suna turawa social net kamar su facebook, instagram, whatsapp da sauran su, kowa da kalar labarin da yake qirqira akan ta, amma ba masu daɗi bane kaff labaran, an rasa mai taimakawa koda farfadowa ne a samu ma tayi.

Wani bawan Allah ne ya kutsa ya hau tura mutane baya yana masifa,

"Meke damun ku ne mutanen wannan zamani ? Kun manta da taimako Allah Allah kuke ayi wani abun ku fara qirqirar qarya kuna yaɗawa, yanzu da kuka d'au hotuna da video shine abinda tafi buqata? Ba mai qoqarin kaita asibiti, dubi qafar ta yanda ta kumbura, yanzu da kun tura social net wasu masu qaramin tunanin zasu yi ta sharing, wanda in da wani abun alkhairi aka rubuta da zai amfani al'ummar annabi ba za a yi sharing ba, sai labaran batsa, da videos na batsa, da labarai masu saka shubuha da masu fidda mutum a musulunci ma dika kuji tsoron Allah fa tamm"

"Kaii kama min ita mu kaita asibiti daga can sai mu bada cigiyar 'yan uwan ta,"

"Haka kuwa aka yi nan aka sanya ta a motar bawan Allahn nan ya tuqa suka tafi basu tsaya a ko ina ba sai a asibiti, accident and emergency aka shige da ita nan take likita da nurses suka fara bata taimakon gaggawa da sun ce sai an kawo police, mutumin yace indai basu kula da ita ba ta mutu shi kuma zai maka su kotu.

Yana ganin sun amshe ta ya koma gefe ya jira a waje yana hoping ta tashi ta fada masa ita wace ce? a ina take?........







*Hummmm wanda bai ji bari ba zai ji hoho ai, Allah gwai inji Kabawa😂*
[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻














WRITTEN BY HAERMEEBRAERH










PAGE 33












Mum ce zaune a parlour ita da Umaimah wadda ta kai wa iyayen nata ziyara,suke tattauna wa game da halin Jameelaa.

"Umaimah ni fa halayen qawar ki gaba ɗaya sun sauya, rabon ta da ta zo  gidanan har na manta,an ce masu Daddyn ku ba lafiya, Umar yazo yafi sau huɗu amma ita bata zo ba, nima nayi ciwo ko aiki bana zuwa amma yarinyar nan bata zo dubani ba, da na ji sauqi naje dan na ga lafiya suke ko fitowa daga d'aki batai ba, sai da na gaji da zama na tafi, sannan ta min waya wai tana toilet ne, can u imagen, tana toilet for over an hour kenan? Habaa ai dai mai motsuwar kai ma ba zai ɗauka ba balle ni, abinda ya fi ban mamaki jiya na je gidan Kulu ta kawon lemon abarba da suke yi su aje a fridge wai yarinyar nan take tambayar kulu dika ta juyo min? Kulu tace ah ah ba dika bane, sai kulu tace ai yana nan cike da jarka babba.

Yau ko dika aka juyo min kuma bata sha ba ai a gani na bai kamata ta yi magana akai ba, kuma tana gama maganar ta shige d'aki ta kwanta tana wasa da yarinya, sai da na gaji da zama bata fito ba na yima kulu sallama na wuce, dan bana son na kai lokacin dawowar Umar ya ji me tamin na haddasa masu rikici,"


"Hummm Mum ko Malam ma haka yace Jameelah fuska biyu gare ta mune bamu gane ta ba har yanzu, tana da munanan halaye wanda sai mai wayo ne zai gane tana dasu,  nima wataran na kan fuskanci wasu abubuwan a tattare da itan na rashin kyautawa, ga qazantar tsiya, ki duba ki ga lokacin da tana ita ɗaya yanda gidan yake, yanzu da kulu tazo ne aka samu sauqi,amma d'akin baccin su ko dawasa yanda kike da tsafta ba zaki iya shiga ki jima ba,"


"To ubangiji ya ganar da mu abinda bamu da ilimi akai,ya kawo mana mafita mafi alkhairi,"

"Mum bari na zo na koma,Malam yace daga kasuwa zai wuce gida, basu da makaranta,gashi har yamma tayi ban kula bama"


"Ya kamata ki koma kam,Allah ya maku albarka, ya sauke ki lafiya,"

"Mummmm, ni dai ban da komai, dan Allah ki daina min irin wannan maganar,"

"Kinji da gulmar ki,muje na raka ki,"

"Mum sammin dambun nama da dadaddawa, in kina da kuka a ɗebar min, ina son na yi tuwo yau,"


"Muje kitchen din, sai na d'eba maki"

Komai data lissafa sai da Mum ta d'ibar mata, harda wanda ma bata ce ba driver ya maida ta gidan ta.

Haroon ne ke kitchen yana tuqa masu tuwon semo ta yi sallama ta shiga, dariya ta fashe dashi ganin yadda dik ya zubar da garin a qasa, gashi ya shafa wani a gemun shi, sannu da aiki ta yi masa ya maqale kafad'a ya buɗe mata hannayen shi, zuwa tayi ta kwanta a jikin shi, ya maida hannayen shi ya rufe, sannan ya yi mata kiss a wuyan ta lumshe ido tayi, tace

"Bari na je na rage kayan jiki na sai na zo mu qarasa girkin tare, da baka wahal da kan ka ba ma babe tinda ga abinci nan na aje maka,"


"Duba ki ga na tashi da shi tsaf, yau ai a gajiye na dawo kuma da yunwa, kuma na ga ya kamata na taya ki ne, tinda kina yin tuwon nan kullum, na rasa me kike ji a cikin tuwo sam baki gajiya da shi,"


"Hummm ba zaka gane ba na ma samo kuka da daddawa harda kub'ewa busasshiya, yau ba miyar taushe zan mana ba miyar yauqi zan yi,"

"Me ciki,"

"Ni dai bana so, ka daina kirana haka, wani in yaji sai a ce min 'yar....."

"Yar me?"

"Immm 'yarr...immm shikenan ina zuwa,"

"Zo nan ba inda zaki je sai kin faɗi me za a kira ki da shi,"

Matse ta yayi a jikin shi tare da daga mata kai tana kallon shi can ta sauke idon ta tana murmushi tace,

"Ɗan sake ni na fada maka ka matse ni da yawa zafi na ke ji,"

Sassauta mata riqon yayi, ai kuwa ta balle ta ruga daki da gudu tana dariya,

"Zan kama ki ne zaki qarasa me za a kira ki dashi,"

Juyawa yayi ya fara kwashe tuwon dan yayi ba shi da yawa, a leda ya daure ya kashe gas ya fita, bai ɗauke komai ba a wajen ya bar su, sai da ta kammala sauya kaya da wata guntuwar riga mai faɗi daga qasa, daga sama ta kama ta, armless ce rigar kalar baqi da flowrs jajaye, ta saka hula baqa a kan ta.

Gyara kitchen ɗin tayi ta zubawa tukunyar ruwa, ta aje a cikin sink, ta ci gaba da haɗa miyar ta tana yi suna hira, shi kuma yana ta mata wasanni, sai kauce wa take amma yaqi barin ta tayi aikin ta da dad'in rai.

Sallamar Sapnah ce ta dawo da shi nutsuwar shi ya shige d'aki ya yi zaman shi.

"Oyoyoooo Sapnah saukar yaushe? Ba ko waya na tanadar maki abun daɗi?"


"Kar ki damu ai gani a yi abun daɗin a gabana naci, me kike yi ne haka, nake ta jin qamshin girkin tsoffi?"

"Tuwo nake yi ya karatu?"

"Ahhh lallai zamu ci daɗi ashe...karatu sai godiya, mun kammala shi alhamdulillahi yanzu sauran mu jira Allah ya kawo mana miji muyi aure, dan kuwa Abban mu yace sai munyi aure zamu fara aiki,"

"Masha Allahu, Allah ya taimaka gaskiya na taya ki murna, nima Malam yace inshaa Allahu zan ci gaba da karatu, har sai na ce ya isheni, ina son karatu sosai Sapna,"

"Yauwa dakata wai dan Allah meye na cewa mijin ki malam? Ki waye mana, ko ɗan sunan zamanin nan ke baki sa masa ba sai wani malam, kamar a makarantar allo, ko bokon yanzu an daina cewa Malam,"

"Baki da dama Sapnah, Allah ya nuna min mijin ki, na san zai sha gata da tarairaya da kulawa,kuma ni ba Malam nake kiran shi ba ni da shi, a gaban mutane ne nake cewa Malam kawai"

"Kwarai da gaske, dan kuwa inna auri mijin da ya iya soyayya shima sai mun fi Lailah majnun soyewa,"

Dariya suka yi a tare sannan suka tafa,haka sukai ta hira suna qarasa aiki, dan Umaimah ta qara samun wayewa ta zamani tunda ta kula Sapnah na da ita sai ta ce mata,

"To yanzu dan Allah bayan Baby wanne suna kike ganin zan dinga kiran shi da shi?"

"Ai shi miji ba dole sai suna ɗaya ake kiran shi da shi ba, ya danganta da yanayin da kuke ciki ne kawai,kawai dai ana son ki riqe suna ɗaya da in kin faɗa ko a gaban waye an san shi kike nufi,amma ke da shi ki dinga faɗa masa dik kala-kalan suna masu daɗi da ki ka sani, ki dinga la'akari da yanayin da kuke ciki ke da shi, in kina shagwab'a kina kiran shi da suna kamar Sweet one,zaunjee, mineeee, in kin zo qarshen kina ja cikin shagwab'ar, in ko miji ne ke maki shagwab'a, kina kiran shi da Baby, ko My baby, ko mine, su kuma irin su sweetheart, ko my dear, My love da honey, su misalin sunaye ne da zaki iya kiran shi da shi a ko ina Kuma a koda yaushe.

Sannan akwai sunayen da in yana maki abu mai daɗi zaki dinga fad'in su, da yaren da kuke magana dan yafi shigar shi, ke ni fa na matsu nai aure na fara gabatar da dik wani ilimin gidan miji dana sani, nan da kika ganni practical ne kawai ban ba amma komai na sani akai na"

"Ohhh ni Umaimah na shiga uku, 'yan matan yanzu sai su tsorata ka "

"Dalla rufen baki ban girme ki ba? Amma kike a dakin miji har da result ɗin abinda kuke yi a d'aki, ke yanzu yarinyar primary ma ta san komai balle ni dana gama Jami'a"

"Haka ne kuma, Allah dai ya tsare mana imanin mu,"

"Ameen... ina mijin naki, ko bai dawo daga makaranta ba?"


"Yana d'aki ai ya dawo yau ko makarantar ma be je ba,"

Cike da jin kunya Sapnah ta ce,

"Innalillahi Umaimah kin kashe ni, shine baki faɗan ba nake ta zuba kamar kanya? Ba zan sake shigowa wajen ki ba,tinda ni dai bakina baya iya shiru, sai anjima mun b'ata dake,"

"Dan Allah ki yi hakuri ki zo kici kayan daɗin nan,"

"Ke wasa nake maki a qoshe nake, ki ci abinki ki qoshi, dambun naman kawai zaki debar min na wice gida,"

"Ba dai gida zaki koma ba,"

"Ah ah ina nan sai aunty ta haihu, na ga yau ma tin da ta tashi sai yatsina take,anya ba ta fara naquda ba a tsaitsaye?"


"Anyaa? ni dai ɗazu dana shiga normal na gan ta,"

"Aiko yanzu ta sauya kinga bani na tafi, dan ba zan so haɗuwa da mijin ki yau ba, kullum sai ya kama ni ina shegen surutuna da bana gajiya"


Dariya suka yi tayi umaimah ta d'eba mata dambun naman ta tafi.

Dakin ta ta shiga wanda a da shine d'akin Haroon, kwantawa tayi ta lumshe idon ta ganin Umaimah da hira da ita ya sanyaya mata zuciyar ta, dik da yayan ta taso gani ba ita ba, amma ta danji daɗin ranta.


***********************



Sadeeq mahaifan shi sun aura masa wata bazawara dake maqotaka da gidan su yarinya ce shakaf sakin wawa, yarinyar akwai nutsuwa da hankali sosai, ga ta da kamun kai da tawakkali hakurin ta shi ke sa Sadeeq sake mata fuska, saboda har yanzu soyayyar Mamalo na nan a danqare a ran shi, sai ma kewar ta da yake ji a kullum na qaruwa, yarinyar bata damuwa, dan wataran ma mantawa yake da sunan ta ya kira ta da Fateema haka zata amsa ta masa abinda yake so, a hankali kunyar ta ta fara shigar shi, tin baya damuwa dan ya kira ta da sunan mamalo har ya fara jin nauyin ta, zaune suke cikin girmama juna har yau ba abinda ya shiga tsakanin su na auratayya, saboda ba shi da sha'awar kowacce mace in ba Mamalo ba.

(Muje zuwa zama ka ware ne d'annan, indai mace ce ).






**********************

Hauwa ke ta naquda dik ta jiga ta tsabar tausayi ya sa Sapnah kuka, dik fuskar ta yayi jawur, dik surutun ta kamar an dinke mata baki a ranar, addu'a kawai take Allah ya sauki yayar ta ta lafiya,midwife din da ke karb'ar haihuwar Hauwaa ce ta fito ta same su a bakin d'akin da aka shigar da ita, tace ma Ishaaq ya miqo kayan haihuwar da suka zo da shi ta kusa yanzu kam.


Jiki na rawa ya tafi inda sukai parking ya d'akko kayan kafin ya dawo har ta haihu, yana isowa yaga Sapnah na dariya hawaye na bin fuskar ta cikin wani irin yanayi ya ce,

"Sapnah lafiya?"

"Yaya ta haihu lafiya kai ake jira ta sauka, sunqi sanar dani me aka samu sai dariya suke yi min"

"Alhamdu lilLAAH Allah abin godiya, miqa masu kayan maza maza,"

Da sauri kuwa ta kai kayan sai da suka gama gyara su sannan suka miqo masu jaririn, yaro ne qaton gaske kamar ba ita ta haife shi ba.

Ishaaq sai da ya zubda hawaye dan farin ciki ya manna yaron da qirjin shi, sanan ya masa addu'o'i, Hauwaa sai washe baki take bayan an maida ta wani d'akin dan hutawa.

Nan da nan kuwa suka fara bugawa 'yan uwa da abokan arziqi waya ana sanar da su haihuwar, Sapnah sarkin surutu sai faɗa ma mutane take baby da ita yake kama.

Umaimah ta sanar da Jameelaa haihuwar matar wan mijin nata, dan haka ta masu alqawarin zuwa in Umar ya dawo.

Basu zo ba a ranar sai washegari da aka sallame su zuwa gida, tinda lafiya qlou suke daga ita har jaririn.

Har cikin gida su Umar suka shiga Ishaaq ya ji daɗi sosai kuwa, ya na alfahari da yanda zumuncin su yake qara qarfi da su Umaimah tinda suna ziyartar juna.

Sapnah ce ta kawo masu abin sha Jameelaa tana zaune ta na yatsina hayaniya tayi yawa wai a fad'ar ta, ta tashi ta yi ta koma ɓangaren Umaimah ita ɗaya kamar mayya, tana ta chatting da qawayen ta masu hannu da maiqo, nan kuwa Umar da Sapnah da umaimah har da mai jegon suka kafa dandalin hira, ba qaramin jin daɗin hirar Umar ya ke yi ba, Sapnah kuwa tafi kowa jin daɗin faruwar hakan,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login