Showing 21001 words to 24000 words out of 115850 words

Chapter 8 - BABBAN GORO Complete by Khadeeja Candy .txt

02 Dec 2024

5663

mata kiran, tare suka juyo, suna kallon wadda yayi mata kiran, yana karasowa kusa dasu sai kawai ya mika mata hannu,


“Hi Minal”


Da far'ah tace


“Isma'il”


Zata mikasa hannu Saif ya rike ya mika masa nashi, Kallon Saif mutunen yayi kamin ya sake kallon Minal yace


“You look so cute”


Kamin ta amsa Saif ya tigata,


“Thank you”


Ya fisgi hannunta suka fice daga gurin, Bayan sun shiga Mota ya kalleta yace


“Wanene wannan Minal?”


“Yayan wata friend ďita ce”


Ya kunan motae yana faďin


“Na ďauka shima abokin ki ne kamar Deen”


“Deen is my best friend ever”


“Tell me something about Deen”
Murmushi tayi,


“Deen mutun ne mai kyau hali yana da amana gashi da hakuri ga kawaici”


“Ya akayi kika haďu dashi”


“Why you ask me?”


“Nothing just”


“Naje karatun faransanci a faransa a lokacin muka haďu dashi class ďin mu ďaya dashi kuma gurin zaman mu ma ďaya gashi kuma kasar mu ma ďaya hakan yasa muka shaku dashi yana so na sosai yana nunamin kulawa, sai kuma wata kawar tawa Sarah ita kan bafaranshi yace yar faransa mu uku ne kawayen juna,
bayan mun kare makaranta muka zama AMINAN JUNA har ďayan mu baya iya siyen abu bai saya ma đayan ba a haka muka mua haďa kuďi muka siye gida a New York lokaci lokaci mukan je hutu a can, da muka dawo na nageriya sai shakuwar mu da Deen ta karu”


Tana kaiwa nan ya sauke ajiyar zuciya, yace


“Wace Hotal kike son ki ci abinci?”


“Hotal mafi tsada”


Shiru ya ďanyi kamar mai tunani sannan ya kara gudun motarsa,


Sha biyu saura kwata yayi fakin gidansu Minal. cike da jindaďi ta fita motar ta shiga cikin gidan, shi kuma ya kama hanyar gidansa,
Koda ya Isa sha biyu da shirin, yana fita motar ya nufi cikin gidan, tunane-tunane, Yana tura kofar Falon Huda ta tashi tsaye Fuskarta shakaf da hawaye, tsayawa tayi tana kallonta. ita kuma ta nufo tana kuka ta kamma hannunshi ta rike,
Wani kallo yake mata wadda ba zan iya cewa ga fassarar sa ba, can yace


“Baki bachi ba?”


Kai ta ďaga masa dan bazata iya magana ba, janta yayi ya rumgume nan ta kara fashewa da kuka,
Sunyo minti biyar a haka sannan ya ya zauna saman kujera rike da ita, sai da ta tsagaita kukan sannan ya dago kanta yace


“Baki yi bachi ba?”


“Ya za'ayi na iya bachi bayan ka fita tun wuri baka dawo ba sai yanzu kuma nasan duk saboda ni ce kake haka Dan Allah Saif ka yafe min zan iya jure komai amman banda rashinka karka min horon da zai cutar dani ko Allah mukayi ma laifi yana yafe mana dan Allah kayi hakuri Saif”


Kanta ya shafa, yana sauke ajiyar zuciya


“Na yafe miki Huda amman karki kara”


“Da gaske?”


Hancinta ya lakata,


“Na saba yi miki karya ne?”


Murmushi tayi ta girgiza kai da jajayen idanunta ta koma kirginsa ya rumgume ta.






WASHE GARI.....................
Tare suka haďa kayan kari, cikin farinciki da jindaďi ,musamman Huda dan nata baya misaltuwa daman haka take so, shi Kuma Saif ya sake jiki kamar babu abund ya ta6a shiga tsakaninsu. bayan sun karya ya shiga ďakinsa yayi shirin ofis.har gurin mota ta rakashi, ya fice tana ďaga masa hannu.




Uku da yan mintuna ya tashi daga ofis ďin, bai zame ko'ina ba sai gidansu Minal, Dr. Salamatu tayi mamakin ganinsa tana tunanin abunda zai kawo shi gidan yanzu,
Da far'ah ta tar6e tasa aka kawo masa drink, Kaďan ya kur6a ya kalleta


“Wata magana nake son muyi dake idan ba damuwa”


Kai ta ďaga masa,


“Babu komai Saif ina sauraren ka”


“Mi yasa kike kyale Minal tana taka rawar da taga dama?”


Bugun zuciyar ta ne ya karu, daman can jikin yana bata akwai wani abinda ya kawo shi gidan,


“Saif ina tunanin Minal ko abunda ya shafe ta yana tsakanin ni da ita ne”


Yi yayi kamar bai jita ba ya sake jefa mata wata tambayar,


“Baki tunanin abunda ya faru da ke zai iya faruwa da ita? ace tana y’a mace amman taje wani gurin ta kwana, tayi shigar da duk tga dama har Club take zuwa kuma duk a tana musulma ďiyar musulma ? yanzu kina ganin gatane kike nuna mata ace ta bar kuma ba zata dwo ba sai taga dama wace amsa zaki bawa Allah idan ya tambaye akan tarbiyar ta?”


Kawar da fuska tayi, cike da sanyin jiki


“Saif bani da yadda zanyi ne duk lokacin data fita hankalina a tashe yake har sai naga ta dawo”


“Kuma ba zaki iya hana ta ba ko?”


“Ba zan iya hana ta ba Saif bana son abunda zai 6ata mata rai”


Kai ya jinjina,


“Lallai Annabi yayi gaskiya daman yace karshen duniya kuyanga zata haifi uwar gijiyar ta”


Jin motsin ta6a kofa yasa tayi saurin share hawayenta. Minal ve ta shigo Falon sanye da dogon wando da wata yar t-shart fara marar hannu sai wata riga mai kamar ta sanyi data ďaura a kugu, tayi fakin ďin gashin kanta guri ďaya hannunta rike da magazin.
Tana ganin Saif ta karasa gurin tana murmushi, kusa dashi ta zauna


“Sannu Saif yanxu kazo?”


“Eh yanzu na zo”


Ya bata amsa yana ďan kirkiro murmushi, juyowa tayi ta kalli Mummy tare da mikaata magazin ďin, da murmushi ta kar6a ta shig dubawa, kamin ta ďago kai ta kalleta


“Oxford University Minal?”


“Yes Mummy ita nake son junawa makarantar tana da kyau sosai ki shiga online ki gani”


Cike da damuwa Mummy tace,


“Minal ba zaki tsayar da karatun nan haka nan ba?”


Dariya tayi,


“Mummy idan banyi karatun nan ba mi xanyi?”


“Aure mana” faďar Saif dake gefenta, Mummy ta ďaga kai


“Haka ne Minal kiyi aure zaifi karatun nan kinga hankalina xai fi kwanciya”


Tashi tayi ta koma kusa da Mummy ta zauna,


“First i want you to know that a m old enough to know what I want or is good enough for me to Mummy karatun nan shi nake so kuma shine abunda tafi dacewa dani kuma mummy karki manta kema karatun nan kikayi har ika kawo inda kike yanxu har kike yi min gata and Mummy everyone has got the right to decide his own destiny”


Shiru Mummy tayi, Saif zaiyi magana ta tari numfashinsa,


“She is right Saif she old enough to decide her future”


“A wace aya ko hadisi.?”


Duk kallonshi sukayi ganin yadda ya jefo musu tambayar, Minal tace


“Saif muna maganar rayuwa ne”


“Rayuwa babu ska addini a ciki ? mi kik ďauki kanki ne sak tufafin da zasu fitar miki da tsiraici da zuwa club ko kwana wajen gida shine rayuwa? duk wani abunda Allah yace baki yinsa kin đauki rayuwar turawa kin makkalawa kanki abun kunya abun bakin ciki kina yar musulma”


Wani irin baci ran minal yayi, na take ta zaburo masa,


“Haka nake so kuma bazan chanja ra'ayi naba dan bazan bi ra'ayin kowa ba”


Tashi yayi tsaye yana nuna ta da hannu,


“Tirrrr dake Minal Tirrr da mai hali irin naki kin kaskanta kanki tunda kike koyi da kafirai ina son kisani duk abunda kake so tare dashi zaka tashi ranar alkiyama kuma duk abunda ka mutu kana aikatawa akanshi zaka tashi ranar lafira”


Hawaye ne suka wanke ma Minal fuska, lallai BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE idan ba Saif ba waya isa ya tsaya gaban Minal ya faďa mata waďannan kalaman? wani kallo take masa ta rasa abunda zata ce masa dan ya riga ya gama da ita,
Ganin haka yasa Dr.Salamatu ta kalli Saif,


“Saif wannan ba..-”


Hannu na ďaga mata,


“Excuse me Dr. Salamatu dole ne ki faďa mata gaskiya dolene ki faďa mata abunda musulunci ya shar'anta mata dan musulmace ita ma ba ki kyale ta tabi son ranta ba, idan kuma ba zaki iya ba toh ki barni ni na faďa mata”


Da gudu Minal ta nufi Upstairs tana kuka, ta shige ďakinta, Saif ya kalli Dr.Salamatu,


“Ban san abunda yasa kika nuna ma Minal gatan da babu wadda ya isa ya tsayafaďa mata gaskiya ba”


Komawa tayi ta zauna saman kujera tana sauke ajiyar zuciya,


“Saif ban ta6a faďa maka wani abu game da Minal ba, Saif Minal ba ba ďaya take da sauran mutane ba”


Kallon rashin fahimta yayi mata,


“Kamar Ya.?”






_GHOST READER'S PLEASE_
_VOTE! VOTE!! VOTE!!!_
[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...!


NA


KHADEEJA CANDY




WATTPAD @khadeeja_candy




BABI NA GOMA SHA BAKWAI___17


Shiru Mummy ta ďanyi, sannan tace “Saif Minal tana da cutar sikila da ita aka haife ta shiyasa kullum cikin rashin lafiya take, idan ka lura haka jikinta yake bata kiba kuma abu kaďan ya isa yasa ciwon ta ya tashi.
Saif duk mai cutar Sikila in har sun rayu sun girma basa wuce shekara 25, Shekarun Minal 23 a duniya, Saif bansan ta rai ba amman Minal tausayi take bani gashi ita kaďai na haifa bani da kowa sai ita idan ban barta tayi yadda take so ba sai naga kamar na cutar da ita .zuwa zuwa nasan wata rana za'a wayi gari ba ita....- ”


Kuka ne ya ci karfinta ta kasa karasawa, Lumshe ido Saif yayi cike da tsumayi, can kasa kasa ya sinkayo muyar Dr.Salamatu tana cewa,


“Ba a nan kawai a abun ya tsaya ba Minal tana da blood cancer Kuma kasan blood cancer bazai ta6a fita ba har sai an chanja jini, gurin chanjin jini kuma mutun zai iya rasa ransa dan babu tabbas ko zai rayu.Saif bazanbiya hana minal abunda take so ba koda raina take so ba zan iya hana ta ba matukar yana sata farinciki ina fatar ka fahimce ni”


Bai ce da Mummy komai ba dan baya jin akwai abunda zai iya furta mata a yanzu, tshi yayi tsaye tare da saka hannayensa aljihu, ya nufi kofar fita,
Jinginawa Mummy tayi jikin kujera tana kallon Saif har ya fice, sannan ta sauke ajiyar zuciya ta share hawayen da suka zubo mata,




**********
Har ya isa gida tunanin maganar da Mummy ta faďa masa ta Minal yake, Tabbas Minal abar tausayi ce amman wannan ba zai zama dalilin da xai sa mummy ta rika kyaleta tana yadda take so ba.

“Sannu da zuwa Dear”


Cike da fa'ah ta tar6eshi dai-dai lokacin daya kawo baki qafar falo. Da murmushi ya amsa,


“Yauwa sannu wannan kwaliyar fa?”


Fari tayi da ido, ta kar6i makulin motar dake hannunshi


“Kai akayi ma. Muje kayi wanka muci abinci”


Ba musu suka nufi Upstairs tare, har ďakinsa ta rakashi ta taya shi cire kayan jikinsa ya ďaura tawul ya shiga wanka,
Ita kuma ta buďe waduraf ďinsa ta ďauko masa janabiya da guntun wando ta ďora masa saman gado sannan ta fice ta nufi dining tana shirya kwanukan abincin.




****** ****** *****




Zaune suke falo, tana kwance saman jikinsa yana wasa da yatsun hannunta. Kallo ɗaya zakayi mashi kasan hankalinshi baya gurin, dan idonsa ma ba akan tv suke ba.
Bugun kofar da akayi ne, ya ďago hankalinsa zuwa gurin kofar. Huda kan yin tayi kamar ba taji ba daman can haka halinta yake indai akan bugun kofa ne. Sai tayi banza da mutun sai yayi ya gaji sannan ta buɗe. irin matan nan ne masu wulakanci da kyaluwa, (Iri Mrs J Mood 😜).


Yunkurin tashi yayi da nufin zuwa gurin kofar, da sauri ta rike masa hannu


“Ina zaka.?”


“Ba kiji ana buga kofa ba?”


“Naji mana ka kyale ko wanene har sai munga damar tashi mana”


“A'a idan ba zaki ba ni bari na duba”


“Zauna bari na duba ďin”


Tashi tayi ba dan taso ba, ta nufi kofar. A fusace ta buďe da nufin yima ko wanene masifa, sai kawai taga Budurwa tsaye cikin doguwar rigar atamfa da gyale.


“Sannu”


Kairat tace da ita.
Wani kallo Huda ta watsa mata tun daga saman ta har kasa, bata ga alamun talauci ko makamancin hka a tattare da ita ba, tun daga kan tufafinta Juwa halittar jikinta hakan yasa batayi gaggancin faďa mata wata banzar magana ba. Tun da batasan ko wacece ba sai kawai ta ďauke kai tace.


“Wa kike nema.?”


“Saif. yana ciki?”


“Wacece ke.?”


“Sunana Kairat Ibrahim Ahlam”


_Ibrahim Ahlam_ a zuciyarta ta maimaita sunan. tasan waye Ubanta koda bata san wacece ita ba. fitattacen mai kuďi kuma sanannen ďan siyasa mai faďa a ji cikin najeriya,


“Saif nake nema nace yana ciki.?”


Ganin yadda ta tsaya kallonta yasa Kairat, maimaita mata tambayar. Juyowa Huda tayi gurin Saif,


“Dear. kasan Kairat.?”


“Kairat.?”


Da karfi ya zaburo, jin ta ambaci Kairat, ya nufi kofar.
Mamaki ne ya kamata ganin yadda ya kar6a sunan ya kuma nufo kofar jiki na rawa.
Yana isa, ya kara buďe kofar yana faďin,


“Kairat shigo mana”


Sai a lokacin ta ďanyi murmushi, ta tako kafarta ta shigo cikin falon, wani 6angare na falon ya nufa da ita, ya nuna mata kujera


“Zauna ina zuwa”


Zaunawa tayi tana karewa hotunan su dake manne kallo. Wani gurin yana rik'e da Huda wani gurin kuma suna manne da juna, har ma da inda yayi mata kiss.
Haka nan sai taji wani irin, duk bata jidaďin ganin hotunnan nasu ba. _Ko miye dalili oho!_

Da kansa ya ďauko mata abun sha da cup, ya dire mata, sannan ya zauna a kujerar dake fuskantar, ta ya sakar mata manyan idanunsa dake kwance da wasu ruwa saboda fari.

Tsif falon yayi Huda na can daga zaune can gefen tana satar kallonsu. Kairat kuma tun lokacin data zuba drins ďin ta maida kanta kasa,
Saif kuma jiran yake ta fara masa magana dan yasan bazai wuce abunda ya faru tsakanin su da Minal ba daman hankalinsa ya kasa kwanciya tun lokacin da ya baro gidan, ganin ya saka Minal da mahaifiyarta kuka.


Kairat. Sai da tasha lemun sannan ta kalleshi cike da nauyin ido,


“Saif. Naje gidanku akace nazo nan, na tararda kai tare da iyalanka kayi hakuri da takurawar da nayi maku”


Murmusawa ya ďanyi ya shafi dogon hancinsa,


“Ba komai what is important now you are here”


“Saif. I want to talk to you about what you say to Minal earlier”


Gyara zamansa yayi, ya tattara hankalinsa ya mika mata, yana kallonta cike da natsuwa.


“All my ears Pretty Kaiyrat”


Har cikin jijiyar jinin zuciyar ta taji kiran sunan nata da yayi, wata rahama ce ta rufe mata jiki sai taji kamar babu wadda ya iya kiran sunan nata daďi irinshi.








```Don't forget to Vote Comment and share.




#KhadijaAbubakarAlkali
#OneheartOnelove```
[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO.


NA


KHADEEJA CANDY


Candynovels.wordpress.com


WATTPAD @khadeeja_candy




_Masu cewa idan ba zan karasa ba na faďa da masu cewa sai an manta page nake typing da masu cewa yanga nake kuma bana yi da yawa duk kuyi hakuri dani bana da time ne sosai shiyasa, LOVE YOU ALL._




BABI NA ASHIRIN__20


Sai ya tabbatar da hankalinta ya kwanta sannan ya ďago ta yana faďin,


“Kar fa kiyi bachi nasan halinki Yar baby”


Dariya tayi ta kallesa,


“thanks for your caring”


Murmushi yayi mata,


“It's my pleasure”


Ya sake ďaga kai ya kalli windo sannan ya juya yana faďin,


“Tunda kin hakura bari naje gida ki gaida min da Dr.Salamatu”


“Ai da ka shiga ka gaishe ta”


“A a wannan zuwana naki ne bana kowa ba sai dai wani lokacin Ki gaida min da Kairat”


Dariya ta sake yi cike da jindaďi ta mika hannu ta riko hannunsa,
Bai yi unkurin hana ta ba har ya kai gurin da ya faka motarsa. Sai da taga zai shiga sannan ta sakeshi fuskarta shimfiďe da murmushi.


Tsaye tayi tana kallonsa har ya fice sannan ta juyo ta shiga falo cike da nishaďi,
Kai tsaye upstairs, ta nufa hannunta a baki kamar irin yarinya,


“Kairat”


Ta kira sunan ta tana kokarin buďe kofar ďakin.
Da sauri Kairat ta share hawayen dake idonta ta kalleta tana murmushi,


“Na'am sister”


Kusa da ita ta zauna, tana murza ďan hannunta.


“Yanzu ya tafi ya bani hakuri kuma yace na gaishe ki”


Murmushi tayi ta rika fuskar Minal,


“Yanxu kin hakura ko komai ya wuce?”


“Eh man tunda ya bani hakuri ai na hakura”


“Uhmmm amman ni da Mummy babu yadda ba muyi dake ba kika ki hakura”


“Ai toh ai shine ya 6ata min rai kuma yaban hakuri kinsan shi na daban ne”


Kairat ta haďe yawun dake bakinta, ta sake mata hannaye


“Toh yanxu hankali ya kwanta”


“Yes Sis”


A nan ta tashi tana murmushi ta nufi hanyar ďakinta.
Ajiyar zuciya Kairat ta sauke ta kwantar da kanta saman filo ta lumshe ido, tana numfashi a hankali.


Minal tana shiga ďakinta ta faďi zaune saman kujera tana murmushin da ta kasa dainawa tun ďazu,
Kalma ďaya zuwa biyu ta hana mata sukuni. _Ina kinshinki ina bacin ciki wani namiji wadda ba muharraminki ba ya kalli surar jikinki_ me yake nufi ne.? Miyasa yake kishi na ? Mi yasa ya damu dani sosai.? Dubu yadda yazo yake bani hakuri kamar bashi ya 6ata min rai ba,
Dora kafafunta tayi saman hannun kujerar tana lumshe ido.




****************


K'ARFE TAKWAS DA RABI......
8:30pm.
Juye juye take tayi saman carpet ranta a jagule jikinta kuma a mace, kamar marar lafiya.
Tashi tayi ta ďauki wayarta ta kunna wakar Rihanna _work work work_ ta saka iyafis ta faďa kife saman gadon ta rumtse ido. Bata samu yadda take so ba, sauran ďan sukunin daya rage mata sai ya kara fita ba shiri ta tashi zaune ta cire iyafes ďin ta kunna kira'ar Shuraim, ta kai bolon đin karshe.
Ahankali take bin suratul Baqara ďin suna karantawa tare. Can ta janyo Laptop, ďinta ta shiga facebook. Notifications ta fara dubawa kamin ta kai gurin massages, sama-sama tayi reply ďin wasu massages wasu kuma ta kyale su, ta koma newsfeed. Posts ta ďinga dubawa wadda ya dace ta dabnawa like ta danna. Daf da zata sauka online ta duba friendsrequest.
Saif Bashir Bature ta gani, first friendsrequest. Da sauri ta duba profile ďinshi, information ďin data gani about him ya tabbatar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login