Showing 33001 words to 36000 words out of 115850 words
Chapter 12 - BABBAN GORO Complete by Khadeeja Candy .txt
biyo fita zakayi ne.?”
“Ae zan ďan leka gari ne kinsan yau sunday amman Huda tana ciki ai”
“Okey Allah ya tsare bari na shiga mu gaisa,”
Ra6awa tayi gefensa ta shiga falon tana faďin daman ai ba gurinka nazo ba.
Kujera ta samu ta zauna,sai da taji tashin motarsa sannan ta kwalama Huda kira.
“Anty Huda fito gani a falo”
Ta ďan daďe zauna kamin ta tashi, ta nufi hanyar falon, Tun kamin ta sauko kasa ta haskaka fuskarta da murmushi, bayan ta sauko ta zauna kusa da ita tana faďin
“Sannu da zuwa yan matan Hajiya”
“Yauwa ya gidan?”
“Lafiya, aiko yanzu Yayanki ya fita”
“Ae na gamu dashi ai har mun gaisa daman Allah Allah nake karna tarardashi”
“Hmmm ai yanzu bai fiye zama gida ba kullum busy yake”
“Ki kwantar da hankalinki mijinki ya kusa dawo wa gareki nan da wasu yan kwanaki”
Huda ta gyara zamanta ta dafata,
“Amman safiyyah ta wace hanya kike ganin zaki iya hana auren nan.?”
“Ta harya da muka shirya nida Sauranyinta idan ya amince”
“Saurayinta kuma waye kenan”
“Abokin ta ko kuma ma nace amininta wadda yakr shirin aurenta taki aurenshi ta za6i Saif”
“Me zakuyi kenan zai aure ta ne?”
“A a na aurenta zaiyi ba ai yanzu babu yadda za'ayi ya iya aurenta saboda an riga ansa rana yanzu haka daga gurinshi nake kuma idan har ya amince ana ďaura auren auren zai mutu”
Sam maganar bata yima Huda daďi ba dan ita so take a hana auren ba wai sai anyi a lalata ba, toh idan kuma hakan bai yiyu ba fa zamansu na aure zasuyi wadda ita kuma ba zata iya jurar ganin mijinta ta ko wace mace ba.
Cikin yanayin damuwa ta kalli Safiyyah,
“Amman kina ganin hakan zai yiyu kuwa karfa aje ayi auren daga karshe yaki rabuwa ni wata qawata ma faďa min take na shiga malamai nasa a lalata auren”
Safiyyah ta girgiza mata kai,
“Ban yarda da wannan ba ban baki shawarar shiga malamai ba dan ba hanya bace ni nan ni na tsara komai kuma ina son ki bar min komai a hannuna kawai abunda nake so dake ki daina nuna masa kishi da damuwa ki nuna masa kin yarda da kaddara”
“Zanyi amman ina son kiyi min alkawarin ba za a samu matsala ba”
Tashi tayi tsaye ta rataya jakarta, tana faďin
“Nayi miki bari naje gida kar Momi ta neme ni dan tun safe na baro gida Gurin Deen na daďe shiyasa kika ga ban zo nan da wuri ba”
“Ok zanyi duk yadda kika ce Allah ya bamu sa'ah”
Murmushi tayi, har ta juya sai kuma ta juyo tana wani abu da baki,
“Kafin na manta zaki bamu tsohon saurayinki aro dan shima zanu anfani dashi”
Dakan uku-uku gaban Huda yayi, wane tsohon saurayinta take magana ne, ya akayi tasan har yanzu suna tare, ina ma ta sanshi, cikin ranta take wannan tunanin nurmfashinta na wani abu irin na marasa gaskiya,
“Mi kike nufi ne ban fahimta ba”
Cikin karfi hali da taku tayi mata tambayar. Safiyyah ta bushe da dariya twyi kwallon cingan ďin dake bakinta,
“Kinfi ni sanin abunda nake nufi mana anty Habib nakr nufi tsohon saurayinki na da da yanzu abokin mijinki”
Zaunawa Huda tayi saman kujerar da raunanin idanu gumi na karyo mata. Nan Safiyyah ta kai hannu ta dafa kafaďarta,
“Ki kwantar da hankalinki na daďe da sanin kuna tare tun kamin ki auri Yaya ammanbban ta6a faďawa kowa ba yanzu ma dan kawai ta kama sai munyi amfanin dashi ne da bazaki sani ba”
Huda bata iya ce mata komai ba sai kawai ta bita da ido tana kallonta har ta fice. sannan ya jingina da kujerar tana mamakin yadda akayi tasan suna tare, toh ko dai itama yana tare da ita ďin ne, ko kuma wanine ya faďa mata amman kuma wayasan suna tare balle ya faďa mata, ? toh ya akayi tasan suna taren ne.? wannan tambayar ita ta tsaya mata a rai.
*****************
“Mummy wai...-”
Ganin hawayen dake idonta yasa Minal ta kasa karasa maganar ta nufeta da sauri tana tambaya
“Lafiya Mummy kike kuka mi akayi maki ne.?”
Ďagowa mummy tayi da murmushi a fuskarta tace,
“Hawayen Farin ciki ne Minal bana bakinciki ba ashe zan ga wannan ranar da zan rika katin ďaurin aurenki a hannuna”
Rumgumeta Minal tayi,
“Ai kinsan Mummy komai lokacine dashi kuma yadda duk Allah ya tsara wani bai isa ya sauya shi ba”
“Haka ne Minal nayi farinciki na jidađi sosai ko ina zan aika wannan katin (iv) har gurin dangina”
A nan Minal ta gyara zamanta ta gaďiye yawun dake bakinta,
“Yauwa Mummy kinsan inda dangin mahaifina suke.? zaki iya kwatanta min su?”
Maganar sam batayi ma Mummy daďi ba, a fuskarta ma karara zaka iya karantar hakan,
“Miyasa Minal.? miyasa ke zaki neme su bayan su basu nemeki ba mi zakiyi musu.?”
Kwantowa tayi jikin Mummy, ganin yadda fuskarta ta nuna rashin jindađin maganar da tayi mata, sai ta canja manufar maganar ta
“Ni mi zan musu kawai dai zan yima masa cin mutunci ne jifa yadda na wulakanta ni”
Kanta Mummy ta shafa, tana sauke ajiyar zuciya,
“Basai kinyi mashi ba Allah yana kallo ai shine zai saka miki ki kyaleshi kinji.?”
“Okey my Mummy bazan sake ba”
“Allah yayi miki albarka yabkara miki lafiya”
“Amin mummy bari naje zamu duba gurin da zayi diner ne da irin kwaliyar da za'ayi masa”
“Ok sai kin dawo ki kula da kanki”
Murmushi tayi, ta tashi ta fice. Mummy kuma ta janyo wayarta ta shiga kiran masu fanti.
*☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆*
Shi na mussaman Mummy take, dan ko zama yanzu bata samu, bayan tasa ana gyara mata yar'ta, sai ita kuma ta shiga gyaran gida, da kuma maida hankali gurin shiraruwan biki.
Kullum mai dilka take zuwa tayi ma Minal, abunda da mai kyaun jiki cikin kwana biyu ta canja kala tayi kyau sosai batar jikinta ta wani taushi kamar kaďa, Yau ma kamar kullum tana zaune ana gyara mata jikin Safiyyah ta turo kofa ta shiga cike da natsuwa, kamar ba ita ba,
Da sauri Minal ta tashi tsaye tana kallonta,
“Yau kuma da wace kike zo wane kalar cin mutunci kika zo dashi.?”
Minal ta tambayeta tana yatsinar hanci alamar masifa, dan yau koma da wace tazo ba raga mata zatayi ba, wacan karon ma dan bata da tabbacin son da Saif yake mata ne yasa ta kyaleta, amman yanzu kan sai ta mata tas tunda cin mutunci ba gado bane kowa ya iya,
A hankali ta dako kafarta har kusa da Minal, idonta cike da hawayen qarya ta soma magana,
“Banzo dan na 6ata miki rai ba Minal nazo ne danna nemi yafiyarki akan abunda nayi maki, ada ina ganin kamar ba daidai bane Yaya ya aure saboda abunda nake ganinki dashi a zahiri, sai Yaya ya zaunar dani ya karantar dani wacece ke ya kuma nuna min halinki, Minal na gane kuskure na kuma ina neman yafiyarki dan Allah ki yafe min”
Da sauri Minal takai hannu ta share mata hawaye,
“Daina kuka, ni daman ban rike ki da komai ba na yafe miki kuma naji dađi da kika gane haka”
Da kuka ta Qanqameta tana fađin na gode sosai Minal,
Abunda da wayayyiyar mace nan da nan ta murje ido kamar ba ita ba sai jan Minal take da fira, tana yaba kyauta da fađin wai yayansu yayi dace,
Sai kusan magari ba tabar gidan bayan Minal ta cika mata bayan mota da alherai babu yadda ba tayi ba akan ita ba zata da komai amman minal ta rantse sai ta jedasu hakan yasa dole ta yarda tana mata godiya har ta bar gidan.
Babu inda Mummy batw raba Iv ba, sai faman zirga zirga take za ayima yar gwalo aure, kowa farinciki yake agidan banda Kairat da sai dai ta nuna a fuska amman a ranta jin take kamar an ďaure ta da sarqa.
Anko kusan kala shida akayi dan ko wane event sai da ka fitar masa da kalar kayan da za'a saka, Amarya kan aba'a magana dan tsaddandin kaya Mummy tasa aka ďinka mata banda waďanda ango ya kawo mata ga kuma na lefe,
Tun daga Sokoto aka ďauko maiyi mata lalle da kitso.
Ranar laraba akayi sa lalle, kuma ranar akayi anki amarya kamar yadda al'ada ta tana da, washe garin ranar akayi kamu. ranar jumma'ah akayi walima da daren ranar akayi arabiya night, A maimakon dina.
Ranar assabar akayi ďaura aure bisa sadaki dubu hamsi ďaurin auren da yasamu halartar manyan yan'siyasa da masu hannu da shuni da kuma manyan yanbkasuwa har ma da yan kasashen waje abunda dai sai wadda ya gani, maroka kan an kwashi kuďi kamar ciyayi, Ango yayi kyau matuka kallo ďaya zaka masa kaga anihin zatinsa saboda yadda kayan suka kar6i jikinshi.
Sa maraicen ranar yan 6angaren amarya sukayi Fulani day, abun gwanin sha'awa kowa sai yabon bikin yake yan ďaukar hoto da bidiyo kullum sai sunyi aikinsu, sai kunga yadda Safiyyah ta saki jiki tana shigema amarya kamar ba ita ba,
Babu irin mutane da ba'a gayyato ba girin bikin har da mawaqan kudu Rahama sadau sune gaba gaba da Adam a zango cikin waďanda aka kayyato nan arewa,
Anyi 6arin kuďi kamar ba'a san zafin neman su ba, nikan nace ai kara da sukayi dan _idan da dama, dawo, adama asha da dama. ayi ta riya_ 😀
Da daren Ranar motocin ďaukar amarya suna iso, haka aka jerasu yadda kasan gwafna zaije kanfe, ko wace mota na tashi da wakar auren da Nura m inuwa yayi musu, kalolin motocin ďaya ko wace bak'a,
Nasiha sosai Alhaji Ibrahim Ahlam yayi mata, kasancewar daga gidansa za a wuce da ita gidan angonta, mummy kuma tun kamin tazo tayi mata tana, Kuka sosai Minal take na rabon da dayi da Mummy da kuma ganin yadda ita Mummy take kuka, sai kace waďanda suka rabu har abada,
Daker aka sakata, Kairat sai hanquri take bata tana kukan itama wadda ya zame mata biyu, riqe take da hannun Kairat har aka isa gidan angon nata.
Gida na gani na faďa tsabar haske sai kace da rana ne, ko ina na gudan fulawoyi ne.
A hankali aka fito da amarya bayan an buďe mata motar, falo sai kace aljannar duniya, dan bazaka ta6a gane najeriya kake ba sai ka fito waje,
Har cikin ďaki suka kai ta suka zaunar da ita saman gadon tunda Allah ya hallince ban ta6a ganin irinsa ba tsaya kwatanta muku yadda kyawon ďakin yake 6ata lokacine.
Basu fi minti ashirin da zama ba, ango ya iso tare da abokansa sai tsiya suke masa, sai kace yanzu ne yayi auren fari, Kallo ďaya Kairat tayi masa ta ďauke kai shi kan ko inda take bai kallaba, ita dashi ango sukayi dan ita blue shadda tasa irin tashi.
Bayan anyi abubuwan da al'ada ta tana da suyi musu sallama suka fice, har bakin kofar falo Saif ya rako abokaninshi yana musu godiya, su kuma sai sheďana suke masa.
Da suka fice, ya umarce masu gaďi da su rufe masa gate, shi kuma ya rufe kofar falo, ya nufi hanyar ďaki,
Kanta a kasa ya tararda ita, cikin wani kyakkyawan mayafi da alama kuka take, baiyi mamakin kuka nata ba tunda yasan duk mace d bat ta6a aure ba sai ta samu kanta cikin wani kalar yanayi,
Kusa ita ya zauna yasa hannu ya yaye mayafin dake jikinta yana murmushi,
“Kuka name kuka Minal tashi zakiyi muyi alwala muyi sallah nafila mu gude Allah ko”
Kai kawai ta ďaga masa alamar eh idonta na kasa ta kasa ďagosu ta kalleshi, ganin hakan yasa ya cire babbar rigarsa ya rika hannunta suka nufi banďaki,
tare sukayi alwalar suka fito, ya shimfiďa musu abun sallah bayan ya mika mata katon hijab. Raka'a biyu sukayi, suka sallame sannan ya rika kanta yayi mta add'ah kamar yadda Annabi ya koyar damu,
Sannan ta tashi ta ďauko plate da kofi ya zuba mata kaza da madara wadda aka aje a gefe sai kace kantin sai dasu, ya shiga bata da kansa tana ci a hankali kamar wata karamar yarinya, madarar da zai bata ma sai da ya kwatar da ita saman jikinsa, sannan ya bata, bayan sun gama ya goge bakinsa ya goge mata nata, maida plate ďin azauninsa ya buďe akwatin kayanta ya fiddo mata kayan bachi ya mika mata,
Hannu biyu tasa ta kar6a kamar yadda Mummy ta karantar da ita, duk rashin kunyar Minal yau sai ta samu kanta da kasa saka kayan gaban Saif wani irin nauyinshi take ji, dan haka ta nufi banďaki ta kulle kanta sannan ta saka kayan bachin,
Koda ta fito shima ya saka nashi, akasale ta karaso ta aje kayan data cire saman kujera. Bata ankara ba taji ya ja mata hanci yana dariya,
“Wai yau Minal kunya ta kike ji ne.? nifa ban gane wannan noce noce kanba kodan na rabaki da Mummy yau?”
Ita dai har lokacin bata iya ce masa komai ba. Ganin hakan yasa ya nuna mata gado,
“Hau ki kwanta nasan kin gaji da yawa yanzu nima bachi nake ji”
Ba musu ta nufi gadon ta kwanta, nan shima ya kashe wutar ďakin yazo bayanta ya kwanta yaja bargo ya lullu6e ta, ya kuma lullu6e kansa.
[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO
NA
KHADEEJA CANDY
Candynovels.wordpress.com
WATTPAD @khadeeja_candy
*27*
Bayan ya shafa addu'ar da yake, ya tashi daga saman sallayar ya nufi gadon, Bargon da ta rufa dashi ya fara janyewa, ya hura mata iska a hankali cikin kunne ya raɗa mata
“Tashi kiyi Sallah Bakwai ta kusa”
Cike da nauyin bachi ta buɗe idon ta kalli kyakkyawar fuskarshi daya kawata da murmushi, murmushin ta mayar masa sannan tayi unkurin tashi tana mika,
Bayan ta kare Sallah yazo gefenta ya zauna, ya zuba mata ido yana kallonta, sai da ta shafa addu ah sannan yace,
“Ga abinci can Mummy ta aiko tun ɗazu kuma tace zata sake aiko wani”
Juyowa tayi cike ta ladabi tace
“Ina kwana”
“Lafiya kalau kin tashi lafiya”
Da murmushi ya amsa mata yaji daɗi sosai, abunda huda bata saba masa ba tun zuwanta gidan, wai ita a ganinta ka kwana gida ɗaya da mutun kuma da safe ka gaidashi, ita a gurinta bako akeyima haka.
“Lafiya kalau”
“Toh. yayi kyau sai ki tashi muje muci abinci dan Mummy tace baki jikirin yunwa tunda uwar safiya kike karyawa”
“Laaaahhh”
Ta ɗan zaro ido tana kallonshi,
“Yaushe tace maka kodai kai kace da kanka.?”
Taɓe baki yayi ya ɗan juyarda fuska,
“Ta dai ce ke, sai idan mistake tayi ko bake take nufi ba, amman kuma idan ba ke bace mi yasa ta kawo wannan abincin da wuri haka tun gari baiyi haske ba”
Murmushi tayi mai sauti,
“Kawai malam kace min yunwa kake ji na tashi mije muci abinci ba wai ka ɗinga wani noke noke ba”
“A'a walllahi ai ni nakan kai sha biyu ma ban karya ba kuma jikina lafiya kalau ba kamar ke ba daman ace marasa kiba sunfi cin abinci”
Tashi yayi ya rika hannunta,
“Muje kiyi buroshi sai muci abincin”
Bathroom ya nufa rike da hannunta, Da kanshi yayi mata buroshi sannan yayi ma kanshi suka fito, a nan ya ɗauketa kamar wata yar baby ya nufi dinning room da ita, ita kuma ta shigar da kanta cikin kirjinsa sai faman dariya take tana faɗin ya sauke ta zata iya tafiya.
Sai da ya sauke ta saman kujerar sannan yace,
“Ai nasan zaki iya tafiya kawai bana son ki wahala ne”
Dariya tayi, shi kuma ya kashe mata ido ya shiga zuba mata abincin.
Da kanshi ya rik'a bata tana ci har sai da ya tabbatar da ta koshi sannan ya soma cin nasa, ido ta kura mishi kamar ba taɓa ganinshi ba, bai ankaro ba har sai da yq sarke da ruwan tea daya kuɓa,
“Ke kus kici kanki wannan kallo har ina kika kokarin sa na ka sarke”
Dariya tayi, ta tashi ta nufi kofar da ake bugawa,
Direban Dr. Salamatu ne rike da manyan kuloli da katon kwando gabansa,
Cike da girmamawa ya gaisheta, yace
“Wai gashi inji Hajiya tace a kawo muku kuma tace a gaida ku”
Kofar ta kara buɗe masa,
“Shiga dasu ciki amman kai ta aiko ɗazu.?”
“A a”
Ya faɗa bayan ya aje kalolin, sannan yasa hannu aljihu ya ciro wayarta ya mika mata,
“Ga wayarki inji Kairat”
Kai kawai ta ɗaga masa tana mamaki, ta mika hannu ta karɓa, shi kuma ya fice.
Rufe kofar tayi, ta nufo Saif yana faɗin,
“Toh Mr stomach ga wani abincin nn Mummy ta aiko”
“Wace Mummy.?”
“Mummy na mana”
Ta bashi amsa daidai lokacin da ta zauna saman kujerar dake fuskartarshi,
“Toh waya aiko da wannan? Ba mummy bace”
“I don't think so dan kasan bazata aiko da abinci biyu lokaci ɗaya ba”
“toh waya kawo.?”
“Kai ya kamata na tambaya”
“Wani ne ya kawo i thought ko direban Mummy ne”
Minal ta ɗan yatsine hanci,
“Or maybe aljani ne”
Wata irin dariya yayi,
“Daɗin abin dai tare muka ci ko! Ni har kinsa ma naji na koshi”
Itama dariyar tayi, ta tashi da sauri ta nufi ɗaki ganin yadda ya nufota.
Guraren biyar da rabi motar Safiyyah ta faka a gidan Minal, ta ɗan daɗe kamun ta fito cikin motar ta nufi babbar kofar falon,
Tana tura kofar falon kanshun turaren wuta ya daki Hancinta,
“Ina wuninku”
Tace da mutanen data tarar zaune falon cikin far'ah,
Duk suka amsa mata da lafiya kalau suna mata ya gida,
“Lafiya kalau ina Anty Minal?”
“Tana ciki wuce”
Ta fan gudu ta hau stars ɗin ta shiga ɗakin ta take zaton Minal ta ciki, katsancewar ɗakunann ba ɗaya bane,
Cikin sa'ah kuwa ta tararda ita zaune ita da wasu friends nata suna fira,
Da far'ah Minal ta tarɓeta, tana nuna mata kujera,