Showing 111001 words to 114000 words out of 115850 words
Chapter 38 - BABBAN GORO Complete by Khadeeja Candy .txt
shi ne abunda take ta tunano wa take kuma tambayar kanta amman ba amsa, bayan fitar likitocin Mummy ta rumgume tana kuka, tana yima Allah hamdala,
"Mummy miya faru dani"
"Komai ma ya faru dear na gode Allah da ya dawo min dake daidai"
Tana kallon Saif ya sakar mata murmushi, sannan ya zauna saman gadon yama mai lumshe ido da buɗewa, Mummy ta tashi cikin zumuɗi
"Bari na haɗo miki tea ki sha ko kina son wani abun"
"Tea ma is okey"
Cikin sauri ta fita, sai ita kuma ta kalli Saif da fuskar damuwa
"Miyasa aka kawo ni asibiti? Mi ya faru dani ne wai?"
Murmushi yayi,
"Ni kai na bansan abinda ya faru dake ba, ni dai na dawo ne sai na tararda ke kwace a kasa kin dafe ciki baki iya magana, a nan ne sai na kawo ki asibiti daga lokacin sai hankakinki ya bar jikin ki"
Shigowar Mummy ce tasa duk suka kalli kofa, Kairat sai nazarin maganar take dan har yanzu bata gano musabbabin abun ba, Mummy da kanta ta rika bata tea cikin wani irin jindaɗi, Kairat ta lura da hakan, sai tasa hannunta ta rika hannun Mummy, Mummy kuma ta jimke hannun jinjinjin,
"Da ace na rasa ki Kairat da bansan yadda rayuwata zata kare ba"
"Mummy ba zaki rasa ni ba, ki daina tunanin hakan"
Ta shafi kanta zuwa gefen fuskarta, idonta cike da hawaye ta ce
"Ina fatar haka"
Ta ɗauki lokaci a ɗakin, sannan ta ɗauki cup ɗin tea ta fita, Saif kamar ita yake jira ya dawo kusa da matarsa, ya rungume ta.
A jikinsa ta karasa bachin, duk da ba wani bachi sukayi ba. Hasken asuba na fara fitowa su Hajiya Suwaiba suka iso tare da Abbah, daman tun cikin dare Mummy tayi musu waya ta sanar musu, ganin su ne yasa Saif mika ma Mummy cup ɗin tea dake hanmunsa, ya ɗan matsa ba bada space tsakani su, sai Mummy ta cigaba da bata tea shi kuma yana gaisawa da su, Abbah ya kalli Mummy yana murmushi
"Hankali ya kwanta ko Ummu Kairat?"
Murmushin itama tayi, ta shafi kan Kairat, Hajiya Suwaiba sam bata jindaɗin maganar ba sai dai bata nuna masa ba, dan a yadda ta fahimta a yanzu yana son Mummy fiye da tunanin ta, ganin yadda duk damuwar ta ta zame masa tasa, a halin da Kairat take cikin ta fahimci Mummy yafi tausaya ma sama da ƴarsa Kairat. Hajiya ta murmusa irin murmushin da bai kai zuci ba tace
"Yanzu kuma ai kuka da tunani ya kare ko?"
Mummy dai murmushi kawai tayi ta tashi ta nuna ma Abbah kujera, ita kuma ta tsaya daidai Hajiya Suwaiba still tana murmushin,
"Ga kujera a zauna"
Murmushin yayi mata ya zauna yana yi ma Kairat ya jiki,
"Jiki da sauki Abbah"
Ta amsa tana kallon Hajiya Suwaiba dake kallon Mummy ita kuma tana kallonta. Basu jata da fira sosai ba, suna gurin aka kawo mata breakfast daga gurin Momy kamar yadda aka saba, tara saura Saif ya bar ɗakin ganin basa da niyar fita ya nufo gida da zimmar ya sanar da Momy ya kuma yi wanka ya canja tufafi, a part ɗinsa yayi parking ya fito daga motar da zimmar ya shiga yayi wanka amman sai ya kasa zimuɗin sanar Momy yake, haka ya nufo part ɗinta zuciyarsa cikeda farinciki a fuskarsa ma zaka iya gane hakan, dan tun daga nisa Momy ta gane yau ɗan nata yana cikin farinciki,
"Momy ya na ganki da shiri haka? Kar dai ace kinji?"
Ya faɗa lokacin daya karaso kusa da ita hakoransa a buɗe, Momy ta ɗanyi fuskar mamaki
"Naji me? Da wani labarin ne?"
"Yes Momy ba Kairat ta tashi ba"
Ya faɗa yana wani abu kamar yanzu ya soma jin tashin nata a zuciyarsa, jin yayi ba zai iya ɓoye murnar sa ba har sai da ya rumgume Momy, Momy tayi dariya tare da godiya ga Allah
"Alhamdulillahi amman naji daɗin wannan abun, cuta ba mutuwa ba"
"Wallahi Momy tun jiyada dare fa, kar ki so ganin yadda nake jindaɗi"
"Ai na gani kan, gashi nan ya kasa ɓoyuwa a fuskarka, aiko yanzu shirin nan da nayi ina son naje duba ta ne idan na fito gurin Safiyyah"
"Da banyi sauri ba da kin tararda ni a can ashe"
"Lallai kan, bari naje so nake na dawo da gurin akwai bakin da za'ayi daga Europe"
"Okey Momy nima wanka kawai zanyi na koma"
Murmushi Momy tayi, aka buɗe mata motar ta shiga Saif ya maida ya rufe yana mata Allah ya tsare.
Kamar yadda ta faɗa, a harabar gidan su Gwaggo driver yayi parking wani ya fito daga ɗayar motar da sauri ya buɗe mata cikin girmamawa, sauran suka shiga fito da kayanyakin da dace musu a nan zasu kawo, kayan kwalama ne waɗanda tasan Safiyyah tana so, kamar ko yaushe yau ma da sallama ta shiga parlour fuskarta ɗaukeda murmushi duk da Faɗuwar gaba ne a zuciya wanda ita kanta bata sam dalilin sa ba,
Sallamarta da kuma sautin takun tafiyarta kana da kanshim turaren ta shine ya tabbatar mata Safiyyah Momy ce ta shigo,
"Momy..."
Ta kira sunan nata dan ta tabbatar, kasancewar ita kaɗai ce ke parlour, sai da Momy bata amsa ba har sai da ta zauna kusa da ita,
"Na'am Y'ata"
Hannu ta kai tana shafa jikin Momy har ta kai ga fuskarta,
"Momy kece?"
Shiru Momy tayi tana kallonta jikinta a sanyaye, dan ta kasa gasgata abunda idanunta suke gane mata,
"Momy ke ce amsa min magana"
Ta faɗa muryar tana gaf da kuka, Momy ta rika hannunta
"Ba ki gan ni bane safiya"
"Bana iya ganin ki Momy idanuwana a yanzu rufe suke bana iya bambance baki da fari ko kuma haske da duhu, na kan kane kowa neta hanyar murya ko kuma kanshim turare ne kawai amman ba da ido ba"
Hawaye na mata zuba take magana, Momy bata san lokacin da hawayen idanunta suka fara fita ba, ta sauko daga saman kujerar bakinta na rawa ta ce
"Safiyyah baki gani kike nufi? Yaushe makanta ta same ki?"
"Momy bana gani, a yanzu haka ban gani komai sai duhu"
"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un, yaushe wannan abun ya same ki?"
"An kwana biyu yanzu, Momy rayuwa ta kenan haka Allah ya kaddara min nawa al'amarin"
Duk kan su cikin kuka suke maganar, musamman Safiyyah,
"Momy ni da kaina na jefa kai cikin ramen daba zan iya fita ba, ni ka kona kaina da raina ni na salwantar da rayuwarta dan kawai biyan bukatar duniya kuma gashi ban samun biyan bukata ba,
Momy abunda nayi neya dawo min, nayi nadamar abun da nayi, sanadin hakan nayi hauka yanzu kuma makanta na rasa masoya na guda biyu akan biyan bukatar da har gobe ba zata biya ba,
Momy da ace na karɓi shawarar ki tun farko da ban faɗa wannan halin ba"
Lumshe ido Momy tayi hawaye na mata zuba,
"Kaddara ta riga fata Safiyyah haka Allah ya kaddaro miki rayuwar ki, haka aka so ya kasance a gareki"
Gwaggo ce take maganar tana tsaye kofar kicin tana hawaye, Momy ta ɗago ta kalleta sannan ta share hawayen idonta,
"Miyasa ba a faɗa min tun lokacin da abun ya same ta?"
"Saboda babu abunda zaki iya yi mata, da kin damu da ita har haka ai da bata shiga halin da take ciki ba yanzu"
Cikin kuka Safiyyah ta ce
"Gwaggo, Momy bata laifin a nan nice da kai na siyar da kai na inda kuɗin fansar kaina ba zai taɓa samu ba, ba zata iya goge abunda yake rubuce tun kamin a haife ni ba, bata iya tayi min abunda Allah baiyi min ba,
Hakika ko wane mumini yaba zama mumini har sai da jarrabawa, ni kuma an jarrabe ni sai dai ban ci tawa jarrabawar ba,
Ina ma gaba na zai koma baya baya kuma ta dawo gaba da na gyara komai na rayuwata"
"Miyasa kika aikata Safiyyah?"
"Sheɗan ne Momy, ya rika doka min gangan ina rawa, ta kuma rufe min ido na rik'a hangen kamar nasara ce, ashe bakin ciki da dana sani ne suke kwankwaso min kofa, ni kuma na amsa musu ba tare da sani ba"
Kuka sosai Momy tayi ita da Safiyyah babu mai iya ba wani hak'uri, jinjina al'amari take tana tausayin yadda mai ido farat ɗaya zai zama makaho, hannayen Momy ta kama ta rike gam
"Idan har kaddara ta tsaya a nan toh na gode Allah saboda nice na ɗebo ruwan dafa kai na da kai na, a yanzu na zama wata irin kalar mace hakika na cuci kai na da kuma cutar da wasu, bai haifar min da komai ba sai nadama da hasara, ki yafe min Momy"
"Baki yi min komai ba Safiyyah koma kin yi min na yafe miki Allah ya warkar miki da wannan lalurar, zanyi duk yadda zanyi wajen ganin kin samu lafiya insha Allah"
Cikin kuka Momy tayi maganar, sai da ta samu kujan nata ya ɗan tsagaita sannan ta share hawayen ta tashi jiki ba karfi ta fice.
Bata je asibitin ba kamar yadda tayi niya, snanin bakin ciki da ɓacin rai har ta iso gida kuka take, daker ta iya labarta ma Lubna halin da Safiyyah take ciki, itakan bata yi mamaki ba, dan tun lokacin da abun ya same ta ta samu labari, ita tama yi tsammanin sama da haka ne zai faru da ita tunda ita ta jawa kanta,
"Momy akan me zaki rika damuwa da halin da takr ciki ita fa ta jawa kanta, sannan ke ba wannan tarbiyar kika mata ba, ba ke kika nuna mata wannan hanyar ba, ita ce ta sauya rayuwar ta ɗauki wanda take ganin kamar itace mafita"
"Akwai tausayi Lubna matukar zuciyar musulunci ce jikin ki kika ga Safiyyah sai kin tausaya mata, budurwa da makanta, yarinyar da babu abunda ta nema ta rasa, sanadin so ta kai kanta ta baro kuma ba tare da bukatar ta ta biya ba"
Ajiyar zuciya Lubna ta sauke, ta ɗanyi kamar mai nazari, Momy ta share hawayem idonta ta nisa tana faɗin
"Allah ka tsare mu daga muguwar kaddara, da mugun ji da mugun gani da tsaka mai wuyar sani da aikin inda na sani"
Kanta ta kwantar jikin Momy ta amsa ta
"Amin"
*** *** ***
Kwananta biyu suka sallameta bayan sun tabbatar babu abunda yake damun ta, daker Mummy ta yarda aka maida da gidan mijin dan son tayi ta koma gida har sai yadda hali yayi tukuna, sai gashi Saif yakin yarda a dole ita ta hak'ura,
Tunda suka dawo ba wani aiki take yi sosai ba, ga kula da take samu ta ko ina, duk bayan kwana biyu sai tazo duba ta, a ɓangaren Abbah ma haka yake dan a koda yaushe cikin waya suke,
Bata da matsala ko ɗaya a yanzu, babu kuma abunda take zumuɗi kamar auren Abbah da Mummy, duk da a ɓoye za ayi shi,
amman hakan bai hana Kairat yin wasu abubuwan ba, haka ta rika kai kawo har aka ɗaura auren, aiko ranar farinciki gurin Kairat ba'a magana, gurin Hajiya Suwaiba kan bakinciki ne ya cika ta a nan ne Kairat ta kara tabbatar da Lallai kishi kumallon mata ne tana mamaki yadda Hajiya da ta girmi Mummy amman take kishinta,
haka tayi ta tausar ta da kalama da kuma nuna mata Mummy ba mace bace mai matsala, Abbah yaso Mummy ta tare a ɗayan gidansa ko kuma gidan da Hajiya Suwaiba take ciki amman taki ita dai tafi son gidan da take, tunda aka ɗaura aure sau ɗaya Saif ya yarda Kairat taje gidan Mummy, wai a yanzu shi ba zai yarda tana masa yawo da ciki ba ga kuma lil Minal take fama da quiya tunda aka yayeta a yanzu bata yarda da kowa daga Mah sai Pah,
Wasa wasa lamarin Safiyyah sai karuwa yake tun ana ganin kamar za a warke haran fara fidda rai, dan babu asibitin da kai ta ba ta ido tun daga nan Nijeriya har waje amman abun sai karuwa yake dan a yanzu har kaikayi suke mata,
Tana tafe yar jarorar da Momy ta samo mata tana janta har suka kawo gurin da akace bakon dake sallama da ita yana tsaye,
"Gashi nan"
Yar jarorar ta faɗa sannan ta sake ta ta juya ta basu guri, shirun da taji yayi yawa ne yasa ta mika hannu zata taɓa mutumen
"Ba mutun a gurin ne?"
"Hmmm gani ba ganki amman baki iya gani ba, duniya kenan budurwa wawa, ai ni naso kin fi haka shiga matsala, Kyakkyawan dake amman ba ido,
kin cancanci shiga ko wace irin matsala ta rayuwa, zaki iya tuno lokacin da kika ɓata tsakani na da Minal kika kira ni wawa saboda na biye miki mun aikata abunda kika yaudare ni a kai kuma kika yaudari kan ki, shin wace irin riba kika ci a yanzu?"
Tunda ya soma maganar ta fahimci wanene, wani kalar bakinciki ne ya mamaye mata zuciya lokaci ɗaya hawaye suka rika bin fuskarta wasu na korar wasu,
"Deen... -"
"Yes anything for me again?"
Bata ce komai ba har na tsawon wani lokacin, zuwa can ya kalleta up and down yace
"Nazo ne kawai na ganki kuma na fi kowa farinciki shiga halin da kike ciki ina miki fatan alheri"
Bai jira abunda zata ce ba ya buɗe motarsa ya shiga, ita ma ɗin bata ce komai ba har yaja motarsa ya bar gurin, sannan tasa hannu ta share hawayen idonta ta juyo da yar sandarta ta dafe dafehar ta shiga parlour, yar jarora na ganin ta, ta tashi ta rika ta, ta zaunar,
Ajiyar zuciya ta sauke ta tsura ma carpet ɗin ido kamar wance ke ganin carpet ɗin, wasu siraran hawaye suka zubo mata, ta fi karfi minti talatin a haka sai hawayen take, yarinyar na ganin hakan ta tashi ta faɗa ma Gwaggo, sai gata ta sauko cikin sauri ta zauna kusa da ita
"Me kuma ya faru?"
Sai da share hawayen sannan tace
"Mako mata nake tunani Gwaggo, na cuci mutane da suka yarda dani na zama mai fuska biyu har wanda bai san da zama na ba na cutar da shi"
"Har yaushe zaki daina wannan tunanin Safiyyah yaushe zaki bar zuciyar ki ta huta?"
"Sai ranar da na koma ga Mahalicci na, makoma ta nake tunani Gwaggo, idan amanar wasu ta tashi kama ni ya zata zo min, wata rana zata zo Gwaggo ke kanki zaki gaji dani ki gujeni,
ba zan auru ba Gwaggo dan babu wanda zai auri makauniya, duka kawayena sun bar ni saboda suna ganin yanzu bana iya komai, hakika hausawa sunyi gaskiya da sukace duniya ta ishi kowa ri da wando wanda bai zo ba ta shirya masa balle mu da muke cikin ta"
Gwaggo ta share hawayen idonta tana faɗin
"Babu wannan ranar Safiyyah, bazan taɓa gudun ki ba Allah dai ya baki lafiya"
"Amin amman wannan idon ka ba zan taɓa warke ba"
"Kada ki yanke kauna daga Rahama Allah"
"Kai ni ɗaki na zan kwanta"
Gwaggo da kanta ta rika ta suka nufi ɗaki ko wane zuciyarsa babu daɗi.
**** **** ****
As usual da ledoji ya shigo parlor, ganin bata parlour kuma bai ji motsinta kicin ba ya tabbatar masa da tana ɗaki, a parlour ya aje ledojin ya nufi ɗakinta, ya tura kofar ɗakin yana faɗin
"I'm back"
A wahale ta ɗago ta kalleshi tace
"Sannu da zuwa"
"Yauwa Baby na, ina ɗayar Babyn?"
"Ta raka Lubna da kawayenta rabon anko"
"Kin san ban cika son yawan fitar nan da take ba ko, bana son ta saba da yawon nan"
Ita dai bata ce komai ba nata ya ishata, sai a lokacin ya lura da halin da take ciki,
"Meke damun ki?"
"Marata ke ciwo"
Ta faɗa tana dantsar baki, karasowa yayi ya rik'a ta daker tayi zaune, a nan yaga jini, zaro ido yayi
"Subhanallahi"
Hannayensa yasa ya ɗauke ya nufi bedroom da ita, ya cire mata kayan jikinta ya gyara mata jikin sannan ya ɗauko doguwar riga yasa mata da hijab, ya ɗauke ta ta nufi mota da ita.
60
Safa da marwa ya rik'a yi a bakin kofar, yana haka Mummy ta iso
"Tana ciki?"
Shine abunda ta fara tambaya daga isowa, a natse ya gaishe ta bayan ta amsa yace
"Eh tana ciki"
"Haihuwar ne?"
"Ina jin shine ban dai tabbatar ba"
Kujera ta samu ta zauna, hankalin ta ba a kwance ba, sai Addu'a take, Saif ma ita yake a inda yakr tsaye,
Bayan kamar awa biyu da wani abu wata nurse ta fito daga ɗakin da sauri,
"Kuje ku kawo kayan jariri matar ka ta kusa sauka"
Tana faɗar hakan ta nufi wata hanyar da sauri, shi kan tsaye yayi kamar wanda bai ji abunda tace ba, Mummy ta kalleshi
"Kun sayi kayan jariran?"
Ya ɗaga mata kai
"Eh suna can gida"
"Okey ba ni keys ɗin zan ɗauko"
Mika mata yayi dan shi kan baya jin zai iya barin gurin har sai yaji ance matarsa ta haihu. Mummy na karɓar keys ɗin ta ɗauki jakarta ta fice da sauri, ba tayi minti biyar da fita ba sai ga Momy ta iso tare da Nasir, ganin Momy ne yasa shi zama a kujerar dake gurin yana karfafa ma kansa guiwa, a gurin suma suka zauna ko wanne zuciyarsa cike da zullumi, suna haka har Mummy ta dawo, kusan set set biyar tazo dasu na kayan jarirai da duk wani abun da tasan za'a bukata, isowarta yayi dai dai ta fitowar nurse ɗin tace a bata kayan jarirai, Mummy na cikin gaisawa da Momy ta juyo, ta mika mata kayan, gurin karɓa ne ta kalli Saif tana murmushi tace
"Matarka ta sauka ta haifa maka kyakkyawan kuma lafiyayyen jariri"
"Alhamdulillah"
Shine abunda ya furta ta rungume Nasir yana dariya, Mummy da Momy ma ko wanne fuskarsa ɗauki take da farinciki, suna yi ma Allah godiya,
Bayan sun gama gyara jaririn suka fito dashi daga ɗakin, Momy da Nasir suka rika rigangan gurin karɓa,
"Masha Allah"
Nasir ya faɗa yana rumgumar jaririn a hannunsa, Momy ce ta biyu gurin karɓa bayan Nasir, sannan Mummy, Saif ne na karshe, ya rungume ɗansa