Showing 111001 words to 114000 words out of 124539 words

Chapter 38 - LALATA BOOK COMPLETE DOCUMENT By Sadnaf .txt

Sadnaf   

11 Dec 2024

9278

kala goma ,yabawa Yusrah guda shida,sauran hudun yabawa tasleem sa yace yasan Yusrah tana bukatarsu yanzu datake da ciki, sai tarkacen kayan makulashe daya tarkato,aranar bai je aiki ba,zama yayi abangaren Yusrah yana nan nan da ita,duk da tasleem Ce da girki,tasleem kua ta zage ta gyarawa Yusrah bangarenta dai dai ruwan wanka ita tahadawa Yusrah, el Bahrain ma dan tsabar murna sai daya kira hajiya ya gayamata, itama takira luba cikin farinciki ta gaya mata,luba jitayi kamar ta zuba ruwa akasa tasha dan murna, dan dama burinta kenan Yusrah tariga tasleem samun ciki, kiran el Bahrain tayi awaya tayi mishi murna dan tasan tun yana yaro yake da san yara, tace masa tana nan zua gobe, tinda ga lokacin el Bahrain yakoma yana lallaba Yusrah ko motsi tayi sai yace mata menene,dan bangarenta yakoma zama koda tasleem Ce da girki sai kwanciyar bacci ke kai shi bangaren tasleem,tasleem kua duk ita take aikin gidan dan cikin Yusrah mai laulayi ne sosai,bata cikakken minti ashirin batayi amai ba,inda Yusrah tarame sosai tazama kamar tsinke,dangi sai tururuwa zua suke suna dubata, ciki kua harda abban el Bahrain da hajiya,inda suka ringa sawa tasleem albarka dan yanda take dawainiya da Yusrah,agidansu tasleem ma Umma tazo ta duba Yusrah inda tayo mata abincin gargajiya ko zata Iya ci,dan ba abinda ke zama acikin Yusrah duk abinda taci sai ta amayo shi,aikua tasamu taci abincin dan ummansu tasleem ta iya girki sosai kuma batayi amai ba,ahaka el Bahrain yakoma yana kula da Yusrah dan wani sain shi yake mata wanka,dan bata Iya komai dakanta,yanzu kwata kwata el Bahrain bashida lokacin kansa ballantana yasamu lokacin tasleem, abun yana damun tasleem kawai daurewa takeyi azuciyarta kuma tana addua Allah yakawo ranar dazata samu ciki itama,ana saura kwana biyu ayi daurin auren izzadeen da Mufeeda,da yamma izzadeen na tsaye abakin windown saman Palon yana kallo waje yana tunanin Mufeeda Allah yasa itama ba disvirgin bace yahango tasleem tafito itada su Fateema da Mashida dasuka kawo musu ankon Mashida, tafito zata rakasu,dan adaidaita sahu suka zo drivern su Mashida baya nan,Mashida kuma tace batasan driven,zubawa tasleem ido yayi yaga yanda tayi kyau tayi haske sai dariya take tana labarta musu auren da izzadeen zai kara take inda Fateema da mashida,suma suka ringa kyalkyale dariya dan sun san takarewa izzadeen haka ya zuba mata ido har sai daya daina hangasu,yafara tunanin hanyar dazai bi yamata magana dakansa ya nemi yafiyarta,dan yana tunanin kamar el Bahrain karya yakeyi dayace masa yafada mata ta yafe mishi hangota yayi ta taho ita kadai yasauko daga saman dagudu har yana tuntube,dasauri ya bude kofar dakarfi tasleem dake gab da zua kofar gida ta tsorota,ganin izzadeen yanufota yasa kirjinta fara dukan uku uku
[2/24, 8:21 AM] My Mom: πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š







*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž






❀❀ *agaskiya masoyana bansan yanda zan nuna muku farincikin danake tsintar kaina aciki ba aduk lokacin da aka tabani kuka fito kuka mayar da martani ba abinda zan Ce muku sai dai nace Allah ya saka muku da gidan aljanna inaso kusan wani abu baka taba zama successful arayuwa sai Ka samu challenges sabida haka inaso Ku kwantar da hankalinku wanan alamomine na nassara,Abu daya nake so kuyimin indai kuna kaunata inkunga post na batanci da akamin kudaina forwarding kubarwa mutum kayansa awajen inaga inkukayi haka kun nuna min kauna,nakuma gode da kaunarku agareni sanan ina mai rokonku yawan hiran su tasleem da Yusrah dakukeyi yana janyo CeCe kuci atsakanin readers sosai dan Allah Ku rage,masu ganin novel dina yakarkace ina sanka Ku bari inagama novel din sai kuyi judging dina amma bawai ayanzu da ban gama ayita surutu,ina mika sakon gaisuwata gareku masoyana dama na Iya lissafo sunanku wlh danayi,jinjina gareku masoyana fauza Mrs bb,mhis kubra maman ramla nafeesat Aliyu blessing oliche,hakika naji dadin sakonku* ~love you oll readers oLπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°~πŸ‘πŸ»
􎰽𣐼􎰊
Page 150


Gudu gudu sauri sauri tayi hanyar gida,yayi sauri yasha gabanta,tayi Sauri takara kaucewa, dasauri yakara shan gabanta,pls tasleem ki tsaya ki saurareni minti biyu,innalillahi wa inna ilahi rajiun tasleem tace hankali atashe,dan Allah karufamin asiri kabarni inshiga gida,bazan Iya saurararka Kaba ni matar aurece,tayi sauri takara kaucewa zata shiga gidan, dasauri yakara shan gabanta,to minti daya tasleem bawani dogon magana zan miki ba,laillaha ilallahu Muhammad rasulillahi sallallahu alaihi wa salam,allahuma ajirni fi musabbati wa aklifnin khairan minha,izzadeen anya kanada hankali kua akan me zan tsaya in saurareka,wlh kabani guri in wuce ko namaka ihun kwarto tace rai abace tana kokarin ratsa ta gefensa ta wuce,ganin ba damar yakara shan gabanta tana dab da shiga cikin gidan ne yasa ya ruko hijabinta,juyowa tayi cikn tashin hankali gabanta na faduwa,ta kau da mishi wani wawan mari,ta kwace hijabinta daya rike da Iya karfinta,shikuma yayi kneel down cikin zafin nama,ya rungume kafafuwanta wajen gwiwarta, tasleem tasaki ihu nashiga uku na lalace jamaa ku kawo min agaji,dan Allah kirufamin asiri ki saurareni dan Allah yafiyarki nake nema,kicin kicin tafara yi na ta cire hanunsa Daga jikinta el Bahrain adai dai lokacin ya karyo kwana da motarsa,duka tafara kaiwa hanunsa tana kuka daya cikata,izzadeen yakara ruke kafarta pls kiyafemin,el Bahrain abunda yahango ne yasa yaji kirjinsa yayi wani irin bugawa kamar zai fado,yataka wani wawan birki dayasa suka dago gabadaya hankali atashe tasleem ta Dora hanun aka shikenan Ka kashemin aure,izzadeen yayi sauri yacika mata kafa gabansa nafaduwa,taku daya ne yakai el Bahrain gabansu,ya cakumo wuyan izzadeen yakai mai wani mugun naushi dayasa jini zubowa ahancinsa naushi yayi ta kai masa afuska cikin tsananin bacin rai izzadeen yaringa kokarin kare fuskarsa,matata zaka taba dan bakada mutunci,yakara kai mishi naushi,sabida bakasan darajar aure ba katabamin karungume min kafar mata,izzadeen shima cikin zafin nama yafara kaiwa el Bahrain bugu,dan yaga alama el Bahrain ba a cikin hankalinsa yake ba,tasleem kua ganin hakan ne yasa tafara ihu da akawo mata dauki,zasu kashe junansu,ihunta yasa suhaima tafito,Yusrah dake kwance apalo bacci yafara daukarta itama tasako hijabinta ta fito,ganin abun yakaisu da faduwa akasa ne yasa duka su ukun sukayi kansu dan kwata kwata layin ba jama,a,suhaima rike hanun el Bahrain tayi tana rokonsa,dan shine asaman izzadeen, ya kwace hanunsa ya hankadata,tasleem da Yusrah suma suka rikeshi suna rokonsa daya Daga izzadeen, ganin el Bahrain yariga yafusata ne dan kamar kara zugashi suke, yasa Yusrah tace dan abinda ke cikina kayi hakuri Ka cika shi,tsayar da hanunsa yayi cak,yana huci yadago ya kalli Yusrah,tace pls for the sake of our unborn Bby,ta mika masa hannu,ya rike tare da Daga izzadeen, suhaima tayi sauri tayi wajensa tana kuka,,tafara kokarin Daga izzadeen dake kwance lifelessly agaskiya Allah ya isa bamuyi yafe ba,mai yayi maka haka,dazaka mishi wanan mugun dukan suhaima tace tana kuka,el Bahrain kua kwace hanunsa yayi Daga rukon da Yusrah tayi mishi batare da ya kalli suhaima ba,yayi wajen tasleem dake rabe ajikin bango tana kuka yafuzgo hanunta yayi cikin gida da ita,,yusrah tayi wajen suhaima tana bata hakuri,data Daga izzadeen takai shi gida, ta canza mishi kayan jikinsa takai shi chemist, suhaima ta nemi Yusrah data tayata Daga izzadeen, ta rike baki tace ta rufa mata asiri tayi cikin gida da sauri,suhaima kua dakyar ta Iya Daga izzadeen, yadafata sukayi cikin gidan taringa jera mishi sannu.
[2/24, 8:22 AM] My Mom: πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š




*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž













❀ *wanan page din naku ne manyan aunties dinmu,hajiya shamsiyya ado muktar,da hajiya Hafsat ado muktar Allah yakara girma da daukaka*❀❀






Page 151




el Bahrain kua bangaren tasleem sukayi ya watsar da ita akasan carpet, yaringa kallonta da rinanun idansa dasuka ja kamar gauta,wani irin bakin ciki da kishi suna ratsa shi,takawa yayi yaje gabanta,ya ruko kafadarta,tasleem uban me kikajeyi awaje mai yahadaki da izzadeen dahar zai rungume miki kafa yace atsawace yana girgizata, su su su Fateema naje rakawa tace cikin muryar kuka,da iznin wa kika fita,tasleem ina miki kallon mai hankali nadauka ko waje nace kifita ke kadai bazaki fita ba dan kinsan gidan izzadeen yana kusa damu,shine kika fita purposely bada iznina ba har izzadeen ya Iya taba miki jiki baki dauki dutse kin fasa masa kai ba,kokarin magana take yace shhhh tasleem kinsan ya nake ji azuciyata kua,izzadeen yatabamin jikin danake mugun so fiye da komai kika tsaya kina kallonsa tasleem, mai yasa zaki min haka yace yana girgiza ta cikin tashin hankali,dan Allah kayi hakuri nayi kuskure ban taba tunanin zanganshi ba wlh da ban fita ba,tazame ta durkusa dan Allah Ka yafemin,shigowar Yusrah da sallama ne yasa suka juya suna kallonta,takaraso gurin el Bahrain ta ruko hanunsa taja shi suka fita waje,tasleem ta kwantar akasa taringa birgima tana kuka,yusrah kua dakinsa na bangarenta takaishi ta zaunar dashi akan gado ta durkusa agabansa ta dafa gwiwarsa,tace yaya dan Allah dan annabi kayi hakuri Allah ya huci zuciyarka,bansan mai yafaru ba amma nasan koma mnene bakaramin Abu bane,dan Allah kayi hakuri idan ma aunty tasleem Ce ta bata maka rai nima na ari bakinta nabaka hakuri dan nasan bazatayi abunda zata bata maka rai dagangan ba sai dai in kuskure aka samu,girgiza kafa el Bahrain keyi kawai yana hango yanda izzadeen yarike kafafuwan tasleem zuciyarsa wani bakin ciki ne yakara rufeshi zuciyarsa na masa zafi,mikewa yyi yakara yin bangaren tasleem kai abu kamar wasa fa yazama gaske, dan el Bahrain daya koma sama kuma damko tasleem yayi yana mata fada kamar zai daketa,abinka da Wanda yake da hakuri bai Iya zuciya ba ganin tana ta bashi hakuri,kamar kara zugashi take ne yasa ta fusge jikinta Daga rikon daya mata tayi waje dagudu tayi hanyar gidan izzadeen ,el Bahrain yabi bayanta shima da gudu,Yusrah da ganin yanda sukayi waje da gudun ne yasa itama tabi bayansu,tana gab da shiga gidan el Bahrain yakamota,ta fusge tafara magana cikin kuka,Ka kyalleni tunda bka yarda dani ba,inje insamu izzadeen ya kasheni tinda burinsa arayuwa ya gani abakin ciki,bansan mai yasa izzadeen yake min haka ba,kai danayi tunanin Ka yarda dani kafi kowa sanin halina kai ma gashi Ka murzawa idanka toka,izzadeen dake zaune akan kujerar Palo da kumburarriyar fuska suhaima na Dana mishi fuska da ruwan zafi,muryar tasleem dayake jiyowa ne yasa ya mike yayi hanyar waje,tasleem kua tana hangoshi tayi wajensa dasauri,el bahrain yasha gabanta, yajanyo hanunta yaringa jan hanunta sukayi waje Ka cikani inje ya kasheni ya huta tunda burinsa arayuwa yagani cikin bakin ciki,bai cikata ba har sai da suka koma bangarenta yasa ta adakinta ya kullo kofar,yayi waje, Yusrah data biyosu ta rabe ajikin kofa, tana ganin sun wuce takarasa gurin izzadeen dake tsaya da suhaima, tace wai mai ke faruwa ne izzadeen,mai yahdaka da Anty tasleem ko inda take bai kalla ba yawuce yakoma ciki, yusrah kua ganin haka ne yasa ta juya tare da cewa Allah yakyauta,kicibis sukayi da el Bahrain abakin kofa,ke kuma uban me kikeyi anan,jiki narawa tace bakomai tanufi cikin gidan,el Bahrain kuma yashiga ciki,direct Palon yashiga yaje ya Tarar da izzadeen daya dafe kansa da hannu biyu,izzadeen nazo namaka warning da Babbar murya kafita Daga harkar tasleem, idan bahaka ba wlh abinda zanyi maka nan gaba sai yafi Wanda namaka yanzu








HeadacheπŸ˜“
[2/26, 7:16 PM] My Mom: πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š




*written by*
πŸ’…πŸ’…
*sadnaf*πŸ’ž






Page 152


Kadai ji nagaya maka dan bantaba tunanin akuyancinka yakai duk da tasleem tana da aure karinga bibiyarta ba, izzadeen bakasan halina ba,wlh akan tasleem zan Iya kisan kai,enough kamal,enough of all this nonsense Izzadeen yace atsawace yana mikewa,look kamal let me tell you,dan kaga nama shiru bashi yake nunawa ina tsoronka ba,what's so special agurin tasleem dazan ringa bibiyarta,to bari kaji ingaya maka tasleem na Dade da sata akwandon shara tunda sai Dana gama abinda nakeso da ita na baka sauran,and tunda hankalinka baya jikinka idonka ya rufe akan tasleem wlh wlh wlh sai na kwace tasleem din Daga wajenka,sai narabaku,takarfi da yaji ko bajima ko ba Dade wlh,dan nasan tasleem dan batada option ne yasa ta aureka bawai dan tana sanka ba, in banda ma rashin hankali irin naka har kana da bakin zua kayi min magana akan tasleem,bayan kasan butulci kayimin da cin amana,Ka auri wacce nayi dating, kai wlh inka bani haushi ma har Yusrah sai na rabaku na auresu duka biyun inga ta tsiya dan baka san halina bane I can do anything to have what I want,tunda yafara. Magana el Bahrain yaji kamar kirjinsa ya fito dan bacin rai jin yace zai rabashi da tasleem ne yasa kirjinsa fara dukan uku uku,haka kace ko? ee haka nace,to Allah yabaka saa,ameen izzadeen yace yana jifanshi da mugun kallo da kumburarun idansa,OK we shall see el Bahrain yace tare da juyawa ya fita,izzadeen yayi tsaki yace dan iska kawai zaka san Ka tabani,suhaima da tunda suka fara musayar maganganu tasaki baki tana kallonsu har sai da el Bahrain yafita tadawo da kallonta kan izzadeen, tab izzadeen ashe kai bakaramin dan iska bane,yanzu matar abokinka kake nema,lailai Kai rikakke ne a yan iskan amma in bahaka ba inakai ina Neman matar aure, ni danasan abinda yafaru kenan wlh da mun barshi yamaka ido daya,muga ta inda zaka Iya kallon matar wani,izzadeen cire takalmin kafarsa yayi ya jefata dashi ta kauce,dan ubanki ba gwarani akanki ba matar wani na bi,ke da kika shigowa mutane gida da cikin shege ba fa Yar iska kawai,gaka babban,nufarta yayi aguje ta kwasa da gudu ta shige daki ta kulle,zakici ubanki xaki fito kisameni ya juya yayi hanyar dakinsa.






Yusrah kua tana shiga gida bangaren tasleem tayi,tanufi dakinta dan anan take jiyo kukanta,ta tura kofar taji arufe,aunty tasleem kibar kuka kinji dan Allah zan Bawa yaya hkuri duk da bansan mai yafaru ba,dan Allah kidaina kuka,haka ta karaci tsayuwarta abakin kofa,tana Bawa tasleem hakuri sai data gaji dan kanta ta hakura ta juya tayi bangarenta,apalo taje ta tarar da el Bahrain azaune ya Daga kansa sama yana kallon ceiling, yana girgiza kafa,jijjiyon Kansa sun ta tashi,ganin bai amsa sallamar data mishi bane, yasa jikinta yayi sanyi tasn cewar el Bahrain ransa amutukar bace yake, karasawa tayi gurinsa ta zauna agefensa ta ruko hanunsa,"yaya dan Allah dan annabi kayi hakuri,bana jin dadin ganinka ahaka,nasan abundant yafaru bakaramin bata maka rai yayi ba,duk da bansan mai yafaru ba,tunda Kaine babba kayi hakuri dan kaga itama aunty tasleem gata can sai kuka take,nasan kuma adalilin ka k'i hakura ne yasa take ta kuka,"Yusrah"naam yaya" ki kyalleni banasan magana yanzu, kitafi dakinki kije ki kwantar, magana takesonyi yace kitafi dakinki nace banasan damuwa,mikwa tayi ta tafi dakinta,aranta kuma tana ta tunanin mai yafaru hka








Aranar el Bahrain haka yazauna apalo yana tunanin sai dai inya ji kiran sallah ya tashi,Yusrah kua ganin tasleem bata fito ba har magriba ne yasa tayi hanyar kitchen dan ta Dora musu abinci,dan tunda tafara laulayi tasleem ke girki,koda itace da girki,jollof din taliya tayi niyyar dafa musu dan aganinta sai yafi saurin dahuwa,mai tafara soya taji zuciyarta na tashi,kafin ta Ankara amai ya kwace mata,amai takeyi sosai kamar zata amayo kayan cikinta,adai dai lokacin el Bahrain yadwo Daga massalaci yayi kitchen din dagudu yadagota,yaringa jera mata sannu ya kashe gas cooker din yace waye yace ta Dora girki, da tabarshi ya yo musu takeway,bandaki yanufa da ita, ya wanke mata jikinta,yadawo da ita daki,yaciro mata Riga ta canza kayan jikinta dan na jikinta ya jike, tana canza kayan yayi waje yatafi kitchen yaje ya goge aman.








Bngaren tasleem kua kukanta taci ta koshi taringa tsinewa izzadeen dayakeso ya wargaza mata rayuwa, sabida tsabar kukan dataci yasa ta fara ciwon Kai mai tsanani,adaddafe tayi sallah,ta kwantar akan sallaya ta rike kai tana ta adduoi,wayarta ne yafara ringing,sai da aka mata 5 miascall,bata motsa ba,jin kiran yacigaba da shigowa ne yasa ta rarrafa ta dauko dan tasan watakila Fateema Ce takira tafada mata taje gida lafiya,aikuwa tana dubawa taga itace,dagawa tayi tare da fashewa da kuka,Fateema dake kan sallaya ta mike, innalillahi wa inna ilahi rajiun,aunty tasleem mai yafaru kike kuka tace hankali atashe,Fateema ina cikin wani yanayi takara fashewa da kuka,subhanallahi aunty dan Allah mai ke faruwa ne tace itama cikin muryar kuka
[2/26, 7:17 PM] My Mom: πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š




*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž








Page 153


Dakyar tasleem ta tsayar da kukan datake tabawa Fateema labarin abinda yafaru,sakin wayar Fateema tayi jikinta yaringa rawa,tasleem jin datayi tana ta hello hello,ba amsa ba yasa takashe takara kira,Fateema da sabida tsabar bacin rai jikinta har wani karkarwa yake,dakyar bta Daga wayar,Fateema dan Allah cool your temper banasan Umma taji zancen nan,pls kiyi kokari kishigo gobe sai muyi magana, kashe wayar Fateema tayi,ta canza hijabin jikinta,tadauko kudi ta soka a skirt dinta,tayi hanyar dakin Umma,kafin takarsa dakin ta daidaita fuskarta,tura kofar tayi hade da sallama,Umma tadago ta amsa,ta ajiye bulugul marram din datake karantawa,"ya akayi fateema" Umma kaina ke min ciwo shine nakeso naje chemist na siyo magani,ina basiru ki aikeshi mana,Umma banganshi ba wlh shiysa ma nace bari na siyo dakaina, Fateema ban fiyeso kina fita da magriba ba,dan abbanku bai yaso,yi Sauri kije kidawo kafin abbanki yadawo,to Umma,tajuya dasauri tayi waje, tana fita waje, taga wani mai adaidaita sahu ya sauke wani, dasauri takarasa gurinsa tace yakaita rijiyar zaki,yace ba nan yayi ba,rokonshi tyi daya kaita zata bashi ko nawa yakeso, jin abinda tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login