Showing 87001 words to 90000 words out of 115850 words

Chapter 30 - BABBAN GORO Complete by Khadeeja Candy .txt

02 Dec 2024

5669

ya ware kansa daban yana musu nasiha irin ta zaman aure da kuma hakuri, har sauran abokanin suka rika janshi wai sai kace shi ɗin aure ne dashi. sai da suka canye lokacin su har suka shiga na amarya da ango sannan suka bar gidan bayan anyi abubuwan da al'ada ta tana da.


Gyara zamansa yayi ya kalleta yana sauke ajitar zuciya, shi kansa ba wani farinciki yake ji ba, jinsa yake daban yana tuna rayuwar aurensa ta baya, motsin abun warwaronta ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, ya sake kallonta a karo na biyu


“Godiya ta tabbata ga Allah wanda cikin ikonsa da amincewarsa da rahamar sa ya nuna mana wannan rana, wanda yau gani ga ki a masayin miji da mata, wannan lamarin na Allah ne shi kaɗai yasan abunda ya tsara mana da kuma wanda zai tsara mana nan gaba”


Ita dai har lokacin kanta na kasa cikin mayafi.


“Sai ki tashi muyi ma Allah godiya”


ta shi tayi ta nufi kofar bathroom ɗin tana wata tafiya kamar ta faɗi, bayan ta ɗauko alwala ta fito shima ya shiga yayi ya fito.
A tare suka gabatar da Sallah raka a biyu suka yi addu'ah, sannan ya juyo ya kalleta


“Ga abinci nan nasan baki ci komai ba, ni zanje ɗakina na kwanta”


Bata ce masa komai ba shima ɗin bai jira tace masa ba ya tashi ya nufi ɗakinsa. aiko tana jin rufewar kofar ɗakinsa wani sabon kuka yazo mata ta tashi ta koma saman godon ta kwanta tana rera kuka a hankali. da haka bachi yayi gaba da ita


WASHE GARI.......
Sai tara da rabi Saif ya fito daga ɗakinsa, yana sanye da jallabiya baka tayi masa kyau sosai kamar ba wanda ya tashi daga bachi ba, ganinta tsaye gurin dinning yasa ya karasa gurin yana ɗan murmishi kamin yace wani abu tayi saurin dukawa ta gaidashi cike da ladabi


“Lafiya kalau kin tashi lafiya”


Cikin jindaɗi ya amsa mata. ita kuma ta amsa masa cike da jin kunya,


“Ga abincin ka nan”


Ta faɗa tana kokarin barin gurin.


“Kinci naki ne?”


“Aa a ɗaki zan ci”


Oka kawai ta faɗa yaja kujera ya xauna, bayan ya kare ya koma ɗakinsa ya shiga bathroom yayi wanka yana fitowa ya shirya cikin wata shadda Lemon green yasa hula baka ya nufo ɗakin Kaoeat sai kanshin turare yake.
zaune ya tarar da ita gefen gado sanye da babban hijab wanda ya suturce mata dukan jikinta, da alama ita wankan ta fito kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai


“Ni zan ɗan shiga gari idan kina bukatar wani abun sai ki kirani ko kiyi ma mai gadi magana”


Kai ta ɗaga masa ba tare da kalleshi ba, shi kuma ya juya ya fice daman daga bakin kofa ya tsaya.
Wunin ranar mutane ne suka rika zuwa gidan tun daga ɓangaren Momy har zuwa yan'uwanta da abokanin arziki, masu zolayarta suna yi masu mata nasiha nayi mata. sai kusan insha kowa ya watse aka barta ita kaɗai aiko taji kamar ta fasa ihu ko kuma ta bisu amman ina ba dama yanzu rayuwa ta sauya.
Bayan tayi wanka ta shirya cikin atamfa black and white ta saka bakin hijab ta nufo dinning dan jera kulolin abincin da aka kawo, Tana cikin aikin raji an buga kofa a hankali, sau biyu zuwa uku. yi tayi kamar ba taji ba har sai da aka sake yi sannan tace


“Wanene?”


Shiru ba a amsa mata ba hakan yasa ta nufi kofar ta buɗe, ga mamakinta sai bata ga kowa ba babu ma mutun balle alamunsa. mai da kofar tayi ta rufe ta juyo zata kunno kai cikin parlour,
Buga kofar da akayi yasa ta sake juyowa babu kwankwanto ta buɗe kofar da bismillah.
Minal ce tsaye bakin kofar sanye da bakar riga gashin kanta har godon bayanta tana kallon Kairat da wasu irin kalar idanu manya manya, fuskarta ba yabo ba fallasa. Ba shiri Kairat ta buɗe baki, ta zaro ido tana kallonta numfashinta na kokarin ɗaukewa jikinta kuma ya shiga rawa kamar mazari.


GUESS WHAT?😱 Please keep voting and commenting on every line 😘bohot bohot shukuriya 🙌 love you all guys 😍






49


Ji tayi kamar ana zooming ɗinta saboda tsoro. Daker ta iya rufe idonta ta furta






"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un"


Ta daɗe a haka kamin ta buɗe idon ta sake kallon bakin kofar, neman ta tayi ta rasa, tayi ko sama ko kasa, da sauri ta maida kofar ta rufe tana haki


Saman kujera ta dawo ta zauna dafe da zuciya,


Toh ko dai gizo idonta yake mata ne?


Shine abunda ta tambayi kanta tana lumshe, toh idan ba gizo ba kan minene tun dai Minal ba dawowa zatayi ba, wannan tsoro ne da kuma rashin sabo da zama ke kaɗai.
Tana haka taji an sake turo kofar a karo na biyu an shigo parlour, kulle idonta tayi gam, har sai da taji sallamar Saif sannan ta buɗe idon tana amsa masa


"Wa'alaikumussalam"


"Sannu da zuwa"


"Yauwa sannu dai ke kaɗai ce a gidan"


Ya faɗa yayin da yake kokarin karasawa kusa da ita, ita dai har lokacin kanta na kasa tana doubting abunda ta gani,


"Bari naje nayi wanka sai muci abinci ko?"


As usual bai tsaya jiran abunda zata ce masa ba ya nufi ɗakinsa ita ɗin bata ce masa komai ba dan abunda take tunani ya isheta. Har yayi wankan ya fito a gurin da ya bar ta ya tararda ita kuma har lokacin kanta a kasa, tsayawa yayi yana kallonta kamar maj karantar abu a fuskarta,


"Kaiyrat"


Ya furta a hankali, zabura tayi ta tashi tsaye kamar wanda ta razana,


"Na'am"


Sai kuma tayi kasa da kanta,


"Ga abincin ka can ni na ci nawa"


Bata tsaya jiran abunda zaice ba ta nufi ɗakinta. Shi dai da kallo ya bita har ta shige sannan ya ɗaga kafadunsa ya taɓe baki ya nufi gurin dinning ɗin.


Cike da zullumi da fargaba Kairat tayi bachin ta na biyu a gidan, har garin Allah ya waye tunanin yadda taga Minal take har yanzu ta kasa yarda ita ɗince zigo ne idona suke mani shine abunda take ta maimaitawa tana kawar da tsoron dake ranta, bayan tayi Sallah asuba ne bachi mai daɗi ya ɗauke ta bata farka ba sai kusan goma na safe,


"Alhamdulillahil lazi'ahyana ba'adama a matana wa'ilail-nushur A'uxubillahi minasheidanin'rajin"


Bayan tayi addu'a tashi daga bachin ta mike tana mika ta nufi banɗaki, bakinta kawai ta wanke sai fuska ta fito ta ɗauki hijab ɗinta ta saka sannan ta nufo downstairs.
Zaune ta samu Saif a dining room yana cin abinci, karasawa tayi ta risina har kasa ta gaishe shi dan abunda Mummy ta faɗa mata kenan cikin jindaɗi ya amsa yana mata


"An tashi lafiya"


"Lafiya kalau"


"Ga abinci nan ki ci ban tsaya jiran ki dan nasan ba zaki ci dani ba"


Ya faɗa yana kokarin tashi tsaye, tana daga duken tace


"Yaushe zamu kawo Lil Minal?"


Tsayawa yayi yana kallonta,


"Wai da cewa nayi sai nan da sati biyu ko uku kinga kamin lokacin kin ɗan saba abubuwa ba zasu miki yawa ba"


Jin tayi kamar ta zaburo masa tayi cikinsa da masifa, amman Mummy ta hana ta dan ta faɗa mata wannan ba ɗabi a bace ta matar kirki, bata ce masa 'Eh' ko 'A'a' sai kawai ta tashi ta nufi ɗakinta.
Binta yayi da ido har ta shige sannan shima ƴa tsaya yana tunani miye yanke wannan hukuncin bayan saboda Lil Minal ɗin ta aure shi? Dan da kula da ita, amman shi kan gani yake kamar abun zai zame mata wani irin idan aka kawo mata ita yanzu ganin shekaran jiya nan aka kawota a gidan. Amman kuma miye ruwansa tunda ita take son haka ɗin!
Dakinta ya nufa yana shiga ya same ta dukunkune can gafen gado kamar marar lafiya, ganin shigowarta yasa ta tashi zaune tana jiran abunda zai ce mata.


"Kaiyrat"


Ya kira sunanta kamar ba lakka a jikinsa, shi dai baya jindaɗin yadda take kin sake jikin nan dashi ko kuma nace da gidan. Ta ɗan kalleshi kaɗan yayin da take kokarin amsawa


"Na'am"


Karasawa yayi kusa da ita, cikin yanayi mai kamar ya na damuwa


"Yaushe kike son na kawo miki ita?"


Shiru ta ɗanyi kamar mao nazari can kuma ta ɗan kalleshi


"Gobe?"


Ta faɗa kamar mai neman amsa,


"Allah ya kai mu"


Ya juna ya fice. Wunin ranar wuni Kairat tayi shiru shiru gashi yau gidan ba kamar jiya ba ba mutane sosai, ga kuma abunda yayi mata tsaye a rai tunanin yadda zatayi rayuwa a gidan da kuma yadda zaman ta zai kasance da Saif.
Kaɗan kaɗan take ɗan taɓa fira da kawarta, tana cin kankanar dake gabansu.


"Sai ɗa kinyi hakuri Kairat ita rayuwar Aure yar hakuri ce musamman irin wannan auren naki, ki kawar da komai da yake ranki ki fuskanci Ubangijinki kisa ni bauta kike ba wai zakiyi rayuwar jindaɗi bane, yadda kake son rayuwa ba zata kasance maka a haka ba baka taɓa samun komai 100%"


Kai kawai Kairat ke ɗaga mata tana sauraren nasihohin da take mata kasancewarta matar aure.
Ana sallah la'asar tayi ma Kairat sallama, wai mai gida yace kar ta daɗe, Dariya kawai Kairat tayi tana girgiza kai ita kuma ta rika zolayarta tana mata maganganu irin nasu na matan aure. Har gurin Mota Kairat ta raka ta bayan ta fice ta tsaya tana kare ma harabar gidan kallo.


Biyar saura kwata, Saif ya shigo gidan ya daɗe a mota sannan ya shigo cikin parlour,


"Ummu Minal fito ga Lil Minal ɗin ki"


Shine abunda ya faɗa yana kallon kofar ɗakinta yayin da ya kai tsakiyar parlour. Lekowa ta fayi kamar wata karamar yarinya wai ta gani indan da gaske yake, aiko da gudu ta karasa saukowa ganin Baby a hannunsa,
A maimakon ya mika mata baby sai kawai yaja baya da sauri yana mata kallon zolaya


"Wa zaki fara tarba ni ko ita?"


Kallonsa tayi da kyau shi kuma ya sakar mata manyan idon shi, kun kuyar da kai tayi tana murza yatsun hannunta,


"C'mon answer me mana idan kina son na baki ita"


Ya faɗa yana kallon fuskarta. Sake ɗagowa tayi ta kalle shi sai ta sake sanda kai, wani wasan yana yi mata ne dan ta sake jikinta, amman ina bata da niyar hakan. A dole ya mika mata yar dan yadda taga ta dake ɗin nan tsaye guri ɗaya yasan ba cewa zatayi ba


"BISMILAHI RAHAMANIN RAHIM"


Shine abunda ta furta sannan ta karɓi lil Minal ɗin, rumgume ta tayi a kirjinta. Daman can Kairat mace ce mai son ɗiya ballan tana wannan da take da dalilai na sonta.


"Na gode"


Ta faɗa tana kallonsa idonta cike da hawaye, murmushi yayi mata yace


"Dr tace idan zaki bata nono ki bata nonokin na dama kuma ki wanke shi kamin ki bata sannan tace karki bata nono yanzu sai nan da awa bakwai ko kuma ma ki bari har sai gobe tace duk ba matsala bane Momy tace gobe zata zo tare da wanda zata rika lura miki da ita"


Kasa tayi da kanta alamar kunya, taɓe baki ya ɗanyi shi kan bai ga abun kunya a maganarsa ba tun da ba wata ɓaran ɓaramar yayi ba, a nan ya barta ya shige ɗakinsa.
Sallah ce kawai take sa Kairat ta aje Lil Minal amman duk abunda zatayi tana rumgume da ita.
Bayan Sallar i'sha tayi shirin bachinta ta saka hijab kamar yadda ta saba ta hau saman gadon ta kara jan lil Minal kusa da ita tana mai jindaɗi sai kallonta take tana murmushi da alama ma idon ta biyu duk da idon nata a rufe suke amman sai motsi take da baki tana motsa baki.
Kamar wanda aka ce ɗago ki kalli windo, tana kallo ta ga Minal da siffar da ta ganta a farko kuma nan ɗin ma ita take kallo, wata razanannar kara da saki ta sauko saman gadon ba shiri ta fisgi lil Minal ta bar ɗakin tana ihu.


Keep voting dears






50


Da sauri Saif ya ɗago kai daga daga gurin da yake zaune ya kalli upstairs,


“Lafiya.?”


Ya tambaya yana kokarin aje magazin ɗin hannunsa ya tashi ya nufi upstairs ɗin yana cigaba da tambayar ta, bata faɗa masa gaskiya ba sai ta canja maganar,


“Wata na gani gurin windo”


Kunna kai yayi cikin ɗakin yana dube dube. ganin bai fahimci abunda take nufi ba


“Ba fa a ɗakin ba ta waje a windo na ganta”


Windo ya nufa ya shiga dubawa, shikan bai ga komai ba sai kawai yaja windon ya rufe, ya juyo yana faɗin


“Ina jin ita cen dake waje ne kika ango iska ne ke kaɗasu kinga garin akwai hadari, kuma kin bar windin buɗe amman ai kinga babu yadda za'ayi wai ya iya haurowa ta wannan windon tun da ba kasa yake ba”


Ita dai tana tsaye a bakin kofa rumgume da Lil Minal,


“Ba komai kiyi addu'ah ki kwanta”


Kai ta ɗaga masa ba dan ta yarda ba komai ɗin ba, har ya fice a bakin kofar take tsaye sai wani abu take da fuska kamar mai shirin yin kuka, can taji ba zata iya jure wa ba, ta juyo ta sauko downstairs.
Ba kowa parlour sai tv dake ta aikinsa, haka ta zauna sai kalle kalle take kana ganinta kasan babu natsuwa a tare da ita, sai a jiyar zuciya take saukewa, tana haka Saif ya fito sanye da jallabiya dark blue,


“Gate na dawo mikike so a siyo miki?”


Ya faɗa daidai lokacin da ya karaso kusa da ita


“Bana bukatar komai”


Ta faɗa kamar bata son magana. Sai da ya kai bakin kofa sannan ta ce


“Please karka daɗe”


Juyowa yayi yana murmushi,


“Tunda kina jin tsoro ko.?”


Kasa kasa ta kalleshi ta ɗauke kai. Shi kuma ya fice yana cigaba da murmushin.
Aiko kamar kar ya fita wani irin tsoro ya kara rufeta, ta rumgume Lil Minal a kirjinta gam ta rumtse ido, jin Lil Minal ɗin na motsi yasa ta buɗe idonta ta ajeye ta saman kujera tasan rumgunar ce wata kila bata so, tashi tayi da nufin kashe tv saboda karar da tayi yawa, sai kawai taga an kashe tv ba tare da ta karasa gurin ba, aiko ba shiri tayi baya baya tana haki.


“Ashe ki baki da amana Kairat? saboda zaki aurar min miji? kin yaudare ni cin cuce ni Kairat kuma ba zan taɓa barinki cikin kwanciyar hankali ba matuƙar kina cikin gidan nan”


A gefenta taji maganar tana juyowa ta ganta cikin bakar siffar da ta saba ganinta, wata mahaukaciyar kara ta saki ta faɗi kasa tana ja da baya sai uhun take ba kakkautawa, aiko sai bin ta take tana son kamota Kairat na ganin ta kusa karasowa kusa da ita ta kara sakin wata irin kara. jin an taɓa ta ta baya yasa ta rika numfashin a jure kamar zai ɗauke


“Nine Kairat ni ne”


Ina! tayi nisa bata jin me yake faɗi sai kaiwai ta cigaba da ihun jikinta na rawa, juyowa yayi ta ganta yasa bakinshi cikin nata ya rike kanta gam, sunyi minti goma a haka sannan hankalinta ya dawo ganin hakan yasa ya sake mata kai ya cire bakinshi daga nata ya rika kafaɗunta yana girgizata,


“Kairat”


Bata iya amsawa saboda numfashinta har yanzu rawa yake,


“Close ur eyes”


Da sauri ta rufe idon kamar mai jiran umarni


“Relax, relax ur body”


Ba musu tayi yadda ya umarce ta


“And stop breathing as long as U can”


Dif numfashin nata ya ɗauke ta daƙiƙin tsayar da shi da tayi


“Now breath”


Ya faɗa yana kallon fuskarta. A hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta cigaba da numfashinta,


“Open ur eyes”


Tana kallonsa ya ce


“I m here its me okey”


Fashewa tayi da kuka, ya rumgume ta yana mata magana a kunne kamar mai raɗa


“Shiiiiiiii ya isa faɗa min miya faru?”


“Minal na gani Saif”


Bata ɓoye masa ba, ta faɗa masa dan a yadda ra ganta yanzu ya wuce misali gashi har da magana tayi mata. Lil Minal ya nuna


“Wannan ?”


“A'a Minal dai margayiya”


Kai ya girgiza,


“Oh no no no Kairat baki ganta ba tsoro dai kike ji kuma kinsa tunaninta cikin ranki”


Dagowa tayi daga jikinsa daman ba rumgumar take so ba dan kawai tana jin tsoro ne,


“Wallahi na ganta Saif da ido na, ba wai ina tunaninta bane kuma tayi min magana”


“No Kairat kin taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo? babu kuma mai rai baya ganin mamace ba ita bace tsoro ne kawai kike ji”


Shiru tayi tana hawaye, daman tasan ba zai yarda ba babu ma wanda zata faɗa ma ya yarda da ita amman ita tasan abunda take gani.
Unkurin tashi tayi, daker ta mike tsaye kafafunta basa iya ɗaukarta. A nan shima ya tashi ya lakamo hannunshi ya rika kunkurunta


“Let me help you”


Bata masa musu ba dan tasan ba zata iya kai kanta ɗaki ba, da ɗayan hannunsa ya ɗauki Lil Minal ya nufi upstairs. har cikin ɗakinta ya kaita bayan ya zaunar da ita ya kwantar da Lil Minal, sannan ita ya kwantar da ita ya cire mata hijab ya goge mata fuska.


“Ki daina kuka, kiyi addu'ah”


Blanket ya lulluɓa mata sannan ya kashe wutar ɗakin ya fice. Yana fita, taji ita ba zata iya kwana ɗakin ba duk wani rashin karfi da take ji sai taji ya cire mata, da wani irin kuzari ta walkato saman gadon ta sauko ɗaukar lil Minal ne kawai ya zame mata dole aiko tana ɗaukarta ta fice daga ɗakin a guje. ɗakinsa ta nufa ta daɗe tsaye bakin kofar sai tunane tunane take, kamar ta koma kuma taji ba zata iya ba.Sam ta manta da ba mayafi jikinta haka ta faɗa ɗakin tare da sallama.
yana zaune saman gado laptop na saman kafafunsa yana dannawa ya ɗago ya kalleta


“Again?”


Kai ta girgiza tana karasa shigowa ɗakin,


“A a nan dai zamu kwana ni tsoro nake ji”


Wara ido yayi ya kalli gadonsa sannan ya kalleta yana ɗaga kafaɗunsa


“Zo ki kwanta”


Gefen gadon ta nufa ta zauna kasa rumgume da lil Minal tana faɗin


“Nan ya isa”


Kitson kanta ya tsaya kallo yana mamakin yadda ta zauna aka tsara mata dashi ta kuma wanda ta tsara mata shi, kanana ne kuma an tsara shi cikin waninsa da sarkaki dan wani kan wani akayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login