Showing 15001 words to 18000 words out of 115850 words
Chapter 6 - BABBAN GORO Complete by Khadeeja Candy .txt
na dafa komai ba”
“A'a wasa dai kike ko?”
“Wallahi da gaske nake ba kaga abunda nake ba tun ɗazu nake Online ban samu kayan da suka yi min ba”
Sam bai yarda ba tashi yayi ya nufi downstairs,
Sai da ya duba ta tabbatar da gaske take sannan ya sake nufo ɗakinta rai a bace, bakin kofa ya tsaya fuskar shi a ɗaure,
“Huda wannan wane irin wulakanci ne ace ni da gidana amman bana da halin jindaďi kamar sauran maza wannan wace irin rayuwa ce?”
B'ata fuska tayi “Haba dear wai miyasa baka ganin tausayi nane wai aikin gidan nan kace baka son kowa yayi sai ni tun safe fa nake ta kai da kawo cikin gidan nan ga wannan aikin dake gaba na shin dame kake son naji dan Allah kuma wannan faďan ma kasha yinshi kaga bazan iya wani abun ba tunda gidan mu bamu saba da aiki ba akalla yanzu nayi shekara biyu gidan nan kullum abu ďaya ya kamata ka ďaga min kafa mana”
Wani murmishin jin haushi yayi ya kađa kai kawai ya fice,
D'akinshi ya dawo ya faďa kwance saman gadon yana ta tunanin magagganun da Huda tayi mishi da kuma hali irin nata ,lokaci lokaci yakan ya tsaki yana gwaďa kai hannunshi na hagu na saman cikin shi,
Jin yunwar ba zata barshi ba yasa ya tashi ya ďauki keys ďinshi ya fice.
ROYAL KING HOTEL............
Minal ce a tsaye kusa da reception, sanye da doguwar riga ta farin material mai kyali da yar hula sai kalle kalle take kamar bakuwar gurin,
Juyowar da zatayi ta hango tafe, tun kamin ya karaso ta rika sakar mishi murmushi, shi kan baia san tana yi ba dan hankalinshi kwata kwata baya jikinshi,
Ganin zai wuce ta yasa ta kira sunanshi,
“Saif...”
Juyowa yayi yana neman mai kiran sai a lokacin ya lura da ita, murmushi ya sakar mata
“Minal mi kike yi a nan?”
“Ai kaine ya kamata nayi ma wannan tambayar”
“Ni ai kinga Namiji ne Take away nazo yi ke da wa kika zo nan?”
Hannu sata a baki kamar wata karamar yarinya
“Ni da Mummy tana gurin biyan kuďi”
Hangen Mummy tafe yasa ta karaso kusa dashi tana nuna ta
“Gama ta nan zuwa”
Kallo đaya yayi ma Minal ya ɗauke kai ya kalli Dr. Salamatu da ta k'arasa kusa dasu,
“Good evening Dr. Salamatu”
Fuskarta a sake ta amsa mishi
“Evening Saif ya kake?”
“Lafiya kalau ya hak'uri ya abubuwan?”
“Da godiya na gode sosai Saif Allah ya saka maka da Alheri”
Da sauri ya tari numfashi ta
“Oh ai babu komai Allah ya tsare gaba”
Minal ce ta amsa da 'Amin' ta rik'a hannun Mummy suka nufi kofar fita shi kuma ya kunna kai cikin Hotel ɗin,
WASHE GARI..........
Tunda Minal tayi sallah asuba bata koma bachi ba sai kawai ta nufi kicin, abubuwan duk da tasan Mummy naso gurin breakfast su ta shiga haɗa wa cikin taimakon Allah kuwa ta kammala komai in time,
D'akinta da dawo ta cire kayan bachin dake jikinta ɗaura tawul ta shiga bathroom, bayan tayi wanka ta fito bata tsaya shafa komai ba tana tsane jikinta ta nufi wardrobe ta saka dogon wando jean da riga T shirt green color ta ɗauki wani guntun ribon ta ɗauke gashin ta sannan ta nufo ɗakin Mummy,
Bata tararda kowa ɗakin ba, motsin ruwan da taji ya tabbatar mata da tana bathroom guri ta samu ta zauna tana kallon kofar banɗakin har ta Mummy ta fito,
“Mummy good morning”
Da murmushi Mummy ta amsa
“Morning Minal how are you har kin tashi?”
“Eh tun ɗazu ai nima na haɗa breakfast”
Zaunawa Mummy tayi kusa da ita tana shafa kanta
“Allah yayi miki albarka Minal ya kara miki lafiya ya shirya min ke”
Hannunta Minal ta rik'a “Amin Mummy tashi muje kici abincin”
Ba musu Mummy tashi suka fice,
Downstairs suka nufo, kamin su k'arasa saukowa Minal ta hango Kairat zaune tana breakfast, aiko ba shiri ta saki hannun Mummy ta nufo Dining area da gudu, Kairat na ganinta ta tashi da sauri ta zagaya ta baya tana dariya,
“Minal am so sorry inajin yunwa ne kuma tsohuwa tace min ke kika girka da kanki shine naci naji idan yayi daɗi”
Dariya Mummy tayi ta kalli Kairat
“Nan kika kwana ne?”
“A'a Mummy yanzu na zo ina kwana”
“Lafiya kalau ya gidan?”
Kujera Minal ta jama Mummy
“Mummy zauna a nan kici lokacin zuwa aikin ki yayi”
Nan ta juyo gurin Kairat
“Ke kuma ki wuce ɗakinki ko ki koma gida”
Mummy ta zauna tana faɗin,
“Babu inda zataje kin taɓa ganin mutun ya bar gidan su yaje wani gurin?”
Fuskar shagwaɓa Minal tayi
“Toh Mummy taje ta haɗa ma kanta breakfast ɗin dan ni ba zata ci min abunci b katuwa da ita”
Mummy zatayi magana tsohuwa dake kokarin shigowa ta rigata,
“Yau ku ji min Minal ke da nake dafa miki kina ci fa”
Juyowa Minal tayi “Ke tsohuwa mi ya kawo ki nan, kuma ni ai ba wani girma ne dani sosai ba balle kice ita fa tayi uku ɗina haka kawai zan dafa mata abinci”
Tsohuwa tace "Ai ba ita kika dafa ma Hajiya kika dafa ma Hajiya kuma uwarta ce dan haka dole ta ci”
Dariya Kairat tayi “Yauwa tsohuwa faɗa mata dai cin abinci kan har na gama dai dai kiyi hak'uri”
Mummy dake cin abinci ta kalli Kairat “Zauna kici tun bai huce ba yar mamarta”
Kujera Kairat taja ta zauna tana yima Minal gwalo, ɓata fuska Minal tayi kamar ta fasa kuka
“Har da ke ko Mummy”
Mummy ta kalleta “Yau toh ya zanyi Minal ya tace fa”
Rumgume hannayenta tayi “Toh duk ku tashi ma na fasa baku abincin”
Tsohuwa ta rik'e baki “Har da Hajiya?”
“Eh har da ita kuma kema ba zaki ki ci shi ba”
“Yau ni tsohuwa dani mi zanyi da kwai da plantain ni tun da safe na karya da koko da kosai kuma kuma na ci ɗumame dan haka ki rike abinki indan ni”
Fuskar shanu Minal tayi ta koma saman kujerar parlor ta zauna, dariya tsohuwa tasa mata ta nufi kicin tana gyara tsintsiyar da ta shigo da ita, Mummy da Kairat ma dariya suka rik'a yi mata Kairat har da wani rawar kai
Sai da Mummy ta gama cin abinci ta sannan ta tashi yana hamdala tace “Minal Allah yayi miki albarka abincin nan yayi daɗi kin iya girki”
Kawar da fuska tayi “Nidai Mummy kyale ni bazan sake dafa miki ba”
Murmushi Mummy tayi nufi upstairs tana faďin “Na kyale ki kinga ma tafiya ta amman dai ayi hakuri a sake dafa min yayi daďi kin iya girki”
Wink Kairat tayi mata da ido tace “Mummy so fa take ta nuna miki ta iya girki ayi mata Aure”
Filon kujera Minal ta ďauka ta jefe ta dashi “Tashi ki bar gidan nan busa kawai kibar biredi”
Fashewa Kairat tayi da dariya “Ai ni bana da Wata muguwar kiba dan kina kamar ki kare ne kike ganin kiba ta amman ni daidai nake yanzu ma maza son fi son masu ďan jiki ba irinki ba masu kamar su kare”
Minal tace “Wallahi karya ne anfi son irin mu na gaban mota”
Kai Kairat ta girgiza,
“Ki yarda kawai Allah anfi son irin mu yanzu idan muka auri miji ďaya sai yafi sona dake”
Sai a lokacin minal tayi dariya
“Lallai Yarinya waya faďa miki miji ďaya zamu aura har ya fi sonki dani? Ai ni bazan aure mijin wata ba wata kuma ba zata auri miji na ba”
“Toh wanene mijinki wanene kuma mijin wata?” Kairat ta tambaya,
“Idan na auri mai mata toh mijin wata ne ni na aurar mata miji dan zaki ji ance mijin wance ta aura, idan kuma wata ta auri mijina ita ce ta aurar min miji dan haka bazan auri mijin wata ba saurayi zan aura ba kuma zan bari wata ta aurar min miji ba”
Tasowa Kairat tayi ta dawo kusa da ita tana zolayar ta,
“Koma minene kara ki chanja da gaskiya miji ďaya zamu aura”
“Lol Ke kama kanki ba zaki iya kishi dani ba dan ni bana son kishiya”
“Yau ai nima ba kanwar lasa bace kinga tun nan mun saba da munje can cigaba kawai za muyi”
Da dariya tsohuwa ta fito kicin tana zolayar Minal, daďi Kairat taji ta samu mai kama mata suka rika caccakar Minal tun tana ramawa har ta gaji ta samu su ido,
Suna haka Mummy ta fito da shirinta na zuwa office, tana sauko downstairs Kairat ta tare ta “Mummy dan Allah a aura mana miji ďaya da Minal”
Watseta Mummy tayi “Ke dan Allah rufe min baki tun ďazu ina jinku kun tarar mata har da tsohuwa kuna takura mata yar baiwar Allah”
Daďi Minal taji, “Ai dama kin aura mana miji ďaya ďin da ita wallahi da kin sha wahala”
Minal ta karasa maganar tana hararar Kairat, kallonta mummy tayi “A haka Minal da wannan jiki”
B'ata fuska Minal tayi “Oh Mummy har da ke ko?”
Da fata Mummy tayi “A a ina nufin kina da kiba”
Ture hannun Mummy tayi ta nufi upstairs, Kairat da tsohuwa suka sa mta dariya har Mummy sai da tayi mata dariya sannan ta fice Kairat nayi mata Allah ya kiyaye,
Haka suka cigaba da rayuwarsu cikin farinciki da kwanciyar hankali da kuma jindaďI,
Mummy tafi kowa farin ciki da daman haka take son ganin farincikin Minal shine kwanciyar hankalinta, yadda suke rayuwa yanzu har yafi na da kamar ba uwa da ya ba sai ka dauka kawaye ne ko kuma abokanin wasa tsakanint da Mummy har ma Kairat.
*I'm still on wattpad @khadeeja_candy*
_Don't forget to vote and comment_
[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...!
NA
KHADEEJA CANDY
BABI NA GOMA SHA HUDU___14
Wattpad @khadeeja_candy
BAYAN WATANI UKU............
A firgice Saif ya farka sakamakon ringing ɗin da wayarshi take, sai da ya ɗan murza ido sannan ya ɗauki wayar ya duba ganin bakuwar number yasa ya maida wayar mazauni ta ya juya ya cigaba da bachin shi,
yaji kiran yayi yawa sannan ya mika hannu ya ɗauki wayar ya danna picking ya kara a kunne, cikin murya bachi ya ce
“Hello”
“Hello Saif how are you?”
“I'm fine who is on the line.?”
“Minal ce”
Daga kwance da yake ya shafi kanshi,
“Oh ya kike?”
“Lafiya kalau”
Sai da ya nisa sannan yace
“Kina bukatar wani abun ne.?”
Shiru ta ɗanyi,
“Eh ina bukatar ganin ka idan kana free”
Tashi yayi zaune
“Ok amman sai jibi nake free zan shigo idan na kare abun da nake”
Cike da jindaɗi tace
“Ok ba matsala @.?”
Sai da ya kalli a gogon ɗakin sannan yace
“@9pm”
“Ok see you”
“Alright bye”
Ya kashe wayar yana sauke ajiyar zuciya, sai a lokacin yaji sarar da kanshi yake na farkawar da yayi a firgice. Ya ɗan daɗe zaune sannan ya sauko saman gadon ya nufi bathroom,
kamin ya kai wayarshi ta sake yin ringing, da tsaki ya juyo dan a zatonsa Minal ce ta sake kiran, yana dubawa yaga PA ɗinshi nan yayi wurgi da wayar saman. Gado ya shiga bathroom ɗin,
Bayan ya fito ya shirya cikin farar shadda da bakar hula da takalmi suma bakake, yayi kyau sosai haka ya fito kamar wani karamin saurayi,
Keys ɗinsa ya ɗauka tare da waya ya saka aljihu ya fice,
Hanyar downstairs ya nufa, kuskuskus ɗin da kunnuwa shi suka jiyo yana tashi ɗakin Huda ne yasa shi da wowa da baya ya tsaya daidai kofar yana sauraren su,
“Kawata kiyi amfani da wannan ance shi baya saka komai, kuma yana kariya sosai ba kamar wacan ba”
“Yauwa ta waje na haka nake so na gode sosai wallahi, kinga wannan ai ya fiye min allura da magungunan gargajiyar nan dan ni ba yarda nake dasu ba sai naga ma kamar basa yi”
“Ai ki gwada wannan kawai yar gari, nima dashi nake amfani kuma har yanzu ban taɓa samun wata matsalar ba shiyasa ma nace bari kema na kawo miki”
“Ai kuwa Wallahi kin kyauta na gode sosai Allah ya bar Zumunci”
“Amin kinga bari na tashi kar mijinki ya dawo ya same ni yace kullum cikin yawon zuwa gidan ki nake”
“Hahaha Saratu sarkin tsoro ai mijina bashi da wata matsala kiyi zaman ki mu sheki ayar mu”
“A a kara dai na tashi, gidan su Hauwa nake son biya wa itama akwai nata sakon”
Jin alaman fitowar ta yasa shi saurin komawa ɗakin shi, magana ɗaya da biyu da shiga masa yawo a kunne, _Ta fiye mata alura, ita bata son mai matsala_ me hakan yake nufi kenan?, Huda na shan maganin hana haihuwa ne ko kuma me? Wai shin mema wannan Qawar ta ta take yawan zuwa yi a gidan ne tun da gashi har ita da bakinta ta faɗa wai kar yace tana yawan zuwa gaskiya ya kamata ya bincika dan ga dukan alamu akwai wani abu a kasa,
Hular shi ya cire ya dora saman mirror, sai kai da kawo yake cikin ɗakin saman gadonsa ya kwanta yana nazari da tunano wasu maganganun da kunnenshi suka jiyo masa,
Bayan kamar mintuna arba'in ya tashi ya fito daga cikin ɗakin, daga bakin kofar ɗakin sa ya hango Huda zaune a parlor tana aikin data saba na kallo,
Hakan ya bashi damar wuce wa ɗakinta kai tsaye dan tabbatar da abunda yake zargi.
Bincike ya shiga mata kamar wadda ya bata ajiya, ya buɗa can ya buɗe can har jakar yan kullenta sai da ya zazzage, amman bai ga komai ba,
Har ya juya da nufin barin ɗakin sai kuma yaji a zuciyar sa da akwai wani abun, Wardrobe ɗinta ya nufa ya buɗe duk sai da ya zubar mata da tufafi kasa gurin bincike nan ma ba komai,
Kamar wadda aka tsakura sai kawai ya leka karkashin gadonta, akwati ya hango ɗan karama, da sauri yasa hannu ya janyo shi ya hau saman gadon ya zauna yana kokarin balle kwaɗo da aka rufe shi dashi,
Yayi iya yinsa wajen ganin ya ɓalle kwaɗon amman abun yaci tura, hakan yasa ya buɗe wata yar durowa da yasan tana aje keys ɗinta, gaba ɗaya ya kwaso so ya shiga gadawa, cikin sa'a kowa ya samu mai daidai da kwaɗon, jiki na rawa ya lakkama ya buɗe akwatin,
Magunguna ya gani kala kala wadda cikin zan iya cewa har da na mata, ya mutsa ya shigayi kamar mai ɗatu, wani table naga ya ɗauko mai kananan ɗiya yana dubawa gaba da baya,
Kai naga ya girgiza, ya tashi a fusace ya fice tare da maganin,
Downstairs ya nufo tun kamin ya karaso ya kwala mata kira,
“Huda minene wannan.?”
Yanayin kiran yasa gabanta ya faɗi, ɗago kai tayi tana kallon shi har ya sauko, maganin ya watsa mata a jiki yana mata wani mugun kallo,
Tana ganin maganin gabanta ya faɗi, sai a lokacin ta tuna da baya gidan toh yaushe ya shigo bata sani ba miya kai shi ɗauko wannan maganin bincike yayi mata kenan? Ko dai yaji abunda suka tattauna ne? Ba mamaki ma a fili na aje shi har ya gani, Wani rabon ido take tana mamakin lokacin daya shigo da kuma ganin maganin da yayi, cikin taku tace
“Wai wannan kake magana? Jiya da qawata tazo ta manta dashi”
“Ke karki raina min hankali wace Qawar ce zata shigo cikin gidan nan har tasa miki shi a akwati”
Tashi tayi tsaye ganin yadda yake tada jijiyoyin wuya, ga fuskar sa ba rahama,
“Saif Wallahi.. -”
Kasa k'arasa maganar tayi sakamakon hannun daya ɗaga mata,
“Bana son rantsuwa Huda kinyi matukar kaiwa karshe halinki ya isheni wannan wace irin rayuwa ce? Kinfi kowa sanin yadda nake son haihuwa amman kika ɗauki maganin hana haihuwa kika sha, for what.? Ance miki bana iya kula da yaran ne ko nace miki sunyi min yawa ne.? Ko kuma baki da lafiyar da zaki haihu ne?”
Kasa bashi amsa tayi, zufa sai karyo mata take, abunka da marar gaskiya lokaci ɗaya ta zube kasan gwuiwoyinta ta fashe da kuka,
“Dan Allah Saif ka yafe min kayi hak'uri Wallahi kuskure ne”
Hannayensa ya rungume ya ɗaga kansa sama,
“Ban san mi yasa na fara son mace irinki ba Huda har ya kai ni ga Aurenki, bansan wace irin kalar mace bace ke komai naki ya banbanta dana sauran mata duk wata rayuwa da macen Aure take a gidan mijin ta ke baki yi,
Damuwar mijinki bata dame ki ba damuwar ki kawai kika sawa gaba komai sai kinga dama kike yi a gidan nan amman duk wannan bai ishe ki ba sai kin sha maganin hana haihuwa, wadda ke kanki kinsan zai iya haifar miki da matsala wai haihuwar ce baki so ko me?”
Kuka take sosai tana tushe baki,
“Indai har haihuwar ne baki so ba sai kin kara shan maganin ba ni zan ɗauki mata ki”
Da sauri ta kalleshi, tana ganin juya ta rik'o kafarshi,
“Dan Allah Saif ka yafe min karka aikata abunda zaisa mu shiga wani halin kafi kowa sanin halin dana shiga a baya bazan iya rayuwa ba kai ba Saif karka min abunda kasan zai iya zama ajalina Saif ina sonka”
“Yes, kina sona Huda shine kawai abinda kika sani kuma kika iya dana taɓa ki kice kina sona sai yawan nuna kishi a kai na, amman duk abinda zai faranta min rai ruwanki dashi damuwa ta bata dame ki ba,
Na gaji huda kalaman nan su nake ta maimaita miki kuma da bakinki kince bazaki iya chanja wa ba na ɗaga miki kafa dan haka zan ɗaga miki kafar daga yau”
Yana kai wa nan ya fisge kafarsa ya nufi ɗakinshi, toshe bakin ta tayi yana matsar kukan daya zo mata, sai wani abu takr tana numfashi da karfi, da gudu ta tashi ta nufi ɗakinta.
[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...!
NA
KHADEEJA CANDY
_I dedicated this page to