Showing 78001 words to 81000 words out of 115850 words
Chapter 27 - BABBAN GORO Complete by Khadeeja Candy .txt
katon hijab tasa ta nufo downstairs dan tun tana bathroom Talatu ta faɗa mata mutumen ya shigo,
“Ina yake?”
Mummy ta tambaya tana kallon talatu dan ita bata ga kowa a parlour ba, Nuna mata shi talatu tayi
“Gaya a can”
Nuna shi da Talatu tayi yasa ya taso ya nufo mummy idonsa cike da hawaye, da rawar murya ya kira sunanta
“Sala...ma..tu...”
Yana kiran sunan nata ta watsa masa mari ta sake watsa masa mari, bai yi unkurin hana ta ba har ta wanke masa fuska da mari takwas masu kyau. sannan ta nuna masa kofar fita da yatsa dan bata iya masa magana.
WAI INA DEEN NE?
INA LABARIN HUDA?
ME ZAKU CE AKAN WANNAN DOGON PAGE?
ME KUKA HANGO ZAI FARU A GABA?
PLEASE VOTE VOTE VOTE AND COMMENT ON EVERY LINE.
46
Wannan Shafin Sadaukarwa Ce Gare Ki FEENAH BABY
Hawaye ne suka gangaro daga idon dattijon, ya kalli Mummy da fuskar tausayi ya ce
“Kiyi min ko wane irin hukunci Salamatu na cancanci ko wane irin hulakanci daga gare ki amman ina son ki saurare ni ki kuma....”
Bai karasa ba Mummy ta ɗaga masa hannu har lokacin batayi magana ba ta nuna masa kofa, a maimakon ya juya ya fita sai kawai ya faɗi zaune yana kuka
“Dan Allah ki saurare ni nasan ni mai laifi ne amman kiyi ma girman Allah ki saurare ni”
Sai a lokacin Mummy tayi masa magana da jan ido,
“Sauraren tsawar bakin hadari yafi min saurarenka ganin mutuwa ta yafi min ganin ka, ka fice daga gidan nan tun kamin na kashe ka!”
Kallo ɗaya zaka yi fuskata ka tabbatar da furucin dake fita daga bakinta har cikin zuciyarta yake, shi kuma ya wani marairaice ya koma abun tausayi sai kuka yake yana kokarin rika kafarta
“Ki kashe ni Salamatu matukar kashe ni zai sa ki sassauta min wallahi a shirye nake na mika miki rayuwa ta Salamatu dan Allah ki saurare ni”
“Wallahi ko zan kashe ka ka sake rai na sake kashe ka ka sake rai na sake kashe ka bazan sassauta maka ba dan haka ka fice min daga gida”
Kuka yake sosai kuka mai ban tausayi,
“Dan Allah ki saurare ni Salamatu ko dan yar mu....!”
“Y'a ....”
Mummy ta ɗan ja baya tana mishi wani kallo da ba zan iya fassara shi ba, shi dai ba kallon mamaki ba, kuma ba kallon tsoro ba, ba kuma kallon tausayi ba.
“Kai baka ji kunyar furta wannan kalamin daga bakin ka ba? ashe kasan kana da Y'a lallai rashin kunyar ka da yawa yake”
Mummy ta kalli Talatu tun ɗazu take tsaye tana kallon ikon Allah
“Ki ra min Sani da Mu'azu”
Cikin sauri ta juya ta fita, bata daɗe ba tadawo tare da su ko wanne sai kallon Dattijon yake da alama ta labarta musu gulmar. Mummy ta nuna musu shi
“Kun ga fuskarsa kun ga kamaninsa?”
Duk suka ce Eh har talatu, Sani ne ya duka yana kallonsa dan kara tabbatar da kamanin nasa.
“Ku fitar min da shi kuma karku sake bari ya shigo min gida duk kuka barshi ya shigo min gida a bakin aikin ku!”
Kallonta sukayi suka sake kallonta jin furucinta sannan suka shiga kokarin mikar dashi tsaye.
“Idan ke ba zaki saurare ni ba toh ki sadani da Y'a ta, dan Allah ki nuna min ita”
Ya faɗa cikin kuka yana kara zubewa. Hannu Mummy ta ɗaga musu alamar su rabu da shi ta nufi upstairs tana faɗin
“Biyo ni na nuna maka Y'ar ka”
Cike da kwarin guiwa ya tashi ya rufe mata baya har suka shiga ɗakin Minal. Mummy sai da ta kai tsakiyar ɗakin sannan ta juyo ta kalleshi ta nuna masa pictures ɗinta
“Ka ganta nan, gaka tufafin nan, kaga takalminta nan, ga gadonta can da kayan kwaliyarta”
Duk abunda ta nuna masa kallo yake dan shi sam bai gane inda ta dosa ba, can ya ɗaga kai yana kallon hotunan nata,
Wani gurin tana tare da Mummy wani gurin da Kairat wani da Yan makarantar su wani kuma da Deen sai wanda sukayi da abokanta na kasar waje da kuma wanda tayi tare da Mummy da Kairat. Tabbas yarsa ce dan babu abunda ta rage a kamaninsa wani kallo ya bi ɗakin da shi wanda zan iya cewa na farin ciki ne da kuma jindaɗi.
“Ina take.?”
Ya tambaya yana kallon Mummy idonsa na zubar da hawaye.
Mummy kamar mai jira a take ta bashi amsa,
“Ta tafi inda zaka je zanje mu tsayu da ni da kai da ita a gaban mahalincin mu ayi mana hisabi na jidaɗin da ba kayi ido biyu da ita ba na jidaɗin da bata raye bata ga wulakantaccen uban ta ba!”
Nan take kalarsa ta canja hawayen da ke masa zuba suka tsaya, ya saka hannunsa ya dafe gefen zuciyarsa ya faɗi zaune yana kallon tile ɗin ɗakin kamar wanda bai san inda yake ba.
Mummy ta kwala ma Sani kira, yana shigowa ta nuna masa shi.
“Ku fitar min da shi karku sake bari ya shigo min gida”
“Toh Hajiya”
Da sauri ya duka ya shiga kokarin tayar da Dattijon tsaye, daker ya tashi tsaye har lokacin yana dafe da zuciyarsa ya rika tafiya a hankali sani na ruke dashi har suka sauka downstairs.
faɗuwa Mummy tayi zaune ta kai hannunta gurin takalmin Minal taja ɗaya ta rumgume ta fashe da wani irin kuka muryarta har rawa take.
*** *** ***
A hankali Kairat take driving, har ta isa gidansu, bayan tayi parking taja gyalenta ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta fito ta nufi cikin gidan. Babu kowa farlon hakan yasa ta nufi ɗakin Hajiya. tun kamin ta karasa take jin shesshekar kukan Hajiya, ta daɗe bakin kofar sannan ta kai hannu ta tura kofar a hankali.
Unkurin ɓoye kukanta Hajiya tayi ta maida fuskarta gefe tana share hawaye. Kairat ta karasa kusa da ita ta risina ta ɗora hannayenta saman guiwoyin Hajiya
“Ga ni Hajiya gani na dawo”
Bayan ya gama share hawayen nata ta juyo ta kalli Kairat
“Ai kara da kika dawo ba zaki sake zama can gidan ba”
A hankali Kairat ta soma magana
“Hajiya yanzu idan na mutu ya zaki ji?”
Wani kallo tayi mata
“Wace irin magana ce wannan?”
“Hajiya ki auna ki gani yanzu idan na mutu ya zaki ji. naga ke baki shaku da ni kamar yadda Mummy ta shaku da ni ba a hannunta na tashi tun ina karama ita tayi ta ɗawainiya da ni har na kawo a inda nake yanzu rana tsaka sai kika ce zaki raba mu bayan mun shaku da juna kuma ni kaɗaice farincikin ta a yanzu shin idan kece ya zaki ji?”
Shiru Hajiya ta ɗanyi kamin ta kalli Kairat
“Toh saboda me zata sa kije gurin Abban ku kice ya aure ta wane irin halacci ne ba muyi mata ba!”
Tashi Kairat tayi tsaye, ta zauna kusa da ita ta yadda zata fuskance ta.
“Hajiya na tabbatar zuciya ce a kirjin ki Hajiya ba ko taɓa tausayin Mummy ba? ba ki taɓa mata fata na ta sake samun wasu yayan ba? Mummy bata taɓa yi ma Abbah kallon so ba kullum a uba take ganin shi bata taɓa sha'awar auren mijinki ba tun zaman ta gidan nan bata taɓa cin amanar wani ba baki taɓa jin ance an ganta da wani ba,
Duk da hakan zuciyarki bata yi sha'awar ta kasance abokiyar zaman ki ba? Wallahil azim Hajiya Mummy ba ita ta tura ni tasa nayi ma Abbah magana ba nice naga dacewar hakan kuma nayi masa bata sam da wannan maganar ba sai yau sanadin haka yasa tayi min wannan marin”
Ta nuna ma hajiya gefen fuskarta gurin da yatsun Mummy suka kwanta mata a kunci. ido Hajiya ta tsura mata tana kallonta kamar mai karantar abu a fuskarta. zuwa can ta ɗauke kai ta sauke ajiyar zuciya. Kairat ta rika hannunta
“Na sani Hajiya Mummy ba zata taɓa yarda ta auru Abbah ba. saboda halaccin ta ki kwantar da hankalinki aure ba zai taɓa shiga tsakanin Mummy da Abbah ba”
Hajiya dao bata ce mata komai ba, hawayen dake makkale a idonta suka zubo mata a nan ta dantse bakinta. Sun daɗe a haka ganin bata da niyar magana yasa Kairat ta tashi. har ta kai bakin kofa sai kuma ta juyo ta ta kalleta daga gun da take da duka kasa ta haɗe hannayenta kamar mai neman gafara tana hawaye tace
“Na haɗa ki da girman Allah Hajiya karki hana ni shayar da Lil Minal, Hajiya ko da Minal na raye ni mai iya shayar da Y'arta ce balle bata raye, Kullum Minal tana faɗa har a gaban ki cewar idan ta haihu ni zan raini yarta dan Allah Hajiya karki hana ni yin wannan shi ne farin ciki ne”
Har lokacin Hajiya bace mata komai ba sai hawaye take. Kairat ma bata sake cewa wani abun ba ta tashi jiki ba gwari ta fice.
*** *** ***
Nasir ya sauke ajiyar zuciya tare da shafa kansa,
“Toh kai yanzu ya kake ganin za'ayi?”
“Ya za'ayi ban da a kyale ta in yaso sai Safiyyah ta shayar da ita”
“No”
Nasir ya girgiza kai
“Ni kaina ban yarda Safiyyah ta shayar da ita ba Kairat ce ta cancanta ta shayar da ita kuma na tabbata da ta samu damar yin wasiya da sai ta faɗi haka”
Shiru Saif yayi yayi ma bakins wani abu alamar damuwa
“marry her and make her happy shi ne abunda Minal ta faɗa min lokacin da zata rasu tace min ka auri Kairat dan ku kula min da abunda zan bari that's mean na bar Kairat ta kula da yarta but the problem is ita ta ki aminta”
Nasir ya tari numfashinsa
“Wannan ba hujja bace kamata ƴyayi ka lallaɓa ta baka san dalilinta ba tun da kaga abun ya kai har gurin iyayenta”
Saif ya kalleshi
“Lallaɓa ta? karamar yarinya ce da zan lallaɓa ta”
“Ba a haka Saif yarinyar yar ka ce bai kamata ka nuna halin ko in kula ba beside ni wallahi Kairat ɗin nan har tausayi take bani yarinya ce mai hakuri da hangen nesa ta raba hankalinta gida biyu ni ina ganin ma ta wannan hanyar zaka iya cika burin ka ka kuma cika wasiyar Minal”
Kai Saif ya gyaɗa
“I'm not ready yet”
Nasir zaiyi magana wayar Saif tayi kara, ganin number Abbah yasa shi saurin ɗauka,
“Hello. okey gani nan zuwa”
Shine kawai abunda ya faɗa ya kashe wayar ya kalli Nasir
“Daddy na nema na”
“Ok muje kaji kiran nasa sai muje gidan su Kairat ɗin”
Tashi sukayi tare suka shi ya nufi part ɗin Daddy Nasir kuma ya nufi parlour Mummy.
Da sallama ya shiga. bayan ya samu guri ya zauna ya kalli Daddy yace
“Gani Dad”
Sai da ya gama duba jaridar dake gabansa sannan ya ɗago ya kalli Saif.
“Akan maganar Huda ne ko ɗazu sai da Mahaifinta yazo gidan nan, ya faɗa min ko abinci bata iya ci a yanzu ta koma wata kalar mace su kansu yanzu abun ya dame su”
“Toh ya za'ayi da Kaddara tayi hakuri kawai haka Allah yaso”
“Ba haka naso ji daga bakin ka ba Saifullahi ya kamata ace a yanzu ka duba mata nasan iya nadama yanzu tayi ta kuma kaga ko dan yawon da mahaifinta yake a gidan nan ya kamata ka mutun ta shi”
Bakinsa ya cika ma iska
“Dad ni fa ban gane ma maganar ka ba wannan zirga-zirgar da mahaifinta yake yi ban ga amfaninsa ba kai ma sai naga kamar kana manta babu aure tsakani na da Huda”
“Akwai aure tsakanin ku mana ba saki biyu ka yi mata ba?”
“Biyu nayi mata a yanzu can farko na yi mata ɗaya kaga babu aure kenan ya cika uku”
“Subhanallahi”
Daddy ya faɗa yana ɗan nazari
“Dad ita kanta tasan da haka sai idan sune bata faɗa ma ba amman Momy ma tasan da wannan”
Nisawa Daddy yayi
“Bari zanyi magana da Abban nata amman ka tabbata da gaske ne dai ko?”
“Wallahi Daddy da gaske ne ka tambayi Momy tasan komai”
Kai Daddy ya ɗaga masa yana tunano abubuwan da suka faru.
*** **** *****
Kairat na shigowa parlour Talatu ta tashi tsaye da sauri tana faɗin
“Yauwa kara da Allah ya kawo ki”
Kairat ta kalleta
“Lafiya ina Mummy?”
“Tana can kuma ina jin kuka take. wani ne yazo mai kama da Minal wallahi fuskarsu ɗaya ina jin Babanta ne ko kuma ɗan'uwan Babanta shi ta shiga ɗakin Minal tun ɗazu har yanzu ta ko fitowa tun ina jin sautin kukan har na daina”
Da gudu Kairat ta nufi upstairs. Kwance ta tararda Mummy duk ta watse komai na ɗakin fuskarta a kumbure idonta kuma suyi jawur alamar taci kuka har ta gaji. Sai da Kairat ta karema ɗakin kallon sannan tayi cikin Mummy da masifa
“Haba Mummy kefa ba yarinya ce yar da kaddara nai da marar kyau yana cikin imani. Allah baya ɗorawa rayuwa abunda ba xata iya ɗauka ba. duk abunda Ubangiji yayi dai-dai ne Mumny ki yarda da wannan Allah bai raba ki da Familyn ki ba sai da ya baki wasu, bai karɓe miki farinciki ba sai da ya baki wani yanzu kuma ya karɓe miki Minal kin san abunda yayi miki tana di ? dukan tsanani yana tate da sauki Mummy yaushe zaki san da haka?”
A maimakon Mummy tayi magana sai kawai ta fashe da wani sabon kuka, nan itama Kairat tasa nata kuka
“Kuka kike yi Mummy, Hajiya ma kuka na baro tana yi. ya kuke son nayi da raina ne?. Wayyo Allah na ina ma ni ce na mutu ba Minal ba da baki shiga halin da kike ciki ba yanzu da ran Hajiya bai ɓace ba har ya kai ta gayin saɓani da ke, da Saif bai rasa matarsa da lil Minal bata rasa mai shayar da ita ba Alhamdulillah Allah ni kan na gode maka”
Ta faɗa ta karfi sannan ta juya tana kuka ta bar ɗakin. Tashi Mummy tayi zaune ta share hawayenta sai kuma tayi shiru kamar mai tunani zuwa can ta tashi ta nufi ɗakinta.
*** *** ***
Tare suka shigo parlour ko wanne sanye da farar shadda, bayan sun gaisa da talatu Nasir ya zauna Saif kan tsaye yayi kamar bako.
“Ina mutan gidan?”
Nasir ya tambaya yana kallon upstairs, Talatu ta tashi tana faɗin
“Tana ciki bari na mata magana Kairat kan tana Garden”
Kai Nasir ya ɗaga mata Saif kuma ya juya ya nufi hanyar Garɗen ɗin.
Sautin kukan ta ne ya sadashi da gurin da take, zaune ya hango ta ta kufa kai da guiwa tana kuka, ya daɗe yana kallonta haka kawai sai ya samu kansa da rashin jindaɗin kukan nata. karasawa yayi kusa da ita rumgume da hannayensa.
Kanshin turaren da taji ne yasa tayi saurin juyowa ta kalleshi, sai kuma ta maida fuskarta ta shiga share hawayenta
“Me kike yi ma kuka.?”
Ya tambaya yana kara gyara tsayuwarsa
“Ba komai ba kuka nake ba”
“Ba komai kamar ya ko wani abun akayi miki ne?”
“Nace maka ba komai”
Ta faɗa kamar mai shirin sake yin kukan. Tashi tayi tsaye ta saka takalmin ta ta nufi hanyar parlour abunta ta barshi tsaye. kafaɗunsa ya ɗaga ya rufa mata baya. Da ruwan kuka ta shiga parlour ganin Nasir yasa ta sha jinin jikinta ta ɗan natsu
“Ina wuni”
Tace dashi tana kokarin ɓoye kuka nata, bai amsa mata ba ya kalli Saif dake bayanta ya sake kallonta ya kalleshi, Saif ya ɗaga kafaɗunsa alamar bashi da ruwa a kukanta, a sannan Nasir ya amsa gaisuwarta
“Lafiya kalau ya gida?”
“Lafiya kalau”
Ta zauna saman kujera tana kallon center carpet, Nan shi ma Saif ya samu guri ya zauna yana kallonta
“Saif ya faɗa min Mummy tace masa wai kin fasa shayar da Lil Minal haka ne?”
Shiru ta ɗanyi, ita dai bata san tayi wannan maganar da Mummy ba maybe Mummy tace haka ne dan ta hana ta shayar da ita, sai da ta ɗanyi gyaran murya sannan tace
“A da ba amman yanzu ni zan shayar da ita”
“Ba zaki shayar da ita ba Kairat Saif na faɗa maka ka nemo mai shayar ita Kairat ba zata shayar da ita ba ba matar aure bace ba bazawara bace ba kuma tsohuwa bace ba zan yarda ta shayar da ita ba!”
Mummy ta faɗa tana saukowa downstairs, Nasir ya kalleta dai-dai lokacin da ta karasa saukowa
“Wannan ba matsala bane Mummy Kairat ba zata fara shayar da Lil Minal ba sai Saif ya aureta. shi kansa yayi tunani akan hakan shiyasa ya yanke wannan shawarar”
Daga Saif har Kairat tashi sukayi tsaye suna kallonsa, Kairat ta saki baki tana kallon ikon Allah, Nasir ya ɗan taɓe baki
“Kunyar kake ji ne? ba shine abunda ya kawo mu ba ba kai da kanka ka faɗi hakan ba?”
Mummy dai sai kallon Saif take shi kuma ya sakar ma Nasir ido yana masa kallon da shi kaɗai ya san amsar sa.Nasir ma daga zaunen da yake ya tsare Saif da ido yana masa kallon jiran amsa.
ME KUKE TUNANIN SAIF ZAI CE?
SHIN KAIRAT ZATA YARDA?
YA SAFIYYAH ZATA JI INA TAJI WANNAN MAGANAR WANE MATAKI KUKE GANIN ZATA DAUKA?
MIYASA DATTIJON NAN YAKE SON MUMMY TA SAURARE SHI?
ME KUKE TSAMMANI GABA?
KEEP VOTING AND COMMENTING, I WILL UPDATE