Showing 84001 words to 87000 words out of 115850 words

Chapter 29 - BABBAN GORO Complete by Khadeeja Candy .txt

02 Dec 2024

5675

ba sai ina da aure amman kuma ba zan iya auren Mijin Minal ba, i can't”


“Ba Mijin wata zaki aura ba mijin ki zaki aura uban yayanki”


Ya faɗa yana kallonta ita, ma shi take kallo. hakan yasa ya kara fuskantar ta


“Kairat bana son ki ra a ranki zamuyi wannan auren ne dan so da kauna kisa a ranki zamuyi wannan auren ne dan sadaukarwa.
Zakiyi hakan dan Mummy da lil Minal kinsan me? a lokacin da Minal zata rasu ta faɗa min na aure ki na saki cikin farinciki, even on her bed dying ta kula da farin cikin ki misa ke ba zaki iya kula farin cikin yarta ba? ya kike tunanin lil minal ta girma ta buɗe ido taga mahaifiyarta ba raye ba?”


Kai ta girgiza idonta cike da hawaye


“Ba zan iya auren ka ba, ba zan nuna ma lil Minal bani na haife ta ba”


“Taya zaki nuna mata hakan bayan baki auri mahaifinta ba.? banyi wani dogon zama da Minal ba Kairat abunda kike tunani ba shi bane nasan zakiyi rika ga yadda na saba rayuwata da minal ke kuma nayi rayuwa dake no ba haka bane kanun Minal ina da wata matar kin tuna kuma na zauna da ita mukayi tamu rayuwar daban ki sa a ranku saurayi zaki aura wanda bai taɓa aure ba ke zaki koya masa rayuwar aure ki karantar dashi naki karantun a makarantar ki”


Kallonshi take tana mamakin yadda waɗannan kalaman ke fita bakinsa kamar bashi ne yake maganar ba sai kuma ta girgiza kai


“Still ba zan iya ba Saif ya duniya zata kalleni...? i just can't.”


Murmushi yayi mai sauti murmushin da ya kara fitar da kyau da kuma kamalarsa,


“Duniya zata rik'a ɗaga ki ne, mutanen cikin ta kuma su rika kallonki karkace kiyi ta tafiya haka har baki ankara ba lokaci ya k'ure miki baki yi abunda zai amfane ki ba. Nasan yadda kike ji Kairat I feel the same way”


Hannu ta kai ta ɗauki handbag ɗinta ta rata ya


“I need to go home”


tashi shima yayi tsaye,


“Yes go home Kaiyrat kije kiyi tunani mai kyau kiyi abunda zai fidda ki karki manta da baya Kaiyrat karki cutar da kanki karki cutar kar kuma ki bujirewa Minal”


Cikin kwayar idonsa take karantar abunda yake fita bakinsa, kallon kallo suka rika yima junan su kowanne ta tasa sakar a zuciya. ita ce ta fara yin jihaɗin ɗauke nata idon daga nashi ta haɗeye yawun karamin bakinta ta, taka a hankali tana tafiya kamar mai tausayin kasa.


Da ido ya bi ta yana mata kallon da shi kansa bai san na minene ba? sha'awa, tausayi, so, ko kuma kauna! wani kalar yanayi nake jin kansa ciki yanayin da bai taɓa jin kansa ciki ba wani kalar yanayi ne mai wuyar fassara.
A hankali ya kai hannu ya shafa kyakyawan gashin kansa ya tada kai yana kallon itace dake gurin yana lumshe manyan idonsa a hankali.
Mamakin kansa yake yadda yake rokonta ta aure shi bayan bai taɓa yi ma wata mace hakan ba. wani gurin kuma gani yake yana da gaskiya saboda wasiyar Minal da kuma lil Minal.


**** *** *****


BAYAN KWANA BIYU....


Safiyyah ce kwance ɗakinta fuskarta ɗauke da murmushi sai juyi take ta kafa tana jindaɗi. yau ne zata fara gwada maganin da malamin ta ya bata kuma ta yarda zaiyi mata aiki. tana jin fakawar Motar Saif ta tashi ta sauri ta leka windo ganin shi ɗin ne ya kara mata jindaɗi,
Da sauri ta dawo ta buɗe jakar ta ta ɗauko wani kwalli ta buɗe maciyin ta kira sunan Saif sau uku ta tofa sannan ya shafa. daman haka yace mata duk zata shafa ta kira sunansa dan da sunan akayi aikin.

Tana gama shafawa ta mayar a jaka ta nufi madubi ta dauki hoda ta shafa ta gyara jan bakinta ta buɗe wata durowa ta ɗauko wani turare daga ganinsa kasan na magani ta shafa, sannan ta juyo jiki na rwa ta nufo parlour.
Ta koyi sa'ah tana saukowa yana danno kai cikin parlour, yana sanye da shada sky blue tayi masa kyau sosai kansa ɗauke da bakar hula.
wani fari tayi masa da ido ta sakar masa mirmushi


“Ya Saif sannu da zuwa”


A maimakon ya amsa sai kawai ya wanke mata fuska da mari.






Kuyi Hakuri da wannan Anjima Wani Zai Zo Amman Ban Muku Alkawarin Mai Yawa Ba.😀
just keep voting and commenting on every single line. Stay bless Candy Love you from the bottom of her heart.😍


MY QUESTIONS.


TUN FARKON FARA KARANTA LITTAFIN NAN ZUWA YANZU ME YAFI BURGE KU?


INA YAFI BAKU HAUSHI?


INA YAFI BAKU TAUSAYI?




48


Ja tayi baya da sauri ta dafe junco dan ba karamin mari yayi mata ba,


“Lafiya mi tayi maka haka?”


Momy ta tambaya tana tashi tsaye, sai a lokacin ya lura da Momy, juyar da fuska yayi ya ɗan haɗe rai. A nan ya shiga neman dalilin marin nata da yayi ya rasa, shi kan shi bai san dalilin marin nata dayayi ba shi dai kawai ya samu kansa da jin haushin murmushin da tayi masa da magana.


“Momy parking tayi ba dai-dai ba gurin da nake aje mota na take ta aje”


Ya faɗa yana kokarin kare kansa, tunawa da yau gurin da yake parking yaga motar ta fake,


“Haba dan Allah dan Annabi sai kuma kayi mata wannan mari haka? Sai kace karamar yarinya, ai sai kaje kace ta ɗauke motar ko.? Ba ma ita ra fita da Mota ba Lubna ce”


Shafa kansa yayi yana ɗan yatsinar fuska ya zauna saman kujera, kallonta yayi kamar yace tayi hakuri sai kuma yaji ba zai iya ba, ya kalli Momy data ranta ya ɓace ya ce


“Na ɗauka ita ce sorry Momy”


Banza Momy tayi dashi tana kallon Safiyyah da ta rufe ido tana hawaye, juyawa tayi kamar kazar da kwai ya fashe ma ta nufi ɗakin.


“Ni Wallahi halin naka ya fara isa ta bana son abunda kake yima yarinyar nan ko kaɗan”


Momy ta faɗa tana jan tsaki cike da ɓacin rai. Kallonta ya sake yi


“Momy kiyi hakuri”


“Wane irin nayi hakuri fusabilillahi abun da kake mata kyautawa ne? Ko kuma dan tana zama nan gidan sai ya baka damar yi mata duk wulakancin da kaga dama”


“Momy mistake ne fa”


“Wane irin mistake daga shigowar ka ka fece yarinya da mari kace mistake haka ake mistake to Wallahi daga yau sai yau ko Kallon banza karka sake mata balle ka ɗaga hannu ka dake ta”


Momy na kawai nan, ta tashi a fusace ta shige ɗakinta. Gashin kansa ya shafa ya ɗaga kansa


“Oh my goodness Momy ba zaki saurari abunda nazo dashi ba akan na mari Safiyyah, ya salam!”


Ya faɗa yana girgiza kai.


*** **** ***


“Assalamu Alaikum”


Yayi sallamar yana kokarin kunno kai cikin parlor, cikin taku irin nasu na manya. Dr Salamatu ce ta amsa masa Kairat kuma ta karasa gurinsa a guje ta rumgume shi


“Sannu da zuwa Abbah”


Ta faɗa cikin wani irin jindaɗi tana dariya, shina dariyar yayi yana faɗin


“Yauwa yar Salamatu ya gidan naku?”


“Gida lafiya kalau”


Ta masa yayin da take ɗago kanta daga jikinsa, hannunta ya rika suka nufi three sitter suka zauna.


“Ina wuni Salamatu”


Abbah ya gaishe ta ganin yadda ita ɗin ta kasa masa magana sai wani abu take kamar ba ta jidaɗin ganin shi ba. Daker ta asa tana ɗan murmushi. Kairat ta tashi cike da zumuɗi


“Abbah bari na kawo maka Abinci yanzu muka gama ni da Mummy”


“Toh yar Mummy ba sai kin kawo min ba ruwa ma ya isa”


Kicin ɗin ta nufa tana faɗin,


“Toh Abbah”


Bata daɗe ba ta fito ɗauke da ture mai drinks da cup, a gaban sa ta dire ta ɗauki lemu ta zuba masa ta mika masa


“Gashi Abbah kasha lemon gidan mu”


Karɓa yayi yana murmushi ya kurba kaɗan ya aje sannan yayi ma Mummy kallon natsuwa.


“Gurin ki nazo ke da yarki”


“Allah yasa ba laifi muka yi ba”


Mummy ta faɗa tana ɗan murmushi, Abbah ya gyara zaman sa


“Jiya ne iyalan Alhaji. Bashir bature suka zo gidana akan maganar Kairat sun ce min daga nan aka turo su kuma yace da amincewar ku, haka ne?”


Kairat tayi saurin yin kasa da kanta cikin kunya ta mataa gurin Mummy, Mummy kuma tasa dariya tana shafa kanta


“Eh haka ne daga nan na tura su can”


Abbah yayi dariya


“Ance Saifullahi ne mijin margayiya”


“Eh. Haka ne sun daidaita dashi da ita ne sai nace idan har da gaske yake yaje can ya same ka ashe ya je”


“Eh sunje Jiya, ni kuma nace ba zan ce komai ba sai naji ta bakin ku, amman naji daɗi wannan abun sosai Allah ya tabbatar mana da alheri”


Mummy ta amsa da


“Amin”


Abbah yayi dariya yana kallon Kairat


“Toh ke kina son shi dai ko?”


A gudu ta tashi ta shige ɗaki tana rufe ido. Abbah ya kalli Mummy da ta bita da kallo ya ce


“Sai a samu su rana kenan?”


“Eah a sa musu amman kayi shawara da Hajiya tukuna”


“Nayi mata magana ai tace nazo nan na same ki ai kece uwarta”


Shiru Mummy tayi tana nazari, ke hakan yake nufi kenan? Babu ruwanta da lamarin auren ko muma me? Maybe bata ji daɗin haɗin auren da aka yi ba. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalli Abbah


“A sa musu kuma inda hali kar asa da tsawo saboda Babyn ta kasan an kusa sallamo ta daga asibiti kuma kasan ita ce zata shayar da ita”


“Masha Allah amman kunyi tunani mai kyau gaskiya dan ba kowa bane zai iya yima ma rokon gaskiya ba, Bari na saka muku wata ɗaya yayi?”


“Wata ɗaya bai yi nisa ba?”


“Toh bari aka muku sati biyu”


“Toh ina madallah da hakan Allah yasa albarka”


“Amin”


Shiru ne ya biyo baya kowa hankalinsa ya koma kan tv, zuwa can Abbah ya kalleta


“Toh ni kan zan wuce inda wata matsalar zaki iya sanar min, duk da akawai wata maganar da nale son yi dake amman ina ganin sai an gama wannan hidimar ta Kairat”


Mummy ma tashi tayi ganin ya tashi tace


“Na gode sosai ka gaida Hajiya”


Ta basar da wacan maganar, murmushi kawai yayi dan yasan da gangan tayi hakan, ya nufi kofa ita kuma tayi masa rakiya har gurin Mota.


Kuka Kairat ta samu kanta dayi lokacin da ta shiga ɗakinta kuka marar dalili dan itama kanta bata san dalilin kukan nata ba, ita dai kawai taji kuka yazo mata ba kakkautawa.
Kusa da ita Mummy ta zauna lokacin dats shigo cikin ɗakin ta kalleta cikin damuwa


“Kairat bana nufin cilasta ki, bana burin kiyi auren da baki so ban roke ki ki auri Saif sai dan ansan akwai ɗigon son shi cikin zuciyarki, na haɗa ki da girman Allah karki auri Saif matukar kina tunanin aurensa zai zame miki matsala ko kuma tursasawa daga gare ni”


Dagowa tayi ta ɗora kanta saman cinyar Mummy,


“Wallahi Mummy ni kaina ban san dalilin wannan kukan nawa ba, kawai dai ina jin wani abun ne daban, babu cilastawar ki ko ɗaya a wannan auren ni naji zan iya kuma nasa kai na karki taba zargin kanki”


“Amman Kairat bana jindaɗin wannan kukan da kike yi yana kuna min zuciya”


“Ba zan sake ba Mummy insha Allah”


Ta faɗa tana share hawayen ta, Mummy ta shafa kanta.


“Allah yayi miki albarka ya biya ki”


“Amin”


☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆


Cikin satin Abbah yasa yanka musu sadaki ya kuma duk wani abun da yace uba yayi ma yarsa, cikin satin kuma akayi komai cikin har da kawo tufafin da Kairat zata saka, Saif yasha mayar nu gidan yana tambayarta ko da wani abun datake bukata tace masa a a. duk wani abu da yan mata suke yi ita kinyin tayi ciki har da kin raba katin aurenta, walima ma dan Mummy ce ta shirya ta shiyasa kawai zata halarta. babu yadda Mummy bata yi da ita ba akan ta ɗan yi wani event ko da ɗaya ne amman taki.
Safiyyah kan tattarawa tayi ta koma gidan Gwaggonta wai ba zata iya zama a gidan Momy ba dan ba zata iya jure yadda Saif yake disgata ba, gashi yanzu abu ɗaya da biyu zai sako maganar Kairat ko lil Minal.
Duk wani abu da ya dace ya tayi ma yarta sai da Mummy tayi ma Kairat shi, tun daga gyaran jiki zuwa tufafi har kan abunda za a saka mata a ɗakin. hakan sai yasa Kairat ta zama yar gata dan Hajiya ma irin nata gatan take nuna mata, Abbah ma duk abunda aka siyo sai ya nuna mata ya kuma tambaye ta abunda take so, amman hakan bai taɓa sa taji daɗi ko da sau ɗaya ba.
Ana saura kwana biyu a ɗaura aure Hajiya Suwaiba ta zo gidan, Mummy taji tsoron ganin ta dan bata san da wace tazo ba, tunawa da zuwanta na karshe a gidan, Murmushi dake fuskarta yaba Mummy karfin gwuiwar yi mata magana


“Sannu da zuwa Hajiya Allah dai yasa ba laifi muk yi ba”


Hajiya ta zauna tana murmushi tana kokarin zaunawa,


“Ya gida ya hidima”

“Alhamdulillahi ya naku?”


Mummy ta faɗa tana kallon Fusakarta.


“Masha Allahu na fito gidan Ramatu ne nace bari na biyo tun da ku baku zuwa ga shirye shirye yayi nisa”


Dariya Mummy tayi suka cigaba da fira sai dai kowa bai sake jikin kasancewar Mummy tunanin da wace tazo, ita kuma tana jin nauyin Mummy akan abunda tayi masa.



RANAR ASSABAR.........
Rana ce da da dandanzon mutane suka shedi ɗaurin auren KAIRAT IBRAHIM AHLAM da SAIFULLAH BASHIR BATURE, anyi taro kosai tun daga kan yan'siyasa yan kasuwa sarakauna malamai da kuma daidai kun jama'ah, Daga garuruwa daban daban, bayan ɗaurun Auren mutane suka ɗugun zuma zuwa gurin liyafar cin abinci.
Bayan gama liyafar Saif ya nufo gida tare da wasu abokaninsa, Kallo ɗaya zakayi masa ka ganr shine angon duba da yanayin shigarsa da kuma yadda fuskarsa ke annuri kanshi turare kan ba a magana, kallo ɗaya Safiyyah tayi masa ta ɗauke kai ta cigaba da kallon tv tana wasa da makulin hannunta,


“Sannu Ango Allah ya bada zama lafiya”


Shafa ta faɗa tana murmushi, Safiyyah ce ta amsa da amin kamar ba komai, sannan ta kalli Lubna take da zuba da Nasir tana faɗin


“Ke suda muje ni dai akwai gun da naƙe son zuwa”


“Ina zaku?”


Nasir ya tambaya yana kallon Lubna dake tsaye kusa dashi ta rike masa hula


“Yauwa Ya Nasir muje ma ka kai mu gidan Ya Saif zamu je ɗakin Lil minal zamu gyara”


“Ita lil Minal ɗin har an mata ɗaki?”


Tayi wani fari da ido,


“Taf tun yaushe yau ɗin ma wasu kayan zamu kara sakawa”


“Toh masu abu su keci da rana kuna shagalin ku”


Duk suka sa dariya har Safiyyah, a nan Luban ta tirsasa shi tasa shi gaba a dole ya kai sai da yayi driving ɗin su har gidan a mota in banda tsokanar Lubna babu abunda yake har ta saka masa kuka.
Dukan su sun yaba kyau gidan da kuma yadda aka gyara ɗakunan musamman ɗakin Lil Minal sasancewarsa ɗakin yara yana da ɗaukar hankali idan an gyara shi. A tare suka shiga jera sauran kayan ganin aikin nasu ba mai karewa bane yasa Nasir yayi tafiyarsa yace idan sun maga su buga masa zai zo ya ɗauke su. Ai ko Safiyyah ta jidaɗi sosai yana fita itama ta fita daga ɗakin ta nufi gurin da aka dasa itace dan kwaliya, hannu ta kai ta kalli wani ɗan karamin ice ta duka a gurin tana gina, wani abu naga ta ɗauko ta saka cikin karamin ramen ta rufe waige waige take har taƴi ta gama tana Allah Allah kar wani ya ganta, Tashi tayi tana karkaɗe jikinta ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya can kuma ta buɗe ta nufi cikin gidan.
wani kallo Shafa tayi mata mai alamar tambaya ita kuma ta ɗaga mata kai, sai ko wannenasu ya ɗauke kai suka cigaba da shirya ɗakin.


Nasiha Sosai Mummy tayi ma Kairat bayan Abbah da Hajiya sunyi mata nasu, Kuka sosai Kairat ta rikayi kamar ranta zai fita kwaliyar da akayi mata duk ta bace Mummy ma ba karamin kuka tayi ba, saboda tunawa da auren Minal da kuma ganin za a barta ita kaɗai. daker aka ɓanɓare hannun Kairat a jikin Mummy, Motar ma daker aka saka ta, sai wani abu take kamar mai aljannu. ko kuma nace wanda za a cire ma rai, har wani numfashi take saboda kuka.
Har a ka isa da ita gidan angonta kuka a motar ma ba karamin yaki akayi ba wajen fitowa da ita a shiga cikin gidan ba, a ɗakin aka wuce da ita kowa sai yaba kyau gidan yake da kuma kayan da ka zuba ma Kairat, masu ɗaukar hoto nayi an video camera ma nasu aikin suke. ita kan bata kula komai ba kuka take har abokanin ango suka shigo dashi. zolayarsa suka rikayi shi dai in banda murmushi babu abunda yake shima kana gani zaka san bai kai zuci ba, Nasir ne kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login