Showing 90001 words to 93000 words out of 118783 words
shi tayi jawur saboda tsananin ɓacin rai da shiga tashin hankali da baqin ciki akan abinda yake gani a gaban shi,Jameelahn shi mai natsuwa da kamala da hankali ce yau ta tura mahaifiyar shi abar son shi da qaunar shi qasa????...........
*Hummmmmm lallai ne Jameelaa, Umar yau ka nuna min ka haihu cikin Mum😡*
*Makaranta ina son jin qarin bayani a game da zuwan Jameelaa gidan boka, da nasarar da take samu, akwai wadda ta fahimci abinda na fahimta kuwa? Sai naji amso shin ku zan gane ko akwai mai irin tinani na ko wadda ta fini ganewa*
*Haermeen Haermmearh love u XoXo❤*
[09/09, 10:32 am] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 38:
Juyawa tayi zata ci gaba da yi ma Umar masifa taji wani gigitaccen mari ya ziyarce ta wanda ya sa ta tafi da baya zata faɗi qasa, da sauri ya tare goyon nata ya kwance 'yar shi cike da fushi mai tsanani ya qarasa turata qasa, zai bi ta ya take Mum ta kira sunan shi da qarfi, juyawa yayi idon shi ya kad'a yayi jawur, Mum bata taɓa ganin ɗan nata a wannan yanayin ba duk da yanda kowa ya san masu sunan Umar da zafi da faɗa nata Umar ɗin nada sauqin hali da sanyin hali, ashe dai ba a taɓa samun wanda ya yi pressing ɗin shi irin haka bane, ita kan ta sai da ta ji shakkar shi ta kama ta , sai ta kasa furta masa komai,Haroon da Ishaaq kusan a tare suka iso gidan, gani suka yi qofar gidan nasu an cika ana ta kallo,haka suka kutsa suma nan suka yi arba da abinda ke faruwa, Haroon ne ya je gaban Umar ya dafa kafad'ar shi yace,
"Broth ko me ke faruwa kayi hakuri mu shiga ciki, sai a gama maganar a cikin gida, kaga mutane suna ta kallo"
"Da wa za a shiga gidan? Ni Umar ni nake auren Jameelaah Jameel ko? to yau na sawwaqe mata aurena akan ta da igiya ɗaya, ko gidana ban amince ta shiga ba, in kuma zata shiga gidan ku ni zan tafi na bar maku gidan,"
"Ta shiga ta yi mana mi? Muje ciki "
In ji cewar Haroon da tun asali ya washi Jameelaah, tun da ya ga haka ta faru kuwa ya san asirin ta ne ya tonu.
Nan suka shige suka rufe gate suka bar Jameelaa tsaye baki sake, ta kasa tantace ita Jameelan aka saka ko wa? Ganin kowa ya watse an barta a wajen, kuma an shige da Humairah ta kwalla wata qara cike da hargowa ta bi su, ta dinga buga gate tana kuka tana baiwa Umar hakuri, akan ya maida ta d'akin ta ta tuba ba zata sake ba, sai kiran sunan Mum take tana kuka,ba wanda ya kula ta, suka shige ciki,da ta dame su Umar ya zabura zai je ya mata rashin mutunci Mum ta hana shi Umaimah ta tsorata da ganin Umar a wannan yanayin kai har Mum din ma, dan tinda ta haife shi bata taɓa ganin shi cikin irin wannan yanayin ba , Umar mutum ne mai hakuri da son 'yan uwan shi, tare da tausayawa na qasa da shi.
Amma yau gaba ɗaya ya sauya,ko kalar fukar shi ta koma jawur kamar qosai.
"Umar kaayi saurin yanke hukunci da baka sake ta ba, gata da yarinya tana shayarwa, kishi ne kawi ke damun ta ba wani abu ba,"
"Mum dan Allah ki bar wannan maganar, kishi hauka ne? Akan ta aka fara zancen kishiya? Ko ta taɓa jin nace zan yi aure, meye bana yi mata dan kawai ta ji daɗi,dik abinda take min kauda kai nake yi dan a zauna lafiya, bata isa ta taɓa mahaifiya ta a wannan yanayin na kyale ta ba, ban haifu ba ma kenan"
"Yah wai sakin ta kayi? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un"
"Ni dama na dad'e da sanin halayen ta, kune baku gane wace ce Jameelaa ba, har bincike sai da na yi akan ta, ba mutanen kirki bane ita da mahaifiyar ta, mahaifin ta ne mutumin kirki,Allah ya kyauta ya sa hakan shine mafi alkhairi, in da rabon zama a gaba Allah ya shirya ta,"
"Babu ma rabon zama, ba wadda ta isa ta taban mahaifiya ko mahaifa na kyale ta,"
"To Allah ya kyauta mana"
"Ameen"
Kowa ya amsa, sai sannan Haroon ya fara neman jaririyar shi, Ishaaq ya dauke ta ya yi mata addu'a, Haroon ma haka, nan aka fara hira kamar ba abinda ya faru, Umar kuwa ya kulle idon shi yayi shiru, yana jin rad'ad'i a ran shi, wanda ya san na farko dai akwai wulaqanta masa mahaifiya da Jameelaa tayi, na biyu kuma akwai rabuwar shi da macen da yake tsananin so, sannan na uku sanin mummunan halin Jameelaa da yayi, tabbas yayi nadamar fadawa soyayyar ta, Sapnah ke riqe da Humairah, wadda ta lafe a jikin ta kamar mai jin bacci, lokaci zuwa lokaci tana satar kallon Umar, tausayin shi ne fall zuciyar ta, can kamar wanda aka mintsina, ya ɗauki waya ya kira Kulu, tana ringin ta ɗauka tayi sallama, ya amsa sannan yace,
"Kulu ki rufen gidana ki kai min keys gidan Mum ki zauna acan ko waye ya je shiga in bani na dawo ba kar ki bari koda kuwa Jameelaah ce, ki rufe har d'akuna da ko ina,"
Ko amsar ta bai jira ba ya kashe wayar, ya sake kulle idon shi, kowa shiru yayi, Aunty Hauwaa ce ta fara fita, sannan Sapnah ta miqe dan bin bayan ta, ajiye Humairah tayi wajen Mum ai kuwa ta sa kuka, ta riqe mata riga, har qirjin ta na bayyana ta sama, da kyar ta samu ta amshe , Umar ne yace ta miqa masa ita, zuwa tayi ta miqa masa yarinyar, ta tsaya tana kallon shi, sannan ta juya ta kalli sapnah, daga qarshe taje wajen Umar, kowa sai dariyar qiwar ta yake yi, banda Umar da Sapnah, wanda su kadai suka san mene ne a zuqatan su, Umar sai kallon ta yake da yanayi na tsantsar so da qauna, yau ya tabbata ita kaɗai ce zata iya son shi ta haɗa da dangin shi, murmushi ya yi mata a hankali ya furta,
"Thank u"
"For what?"
"For everything"
"Ur welcome, and thank u too"
"For what?"
"For staring"
Murmushi sukayi, ya qarasa karbar Humairah sannan ta yi ma Mum sallama, da mai jego ta tafi.
A nan Umar da Mum sukai magrib, dan kuwa sai da Mum tai wa Umaimah wanka sannan Haroon ya kira Aunty Hauwaa akan su zauna zai maida Mum ya d'akko Kulu ta ci gaba da kula da Umaimah da babyn su.
Haka kuwa aka yi ,Umar ma a gidan su ya kwana ranar, dan kuwa Humairah ba a saba zuwa da ita gidan ba bata saba da Mum ba, kuka ta dinga yi da za a bar ta, dan haka Mum tace ya kwana kawai.
**********************
Jameelaa da ɗan sauran dubu ukun dake jakar ta ta yi gidan bokan ta, dan kuwa bata ga ta zuwa gida ba, in bata je an juyo mata da kan Umar ba ya maida ta a daren.
Koda taje a kulle taga shagon dan haka ta zauna anan, tana jiran shi dik inda yaje ya dawo ya yi mata aikin ta ta koma d'akin ta,sai bayan isha'i ya koma gidan, yana ta zuqar sigarin shi, shida mai adaidaita sahun daya kawo ta ran farko.
Tana ganin su ta miqe ta na hamdala,
"Boka ka taimake ni... dan Allah ka taimaken ka sa mijina ya maida ni gidana, ya sakeni ya raba igiyar dake riqe da auren mu,na shiga uku inna rabu da Umar, shine rayuwa ta, dan Ta kan tsamiya ka taimakamin,"
Kallon juna suka yi da abokin shi, dik da ba wani haske sosai, amma har sun karanci junan su,
"Bude qofar muje ciki,"
Bude qofa mai adaidaita yayi suka shiga gaba ɗayan su, nan boka ya zaro kayan aiki, kamar sokuwa kanta ya toshe ta kasa gane komai ba gaskiya bane.
"Gaskiya kinyi azarb'ab'i, ke da aka ce maki sai anyi wata ana aiki, shine kika kasa hakuri watan yayi? Yanzu haka daga zuwa binne mahaifar karya muke, dan ya zama sai yanda kikai da shi daga qarshen watan nan, gashi nan kin rusa mana komai, dole a sake aiki daga farko, amma yau tinda auren ya qare ki kwana a kwana ana yi maki aiki, shima wannan da kike gani yana taimaka min wataran musamman binne abubuwa a bayan gari, kamar yanda muka je binne wannan mahaifar karyan da shi, maza ki tashi ki tube a fara yi maki aiki, kai jeka daga waje, in za a miqo abu zan kira ka,"
Mai adaidaita waje ya fita yana ta murna, yau zasu yi till down suna raqashewa, ruwa aka fara fesa mata, zuciyar ta ba daɗi samm, ko sha'awa bata da shi, haka ya fara sarrafa ta, yana cikin sarrafa jikin ta, tinani ya fado mata, me yasa yau bai tuma ba na zuwan aljanun Nijer? Sannan yau kwata-kwata bai zancen Ta kan tsamiya ba, ba wani surkulle yau, ga shi an sake ta, anya kuwa bokan gaske ne wannan? Sai zuciyar ta ta fara qaryata shi sai wata ta gaskgata shi, tace da baya ci ai da kwanaki baki samu nasarori wajen Umar ba harda kud'in da kika tara a dakin ki da baki yi nasarar samun su ba, tinawa da kudin data tara a dakin ta ne yasa ta bangaje shi ta miqe tsaye,
Tsawa ya daka mata akan dole ta koma ta kwanta,
"Kina da hankali kuwa? Aljanu na maki aiki zaki miqe a zabure haka ba a maki izini ba? So kike yi ki haukace ko?"
"Kaiii dakata dalla can, kuɗi na ya saken nayi shirme ban koma na kwashi komai ba na zo nan, ga uban kuɗi can a gida, matsa ka ga, in da da gaske aikin ka naci da ba a saken ba yau, da mijina bai daken ba cikin mutane, aure na ya ɓaci ne saboda kai, nayi dana sanin sanin ku a rayuwa ta, kwalama mai a daidaita sahu kira yayi, aikuwa ba a jima ba ya shiga, rufe qofar sukai, sukayi kan ta, daure mata baki suka fara yi, sannan suka ci gaba da yi mata dik abinda suka so, Jameelaa tin tana kuka ta cikin tsumman dankwalin ta har ta kasa, jikin ta ya mutu murus, ko hannun ta kasa d'agawa take, basu barta ta huta ba sai wajen 1 na dare.
Suka wurga mata kayan ta suka fidda ta daga shagon, a adaidaita sahu suka sanya ta, har gida suka kai ta, dan bai manta inda ya kai ta ba ranannan, suna aje ta a qofar gidan suka gudu.
Tsoron dare ne ya kama ta ya sa ta fara buga qofar tasu cikin sanyin jiki.
Ramai a tsorace ta miqe ta tada Baban Jameelaah dake shaqar baccin gajiya,Bukar ma na d'akin shi ya farka yayi wuqi wuqi da idon amma ya kasa motsawa, tinda suka dawo basu taɓa jin an taɓa qofar gidan su ba bayan 10 na dare balle 1 da kusan rabi na dare.
Malam Jameel ne ya kwantar ma da Ramai hankali sannan ya fita, yana ta magana Jameela murya bata fita sai faɗi take tana
"Baba ni ce," amma inaa sam baya jin ta.
Da addu'a ɗauke a bakin shi ya buɗe qofar numfashin shi kamar zai dauke dan fargaba, to muna cikin zamani na kashe-kashe, gani yayi bai ga kowa ba, ya fara jan A'uzubi kalimatillahi.... a zuciyar shi, wataqila aljanu ne suke musu bugu haka, da sauri ya ja baya zai rufe qofar Jameelaa tana daga kwance ta ja jikin ta ta shiga ta kama qafar Baban nata, ihu ya zunduma ya fara karanta qul'uuhiya.
Cikin dasasshiyar murya tace,
"Baba ni ce Jameelaa, nice Baba"
D'agawa yayi daga faduwar da yayi ya kalle ta, nan da nan ya yi shiru, ya tashi zaune sosai ya sake kallon ta, sannan yace,
"Jameelaa? Jameela me ya same ki haka? Kin gan ki kuwa kamar wadda tai artabu da manyan 'yan fashi da makami?"
Kamata yayi suka shiga ciki, Ramai ta qule a qasan gado tin da taji ihun gwarzon mijin ta da bashi da tsoro, ta san ko meye yafi qarfin ta.
Sai kwala mata kira yake amma haka taqi fitowa, Bukar ne yayi ta maza ya fita, ganin Jameelaa ya sanya ya kwala kiran sunan ta da qarfi, tare da zuwa inda take yana tambayar ta lafiya take ko dai fashi aka yi masu ina Yah Umar da Humairah? Ramai na qasan gado ta ce,
"Jameelaa kuma, me zai kawo ta gidannan da tsohon daren nan?"
Sai ta hau qoqarin fito wa daga qasan gadon.
Da kyar Ramai ta fito, har ta rasa ya akai da fari ta shiga qasan gadon ma,abu kamar wadda aka d'agawa ta shige.
"Malam Jameelaa naji kuna kira fa iwar haka, me ya faru"
Ganin jameelaa a qasa ne ya sanya ta ruga wa wajen ta itama da gudu,Ramai ce ta kula ma kamar a sume take da sauri ta janyo butar tsakar gidan ta kuza mata ruwa, ai kuwa tana farkawa ta fashe da kuka mara sauti, dan kuwa muryar ta a dashe take.
"Dora ruwa mai zafi Ramatu a yi mata wanka, dik jikin ta qasa ne ga shi na kula da wani yanayi a tattare da ita, in ta huta taci abinci, ta samu bacci gobe maji meye matsalar tunda mijin ta be kira ba kuma bai zo ba sannan ba tare suke ba"
(Kun ga ko anan hakan ya nuna kyawun halin Umar da kuma yanda ya so Jameelaah ya nuna mata kulawa da tsananin qauna)
Ba b'ata lokaci Ramai ta yi yanda mijin ta yace,a nan tsakar gidan ta wanke ta tass, ta tabbata kuma ta gani da idon ta alamar an sadu da Jameelan, lallai Umar mara mutunci ne, sai da ya gama saduwa da d'iyar tasu ya lallasa ta da dikkan alama shine ta gudo gida,ruwa mai kyau ta sa mata tayi wankan tsarki.
Tinani Ramai ke ta yi akan,wataqila ma gudowa tayi saboda azabar ta yi yawa, Ramai na gyara ta tana kukan tausayin Jameelaa.
Taci abinci sosai dan kuwa tana buqatar shi, koda aka gama mata wankan da kan ta ta iya tsaiwa yau har sallah ta rama tun daga farkon wadda bata yi ba a ranar,bayan ta idar ne ta samu waje ta kwanta, Ramai kuwa bata iya komawa bacci ba ita da Malam Jameel kwana sukai suna sallar dare, dan kaiwa Allah kukan su akan Allah ya bayyana gaskiyar mai gaskiya tsakanin yaran biyu.
Washe gari da safe Jameelaa bayan anyi sallah an karya ta zayyana qarya da gaskiya tace Umar dan zai yi mata kishiya ya sake ta harda duka, amma ta b'oye dik wani laifi data aikata masa da mahaifiyar sa, Malam Jameel ne yace,
"Kashhh anya Jameelaah abinda ya faru kenan? A halayyar ki dana sani yaron nan ba zai maki haka ba, sai dai ma ya girmama ki , ya karrama ki, sai dai in asiri aka masa aka juya kan shi akan ki,"
Cikin sauri ta cafe zancen da cewa,
"Ehhh Baba asiri aka masa, boka na yace asiri aka yi masa aka rabani da shi,"
Fadin bokanta da tai ne ya sanya gabanta yin wata iriyar mummunar fad'uwa da tsittsinkewa, abu na farko tinawa da azabar da suka bata jiyan tayi, sannan ta furta boka a gaban baban ta da Ramai dake yawan mata nasiha a kwanakin nan akan ta gujewa sharrin bokaye maqaryata ne,
"Jameelaah bokan ki fa ki ka ce? Har boka gare ki ma kenan, tabbas ruwa baya tsami banza, dole muje mu bawa iyayen yaron nan hakuri, sannan in ba shi yayi ra'ayin maida ki ba Jameelaa sai dai ki auri wani ko kiyi ta zama damu.
Na maki izini Ramatu kije ki ba mahaifiyar yaron nan hakuri ki jiyo mana asalin me ya faru, ni kuma zan je naji daga wajen mijin nata me ya faru sannan na gana da mahaifin shi Bukar shirya mu tafi yanzu,"
"Inshaa Allahu zani malam anjima, ke kuma kin wa kan ki, kan ki kika zalinta, wai ace dik irin alkhairin da yaron nan yake mana ya sai mana gida, abin hawa, abinci, abin sha, da komai da muke buqata, amma kika qi hakuri akan rayuwar da kike ciki koda mata uku zai auro a rana ɗaya ,haka ki ka murje ido kika qi godewa Allah da dikkan baiwar da ya maki,
Ni kaina na uwar ki aje makaman jahilci na na koma ga Allah, Malam na koyan karatun addini kuma kullum sai na yi maki nasiha a qoqari na na kawar da tunanin ki akan mummunar turbar da na ɗora ki tun farko,kar ki manta fa Jameelah kin haddace qur'ani da wasu littattafan na islama, dik da ba dan Allah ki kayi hakan ba ya kamata ace sun maki amfani yanzu amma inaa, sai taurin kai da kauce hanya ma ki ka sake yi"
"Ramai na shiga uku na lalace Ramai, ina zan saka kaina, abinda na jawa kaina ba qarami bane Ramai, ki taimaka min Umar ya maida ni d'aki na kodan yarinya ta"
Zan ga yanda za ai bari na shirya na je gidan nasu na ji me ya faru dan na san ba zaki taɓa fad'ar gaskiya gaba ɗaya ba ko za a yanka ki..........
*Maji ma gani in tusa zata hura wuta*
[09/09, 10:36 am] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 39:
Ramai ce zaune a parlourn su Umar Humairah na ta wasa a jikin ta, Mum sai mamaki take yi dan ganin yanda yarinyar ta sake da Ramai, can ta daina mamaki tabbas dole yarinya tafi shaquwa da Ramai tinda suna je mata akai-akai, ita aka raina aka raba da jikar ta, dan haka bata san ta ba, shine dalilin yi mata qiwa.
Umar ne ya fito cikin shirin tafiya Office, yana ganin Ramai ya isa ya durqusa gaban ta ya gaida ta, amsawa tai cike da jimami.
"Umar na zo ne dan na baka hakuri, dan kuwa dik wani abu da Jameelaah take aikatawa koda bani nace tayi ba ina da kamasho a ciki, domin nice Ummul aba'isin lalacewar ta,anfi samun kaso mai tsoka na tarbiyya ne daga wajen uwa, ni ɗin na zama mai son kai, shi yasa Jameelaa bata da tarbiyya, lokacin dana gane gaskiya ina nuna mata hanya lokaci kuma ya qure min