Showing 54001 words to 57000 words out of 115850 words
Chapter 19 - BABBAN GORO Complete by Khadeeja Candy .txt
allurar zubar da ciki”
Sakinta Mummy tayi ta jingina jikin gina ta lushe ido tana sauke ajiyar zuciya,
Ta kasa gasgata abunda Kairat ta faɗa da kuma wanda Dr Zainab ta faɗa mata, miye gaskiya mi Dr take kokarin yi?
“Innalillahi wainna ilaihi raji'un”
Ta faɗa a fili still idonta na rufe hawaye suka zubo mata,
“Mummy ya kamata muyi wani abu ba wai mu tsaya tunani ba yanzu ba lokacin tunani ba ne”
Cewar Kairat cike da kaguwa, Mummy tayi mata kallon natsuwa kallon ɗa da uwa irin nasu na manya,
“Kairat Dr Zainab ta faɗa min ciwon Minal yana matakin....karshe ne zan iya rasa ta ko wane lokaci ta faɗa min idan har inason rayuwar ta dole ne nasa hsnnu a fitar da ita waje ayi mata canjin jini and you know yadda canji jinin yake zata iya rasa ranta babu tabbacin rayuwarta”
Dora hannu Kairat tayi saman kai a maimakon tayi kuka sai tayi murmushi mai tare da hawaye murmushin da ake cewa yafi kuka bakin ciki, ta cire ɗankwalin dake kanta ta jefar kasa ta rufe baki tana hawaye,
Mummy ma kuka take amman na zuci ko wannen su xuciyarsa ɗauke take da tausayin Minal, Sun daɗe a gurin babu wanda ya sake cewa wani abu sai faman sauke ajiyar zuciya Mummy ke yi, suna haka Dr Zainab ta iso gurin rike ta wasu files a hannunta, tsayawa tayi dai-dai Kairat ta dafa ta,
“Ki kwantar da hankalin ki ban zubar da cikin nata ba I'm just trying to help alurar bachi nayi mata yanzu haka tana can tana bachi”
Kairat ta kalleta kwakwalwarta a jagule bata ce mata komai ba, Ita bata ji ta ce mata ba ta cigaba,
“Na faɗi hakan ne dan kawai na ɓata Saif a idon Minal, a binciken da nayi na gano Minal tana fama da ciwo zuciya mai tsana ni kuma nasan akan Saif ne, a halin da ake yanzu Minal ta fi son abunda yake cikinta saman da Saif sanadiyar wannan abun da na faɗa zata sasauta ma zuciyarta sonshi ta kula da abunda yake cikinta
Kairat mutuwa ba a hannuna take ba amman Minal zata iya rasa ranta a ko wane lokacin abun tausayi rai biyu za a rasa tun da ga ciki a jikinta”
Sai a lokacin Kairat tayi mata magana,
“Amman taya akayi kika san Minal.na son Saif har haka? Ban yarda dake ba Dr faɗa min wacece ke?”
Murmushi tayi ta gyara tsayuwarta,
“Nasan Abunda yake damun Minal saboda ni likita ce, nasan halin da Minal take ciki saboda ni aminiyar kishiyarta ce Huda nice kaɗai mace da zan iya wanke Minal a.yanzu ni nasan yadda aka kulla komai”
Ja da baya Kairat tayi cike da tsoro tana kallonta, Mummy ms kallonta take cike da rashin fahimta,
Ganin hakan yasa ta cigaba
“Kairat yanzu taimako ɗaya nake son kiyi ma yar'uwarki ina son ki ɗauki waya ki kira Saif ki faɗa masa nayi ma Minal allurar zubar da ciki”
“Saboda me?”
Kairat ta tambaya,
“Saboda yazo nan na faɗa masa gaskiya na wanke minal daga zargin da yake mata kinsan ganin Saif ba abu ne mai sauki ba sai idan shi yaso ganinka”
“Miye dalilinki na taimakon Minal? Bayan ke aminiyar Huda ce wata kila ma dake a ka haɗa kai akayi mata wannan shaerin?”
Mummy ta faɗa tana mata wani kallo mai cike da tsana,
Murmushi kawai tayi ta kalli Kairat,
“Ki kirashi yanzu nan”
Tana kaiwa nan ta juya ta bar gurin, Mummy ta matso kusa da ita,
“Karki kirashi Kairat baki sani ba ko wani sherin ne take son kulla mana”
Kai kawai ta ɗaga ma Mummy ta nufi Hanyar da zata sadata da ɗakin da Minal take kwance, ganin hakan yasa Mummy ta rufa mata baya suka shiga ɗakin tare.
* * * *
Ya daɗe tsaye a bakin kofar sannan ya mika hannu ya buɗe ya shiga, shi kan inba dan faɗan da Momi tayi masa ba jiya babu abunda zaisa ya sake shiga ɗakin dannya bashi haushi shiyasa tun jiya da aka fito da ita daga aikin bai leko ba,
Tana kwance an ɗaga kafarta da akayi ma aikin da wani farin abu hannunta kuma na saman cikinta idonta a buɗe fuskarta so indecent. Sai da ya karaso kusa da ita sannan ya ɗauke idonsa daga kallon tsanar da yake mata, daga jiya zuwa yau tsanar da yake mata ta karu sosai ko dan faɗan da Momi ta masa oho ko kuma dan kowa ganin laifinsa yake yana ganin wai kiyyayar da yake nuna mata yayi yawa ne, shi dai bai san dalili ba daman can Allah bai haɗa jininshi da ita ba tun tashin ta gidan su.
Tun daga buɗe kofar ɗakin tasan shine ya shigo saboda kanshin turarensa jira take har sai yayi mata magana sannan ya juyo ta kalleshi, jin bashi da alamun yi mata magana yasa ta juyo da fuskarta ta kalleshi, hawaye ne suka cika mata ido yana sane da tana sonshi amman yayi mata wulakanci ya tsalake ta yayi mata biyu baya tausayin halin da take ciki shi sam bata gabanshi wannan wane irin mutun ne haka miyasa ma ta kamu da sonshi har haka.....?
Murmushin da yayi mata ne ta katse mata tunani, dan abunda bata taɓa zato bane daga gareshi, hakan yasa ta samu karfin motsawa har da sa ɗayan hannunta ta share hawayen da suka zubo mata,
“Sannu Sister”
Jimmm tayi bata amsa ba bakinta yayi mata nauyi sosai, daman tun da aka fito da ita daga aikin ba wata magana take ba daga ae sai a a,
Kujera yaja ta zauna yana fuskantar ta rasa yayi abunda zai ce mata
“Kin ci abinci.?”
Ya faɗa instead of yace mata ya jiki, daɗin tambayar da yayi mata da hana ta ɗaga masa ko da kai ne balle tace masa ‘Ae’ shi kan ba karamin juriya yake ba gurin sake mata fuska dan kawai yana son bin umarnin Momi ne,
Wayarsa ta tayi kara kamar mai jira ya fito da ita da sauri yana duba mai kiran, Number Kairat ce har yayi kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya dannan picking ya kara a kunne, saboda isa yaki yayi magana duk da faduwar da gabansa yayi saboda kukan da yaji Kairat ɗin nayi,
“What”
ya amsa da karfi tare da mikewa tsaye,
“Waya mata?”
Bansan me aka ce masa ba na dai ga ya kashe wayar ya juya da sauri ya bar ɗakin.
Kai tsaye ya ya nufi asibitin yana isa ya nufi ɗakin da yasan Minal take, yana tura kofar ɗakin ya ganta kwance ya sharar bachinta hankalinta kwance zuciya kuma zaune, numfashinta na tafiya dai-dai, da sauri ya karasa kusa da ita ya shiga duba jikinta kamar wani likita ganin babu alamun wani abu a tattare da ita yasa shi ɗan ja baya ya dafe kai yana sauke ajiyar zuciya, zuwa can kuma ya matso yana kallon fuskarta, ya kai hannu ya shafa cikinta,
“You love her Saif you can't leave her can you?”
Dr. Zainab ta faɗa tana takowa kusa dashi a hankali, a fusace ya juyo yana mata wani wawan kallon
“Me kika mata.?”
“Me kake tunanin zanyi mata? Meye damuwar ka da abunda zanyi mata tun da baka damu da abunda ya shafe ta ba baka son abunda yake cikinta!”
Ta karasa maganar dai-dai lokacin da ta karaso kusa dashi, ta aje wasu files ya kalli Minal cike da tausayi sannan ya sake kallon shi,
“Saif yarinyar nan tana level ɗin da zata iya ransa ranta a yanzu a anjima a gobe, kuma idan ta mutu rai biyu za'a rasa rayuwarta da kuma abinda yake cikinta amman hakan bai dame ka ba baka damu da duk abinda zai same ta ba sai yanzu nake ganin laifin duk mace da take sonka dan baka cancanci a so ka ba baka san miye so ba baka san darajar so ba ba kuma san zafin so ba!
miyasa baka tsaya kayi tunani ba Sai kawai ka ɗauki karan tsana ka ɗorawa Minal ?”
Hannayensa yasa cikin aljihu yana murmushin gefen fuska,
“Kin cancanci a biya ki da wadan nan kalaman tell me nawa suka biya ki i can paid more you know Who I am right?”
“Ba biyana akayi ba Saif gaskiya ce zatayi halinta lokaci yayi da ya kamata kasan wayr Huda wacece Safiyyah kuma wacece Minal”
Tsaki yaja ya ya juya da nufin ficewa daga ɗakin,
“Minal bata aikats abunda kake zarginta dashi ba, Abinda idonka suka gani plan ne da kanwar ka Safiyyah ta haɗa tare da Deen da Huda aka haɗa komai!”
Cak ya tsaya dai-dai lokacin da ya kai bakin kofar ya juyo yana mata wani kallo irin karki raina min hankali fa,ganin hakanyasa ta cigaba
“Ina da sheida akan hakan Saif nasan kasan ni aminiyar Huda ce duk abinda tayi sai ta faɗa min ina da voice record ɗin duk abinda ya faru zan iya haɗa plan ka kama Huda da idonka kaga irin cin amanar da take maka tare da abokinka matarka Huda ita kanwar ka Safiyyah sun same ni har gida suka ce na zubar da cikin Minal saboda idan ta haihu asirin su zai tono zasu bani ko nawa nake so ina sa security camera a gida na tana zan iya nuna maka komai idan kana so Saif Huda bata haihuwa ita kanta tasan da wannan amman tana shan magani hana haihuwa saboda tana jin tsoro kar Allah ya jarrabe ta ta samu ciki da wacan abokin naka kuma tasan duk ta haihu sai ta samu matsaƙa da wacan abokin naka ko kuma nace tsohon saurayinta, baka taɓa ksmata da kwayoyin hana haihuwa ba? ita da kanta ta bugo min waya ta faɗa min”
Shi kan yama kasa gane duniyar da yake shin mafarki ne ko gaske ? maganganun yaji kamar saukar wahayi, idan har da gaske ne miyasa zata tona asirin aminiyarta?
kamar tasan abunda yake ranshi sai kawai ta tako ta karaso kusa dashi
“Nasan zakayi mamakin dalilin fallasa sirrin Aminiya ko? toh akwai dalili duk waɗannan abubuwan dana faɗa maka ba zan tabbatar maka da su ba har sai ka biya min wata bukata tawa”
Kallonta yayi fuskarshi ɗauke da mamaki zuciyarsa kuma cike tambayoyi, bai tanka mata ba ita ma ɗin bata jira ya tanka mata ba tace
“Wani tsoho nake son kasa a sako daga gidan yari ni kuma zanyi maka duk abinda kake so”
Har lokacin bai iya mata magana ba but still yana kallonta maganganun ta sai dawo mishi suke.
KUN SAN WANENE TSOHON.?
[9/16, 6:47 AM] Auntie Candy: BABBAN GORO
NA
KHADEEJA CANDY
®
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
_Filin wasan giwa ba na biri bane idan kaga kashi a turmi bana wadan kare bane kuma wanda ya raina tsayuwar wata sai ya hau ya gyara, ra'ayi riga👌🏿_
*37*
“Wanene wannan Huda..!?”
Ya tambaya cikin tsawa, fuskarsa na nuna ɓacin ransa karara dan har jijiyar wuyansa ta tashi,
Ba jikinta ba har hanjin cikinta zan iya cewa rawa suke, abunka da marar gaskiya sai kawai ta fashe da kuka, Fusata sosai ya karayi cikin ɓacin rai ya zaburo mata da gaggausar murya
“Ba magana nake miki ba ki ban amsa mana karamar yarinya ce ke da zaki tsaya kina min kuka!”
Hantar cikinta ce ta kara kaɗawa yayi mata tsawar da bai taɓa mata irinta ba, da sauri ta share hawayen idonta ta kalleshi da ido kamar zasu fito
“Ban sani ba Saif ban sanshi ba”
Yayi mata wani kallon rainin wayyo
“Baki sanshi ba na samu number shi a wayarki?”
Kukan ne ya sake dawo mata amman wannan karon marar sauti, saukowa tayi saman gadon ta zube kasa kamar mai neman gafara sai murzar hannayenta take tunani take yadda zata kare kanta amman bata da mafita, buɗe baki take sonyi tayi masa magana ta kasa, toh mi zata ce masa hakuri zata fara bashi ko kuma kare kanta zata yi duk tabi ta ɗimauce lokaci ɗaya sai zufa ke karyo mata.
“Tashi kije gida Huda karki yar da ki kwana a gidan nan”
Kamar saukar wahayi taji maganar, abunda bata taɓa zato ba ko da a mafarki ba, ne hakan yake nufi? sakinta yayi kenan ko me?
“Gi....gi...gida ..fa..ka..ce Saif..”
Ta faɗa muryarta ta rawa, shi kuma ya bata amsa a tsawa ce
“Gida nace ki tafi kinsan mi nake nufi ai karki yarda na dawo tarar dake a ɗakin nan”
Yana faɗa ya juya a fuce ya fice, lallai da sauran rina a kafa, dan ba wai ya hakura bane da sauran magana, ita kanta tasan asirinta ya tonu, bata da hanyar kare kanta fatan ta ɗaya kar ya rabu da ita.
* * *
A fusace ya isa asibitin da Safiyyah take, bai damu da dare ba dan goma ta gota shaɗaya ake batu, da wani irin karfi ya tura kofar ɗakin, sai da ganin Momi da Gwaggo ya katse masa hanzari,
“Saif Lafiya dai?”
Momi tayi masa tambayar cikin mamakin ganin shi yanzu da kuma jallabiya, tasan Saif baya son fita da jallabiya a ko ina idan ba gida ba.
Duk yadda yasa ya ɓoye damuwarsa a fuska kasawa yayi saboda ɓacin ran nashi yayi muni da yawa sai dai bai faɗa mata komai,
“Ba komai Momi gurin Safiyyah nazo”
Ya faɗa kamar baya son magana, sautin muryarsa da kuma yanayin fuskarsa ya karantar da Momi halin da ɗan ta yake ciki, lallai ba lafiya ba ganin mai ido da sanda,
Gashi kuma yazo da dare abunda bai taɓa ba tun da aƙka kawo Safiyyah,
“Momi ƙku ɗan bamu guri zamuyi magana”
Maganar ta bata mamaki wace irin magana ce da ba zai iya faɗi a gabanta ba? Gwaggo ce ta katse mata hanzari ta hanyar buɗe kofar fita tana faɗin,
“Bari mu fice tun da ba a son muji”
Ganin ta fice yasa Momi ita ta fice zuciyarta cike da rashin yarda.
Suna fita Safiyyah ta kalleshi fuskarta ba yabo ba fallasa, tasan waye Saif tun kamin tasan kanta ta kuma san irin tsanar da yake mata babu abinda zaisa ya taso cikin dare yazo duba ta daga ganin ma fuskarsa ka san ba lafiya ba, ga kuma guguwar harar da yake watsa mata,
Kofin dake hannunta na tea ta aje ganin yadda ya nufo ta kamar mai shirin ɗaukar ranta yau kan ita dashi sai Allah, gawa ta rike mai mata wanka duk da bata san meke tafe da shi ba amman tasan ba alheri bane,
“Mi Minal tayi miki kike cutar da ita? Mi yasa kike son kashe min ɗana jinina? yaushe zaki karantar da kanki ba zan taɓa son ki ba? wace irin mahaukaciya ce ke?”
A lokaci ɗaya yayi mata waɗannan tambayoyin yana ɗaga murya, hantar cikinta ta kaɗa cikinta ya ɗuri ruwa, yawun dake bakinta ya tsinke asirin ta zai tonu, fuskarsa take kallo idanunta a razane tana neman mafita,
Kura mai wayo abunku da yar bariki a nan take taso saye shi da murya kamar tayi kuka
“Subhanallahi wannan wace irin magana ce haka Yaya? me kake nufi ne? Kar dai a shafa min bakin fantin da aka shafa ma Minal a juyar da wannan lamarin a gare ni”
“Kinsan me nake nufi Safiyyah, kuma wallahi duk wani abu ya samu ɗa na ki kaddara ke ya sama”
Hawayen dake makalle a idonta suka zubo, jin yadda ya katsa mata tsawa
“Na san baka so na yaya maybe yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa aka min wannan sherin amman yaya ba zan aikata maka haka ba me zai sa na aikata maka haka waya yake kokarin haɗa ni da kai ne?”
Kuka take yi ta marairaice murya kamar gaske, bai saurara mata ba dan yanzu baya ganinta da kima balle yaga tausayinta, shi dai so yake ya kara tabbatar da gaskiyar abunda yaji da kuma wanda Dr Zainab ta faɗa masa, ita kuma taki bashi damar hakan dan ta marairaice ita sam ba ita bace haɗa su ake son ayi,
Akwai kamshi gaskiya a labarin da Zainab ta bashi tun da gashi ya kama Huda Safiyyah ce kawai ta rage masa so yake ta amsa da bakinta ta aikata ɗin ko kuma ta nuna masa alamun hakan dan yasan wannan kukan na munafurci ne wai ita yar duniya shi take son rai na ma hankali.
Jin yayi shiru yasa ta fara tunanin ko hakarta ta cin ma ruwa ne? Lallai ya fara yarda da ita tun da har ya tsaya sauraren kukan ta, ta kalleshi idonta rau-rau da hawaye,
“Wai Yaya waya faɗa maka wannan maganar ne?”
“Ubanki ne ya faɗa min”
Bata an karaba yayi mata ɓarin makauniya ya wanke mata fuska da mari biyu masu kyau, har sai da taga wasu yan taurari nan take bakinta ya haɗe da jini da miyau, bai damu da ciwon dake kafarta ta ya ɗebeta kamar kayan wanki ya jefar ya hau shurinta kamar an aiko shi,
Razanannar karar da ta saki yasa Momi suka shigo da gudu, Yadda yake aika mata shurin sai da yaba Momi tsoro, duk yadda taso ta jashi baya kasawa tayi shi kuma yaki ma kallonta sai shurin Safiyyah yake,
Tassss-Tasss Momi ta watsa masa mari, bai ji zafin marin ba duk da marin ne yasa ya ɗan natsu ya kalleta,
“Ba kada Hankali baka da imani Saifullah mi yarinyar nan tayi maka haka? koma wani abun tayi maka aika duba halin da take ciki”
Cikin kuka Momi tayi masa wannan kalamin, dai-dai lokacin Nurses suka shigo tare da Gwaggo dan ita ce ya fita ta kirasu ganin Safiyyah ta suma,
. Kukan Momi yasa jin ba daɗi shiyasa shi bai ma jidaɗin da ya tararda ita a asibitin ba daman yasan hakan sai ya faru ko da bayan idonta balle a gabanta,
“Momi yarinyar nan ita ta kulla komai duk abinda ya faru da Minal ita ce ta kullah kuma a yanzu haka so take ta zubar da cikin Minal”
Yana kai aya Momi ta sake watsa masa wani mari, ta kalleshi rai