Showing 57001 words to 60000 words out of 124539 words

Chapter 20 - LALATA BOOK COMPLETE DOCUMENT By Sadnaf .txt

Sadnaf   

11 Dec 2024

9269

dake kwance,yauwa kamal kai mun Yusrah chemist abata magunguna kanta ke ciwo kasan bata fiyesan hayaniya ba,Indai kanta ke ciwo bari nakarbo mata maganin ciwon kan,aa kuje tare tafi yi musu bayanin yanda takejin ciwon kan, Yusrah tashi yakai ki chemist din kinji,ta riko hanunta ta mikar da ita, ungo ribbon dinki karba tayi kanta asunkuye tayi parking gashinta,tasa hannu tadauko hijabinta tasa,ta Mike tabi bayansa,ta baya suka bi sabida gudun tsokana,waje suka fita dan dama bai shigo da motar ba,sabida masu decoration basu gama kwashe kujerunsu ba,babu wajen parking aciki,shiga motar sukayi ya tayar suka hau kan titi yaringa driving ahankali....
[2/20, 3:52 PM] My Mom: šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°






*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž










_A/N fans dina masoyan novel din lalata ina mai bakin cikin sanar daku ainihin abinda yafaru game dacin zarafina da akayi Wanda mukayi tunanin Aunty Sis tamin,inda kuka fito kuka nuna rashin jin dadinku sosai har wasu suka kira aunty sis awaya suka zageta,wasu suka ringa zaginta awatsapp duk adalilin zagin datamin,sai dai kash today being 23 of January at exactly 1 : 10pm na rana,I received a call inda aka min bayanin komai da komai nagame da abinda yafaru Ashe wata makiyata Ce dabata san cigabana tanaso ta janyo min bakin jini taje group din lubie mai tafsir amatsayin sadnaf,taje ta zazzagi ita lubien da aunty sis,takuma Ce musu itace sadnaf anan aka hau musayar kalmomi still same person ta turomin zagina da akayi agrp da irin aibata novel din dasukayi,nikuma na tura dan kun yanke min hukunci irin iskancin da akace na rubuta a novel dina abun yamin ciwo sosai Ashe duk misunderstanding aka samu fake sadnaf Ce ta haddasa komai duk abinda taga anyi posting awani GRP din sai ta turo GRP dina ta kwashi zancen GRP Dina takai wani GRP din duk bansan mai akayi ba sai yau da aka kirani akemin bayani dalla dalla,shiyasa akesan mutum yayi bincike kafin ya yanke hukunci,banida laifi aunty sis batada laifi dan bacin rai ne yasa ta kushe novel dina dan ansan writers da manners approach amma ita fake sadnaf ta hau ta zagi Nima inda bacin ran abinda tayimin na tura muku,kuka karanta har wasu suka nuna bacin ransu,to alhamdulillah Nagano gaskia mun kuma fahimci juna nida aunty sis fata dai Allah ya kiyaye gaba,aunty sis na ara bakin fans dina dasuka zageku nabaki hakuri sabida duk abinda yafaru rashin sani ne,dafatan fans dina sun gane aunty sis bata da laifi,munafukar kuma data hada wanan husumar Allah ya shiryeta ya gane gaskia,Allah ya kiyaye gaba ameen_






page 80






Yaringa driving ahankali,ya juyo ya kalleta yaga ta sunkuyar dakai,"Yusrah"dagowa tayi tana kallonsa haka kawai yaji gabansa ya fadi,yaga tamasa wani irin kyau na musamman ga wani kamshi dake tashi ajikinta,kinci abinci kua,gyada masa kai tayi,banyarda ba Yusrah watakila yunwa kike ji shiyasa kike ciwon kai,aa yaya ba yunwa nakeji ba,kaina ke ciwo to yaushe rabonki da abinci,tinda safe,shine zaki cemin bakya jin yunwa,ke meyesa bakya san cin abinci? Shiyasa fa bakya kiba kamar ahureki ki fadi,kai yaya duk kibanan tawa kace kamar ahureni infadi,tace ashagwabe,ahaka kike da kiba,hmm baruwana in tasleem taringa zama aruwan cikinki tana zaneki inkika mata laifi sabida rama,fadan hakan dayayi ne yasa taji hawaye na Neman zubo mata,laaa kuka zakiyi wasa nake miki fa little angel,kara nanata sunan daya kirata dashi tayi,little angel, heart beat,kai da banbanci atsakanina da tasleem ita bugun zuciyarsa ni kuma little,tace azuciyarta,am sorry kinji wlh wasa nake miki,nifa ba haushi naji ba,kinji mana,a inda ake. Siyarda kaji da tsire yayi parking yasauka,ina zua kinji 5 minutes, gurin mai siyarwa ya nufa yace yasa mishi kaji biyu,aka kara reheating din dankwala dankwalan kajin akasa mishi aleda,yaje daya side din dasuke siyarda lemo mai sanyi yasiyi lemona masu sanyi yadawo cikin mota yasa su aback seat,yaja motar suka cigaba da tafiya,Amarya ko kibari ki nuna min kwalliyar da aka miki,shine kikayi sauri kika goge kwalliyan dan kar nagani, lah Yaya wlh bahaka bane,wanka nayi fa,bawani nan ai sai kin kara min wani kwalliyar inkika ci abinci kika sha magani ,toh zanyi wani kwalliyar indai Kaine,yadai fi awani chemist suka tsaya yasauka yasiyi paracetamol,suka wuce gida,tare suka fito Daga motar,yadauko ledojin Daga bayan mota, wuce muje side dina,kici abinci kisha magani,yaya Dan Allah kabani inje dakin hajiya ince, ni bazan Iya cin abinci agabanka ba tace tana Rufe fuska,zaki wuce mutafi ko sai kintsaya batamin lokaci,karshen kunya ma gobe in aka daura mana aure waje daya zamu kwana,gaba yayi ta bishi abaya,bude kofar yayi ya shiga da sallama ya ajiye ledojin hanunsa ya juya yaga Yusrah bata biyoshi ba tana tsaye abakin kofa sai zare ido take,bazaki shigo ba sai nazo nadauke ki ,shigowa tayi asanyaye tare da sallama,ya amsa,akasan carpet tazauna shi kuma yaje kan fridge yadauko plate da table knife yakawo gabanta ya ajiye,yakoma yadauko tumbler cup guda daya yadawo gabanta yazauna
[2/20, 3:52 PM] My Mom: šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š


*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž






*kamar yanda namuku bayani an samu misunderstanding, kuma nida aunty sis mun fahimci juna dan naga har yanzu wasu suna min magana ta watsapp suna zagina wai nasa an zagi aunty sis,ni Nafeesa wlh bansa kowa ya zagi aunty sis ba,dan inada hankali niba jahila bace,an Riga anyi kuskure mun kuma gane,sabida haka dan Allah wala fans dina ko na aunty sis dan Allah abar maganan ya wuce kamar ba,ayi ba,dan munafikai duk su suka haddasa wanan abun,adaina biyoni prvt ana zuba min zagi,adaina bin aunty sis ana zaginta,wayanda suka haddasa wanan abun Allah ya shiryesu yaganar dasu gaskia*






Page 81


Ya bude ledar yazaro kaza guda daya ya yayanka da wuka,duk abinda yakeyi yusrah kallonshi kawai take tana karajin kaunarsa azuciyarta,dama nikadai Zan zauna da yaya,danaji dadi arayuwata tace azuciyarta,dagowa yayi ya kalleta oya sa hannu kifara ci kafin minti biyar inaso naga kin miko min plate dinan,waro ido tayi tana kallonsa,yes kike kallona ko bazaki ci bane,yaya kaza daya ai tamin yawa,nadauka nida kai zamuci,keda bazaki Iya cin abinci agabana ba taya zamu ci tare,wasa nake ma yaya muci dan Allah, sa hannu yayi yadauko cinya,yayi bismillah yafara ci,itama cinyar tadauko takai bakinta taringa taunawa ahankali,ganin taki sakin jiki taci sosai yasa yadauko wayarsa yafara Dane Dane hakane yabata dama,taci kazar ba laifi tazuba lemon tasha tayi gyatsa tare da hamdala,dagowa yayi yace ko kefa, sunkuyar dakai tayi tana murza zoben hanunta ballo paracetamol din yayi ya bata karba tayi tana yatsina fuska,sha mana,yaya da daci wlh,kisha ko indura miki,jujuya maganin taringayi ganin zata bata mishi lokaci ne yasa yazuba ruwa acup yanufi bakinta dashi,oya haa,ko na rike ki wlh na baki,bude bakinta tayi ta watsa tabs din abakinta yabata ruwan tasha,yauwa little angel,yanzu tashi muje inrakaki ki kwanta ki huta,tana kokarin tashi wutar palon yadauke,subhanallahi,mai yake faruwa ya wutan yadauke,kuna hasken wayarsa yayi muje in rakaki daganan sai in duba,mikewa tayi yayi gaba tana binshi abaya,ahaka suka fita waje,wayarsa ce tafara ringing,ringing din wayar kawai yaji yasan tasleem Ce dan ringing tone dinta daban,murmushi yasaki har hakoransa suka fito,yana kokarin dagawa yaga Yusrah ta zuba mishi ido,muje mana kika tsaya,ka answer wayar mana,ai nasan aunty tasleem ce,Yusrah ko kishi kike ne,yace yana murmushi,kiranta ne yakara shigowa wayar,siririn tsaki taja tana kokarin juyawa tabar gurin, dasauri ya riko hanunta,taji wani shock tunda ga kanta zua tafin kafarta,shima kusan haka yaji dan hanunta bakaramin laushi ne dashi ba,saurin cikata yayi yana yarfe hannu,am sorry wai fushi kike dani dan yayarki takirani,aa yaya ba fushi nake ba,kace ina gaisheta,tajuya dasauri tabar gurin,bin bayanta yayi da kallo har ta bace,ajiyar zuciya yayi ya girgiza kai aransa kuma yana mamakin yanda Yusrah ta nuna kishinta,kiran tasleem yayi awaya itama sai daya mata miss call uku tadaga,korafi tahau yimishi wai dan yana gaban Amarya shiyasa yaki Daga wayarta bakomai dama tasan yafisan Yusrah akanta ita maneji zaiyi da ita,hakuri yahau bata, yace bays kusa da wayar dakyar yashawo kanta tahakura,sukayi sallama,dafe kansa yayi wai tun yanzu kenan suna Neman dagula min lissafi,dakinsa yashiga yadauro alwala dan yayi sallah,




Washegarin dazaayi daurin aure tin karfe 9 en nesa suka fara zua,dan karfe goma zaayi daurin auren, izzadeen karfe bakwai agidansu el Bahrain tayi masa,suna zaune apalon el Bahrain dawasu abokanansa dasuka zo Daga nesa,bangaren Amarya Yusrah kua tuni ansa tayi wanka tayi kwalliya dawani shadda mai tsadan gaske,fari da aikin golden, tayi kyau sosai..
[2/20, 3:52 PM] My Mom: šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š


*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž














Page 82


Karfe goma dai dai dubanin mutane suka shaida daurin auren kamal ( el Bahrain) da Yusrah inda mahaifin el Bahrain yazama walliyin Yusrah, akan sadaki dubu hamsin,nan el Bahrain yayi ta gaisawa da Jamaa,yana washe baki,abbansu tasleem ma sai dayaje daurin auren, hotuna ango sukayi tayi da abokanansa,suka cikin gida aka zakulo Yusrah dakyar dataje ta buya tun lokacin da akayi daurin auren sabida tsokanarta da akeyi tayi,mayafi golden tayafa har saman kanta,hotuna akayi ta musu da el Bahrain ciki kua harda izzadeen amasu daukan nasu izzadeen shima bakaramin kyau ba,dan in el Bahrain baya gurin tunani zakayi shine angon, Nabeela kawar Yusrah sai rawar kai take ita gata tayi saurayi akayi ta uploading pix din a social network, adai dai lokacin tasleem take chattn aface book ,taga hotunan daurin auren,jikinta ne yayi sanyi dataga hotunan rintse ido tayi hawaye na zubo mata haka kawai taji wani kishi ya rufeta,oo yanzu Yusrah tarigani mallakar el Bahrain amatsayin miji,in ba kaddara ba,ba abinda zaisa in auri mijin wata,amma gashi asanadiyar yaudarar da da namiji yamin banida option dayawuce inje ata biyun,kanwar kanwata amatsayin uwargida,girgiza kai tayi cikin takaici takara kallon hotan da el Bahrain suka dauka da Yusrah suna kallon juna suna murmushi,bakaramin kyau sukayi ba,ajiye wayar tayi ta kwanta tana tunanin, Fatima Ce tashigo dakin da sallamarta,tasleem ta amsa,aunty yanaganki haka kamar Mara lafiya,wlh bakomai kawai bansan me ke damuna ba,murmushi Fatima tayi,ni nasan mai yake damunki Aunty kishi ne kawai,injiwa hmm Aunty nasani fa,kitashi muje friend tazo mu wuce ayimana kunshin daganan mu wuce saloon,ni Ku tafi kawai ma ba inda zani,hmm kinyarda kishine yake damunki tunda gashi kina zancen bazakije ba,alhalin kin Dade kina jiran wanan rana sabida tanadin dakikayi,Aunty kitashi mutafi dan Allah, ai in ba tashi nayi ba haka zaki sakoni agaba taja tsaki,ta mike, ta zura doguwar Riga ta yafa mayafin doguwar Rigar suka fita waje, gaisheta mashida tayi ta amsa,sukayi waje suka tari abin hawa,yakaisu gidan kunshin,basu tarar da layi ba dan sun Dade da booking, aka zanna musu hanunsa da baki da Jan lalle,banda kafa,na tasleem yafi kyau dan nata yafi tsada,daganan saloon suka wuce,aka musu gyaran gashi,ahanyarsu nakomawa gida kafin su samu abun hawa,el Bahrain da abokanansa sun cika mota zasu tafi inda suka kama dan suyi reception,izzadeen ke driving, el Bahrain agefensa,wasu abokanansa biyu abaya,gawasu motocin abayansu,kamar cewa akayi izzadeen ya juya ya hangosu atsaye,kurawa tasleem ido yayi dan alokacin an tsayar dasu, wani kyau yaga takarayi el Bahrain direction din da izz ke kallo ya kalla shima yahango su,haka kawai yaji gabansa yafadi,kai kaga wasu kyakyawa acan most especially chocolate colour dincan,gaskia tahadu,kai bkada ido ne wlh er duma duma can tafi haduwa dan full option Ce,cewar abokanan el Bahrain,juyowa izzadeen yayi cikin bacin rai ya isa haka dan wacce kuke maganarta matata ce,banasan irin wanan indai er duma Duma Ce kuje kusameta,amma banda tasleem kayi hakuri ai bamu sani ba,el Bahrain mutuwar zaune yayi dayaji abinda izzadeen ke cewa,karfin hali yace a zuciyarsa,kara juyawa yayi dan ya kallesu yaga sun tari abin hawa,sun tafi,izzadeen kallonsa yayi abokina ansamu matsala am in critical condition you have to help me out,amma bari agama walimar muyi magana,bai Ce masa komai ba inbanda haushin izz dayake ji azuciyarsa,wayarsa yadauko yayiwa tasleem TeX na soyayya yayi sending, yamar da wayarsa cikin aljihu,ahaka suka karasa inda suka kama dan ayi walimar akaci akasha,akayi hotuna,karfe 6 dai dai aka fara shirin tafiya mothers night,inda Yusrah tayi shigar red and silver,readers kuhango irin kyaun dazatayi amatsayinta nafara,el Bahrain shikuma shima kusan kalar kayan datasa yasa,shi hularsa da takalmi ne ash,sunyi mutukar kyau, bangarensu tasleem ma bakaramin kyau sukayi ba,dan Fatima da mashida shiga iri daya sukayi,da cord less baki,suka sa gwagwaro red anyi musu dinkin Riga da skirt, takalminsu da sarka da dankunne duk red komai nasu iri daya, tasleem kua farin material tasa mai dan banzan kyau, anyi mata dinkin Riga da skirt,sai net pink mai farin flowers da aka Nada mata,takalminta pink dasarka bakaramin kyau sukayi ba,dan tasleem har gyaran jiki Umma tayi mata kasancewarta ta Iya wai tafisan dangin el Bahrain su San hasken fata kawai Yusrah zata gayawa tasleem drivern gidansu mashida yazo yadaukesu...
[2/20, 3:53 PM] My Mom: šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°LšŸ…°šŸ™Š





*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž










Page 83


Drivern gidansu mashida ne yazo yadaukesu,suka dau hanyar meenah event centre,gurin acike yake sosai,zama sukayi acikin motar,suna jiran zua ango da Amarya,minti biyar da zuwansu,Amarya da ango suka karaso,izzadeen ke tukasu Nabeela agefensa tasa anko itama tayi kyau ba laifi sai daukar ido datake dagani kasan ba farinta bane ta shafa mai sai tauna cingam take,el Bahrain da Yusrah abaya,masu video coverage zageyasu sukayi suka fara daukansu hotuna,dakyar aka musu magana suka bada hanya abokanan ango da Amarya sukayi layi,suka sasu atsakiya,Yusrah jikinta sai rawa yake ganin yanda mutane suka sasu agaba har neman faduwa take el Bahrain yayi sauri ya tarota,sai a idansu tasleem kallon juna sukayi,Fatima zatayi magana tasleem tadaga mata hannu,matarsa Ce yanzu karki Ce komai,izzadeen ne yafito Daga motar da rafar Dari Dari ahanunsa yasaka wata dakakkiyar shadda milk colour,bakaramin kyau yayi ba dan izzadeen ya Iya dressing sosai gaban Amarya da ango yaje ya tsaya suna tafiya yana musu liki hangoshi da tasleem da mashida sukayi yasa gabansu faduwa,Fatima kuma taja wani dogon tsaki dan akuya dan iska mayaudarin banza mayaudarin wofi ahaka sai ka dauka mutumin kirki ne nan kua dan bunsuru ne,su tasleem basuce komai ba,illa ma kowace da tunanin datake azuciyarta,sai kutashi mushiga ciki,tinda sun shige Fatima tace,sis,dan Allah karkiyiwa izzadeen komai dan nasan halinki,kinsn el Bahrain baisan komai ba,kina wani abun zai gane, naji Ku tashi mutafi tace tana sauka Daga motar ai wlh ko yaya ne sai na mai rashin mutunci,tace azuciyarta,jerawa sukayi suna taku dai dai,Mashida da Fatima sai juya duwawu suke sabida uban hill din dasuka sa,tasleem takalmin datasa bai kai nasu tsini ba,ahaka suka karasa hall din,suna shiga hall din ido yadawo Kansu dan tasleem suka sa atsakiya kasancewar shigar white tayi su Fatima sukayi black sai sukayi ta daukan ido,el Bahrain dake zaune da Yusrah yana hango tasleem yafara murmushi dan bakaramin kyau tamasa ba,dan gashinta twisting dinshi tayi tayo gefen wuyanta dashi,itama murmushin tayi masa takarasa gurin hajiyarsu el Bahrain ta tsuguna har kasa ta gaisheta,kamo hanunta tayi tana murmushi,taringa nunawa dangi ita,ahaka ta rike hanunta suka karasa gaban ango da Amarya,el Bahrain kua sai binsu yake da ido, gefen Yusrah takai tasleem ita kuma ta tsaya agefen el Bahrain aka fara musu hotuna,atsakiya suka sa hajiyarsu el Bahrain aka daukesu,aka dauki el Bahrain yasa su atsakiya,Fatima da mashida suma shiga sukayi akayi,akayi hotunan dasu ganin sunfara Jan hankalin mutane yasa hajiyarsu tasleem tarike hanun tasleem suka bar wajen mashida cokala wayarta tayi aselfie stick sukayi ta hotuna da ango da Amarya duk abinan da ake izzadeen yatafi anso cake din da Amarya da ango zasu yanka,mashida da Fatima bakaramin tafiya sukayi da imanin abokanan el Bahrain ba,dan bayan sungama hotuna suka fara bude gurin da rawa, inda aka sa wakar kujerar tsakar gida,Mashida sai juya mazaunai take,liki akafara musu sosai ciki harda ango da Amarya,da hajiyarsu el Bahrain video da hotuna akayi ta musu sabida bakaramin burge mutane sukayi ba dan rawa iri daya sukayi tayi,dakyar Dj yace abar Amarya da ango suma suzo su taka,watsewa akayi akabar Amarya da ango afilli dan suyi rawa,Daga el Bahrain har Yusrah kamewa sukayi kamar bishiyar da aka dasa,Yusrah ta sunkuyar dakai kamar zata shige kasa,rufuwa akayi akansu aka fara musu yayyafin kudi,tasleem ma ba abarta abaya ba,en Dari Dari taringa lika musu dangin el Bahrain dasuka San itace amaryar dazai aura, koma kanta sukayi suna mata liki,ahaka mc yakara bukatan amarya da ango su koma su zauna,yana San aminin ango yazo yabada tarihin ango,sunan izzadeen aka ringa kira akaji shiru,har ankoma wajen el Bahrain dan yabada sunan wani sai gashi ya shigo,wani nabiye dashi abaya da cake ahanunsa,lokacin su tasleem na zaune aguri daya, karba lasifikar yayi Daga hanun mc,yayi sallama,ya bude taro da addua,yafara bada tarihin ango,Rabin en Matan gurin jisukayi suna San izzadeen, inda Nabeela taringa fiili da iyayi wai ita ga mai saurayi,tasleem kua lumshe idanta tayi muryarsa na tuna mata moment din dasukayi,mashida ma hka,Fatima kua sai zabga masa harara take kamar idanta zai fado kasa,ahaka yagama bada tarihin ango yamusu fatan zaman lafiya,ya mikawa mc lasifakar,aka tafa mishi, aminiyar Amarya aka kira nabeela dan tabada tarihin Amarya itama tafito tana wani fari,ta makale murya dan kanaji kasan makala muryar tayi tana fara magana Fatima da mashida suka kyalkyale da dariya,sai da tasleem tamusu magana suka daina,ahaka ta bada tarihin Amarya ta koma tazauna...
[2/20, 3:53 PM] My Mom: šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š






*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž








Page 84




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login