Showing 39001 words to 42000 words out of 115850 words

Chapter 14 - BABBAN GORO Complete by Khadeeja Candy .txt

02 Dec 2024

5678

ganin kinyi abunda zaki burge ni a kan Minal? Nasan wacece Minal Safiyyah ba sai kin faɗa min”


Bai tsaya jiran abunda zata ce ba ya juya nufi gurin motarsa,
Har ya iso gida cike yake da jin haushin Safiyyah yana ganin tana masa shigar shagala. yanzu kuma sai yake ganin kamar gaskiya ta faɗa masa,

“Saif... -”


Da raunaniyar murya ta kira sunan nasa, ta tsaya daga bakin kofa tana kallonsa,
Buɗe ido yayi ya tashi zaune ya kalleta cike da son jin abunda zata faɗa. Ganin hakan yasa ta k'araso kusa dashi ta risina kamar mai rokon gafara.


“Saif.... Zan iya faɗa maka wani abu ka yarda?”


Bai ce mata Ae ko a'a ba hasalima bashi niyar yi mata magana har sai yaji karya da zata tsara masa dan yasan karya ce, tunda shi ganau ne ba jiyau ba, Ita bata tsaya jiran abunda zai ce ta cigaba,
“Wallahi Saif na rantse maka da Allah bansan yadda akayi Deen ya shigo cikin gidan nan ba, Wallahi Saif bani na kirasa ba”


Murmushin yak'e yayi,


“Minal kenan, please karki soma faɗa min abunda kika san duk wadda kika faɗawa ba zai yarda ba balle ni dana gani da ido na,
Minal taya Deen zai shigo cikin gidan ya kai har cikin ɗakinki kare da karau har ku fito tare sannan kice baki san yadda akayi ya shigo cikin gidan ba?
Taya ma Deen zai shigo cikin gidan nan ba tare da sanin ki ba gidan dake cike da masu gadi Haba Minal”


“Yushe zuciyarka ta rufe tayi karfi haka daka kasa fahimta ta? Taya zan gayyato wani namiji cikin gidana ina amarya koda halina ne ballantana ba halina bane Saif kasan wacece”


“Yes nasan wacece ke Minal”
Ya tari numfashinta tare da tashi tsaye yana mata wani kazamin kallo,


“Nasan abunda zaki iya aikatawa, nasan kin ɗauki kula wasu mazan ba komai ba, kin faɗa min da bakikin ke babu wadda ya isa yasa ki canja hakinki kin faɗa min ba zaki taɓa iya rabuwa da Deen ba ko kin manta?”


Hannayensa biyu yasa ya tashe ta tsaye, ya dafa kafarɗarta.


“Nasan abu ne mai wahala rabuwarki da Deen Minal, kowa ya san ki dashi ba abun mamaki bane idan ance an ganki dashi yana ɗaya daga cikin dalilin ya yasa na kyaleshi ya fita ba tare da nayi masa komai ba,
Idan anji Minal ni zayi ma dariya ace min Allah ya kara saboda anta jamun kunne akan halinki amman naji na gani nacezan Aurenki i thought that idan na Aure ki zaki zubarda halinki marar kyau na tallafi rayuwarki muyi rayuwa mai kyau da Nagarta ashe nayi kuskure....”


Sakinta yayi ya nufi k'ofar fita, ita kuma har lokacin hawaye take, abunda da farar mace nan da nan fuskarta ta rine tayi wani ja, fatar idonta ta lumburo bakinta sai rawa yake kamar mai jin sanyi, tasan ta baro kyau tun ranar haihuwa tunda tayi ɓarin bakin cewa ba zata iya rabuwa da Deen ba, kuma ba wadda ya isa ya sata abunda bata tashi ba,
Tana haka Saif ya shigo ɗakin riƙe da wayarta ya mika mata,


“Idan shigowar da Deen yayi ba tare da haɗin bakinki bane bakisan ya shigo ba toh wannan saƙon fa waya aika.?”

A hankali ta ɗago ido ta kalli fuskarsa, idonsa sunyi wani irin ja, jijiyar kansa ta tashi kallo ɗaya zakayi nasa ka gane mugun ɓacin rai dake cikin ransa,
A kasale ta mika hannu ta karɓa, sannan ta kai ɗayan hannunta ta share hawayen dake idonta tana duba sakon.


_DEEN. Zanyi miss ɗinki sosai Minal kamin ranar da zamu haɗu_


_MINAL. Na sha faɗa maka Deen ka daina damun kanka aure na da Saif na ɗan lokaci ne kuma zama na dashi ba zai yanke tarayya ta da kai ba_


_DEEN. Bazan iya hak'urin rashin ki ba har na wani lokaci Minal kinsan yadda nake sonki_


_MINAL. Karka damu duk ranar da ya ɗan daga min kafa zan rik'a kiranka_


_DEEN. ok i love you sai na jiki_


_MINAL. i love you too_


SAKON YAU


_MINAL. Deen kazo yanzu idan kana free Saif ya fita amman kayi sauri kamin ya dawo_


_DEEN. ok gani nan zuwa kiyi min kwaliya mai kyau i can't wait to see you dear yau zan zama ango nima_


_MINAL, Ka daiyi sauri karya dawo kasan ba wani daɗewa zamuyi ba_


_DEEN. Yes gani kan hanya mi zan zo miki dashi?_


_MINAL, hot kiss_




Hawayen idonta ne suka rik'a sauka saman wayar, tun tana iya ganin alphabet har ta daina saboda cikar da idonta sukayi da kwallah, yanzu kan bata da hujjar kare kanta ada tana tunani idan da nusar dashi wata kila zai fahimta amman yanzu ba taya zai yarda ba ita ta tura wannan saƙon ba, bayan gashi a wayarta amman ita tasan idan za'a kashe ta a sake sa mata rai a kashe ta ba tasan tayi wannan chat ɗin da Deen ba, hasalima tun ana sauran kwana hudu bikinta bata sake saka shi a idon ta ba, balle a waya,


“Ba ke kikayi ba.?”


Ya tambaya a tsawace fuskarsa kuma babu annuri. Yanzu kan tasan bata da wata mafita babu ta inda zata iya kare kanta, hausawa sukace gudun da ba tsira kwanciya ta fishi, Ganin haka yasa ta kalleshi fuska a raunane tace


“Nice Saif nina aikata”


Duk yadda ransa yake ɓace sai ɓacin ran yanzu yafi na ɗazin saboda ta amsa da kanta ita ta aikata, toh idan kuma bata amsa ba ya zatayi bata da wata mafita sai wannan babu ta inda zata iya kare kanta.


“Miyasa kika karyata farko ? bayan na gani da ido na”


Bata ce masa uffan ba, saboda nauyin da bakinta yayi mata sai ruwan hawaye take kamar kurma, sai kawai ta juya kamar kazar da kwai ya bashema ta ciki ta nufi kofar fita.


“Minal....-”


Cikin muryar maza yayi mata kiran muryar dake da wahalar fassara.
Cak tayi tsaya bakin kofar, ta lumshe ido tana haɗiye wani kololo daya tsaya mata a wuya,


"Thank you so much Minal I really appreciate it”


Har lokacin bata ji tana iya furta masa wata kalmar ba. Buďe idon tayi ta tattara rigarta ta nufi ďakinta da gudu,
Saman gaďo ta faďa ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, tana jan gashin kanta, sosai sosai tayi kukan nan da nan idonta ya rumburo, Zufa ce ta shiga karyo mata ta ko ina sai numfashinta ya rika fita sama-sama, da sauri ta tashi ta cire rigarta ta shiga bathroom ta tsakarwa kanta shawa.




**** **** ****


Safa da marwa Saif ya rikayi cikin ďakin bayan fitar Minal, Tunanin yake miyasa Minal tayi masa haka miyasa ma ya aureta, bayan yasan halinta kuma ta riga ta faďa bazata ta6a canjawa ba, ? _amman miye na mamaki ai daman can haka halinta yake tunda bata ďauki mu'amala da wasu mazan wani abun ba auren da nayi mata nima dai nati ne kawai dan ganin na canja mata hali,_
Wata zuciyar ta soma tunasar dashi abunda ya manta, Amman fa Minal ba karamar yarinya bace a matsayin da take yanzu yaci ace tasan abunda ya dace da wadda bai dace ba, kai Minal tasan komai da gangane take tunda har tasan ta kula wasu mazan ta 6oye ma mijinta, shiyasa Huda take burge ni nasan tana yimin ba dai-dai ba amman bata yarda ta kula wasu mazan tana kokarin kare mutuncinta tana taya ni kishin kanta sosai,


“I hate you Minal.. i hate her so much.-”


A fili ya furta zuciyarsa cike da tsanar ta, Gaba ďaya ma jin yayi ya tsani gidan dan daga ďakinsa yana jiyo kukan da take a ďakinta, Wani dogon tsaki yaja ya fice daga ďakin,
Da wani irin karfi ya buɗe Motarsa yaja ya rufe still da karfin kamar ita ce tayi masa ƙaifin, yadda ya ruƙa horn sai da ya bawa masu gadin tsoro, da gudu suka buɗe masa gate ya fice yana rike da sitarin da wani irin karfi.
.
Ya daɗe zaune cikin motar kansa jingine a sitari sai ajiyar zuciya yake saukewa, daga bisa ya fito ya nufi kofar falon hannayensa zube cikin aljihu yana tafiya guda guda, karaurawar dake gefen ƙofar ya danna ya jingina da ƙofar yana lumshe ido,
Jin an buɗe ƙofar yasa ya ɗago ya kalleta, ita kuma ta sakar masa murmushi tana faɗin,


“Ango kenan shine ƙka tsaya a waje kamar baƙo”


Baice mata komai ba sai kallonta yake fuskarsa ba yabo ba fallasa, daga bisani ya jata zuwa jikinsa ya rumgumeta, yana sauke ajiyar zuciya,


“Ina sonki sosai Huda ina sonki”


Yana faɗar hakan tayi murmushi ta ƙara ƙanƙameshi a ranta tana faɗin _Ta faru kenan_ A fili kuma sai ta ƙara shigewa jikinsa,


“Nima ina sonka sosai Saif”


Sun daɗe a tsaye gurin kowa da abunda yake saƙama zuciyarsa, zuwa can ya saketa jin wayarsa na ruri ya ɗauko wayar daga cikin aljihusa yana duba mai kiran, Nasir ne abokinsa hakan yasa shi saurin dannan picking ya kara wayar a kunne,


“Hello Nasir kana ina ne?”


“Ina majalisa naga kayi min four miss calls lafiya dai?”


“Lafiya amman ba lau ba i need to see you”


“Ok kazo ina gida ai”


“Ok gani zuwa”


Yana kashewa, ya kalli Huda


“Je ki kwanta zan leƙa gari”


Wani maraurauce fuska tayi


“Ba zaka shigo ba?”


Kai kawai ya ɗaga mata dan baya jin iya yi mata magana sosai, tsaye tayi tana kallonsa zuciyarta cike da farin ciki, tana ganin ya shiga motarsa ta rufe ƙofar da sauri ta nufi ɗakinta da ziman kiran Safiyyah,


☆ ☆ ☆


Nasir yaja wani dogon numfashi, yana tattara girarsa yace,


“Kai yanzu Saif ka tabbatar da da kanta ta kira sa?”


“Haba Nasir ga abu ƙarara na gani tayi masa tex sannan kuma ta faɗa da bakinta itacw tace yazo”


“Sai naga kamar Minal ba zata iya yi maka haka ba dan Minal tasan miye aure and..-”


“And what..?”


Saif ya katseshi yana masa wani kallo,


“Ba yaro bane ni Nasir nasan mi nake yi duk abinda ta aikata da ganganta aikata shi, kawai rainin wayo ne yayi mata yawa take son nuna min kamar bata san miye duniya ba”


“Saif ba haka bane Ya kamata ka kwantar da hankalinka ka bincika komai yadda ya kamata Baka sani ba ko wani sherin ne”


“Ba wani sheri malam kai duk yadda zakayi ka kare Minal ka iya wazai mata wani sheri kawai malam ka faɗa min abun yi tunda kace karna sake ta”


“Saki ba yi bane Saif yaushe akayi auren nan ko sati anyi da zaka cw zaka saketa ? yanzu idan ka saketa zaka jefa zuciyarta data mahaifiyarta cikin wani halin, kuma ka koma abun labari”


“Ba damuwa ta bace dan ta shiga wani halin ai ita batayi tunanin halin da zan shiga ba kadan yadda nake ji yanzu”


Nasir ya dafashi,


“Nasan kana da zafin kishi Saif amman ka kwantar da hankalinka ka koma gida yanzu gobe da safe zanzo gidan”


Tashi yayi, tsaye yana jan tsaki,


“Nifa banga wani abun da zaka zo kayi min ba malam”


“No Saif ba haka bane, kasan aba son yanke hukunci cikin fushi kayi haƙuri har zuwa gobe please”


Rausayar da kai yayi ya nufi ƙofar fita Nasir na bayansa yana bashi maganganu.





*** *** ***


Daren ranar baci ƙwara yayi daga idon Minal, ko alamun bachi ba taji ba balle bachin, a zaune ta kwana tana kuka, har aka kira sallah asuba. bayan tayi sallah ta dawo parlour ta zauna idonta sutun sutun ko gani batayi sosai, juyi ta riƙa yi saman kujerar tana jin tsanar duniyar da take ciki.
[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


NA


KHADEEJA CANDY




*29*




Wasa-wasa yau kwanan Minal huɗu bata saka Saif a ido, duk tsawon lokaci ba tada abinci sai kuka iya karta ta sha ɗan ruwa tea ko shi kaɗan daman can Minal ba mace ce mai son cin abinci ba, duk wayar da suke da Mummy bata taɓa faɗa mata ba halin da take ciki ba, duk da Mummy tasha tambayar da koda wata matsalar ne saboda yanayin da take ji na muryar ta ba kamar yadda ta saba jinta ba, Minal bata taɓa nuna mata wani abun ba sai dai tace mata ba komai.


Juyi take tayi saman gado, hawaye nayi mata zuba, tunanin halin da take ciki take da kuma wadda zata shiga, miyasa Deen yayi mata haka? Miyasa Saif ya kasa fahimtarta? Tashi tayi zaune tana tunanin kodai wani aljanin ne yayi mata haka a iya saninta bata san tayi wannan chat ɗin da Deen ba, sannan tana mamakin yadda aka yi ya shigo gidan har yakai cikin ɗakinta ba tare da sanin ta ba? Ita tasan Deen ba zai mata haka ba kuma idan ma yayi mata toh wannan sak'on fa da bata san ta tura ba ya akayi hakan ya faru da ita.


“Anty Minal...-”


Kiran da akayi mata ya katse mata tunani kuma ya tsorata ta, duk da muryar maiyi mata kiran tayi kama da ta Safiyyah amman bata gama tantancewa ba tunda yanzu ta gama tunanin aljanu kuma bata ji shigowar kowa ba sai kiran sunan nata,
Tashi tayi tsaye tana kallon ƙk'ofa zuciyarta sai rawa take,


“Assalamu alaikum Anty”


Safiyyah ta kunno kai cikin ɗakin tare da sallama,
Saida Minal ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa mata tana ƙirƙiro murmushi


“Wa'alaikissalam Safiyyah”


Ta amsa tare da zaunawa a kusa da ita,


“Na'am Anty Lafiya kike kuka?”


Sai a lokacin ta tuno da hawayen dake fuskarta, da sauri tasa hannu ta shafe tana dariyar da bata kai zuci,


“Lafiya kalau kai ido na ne yake ciwo ya su Momi”


“Lafiya ƙalau suke tare muke da Yaya Nasir ƴyana Falo yana jiranki”


Jimmm ta ɗanyi, azuciyarta tana tunanin ko yana tare da Saif ne, bata son wani yasan halin da take ciki duk da tasan bata aikata ba, amman tasan tunda Saif ya kasa fahimtar ta babu wanda zai fahimce ta, dan haka bata son wani yaji, sai ta sake sauke ajiyar xuciya sannan ta kalleta,


“Oke jeki ce masa gani nan zuwa”


“Ok”


Ta faɗa tare da juyawa tana murmushi. Da saƙe-saƙe ta fito ɗakin ta nufo falon har ta zauna bata san ta zauna ba saboda tunanin da take,


“Lafiya?”


Nasir ƴya buƙata, ta kalleshi tare ɗa faɗaɗa murmushinta,


“Lafiya ƙalau gata nan fitowa”


Kai ya ɗaga mata ya ciro wayarsa yana danne-danne. Sautin ƙarar takalminta yasa shi ɗaga kai a hankali yana kalleta,
Yadda take tafiyar kamar wata marar lafiya ko kuma nace marar lakka, ta naɗe jikinta da sari ja irin na shuwa arab, yayi mata kyau sosai kamar wata balaraba, kasa ɗauke mata ido yayi har ta zauna.


“Ina wuni Nasir”


Ta gaisheshe kanta na kallon ƙasa,


“Lafiya ƙalau Minal”


Ya amsa mata still yana kallonta, sai a lokacin yaga ramar da tayi dan har kashin idonta ya fito kamar wata mai ciyon ƙaujamau, Tausayinta ne ya shiga fisgarta ganin yadda idonta ke kwance da ruwan hawaye, kodai wani abun Saif yake mata? Tambayar taya jefa fama kansa kenan yana kallonta,


“Anty kamar akwai abunda yake damun ki?”


Safiyyah ta tambaya fuskarta na nuna damuwa kamar gaske,


“Babu abunda ƴyake damu na”


Ta amsa mata ba tare data kalleta ba,


“Amman Anty naga kinyi rama sosai kuma fuskarki na nuna akwai damuwa a tare dake”


“Babu komai Safiyyah Kinsan daman lafiya bata ishe ni ba”


“Haka ne Allah ya baki lafiya”


“Amin”


Nasir ya kalli Safiyyah,


“Tashi kije waje zamu yi magana”


Ta ɗanyi murmushi,


“Yaya Nasir kenan ba sƙon Yaya Saifu bane ai zaka iya faɗa ai”


Ya haɗe mata fuska,


“Bazan faɗa ba ke kika aiko ne ko kuma lokacin daya bani saƙon a gabanki ya bani? Kinfa san bana son iskanci ko?”


“Yaya miye abun faɗa daga magana, naga ni Ƴar'uwar Saif ce kuma..-”


Ya katse ta, a fusace


“Ke tashi ki fita nace kona ɓata miki rai shiyasa da zan fito kika ce zaki biyo kinsan bana son gardama ko?”


Ta fusata sosai, hakan yasa bata sake musa masa ba ta tashi, duk da taso taji abunda zai faɗa ɗin, amman kuma tasan halinshi zai iya yi mata tass a gaban Minal,


“Na tafi anty”


Ta faɗa tana kallon Nasir,


“Ba awaje zaki jirashi ba”


Minal ta tambaya ganin yadda take gyara gyalenta da rataya jika,

“A a daman ni gida zanje sai nace ya rage min hanya”


“Allah ya kiyaye”


“Amin”


Bata sake cewa Nasir komai ba ta fice,
Bayan kamar minti biyar da fitar ta, Nasir ya kalli Minal yace,


“Mi Saif yake miki wanda har tasaki rama haka”


“Baya min komai babu wata matsala a tsakanin mu”


Ta amsa masa muryarta a raunane,
Hakan ya ƙara karantarda shi halin da take ciki na damuwa,


“Bai kamata ki ɓoye min ba Minal Saif ya faɗa min komai, amman ni ban yarda da abunda ya faɗa min ba saboda nasan ba zaki aikata ba”


Sai a lokacin ta kalleshi, suka haɗa ido,


“Miyasa kace haka Nasir bayan ga gaskiya ƙarara na na aikata”


“Baki aikata ba Minal ba zaki aikata irin wannan abun da auren ki ba zan iya yarda kin kira Deen cikin gidanki ko kuma nace ya kawo miki ziyara amman ban yarda zaki aikata wani abun ba kamar yadda Saif yake zargi,
Bai kamata ace kin bar abu a ranki ba idan wani abun Saif yake miki ki faɗa min Minal?”


“Baya min komai Nasir hasalima tun ranar da abun ya faru ban sake sashi a ido ba, be sake shigowa gidan nan ba kuma idan na kira baƴa ɗauka in na masa text baya reply”


Tagumi tayi tana goge hawayen da suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login