Showing 108001 words to 111000 words out of 115850 words
Chapter 37 - BABBAN GORO Complete by Khadeeja Candy .txt
kowa magana ba, kuma kana ganinsa kasan yana cikin damuwa ta damu sosai, saɓanin Saif da tasan me ke faruwa, da kallo ya bi Momy har ta zauna sannan ya sauke ajiyar zuciya ya girgiza kai yana cika ma bakinsa iska
"Ni Momy ban ga anfanin wannan damuwar da kike sa kanki ba, wannan yarinyar bata da tunani kuma wallahi duk abunda ya samu mata ta sai na raina mata hankali"
"Kai ma ka yarda tana iya yi mata abunda Allah bai yi mata ba kenan"
Kan Momy a kasa take masa maganar, Lubna na zaune kusa da ita cikin da rashin fahimta idan ta kalli Momy ta kalli Saif. Kai ya girgiza
"Aa Momy ni ban yarda da wannan ba, kawai dai ita ce sanadi tun har ta faɗa da kanta"
"Kamar yadda ka zamo mata sanadin shiga halin da ta shiga ko?"
"Oh Momy ki daina shigar mata, kina son shafi laifinta ba, bata gurbi abunda ta shuka ba sai nan gaba"
Tashi yayi yasa hannayensa aljihu, ya nufi kofa
"Karka fasa kwalɓar nan Saif karka sake jefata cikin wani hali"
Tsayawa yayi cak, ba tare da ya juyo ba yace
"Ban jefa ta ba Momy ba kuma zan jefa ta ba, ita dai ta jefa kanta"
"Tun lokacin dana fara haɗuwa da Minal Kairat ce ka fara labarta min, sai kuma gashi kazo min da maganar Minal har ka aure hankalin ka bai kwanta ba har sai da ka auri Kairat, yanzu kuma ta kamu da rashin lafiya duk kabi ka fita hayyacinka har kana kokarin ɓatawa da yar'uwarka,
Nasan Kairat tayi maka hallacin tun da ta shayar da lil Minal kuma yanzu tana ɗauke da wani cikin naka, amman ina son kasan wani abu guda ɗaya, Ana chanja mata ba'a chanja yar'uwa ba shin yanzu idan ka rasa Kairat yaya zaka ji?"
Juyowa yayi da sauri ya kalleta, kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru ya haɗiye maganar, tare da numfashin sa, sai a lokacin ta ɗago ta kalleshi
"Haka zaka misalata yadda Safiyyah take ji a ranta baka da tausayi Saif ka canja kwatakwata kamar ba kai ba kana son kanka da yawa babu ruwanka da damuwar kowa sai taka zuciyarka ta mace! Tirr da irin son da kake yima Kairat tirr da son da xai rufe maka ido ka kasa ganin kowa sai ita kaji tsoron ranar da sonta zai wahalar da kai hakkin Safiyyah ya dawo kanka!"
Tunda ta soma maganar ya dinga jinta gan gan gan kamar ana sara masa gatari aka, sam bai zaci wannan maganar daga Mahaifiyarsa ba, tun tashin ta Momy bata taɓa faɗa masa wata magana makamanciyar wannan ba, amman a yau ta faɗa masa saboda Safiyyah, tsabbas ranta a ɓace yake yake dan har cikin makoshinta furucin ke fitowa,
Wani dogon Numfashi Lubna ta sauke zuciyarta na bugawa da karfi ta kalli Momy ta kalli Saif, Shima kallonta yayi ya kalli Momy sai ya ɗauke kai ya fice.
Wata tafiya ce yake mai kamar sauri-sauri kuma ba sauri ba, kallo ɗaya zaka yi ma fuskarsa ka fahimci tafiyar ɓacin rai ce yake, yadda ya bar gida sai da hankalin securities ɗin ya tashi, haka ya hau tt yana wani irin gudu kamar dansa kawai aka shinfiɗa titin, kamar wani ifiritu haka ya isa gidansa cikin kankanen lokaci. Har ya zauna maganar Momy ce take masa yawo a kai, tashi yayi ya nufi firjin ya bude ya ɗauki robar ruwa ya ɗaga kansa ya kafa kai, da wani irin karfi yake shan su, sai da ya kusa shaye wa sannan ya sauke kansa yana maida numfashi da karfi, ya jefar da kwalbar, saman kujera ya dawo ya ya zauna ya lumshe ido,har na kusan na mintuna talatin, can kuma ya buɗe ido da sauri kamar wanda ya tuna da wani abu ya tashi ya fito harabar gidan, ma'aikatan gidan ya fara kwalama kira, jiki na rawa suka iso cikin girmamawa, ɗaya daga cikin su ya kalla ya nuna masa gefen da itacen gidan suke
"Can nake son kuje kuyi ta binciko min wata kwalba, tana nan cikin kasa ku duba da kyau karku ce min baku ganta ba"
Da "Toh" suka amsa suka nufi gurin shi kuma ya juya ya dawo falon ya zauna, yatsun hannunsa cikin gashin kansa yana matsa gashin.
Bayan kamar minti arba'in, aka kwankwaso kofar parlour, ya ɗan daɗe kamin ya bada izinin shiga
"Yes"
Turo kofar akayi aka shigo, hannunsa rike da kwalbar mai cike da hayaki, ya mika masa
"Ga abunda muka gani"
A hankali ya buɗe ido ya sauke su kan kwalbar, da ido yayi masa nuni daya aje ta saman tebur ɗin dake kusa dashi, yana ajewa ya juya ya fice.
Kwalbar ya tsura ma ido, yana taɓa hancinsa kamar mai tunani, zuwa can ya tashi daga gimciren da yake still yana kallon kwalbar, sai da yayi bismillah sannan ya kai hannu ya rik'a kwalbar ya ɗaga sama yana kare mata kallo, wani abu ne a ciki mai kamar hayaki kamar toka da wani abu kasanta ja kamar ruwa jini,
Bismillah ya sake yi ya cira kwalbar iya karfinsa ya buga kasa, a nan take kwalbar ta watse.
59
Farin hayak'i ne ya turnike gurin daga bi sani hayakin yayi sama ya fita ta windo, Saif kan kallon hayakin yake ba ko kyata ido har sai da ya daina ganinsa, sannan ya kauda kai yana jan numfashi, ya daɗe yana nazarin maganar Safiyyah da kuma ta Momy sai dai maganar Momy ce take ɓata masa rai duk lokacin daya tuna,
abunda ya aikata a yanzu gani yake ya aikata daidai ko ba komai ita ta jama kanta kuma itace silar rashin samun kwanciyar hankalin aurensa ga kuma laifinsa da Momy take gani duk a dalilinta,
koma miye ta aikata can taje ta karata tun ba shi ya aike ta ba. tsiya ke tada tsohon bashi inji Hausawa, a nan ne ya soma tunanin taya akayi Deen ya san da wannan shirin na Safiyyah? Ita tambayar da ta rika zo masa a rai kenan tana masa yawo a kwakwalwah,
wayarsa ce kawai mafita, haka wani ɓangare na zuciyarsa ya amsa masa, a hannunsa ya rik'a juya wayar bayan ya fiddo ta daga aljihu sa, kamin ya soma shafa screen ɗin yana kallon hoton lil Minal, sai da wayar da fara ringing sannan ya maida hankali akan wayar, sai dai bai kaita kunnensa ba sai har sai da mai kiran yayi daf da katsewa,
"Ta ya akayi kasan da wannan labarin?"
"Ta amsa laifinta kenan? Ka tabbatar da gake nake ko?"
Aka amsa masa daga ɗayan ɓangaren, bai damu da ba da amsar tambayar da aka masa ba sai ya a kara jaddada tasa tambayar
"Taya akayi kasan da wannan plan ɗin?"
Shima ya ɗan daɗe kamin ya amsa
"Wata rana ne na fito daga kauyen mu, sai na haɗu da motar Safiyyah ita kuma tana kunna kai cikin kauyen, ganin kamar motar dana sani yasa na juya ya rika bin motar a baya har muka raba hanya,
Ta nan ne na hango fuskar Safiyyah kasancewar glass ɗin motor a sauke yake, a haka nayi ta binsu har naga gurin da sukayi Parking, a bakin kofar gidan wani babban boka dake garin namu,
Nayi mamakin yadda akayi Safiyyah tasan da wannan bokon, tunawa da abunda tayi min ta kuma yi ma Minal sai ya kawar da wacan tunanin nawa,
Bayan naga gidan da suka sauka sai nayi tafiya sai washe gari na dawo gurin bokan na zuba masa kuɗi mai yawa, a nan dake sai ya bayyana min abunda ke tafe da ita da kuma abunda ya aikata mata, ban gasgata hakan ba har sai da naji labarin Kairat ba lafiya,
Dana je gurin Mummy dan sanar mata sai na tarar hankalinta a tashe yake bata ma saurare na balle ta fahimci me nake nufi, nasan kai kaɗai ne mafita wanda zan faɗa ko da ba zaka yarda da ni ba,
Sai dai nasan wata rana zaka gasgata ni ka kuma yarda ada abunda na faɗa"
Lumshe ido Saif yayi, lokacin da Deen ya kai aya a bayanin sa, sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tasa leɓensa ya ce
"Thank you"
Deen bai kara ce masa komai ba ya kashe wayar,bayan kamar minti biyar wani kiran ya kara shigowa, ba tare daya duba mai kiran ba ya dannan picking yasa hands free,
"Kana ina Saif?"
Muryar Nasir ce hakan ya tabbatar masa da shine ya kira ko da ba number sa bace, ya ɗn bata lokaci kamin ya amsa
"Ina gida"
Wayar ya tsurawa ido bayan katse kiran, har lokacin zuciyarsa cike take da ɓacin rai.
Sai da Nasir ya kare masa kallo sannan ya zauna kusa dashi yana faɗin
"Lubna tace min kayi faɗa da Momy miya faru?"
Ba tare daya kalleshi ba ya amsa
"Bata faɗa maka dalilin faɗan ba bata ce maka mi nayi ba?"
"Bata ce min ba, ta dai kira ta faɗa min"
Sai a lokacin Saif ya kalleshi ya soma labarta masa abunda ya faru, dan abokin dariya ba'a ɓoye masa kuka, shiru Nasir yayi yana nazarin lamarin, bai ga. Laifin Saif ba ko kaɗan itama Momy ya san zafin rai ne ya haddasa tayi haka, kallon Saif yayi ya sake kallonsa damuwa ce kwanace a fuskarsa wanda ke nuna ta zuciya tafi wannan yawa, koba komai yasan yadda Saif ke gudun zuciyar Momy baya son ganin ɓacin ranta sam, kuma hakan kan iya haifar da ɓacin ran Abbah, Hannunsa kan kafaɗar Saif ya ce
"Ka kwantar da hankali i will talk to her"
"Ba zata saurare ka ba, idonta a rufe yake a yanzu ta kasa fahimta ta saboda Safiyyah, bata dubi halin da nake ciki da kuma wanda zan shiga"
"That's Why nace zan yi magana da ita Just have a faith zamu samu mafita"
Kai ya girgiza masa, shi kuma ya tashi sai shima ya tashi suka fito tare, shi ya ɗauki hanyar gidan Momy shi kuma ya nufi asibiti,
Yana yin parking Lubna ta fito ta tarbershi, sai da suka kawo kofar shiga parlour ta fara masa magana kamar mai raɗa,
"Momy ba zara saurare ka ba Ya Nasir, ko ta saurare ka ba zata fahimci abunda kake so ta fahimta ba, nima ɗazu akan hakan sai da ta tashi mari na"
Ya ɗan zaro ido yana kallonta da yar dariya
"Kece kema dakin samu rabon ki, amman ni nasan zata saurare ni"
"Wallahi wahalar da kanka kawai zakayi kila ma kai ma ta kwaɗa maka marin"
Wannan karon dariyar gaske yayi
"Tana ina ne?"
"Tana nan parlour ta haɗe rai sosai"
Har lokacin magana take masa a raɗa wai kar Momy taji, kumatunta kawai yaja ya kunna kai cikin parlour, bayan kamar mintuna bakwai ita ta rufa masa baya.
Har kasa ya risina ya gaisheta kamar yadda ya saba, sannan ya zauna a kujerar dake facing ɗin na ta, cike da fargaba ya soma magana dan shi ma kansa ya tsorata ta ganin yanayinta
"Momy, bai kamata a ce kina fushi da Saif ba, bashi da laifi cikin wannan lamarin kuma ki daina ganin laifin Kairat ita ma bata da laifi Momy Saif shine kaɗan ɗa namiji da kika haifa, baya da farinciki sai naki ya kamata a ce ke ce kika fi kowa fahimtar sa"
Yawun bakinta ta haɗe ba tare da ta kalleshi ta ce
"Kasan wani abu Nasir?, Safiyyah tana sa gaskiya naso kai ma da yawa, da ace Saif ne yake son ta da duk yadda zanyi sai naga nayi wajen ganin ya aure ta, ko ka nasan ba karamin shiga da fita zakayi ba wajen ganin abokinka ya samu abunda yake so,
Safiyyah Marainiya ce Nasir a hannu na ta tashi ya kamata ace na sama mata duk wani farinciki da take bukata, ban taɓa saka ta abu tayi min musu ba, duk abunda tasan yana faranta min itace kan gaba wajen aikata shi, sam sam sam ban kyautawa Safiyyah ba"
"Amman Momy yanzu.... -"
Hannu ta ɗaga masa,
"Ka aje kalaman ka Nasir, nasan kana kokarin kare abokin ka ne"
Bata tsaya jiran komai ba ta tashi ta nufi ɗakin ta, a sannan ya maido kallonsa ga Lubna ta ɗaga masa kafaɗu
"Ai na faɗa maka ba zata saurare ka ba"
Sumkuyar da kansa yayi kasa yana jinjina al'amarin.
Abu kamar wasa sai gashi Momy ta kusan kwashe kwana biyu babu ruwanta da Saif da duk abunda ya shafe shi, babu yadda bai yi amman taki ta kula shi, saboda har yanzu bata daina ganin laifinta ta, a duk lokacin da ta tuna Saif take ɗorawa laifin, gashi tana son zuwa sake duba Safiyyah amman ta kasa, saboda tunanin abunda zata ce mata. A ɓangaren Saif kan jin yake kamar ace masa rai ya huta, dan abun yayi masa yawa, ga matarsa a kwance, har yanzu ba wani sabon labari ga matsalan Momy shi, Mummy ma ta shirya komai da zata ayi aka kaita waje don duba lafiyar ta amicewar Saif kawai ake jira shi kuma ya kasa aiwatar da komai saboda Momy taki tasa baki cikin lamarin, cikin yan kwana biyu nan duk yabi ya rame abinci kirki baya ci iya kacinsa yan ruwan tea ko juice, ita kanta Momy tana tausayin halin da ɗan nata yake ciki ta dai ki nuna masa ne saboda har yanzu bata daina ganin laifinsa ba, dan iya kuskure tasan yayi, amman kuma ya za'ayi abun duk da ya girma ya riga ya gama girma, kuma tun ran gini tun ran zane.
Babu ani gwari a tare dashi haka ya shiga ɗakinta, sai da ya zauna kusa da ita kasan carpet sannan ya kalleta
"Momy an wuni lafiya"
"Lafiya kalau ya jikin matar taka?"
"Da sauki, Luban tace kina nema na"
"Eh akan maganar matar ka ne, shawarar da zan baka ka bar matarka a nan, da nan da can duka ɗaya ne tunda Allah dai shine yake bada lafiya kawai kasa Allah a gaba kayi ta mata addu'a"
Dagowa yayi ya kalleta akaro na biyu, dan bayi zaton jin wannan maganar daga bakinta ba,
"Ina nan ina yi Momy kuma Insha Allah haka zanyi"
"Allah ya bata lafiya"
"Amin"
Ganin ta kishingiɗa yasa shi tashi ya fito daga ɗakin zuciyarsa cike da tambayoyi, kao tsaye ɗakin Lubna ya shiga, bayan ya baro ɗakin Momy, tana zaune tasa plate ɗin abinci gabanta sai aikawa take tana dannar waya,
"Ke"
Ta juyo da sauri ta kalleshi,
"Yaya shigo mana ka tsaya can ko wani abu kake so ne?"
Shigowa yayi, yayi mata tsaye a ka,
"Mi akace da Momy yau"
Dariya tayi,
"Daman nasan sai ka tambaye ni shiyasa ya shigo ɗaki ai, kaga ta canja yau ko?"
Kai ya ɗaga mata,
"Wallahi Daddy ne ya rufe ta da ruwan masifa, yace shi sam na zai ɗauki wannan a gidan nan ba, akan me zata rika maka haka, yace idan har bata tausayin halin da kake ciki ai ta tausaya ma lil Minal,
Yace kuma Safiyyah ita ta jefa kanta cikin mugun hali, ba kuma ba a cilasla maka yin abunda baka tashi ba, yace kuma Safiyyah itace shi take yar'uwarsa ba Momy dan haka babu ruwanta da abunda ya shafe ta,
Daga karshe yace duk abunda ya same ka ita ce kuma ba zai kyale ba, yace duk kabi ka rame ka fita hayyacin ka da wani zaka ji!"
Shiru ya ɗanyi kamin ya ce
"Ke taya akayi kika ji?"
"Nice ma kai ma Daddy gulmar ai"
"Wai daman Daddy bai sani ba?"
"Eah mana, wacan karon ma ai ɗan yaga Safiyyah ta haukace ne shiyasa kaga yayi maka wannan faɗan kuma Momy ce take faɗa masa wai ai duk kaine da laifi"
"Thank you"
Haka kawai ya faɗa ya juya, yana murmushi ya fice.
*** *** ***
Kamar ko yaushe, yau ma ya daɗe yana addu'a bayan ya kare sallah Nafila ta karfe uku da yake yi kullum, ya faɗawa Allah bukatar sa ya kai kukan sa a inda za a share masa, sannan ya tashi jiki ba gwari ya nufi kujerar dake gefen gadon ya zauna, tsare ta yayi da ido, yana tunano yar karamar rayuwar da sukayi a tare, sannan ya kai hannu ya shafa fuskarta da ta bushe, daga bisani ya tura hannubsa cikin nata ya rike yana murza yatsunta a hankali, ajiyar zuciya ya sauke ya jinginar da kansa jikin gadon, jin ta motsa hannunta bai sashi ya ɗago ba dan ba sabon abu bane a yan kwana ki nan takan motsa hannun, amman ba magana ko kuma wani motsin,
"Sa... I.. F"
Cikin wahalalliyar murya ta kira sunan nasa, aiko ba shi ya ɗago da sauri ganin idonta a buɗe yasa shi gwalo nashi idon ya saki baki yana kallon ikon Allah, ita kan sai kallonsa take da dishi dishin da take ganin, da ba dan kashin turarenta ba da kuma. Sanyi hannunsa ba da ba zata iya gane shi ba, daga kwance ta dake ya rungume ta, kamin ya ɗauke cak ya rik'a waliliya da itar tsakar ɗakin, zuwa can kuma ya ajeta ya faɗi yayi ma Allah Sujadar godiya, sannan ya ɗago ya sake rungume,
Ita kan sai kallonsa take tun tana gani dishi dishi har ta fara gani daidai, tayi kokarin ta tunano abunda ya faru amman ta kasa, iya abunda ta sani shine ta daɗe tana bachi, zaunawa yayi saman gadon rumgume da ita kamar wata karamar baby ya rik'a fuskarta
"Kairat kina iya gani yanzu kina iya jina? Akwai inda yake miki ciwo? Meke damun ki yanzu?"
Hawaye ne ya gangaro daga idonsa, hawayen da ba zan iya tantance na minene farinciki ko akasin haka!. Hannu tasa ta shafe masa hawayen tana kallon idonsa, wanda da ita dashi ban san na waye yafi zurfi ba,
"Saif kuka kake yi? Mi ya faru da ni?"
"Zan faɗa miki komai daga baya kawai ki faɗa min mike miki ciwo a yanzu?"
"Babu"
"Kin tabbata?"
Kai ta gyaɗa masa, ya tashi, ita dai kallonsa kawai take har ya fice, be daɗe ba ya shigo tare da wasu likitoci guda biyu, Mummy ce ta uku, tayi mamakin ganin yadda ake mamakin tashinta sai abun ya koma mata kamar mafarki,
_Miya faru da ni?_