Showing 96001 words to 99000 words out of 115850 words
Chapter 33 - BABBAN GORO Complete by Khadeeja Candy .txt
jikin da ita kunyarta suke ji musamman Baba sun kan su sunsan abunda sukayi mata basu kyauta ba. itakan sai ta nuna musu kamar komai bai faru ba cikin jindaɗi ta kawo musu breakfast ta bisu da kallo zuciyarya cike da farinciki.
Allah mai Hikima lokacin da ya karɓe min ku sai ya bani Minal yanzu kuma ya karɓe abunsa sai ya dawo min da ku
A ranta take wannan maganar tana kallon yadda suke cin abinci. ba karamin daɗi mummy taji ba ganin Mahaifanta kusa da ita.
**** ***** *****
A hankali Kairat ta kai hannu ta buɗe kofar ɗakin
lil Minal sai a lokacin ta samu damar tsayawa tana kare masa kallo. ɗakine da aka kawata shi da kayan masu kyau ɓangaren tufafinta daban ɓangaren da gadonta yake dabam abun gwanin sha'awa.

Murmushi tayi ta karasa kusa da kayan nata ta buɗe ta ɗauko wata riga mai kamada ta sanyi da hula da talkami ta fito, a palo ta tsaya tana nuna ma Talatu kayan da za a saka mata, karɓa tayi ta tashi tare da Ita ta nufin ɗakinta dan Saif ya hana ayi mata wanka ko ina sai ɗakinta. itama ɗakinta ta nufa taje tayi wanka ta shirya cikin jar a tamfa mai ratsin baki. tana fitowa ta nufi kicin girki tayi na musamman dan Mummy ta faɗa mata tana nan zuwa kuma zata zo mata da wani abun mamaki.
Bayan ta kare ta dawo parlour ta zauna akai akai ta kalli kofa duk ta kosa Mummy tazo sai da ɗauki wayarta kamar ta kira sai kuma ta fasa tana haka har lil Minal ta tashi daga bachi aka kawo mata ita karɓa tayi tana shirin bata nono, taji an taɓa kofa,
“Oh my god”
Da sauri ta tashi tare da ita ta nufi kofar da zumuɗi ta buɗe, da mamakinta sai taga ba Mummy ba,
“Wanene ka.....”
Kasa karasa tayi lokacin da ya ɗago kai ya kalleta, kamannin Minal ta gani shimfiɗe a fuskarsa.
“Shigo”
Ta ce dashi cike da ladabi, ba musu ya shigo cikon palo ya xauna a gurin da ta nuna masa, sannan ya soma magana kamar zaiyi kuka
“Wata alfarma nake nema a gare ki”
“Faɗi ko ta micece zanyi maka matukar bata fi karfi na ba amman ka fara faɗa min wanene kai?”
“Zaki san wanene ni a cikin alfarmar da zakiyi min”
“Wace alfarma ce wannan”
“Na bi duk hanyar da zan bi wajen ganin Salamatu ta saurare amman taki a yanzu ma bana da hurumin bi koda kofar gidan ta ne an faɗa min ta hanyar ki ne kawai zata iya saurare har kuma ta yafe min, so nake ki shiga dani gurin da take ki kuma roke ta data saurare ni ko da ba zata yafe min ba”
Shiru tayi tana kallon yadda yake hawaye jikinta duk yayi sanyi, suna haka wayarta tayi kara alamar kira a sanyaye ta ɗauki kiran
“Hello Mummy”
“Na'am Dear ba zan samu damar zuwa ba amman na kira Saif zak kawo ki yanzu a nan zaku ci abincin rana har Abbahn ki yana nan tare da Suwaiba”
“Okey Mummy”
Ta amsa kamar ba taji daɗi ba, ta kashe wayar. tashi tayi ta nufi ɗakinta, bata fito ba sai da taji shigowar Saif sannan ta aje Lil Minal ta, taso ta nufo downstairs,
“Wow Beauty na”
Ya faɗa yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi,
“Sannu da zuwa”
Sai da ya aika mata kiss sannan ya rumgume ta yana faɗin
“Yauwa Wannan kwaliyar fa?”
Gurin wuyanta ya ɗora kansa yana goga mata dogon hancinsa, ita kuma sai kokarin zame jikinta take
“Akwai mutane a falon fa”
Bai kula ta ba sai da ya gama abunda yake son mata wannan ya juyo yana kare ma falon kallo, sai a lokacin ya lura da abunda take magana a kai, juyowa yayi ya kalleta da ɗan ɓacin rai
“Amman kuma shine baki saka hijab ba?”
“Kai kace min na daina sawa a gida”
“A ina nufin idan mi kaɗai ne a gidan ba jeki ki saka hijab ɗin ki”
Murmushi tayi mai sauti har da fitar da halshe tana masa kallon zolaya, ta juya ta nufi upstairs, shima da kallon ya bita dan bai taɓa ganin hakan a fuskarta ba tun da tazo gidan.
Tana shiga ɗakin ya shigo juyowa tayi ta kalleshi
“Mummy tace ka kai mu gida a can zamu ci abincin rana shine tace mu wuce da wannan mutunen”
Ta faɗa dan tasan sai ya tambaye da wanene kuma bata san karyar da zata nasa ya yarda suje dashi ba,
“Really?”
Ya tambaya kamar bai yarda ba, taɓe baki ta ɗanyi
“Na taɓa maka karya ne?”
“Na sani ko yanzu zaki fara”
Yaja hancinsa juyawa tayi.sanin nufinta yasa shi kisgota ta faɗo saman kirginsa suka faɗa saman gado. sunfi minti talatin a kan gadon yana aika mata da sakwannin ita kuma tana son kwace kanta amman ta kasa har ta gaji ta hakura. sai da yaji wayarsa na ringing sannan ya sake ta ta tashi tana duba wayar number Mummy ce baiyi picking ba dan yasan yana picking zata ce masa ya kawo Kairat. Bathroomƴa nufa, bai daɗe ba fito ya ɗauki keys ɗinsa,
“Saka hijab ɗin ki muje”
Da sauri ta nufi gurin da hijaban nata suke ta ɗauki wanda yayi kala da atamfar ta saka sannan ta ɗauki lil Minal ta kalleshi alamar ta shirya,
Matsowa yayi kusa da ita ta yadda tana iya jin bugun zuciyarsa tana mata wani kallo
“Idan muka dawo anjima zan baki wani muhimmin sako”
“Wane irin Sako ne haka?”
Ta tambaya kamar bata san abunda yake nufi ba duk da tasan manufarsa. murmushi kawai yayi yaja hannunta suka fito.
Sai da zasu shiga mota Saif yake ma Alhasan kallon tsaf nan take gabansa ya rika faɗuwa yanayinsa ya canja. Bai ce da ita komai ba tun da suka shiga motar ita bata ce masa ba har suka gidan kowa da abunda yake tunani. ta ɗan daɗe cikin motar sannan ta fito Talatu ce karshen fita tasa hannu ta karɓi lil Minal ta wuce. A hankali take takawa gabanta na faɗuwa har suka isa cikin palon,
“Miye haɗin ki da wannan Kairat ina kika haɗu da shi?”
Mummy ta tambaya tana nuna sa da yatsa, bata bata amsa ba sai da suka kai tsakoyar parlour sannan ta kalli Mummy tace
“Dan Allah Mummy ki saurare shi na tabbata yayi nadama kuma akwai abunda yake son ce miki”
Tassssss Abbah ya wanke mata fuska da mari cike da ɓacin rai. Da sauri Saif ya jata ya maida gefensa ya ɗago yana Abbah wani kallo kamar zai rama mata.

LIL MINAL
53
Fashewa tayi da kuka Saif ya rumgume ta. Palon yayi tsit baka jin komai sai sautin kukan Kairat, Saif kan duk ya ɓata rai sam bai jidaɗin Marin da akayi mata ba gashi daman ran nasa a ɓace yake. jin kukan yayi yawa yasa Mummy ta nufe ta ta dafa ta
“Kairat”
Nan Saif ya sake ta ta rumgume Mummy ta cigaba da kukan, Mummy ta kalli Abbah
“Da baka mare ta ba”
“Na mare ta akan me zata shigo dashi cikin gidan nan har tace ki saurare shi ina kuka haɗu da shi?”
Ya karasa da faɗa yana kallon Saif, Kamin yayi magana Kairat ta ɗago ta kalle Mummy
“Shine ya kawo kansa akan yana so na masa iso gurin Mummy, saboda kin ki saurare shi, Mummy duk mai rai ajizi ne, matukar akwai rai a jikin ɗan adam toh kullum shi mai aikata laifi ne ubangijin mu ma muna masa ya yafe mana kina ganin da Minal na da rai kinyi mata adalci kenan ki wulakanta mata mahaifi?”
Wani wawan kallo Abbah ya watsa mata
“Sai yanzu na tabbatar da baki da hankali da tunani Kairat kin manta duk abunda yayi mata shi ya raba da duk wani jindaɗi na duniya yanzu har yana da damar da zaice a saurare shi ko an saurare shi yana da abun faɗi ne?”
“Ya zamo sila ne kawai dan haka Allah ya kaddaro mata ko dashi ko ba dashi sai hakan ya same ta miyasa ba zakuyi imani da hakan ba?”
Ta juyo gurin Mummy,
“Kalle shi mummy kalli yanayin shigarsa ke kanki kinsan ba cikin jindaɗi yake ba wannan kawai ya ishe shi ishara”
Hawaye ne suka cika mata ido ta sauke ajiyar zuciya, ta lumshe ido. ta daɗe a haka sannan ta zauna. Kairat ma zaman tayi tana kallon Mummy ganin hakan yasa Abbah ya tashi a fusace ya fice. sai a lokacin Hajiya Suwaiba ta samu damar magana,
“Kiyi hakuri Salama'tu ko bai komai kinyi masa nisa yanzu”
Kallonta Mummy tayi ta Kamar tayi magana sai kuma tayi shiru. Karasowa yayi kusa da Ita ya risina kasa idonsa na hawaye ya ce
“Kiyi hakuri Salamatu ki dubi girman Allah ki yafe min nasan na cutar da ke na kuma yi kuskure, tun daga lokacin da na gudu na barki ban sake ganin Alheri a rayuwa ta ba, lokacin da abun ya faru sai na bar yola na koma katsina da zama gurin yayan mahaifina a nan ne na haɗu da wata yar mai kuɗi muka kulla soyayyah gaf da zamuyi aure mahaifinta ya nema min aiki a Sky Bank sannu sannu har aka bani manager na Bankin sai dai tun da nayi aure duk wani jindaɗi na rayuwar aure da ake samu ni ban samu ba kullum da kalar cin mutumcin da take min saboda ganin karkashin mahaifinta na samu aiki gashi kuma Allah ya jarraɓe ni da wani abu na rashin samun haihuwa dan tun da na aure ta sai dai tayi ɓari amman ba dai cikin ya tsaya ba, muna haka na kulla soyayyah da wata yarinya wanke ke aiki karkashina
Sai muka rika kazantaciyar rayuwar ni da ita ta haka ta yaudare ni tasa na na shiga na fita na ba wani kawunta aron kuɗi kusan miliyan talatin daga lokacin da ta fahimci tafiya ta fara nisa sai ta bar zuwa aikin shi kuma babu shi babu labarinsa. matar da nake aure kuma ta addabe akan sai na sake ta ita ba zata iya zama dani ba, ba dan naso ba na sake ta sai naje na auri wata bazawara mai manyan Yaya duk da hakan ban samu haihuwar ba muna haka banki suka bukaci kuɗinsu ni kuma bana da su tun ina sa musu rana har suka gaji suka sauke ni daga mukamin bayan an same ni da wasu kananan laifuka da suka kama ni dasu daga karshe dai sai suka sayarda duk wani abun da na mallaka suka kuma kai ni kotu daga haka aka saka ni gidan yari, shekaruna shida a can ina cikin ta bakwai kwatsam sai gashi anzo kai tsaye aka ce an sallame ni, bayan sallama ta daga gidan yari na samu labarin mijin yata ne yasa aka sallame ni kuma ya biya kuɗin. a lokacin ne na samu kai na cikin wata rayuwa mai cike da nadama da dana sani tun daga lokacin na saka kafata gurin neman ki amman ban samu hakan ba har naje Yola gurin iyayenki na tabbatar musu da gaskiyar halin da na saki daga haka nazo abunja duk da hakan sai da nasha wahala gurin neman ki duk da yake ba a ɓoye kike ba, bani abun bakin ciki sai na tararda wanda nazo dan ta bata duniyar, bana iya misalta miki halin da na samu kai cikin ba ban san abunda zan ce ma halaccina ba ko da ke kin yafe min ita fa nasan ta tafi da son tasan waye uban ta na cutar da ku na cuci kaina......”
Shine yake kuka mai sauti Mummy kuma hawaye take wasu na bin wasu, Kairat ma kukan take Saif ma idonsa cike da hawaye. Kairat ta tashi ta karɓo Lil Minal a hannun Talatu taje ta mika masa tana faɗin
“Wannan shine abunda Minal ta bar mana. kamin ta rasu kance min ina ma zata ga mahaifinta da zata tambaye shi miyasa ya gudu ya barta baiyi tunani halin da zata shiga ba wace riba ya ci? ita kan tana son tayi masa wannan tambayar”
Rumgume Lil Minal yayi yana wani irin kuka. Saif ya tashi da sauri ya bar parlour, nan mummy ita ma ta fashe da kuka Kairat daman shi takeyi babu wanda baiyi kuka ba cikin parlour mutuwar ta ta dawo musu sabuwa.
Saif na bita ya nufi gurin motar sa ya kifa kansa ya lumshe ido kansa sai sarawa yake. bai ɗago ba har sai da yaji kukan wayarsa yayi yawa number Lubna ya gani yana ɗagawa tace
“Momy na neman ka”
Kashe wayar yayi ya sauke ajiyar zuciya ya buɗe motar ya shiga daman can baya son komawa parlour cikin hanzari ya bar gidan.
Har ya isa gidan ransa a ɓace yake babu abunda yake tunani sai Minal. ya daɗe cikin motar bayan yayi parking sannan ya fito ya nufi hanyar da zata sada shi da parlour gidan. Tsaye yayi yana kallon Safiyyah da ke kwance gurin tana kuka, kanta ba ɗankwali. tana ganinsa ta tashi zaune still tana hawayen abun tausayi. A sanyaye ya karasa kusa da ita ya risina yasa hannunshi a fuskarta yana share mata hawayen. ganin kukan nata yaki tsayawa yasa yaja zuwa kirjinsa ya rungume ta! sai shima ya samu kansa da kukan bai san dalili ba.
“Yaya...”
Lubna ta kira sunan nasa tana tsaye bakin kofar fuskarta ɗauke da mamaki. Haka yayi kamar bai jita ba duk da ya ganta, ya kara kankame Safiyyah ya lumshe ido.
TOFA! ANA WATA SAI GA WATA ? YAYA KENAN?
SHIN KUNA GANIN ABBAN MINAL YA CANCANCI YAFIYA KUWA?
KEEP VOTING DEARS😍
54
Ya daɗe a haka sannan ya buɗe ya ɗago yana share hawaye,. Har lokacin Lubna na tsaye tana kallonsu tada ita yayi tsaye ya rik'a hannunta suka nufi cikin parlour, saman kujera ya zaunar da ita sannan shima ya zauna yana kallonta yana murmushi. Lubna ma zaunawa tayi a kujerar dake fuskantar tasu ta kura musu ido kamar tv.
“Ta ci abinci?”
Ya tambaya yana kallon Lubna, Kai ta girgiza masa, yana ganin haka ya tashi da kansa ya nufi dinning ya zubo abincin a plate, ya dawo kusa da ita ya zauna ya rik'a bata a hankali tana ci,
“Lafiya?”
Ya tambayi Lubna ba tare daya kalleta ba ganin yaddata sakar masu ido ko kyaftawa bata yi, tashi tayi tana faɗin
“Bari na kira maka Momy”
“Ban saki ba”
Ya tari numfashinta, a nan ta koma ta zauna still bata daina kallon nasu ba. Sai da ya tabbatar da ta koshi, ya bata ruwa ta sha. Sannan ya tashi ya nufi ɗakinta Momy.
Goma saura kwata Saif ya shigo gida, kana ganin yanayinsa kasan baya cikin walwalah, kai tsaye ɗakinsa yana tunani, sam bai lurada Kairat dake falo ba har sai da tayi masa magana
“Sannu da zuwa”
Da sauri ya juyo, sai a lokacin ya lura da ita, a maimakon ya amsa sai kawai ya zagayo ya zauna kusa da ita yana murmushi ya kai hannu ya taɓa sakar wuyan ta
“Wannan kwaliyar fa”
“Uhm”
Kawai tace ta ɗauke kai ta tashi, da kallon Saif ya bita har ta shige ɗakinta sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tashi ya shiga ɗakinsa, wanka yayi ya shirya ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya fara da gajeren wando ya fesa body spray, ya hau saman gado ya kwanta yana shafa cikinsa. Babu wanda yake tunani a yanzu sai Minal maganar ta da akayi ɗazun ya dawo masa da tunanin ta a ɗayan ɓangaren kuma ga maganar da Momy tayi masa wai shine silar shigar Safiyyah wannan halin.
Kairat ce ta faɗo masa a rai cikin hanzari ya tashi ya nufi ɗakinta, tana kwance taji an turo kofar ɗakin, Lil Minal na gabanta ta zuba mata ido sai kallon ta take. zuciyarta ta nasalta mata Saif ne ya shigo ga kuma kanshim turarensa da fara kai ma hancinta ziyara tun kamin gayar ya iso, har ya mai da kofar ya rufe bata motsa a daga inda take ba tana jin ya kusa karasowa kusa da ita ta lumshe ido kamar mai bachi. Leka ta ya fara yi yana idonta a rufe, sai ya zauna gefen gadon yana kare mata kallo kamin ya kai hannu ya mirgino ta ta juyo gefensa ya rungume ta tsamtsam a kirjinsa
“I'm so sorry Momy ce ta kira ni shiyasa ban dawo ba, kuma hankalina ya ɗauku ban je na ɗauko ku ba”
Har yayi surutansa ya gama bata motsa ba balle ma tayi masa magana, ganin bata da niyar maganar yasa ya tashe ta zaune ya ɗora bakinsa daidai kunneta ya soma mata magana kamar mai raɗa
“Haba yar gidan Mummy kiyi hakuri mana nasan nayi laifi amman a yafe min dan Allah”
Sai a lokacin ta buɗe idon ta, ta kalleshi
“Amman kuma shine baka dawo ba sai yanzu”
Fuskarta ya rik'a yana rufe ido da buɗewa yace
“Kin san Safiyyah ba lafiya shine na.........”
Sai kuma yayi shiru kamar wanda ya tuna abu, basar da maganar tayi sai ta kalli cikin kwayar idonsa
“Ka ci abinci?”
“A'a tun abincin Safe”
“Miyasa.?”
Bai bata amsa ba, ita ma kuma bata kara tambaya ba sai kawai ta sauka saman gadon ta rika hannunsa for the first time
“Muje kaci abinci”
Tashi yayi tsaye, a maimakon yayi tafiya sai kawai taji ya rungume ta, ta baya yana sauke wani dogon numfashi. Sai gashi ita ma ta samu kanta da sauke numfashin mamancin nashi ta lumshe ido, kamkamkan ya rungume ta shima idon nashi a lumshe, sun daɗe a haka, sai kanshim jikinsa take shaka rahamar jikinsa ta baibayeta a nan ta soma jin sanyin dake fita daga jikinsa kamar raɓa, ɗagowa tayi tasa hannunta ta ɓanɓare rikon da yayi mata ba tare da ta juyo ba tace
“Bari na haɗa maka tea jikinka da sanyi”
Bai ce mata uffan ba ita bata jira yace mata ba ta fice daga ɗakin, Bata daɗe ba ta dawo hannunta rike da plate ɗin fruits ɗayan hannun kuma rike da Cup ɗin tea. Wani ɗan karamin tebur ta jayo ya