Showing 24001 words to 27000 words out of 80635 words
Chapter 9 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt
magana dashi".
"Hamma don Allah ka yi haƙuri a bi komai a hankali". Ta furta cikin kwantar da murya bai kula ta ya miƙe tsaye yana faɗin"na ba ki nan da mako biyu ki sanar da ni amsar tambayata". Yana dasa aya a nan ya shige cikin uwar ɗaka, Adda Azima ce ta hau aikin lallashina da kwantar mini da hankali.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 1️⃣3️⃣
Haka na kwana cikin zulumi duk da Anwar da Adda Azima sun kwantar mini da hankali sosai amma na gaza samun nutsuwa. Sai da aka yi kwana biyu wani yammaci Dada ta ce da ni in shirya ina da baƙo. Sai bayan sallan magrib ya zo, Dada ta ba ni tabarma ta ce na shinfiɗa masa a cikin zaure. Na ƙarba na yi kamar yanda ta faɗa.
A zauren muka zauna na gaishe da shi muryata ƙasa ƙasa, ya amsa mini tare da ɗaurawa da faɗin"kwana biyu yau cur ban yi tozali da ke ba, ina ta so na ƙira Hammanki na tambaya kuma ina jin kunya". Na ƙara yin ƙasa da kaina"to yanzun yaya aka yi kazo?".
"Gaban kaina na yi kawai na zo don ba zan iya jurewa ba, ban sa ni ba ko na yi laifi. Amma na sanya a raina cewar kafin na tafi zamu yi magana dasu na ji lokacin da ya dace ina zuwa". Na jinjina masa kaina hakan ya bashi damar cigaba da cewa"ina fatan yau kafin na tafi na sama amsa daga gare ki domin wallahi zuciyata ta kasa samun sukuni".
Ina wasa da dogayen yatsun hannuna na ce"zan zo ka ba ni lokaci na gudanar da istikara kafin na ce da kai komai". Ya yi ɗan jim kafin ya furta"hakan yana da kyau domin nima kafin na tunkari iyayenki sai na yi na kuma sama nutsuwa da ke, ina fatan na ji alkhairi daga gare ki".
"In sha Allah".
"Ba ki nema ji ki komai dangane da ni ba shin ko hakan baya cikin tsarinki ne?".
"Iyayena sun yi bincike akan ka daga gare su na ji duk wani abun ya dace na sa ni a game da kai". A jikina nake jin idanunsa suna kaina yake faɗin"to ba ni labarin abinda kika sa ni na ji". Na ɗago kaina na saci kallonsa ta gefen ido kafin na sama damar soma faɗin"na san sunanka, sana'arka da kuma inda kake zaune. A binciken da iyayena duka gudanar an same ka da dukkan ɗabi'u kyawawa. Wanda hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwar bari na, na saurare ka".
Sai da na tsagaita ina furzar da iska daga bakina na cigaba"ban taɓa tsayiwa da wani saurayi ba kuma ban taɓa ganin ɗaya daga cikin 'yan uwana tana yi ba, ni ce ta farko saboda haka nake cike da fargaba. Ban taɓa soyayya ba sai a wannan karon don Allah kar ka cutar da zuciyata kar ka zalunce Ni ta hanyar amfani da raunina na 'ya mace.".
"Ɗago idonki ki kalle ni".
Na yi kamar ban ji shi ba sai da ya ƙara maimaita zancen a karo na biyu, sannan na ɗago idona na sanya a cikin nasa.
"Ban taɓa cutar da wani ba balle ke da kika yi rassa a cikin zuciyata. Ban zo gaban iyayenki da nufin yaudara ba face auren da ko yau suka buƙata a shirye nake".
Sosai kalamansa suka ratsa ni tare da yin tasiri a dukkan sassan jikina, na kasa cewa komai tamkar wacce ruwa ya cinye ta.
"Ki ba ni dama zan tabbatar miki da cewar ni na daban ne a cikin sauran maza".
Murmushi kawai na yi masa shima ya maido mini dashi"ke kaɗai ce mace a gidanku?".
Na jijjiga kaina"A'a a wajen su Baffa dai ni ce kawai mace, amma ina da yayu biyu mata na wajen Babanmu Sannan akwai ƙanwata Abasiyya".
"Ban taɓa ganin su ba".
"To sau nawa ma kazo gidan? Kuma Adda Azima ta yi aure lokacin bikinta ne ka fancakala mini ruwa zamu je gidanta. Sannan Adda Abida ma aurenta saura kaɗan da Hamma Adnan".
Sai da jera kalaman masha Allah sau uku sannan ya ce"ke kuma da waye bikinku?".
"Hamma Ahmad sai kuma Allah bai nufa ba".
"Wataƙila rabona ne ya rantse shiyasa kika ga ba ayi ba". Shuru ya biyo bayan zancensa na ƙarshe sai can ya furta"ni kuma ni ne babban ɗa na miji a gidanmu ina da yayu biyu mata sannan ƙanina ɗaya, muna zaune tare da mahaifiyarmu domin Allah ya yiwa mahaifinmu rasuwa da daɗewa".
Cike da jajantawa na ce"Allah ya jiƙansa".
"Amin".
A wannan zuwan nasan mun ɗan tattauna sosai mun kuma ƙara sanin junan mu, da zamu yi sallama ya ce ba zai dawo ba sai na gama gudanar da istikara ya zo ya ji amsa idan Allah ya nufa sai ya turo iyayensa. A kan haka muka yi sallama ya tafi na dawo na sanar da Dada yanda muka yi, ta ce hakan ma daidai ne na yi istikaran.
A daren ranar na fara gudanarwa kafin na gama cike kwanakin na ji sauyi sosai a cikin raina. Haka nan kawai na tsinci kaina da matuƙar son ganin sa. Na fayyacewa Dada komai ta yi hamdala tare da sanya mana albarka.
Washe garin ranar da na gama kuwa ya cika alƙawari ya zo shi, Dada har da ba ni ruwa a sabon ƙofin da ta siyawa Adda Abida na taru ta ce na kai masa. Na tsiyaya masa tare da yi masa bismilla ya nuna mini a ƙoshe yake.
Ina gyara zamana na ce"sai dai ko in baka shan ruwan rijiya ne, amma wanda ya yi tafiya ai dole zai buƙaci ruwa".
"A'a ina sha sosai ma hasalima shi na sha na girma kawai na zaƙu da son jin amsata ne daga gare ki".
"To ka fara shan sannan na sanar da kai".
"Hakan ya yi miki?".
Na gyaɗa masa kaina ya ɗauki kofin ruwan ya sha kaɗan sannan ya ajiye ya ce"ina jin ki".
Na rusunar da kaina ƙasa"na ji a raina cewar kai ne alkhairi na ina farin cikin sanar da kai cewar ka sama gurbin a cikin zuciyata".
Ina ƙare faɗin haka na miƙe da sauri zan shige cikin gidan ya dakatar da ni da kalamansa.
"Ina koma za ki je? Ai dole ki dawo mu raba wannan farin cikin domin ya yi min yawa Ni ɗaya na yi shi". Ban amsa ba na dawo na zauna kaina a ƙasa.
"Na gode da samun wannan damar kuma ina mai tabbatar miki da cewar ba za ki taba yin da na sani ba. Zan wadata ki da dukkan abinda wata 'ya mace take da buƙata daga wajen ɗan miji dai-dai ƙarfina. Ki sanar da gida cewar idan an ba ni dama zan turo iyayena a yi maganar aure".
Kaina na ɗaga masa kafin na amsa cikin faɗin"da Hammana zaka kuyi wannan maganar". Daga haka ban ƙara cewa komai ba har ya miƙe muka yi sallama domin wani kunyarsa ce ta yi mini mamaya.
Sai washe gari na sanar da Dada ta yi murna sosai ta faɗawa da Baba Alhaji ya ce zasu yi magana da Baffa.
Ranar ina zaune ina dama furar da Hamma Adnan ya shigo da ita ya ce a damawa su Baffa. Anwar ya shigo da kallo na bi shi har ya zauna akan tabarmar dake shimfiɗe a wajen na ce"lafiya? Ko baka jin daɗi ne?".
Ya laune leɓansa"lafiya ƙalau wani labari mai daɗin ji nake tafe miki dashi". Na waro idanuna wajen"to wani labari ne wannan?". Ya gyara zamansa yana fuskanto ni sosai sannan ya ce"yanzun nan iyayen Abdul-hameed suka tafi sun zanta da su Baffa kuma an bashi auren ki za a yi tare da na su Hamma Adnan".
Ban san lokacin da na saki ludayin da nake dama furar da ita ta faɗi ƙasa ba, na dafe ƙirjina ban san dalilin tsintar kaina cikin matsanancin faɗuwar gaba ba.
"Lafiya?". Kaina kawai na iya ɗaga masa ina maimaita kalmar hasbunallah a cikin raina a ƙoƙarin samarwa kaina da nutsuwar da na rasa. Na ɗauki ludayin na wanke sannan na cigaba da damun da nake yi. Abasiyya da take zaune a gefe ta taɓe baki gami da faɗin"uhmm duk wanda ya ƙi ji dai to ba zai ƙi gani ba, kuma kowa san cewar tusa bata hura wuta".
Ta miƙe tsam ta shige ɗaki tare da banko labulen, ko kaina ban ɗago na ganta ba balle na ce da ita wani abun na gama abun gaba na shige ɗaki.
Bayan sallan isha'i Baffa ya ce kowa yaje shi yana neman sa, babban tabarma aka shimfiɗa a filin tsakar gidan duk muka zazzauna. Ya yi gyaran murya sannan ya soma magana kamar haka"mun tattauna da iyayen yaron da ke neman auren Aishatu kuma mun ba su aurenta, daidai lokacin da muka sanya na Adnanu haka ita ma za a yi nata. Sai dai ina so ku shaida wani zance ɗaya gabaɗayan ku".
Ƙirjina ya hau dakan lugudai na matse jikina wajen guda, kowa ya yi shuru Baffa kawai ake saurara da ya cigaba da faɗin" Aishatu za ta auri wanda take so bayan ta bijirewa zaɓinmu, ina so ku shaida ba zan laminta wani ƙorafi daga gare ta ba bayan an ɗaura aure a kai ta ɗakinta. Duk abinda zai yi miki ƙi yi haƙuri ki haɗiye tunda ke kika zaɓe shi. In ba sakin ki ya yi ba ban yarda ki ɗauko ƙafarki ki zo gidan nan da sunan yaji ko kin kawo ƙarar sa ba".
Shuru ya karaɗe wajen ni kuwa faɗuwar gaban da nake ji ya kuma tsananta, wata zuciyar tana raya mini cewar na buɗe baki na ce dasu na fasa auren amma hakan ma na san ba zai zama mafita ba. Domin Baffa ba zai taɓa laminta ba, ba ya yin magana biyu a rayuwarsa kuma ba ya yin zance ya janye duk abinda ya furta sai ya aiwatar.
"In sha Allah Yaya hakan ma ba zai faru, mu yi musu fatan samun zaman lafiya a cikin auren su".
Furucin Baba Alhaji kenan da ya sanya Baffa gyaɗa kansa kawai ya yi shuru. Baba Alhaji ya ɗaura da" za a yi bikin nan da wata ɗaya don haka duk wani shirye-shiryen da za ku yi sai ku fara shi tun daga yanzu".
Umma da Dada suka amsa a tare, a haka taron ya watse na je na kwanta gabaɗaya ina ji na wani iri. Na rasa me yake yi mini daɗi.
Washe gari ya kasance ranar juma'a ana ƙwalla rana mai zafi sosai, bayan an sauƙo daga juma'a 'yan mazan gidan mu gabaɗaya suka shigo. Hamma Ahmad ne yake shaida mini cewar ina da baƙo a zaure.
Na sako hijabina na fita na iske shi yana zaune har an shimfiɗa masa tabarma na gaishe shi ya amsa mini yana bi na da kallo.
"Na kwana cikin murna da godewa Allah daren jiya da iyayena suka shaida min cewar an bani ke".
Ban ce dashi komai ba ya cigaba da"ina so na yi miki wani tambaya". Na musguta"ina jin ka".
Sai da ya ɗan ɗau lokaci kana ya ce"shin za ki iya zama da uwar miji a gida ɗaya?".
Ban san sanda na ɗago idona na yi masa kallon ido cikin ido ba kafin na janye nawa.
"Me yasa ka yi mini wannan tambayar?".
"Ina son na ji daga gare ki naki ra'ayin game da hakan".
Na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina"a tunanina idan har ina son ɗanta da ya tsaga jikinta ya fito to dole ita ma na so ta. Idan zan iya jure halin tawa uwar na zauna da ita ko yaya take to tabbas zan iya zama da mahaifiyarsa domin ita ma mahaifiya ce a gare ni".
Ya ƙura mini ido na tsawon wasu daƙiƙu kafin ya saki numfashin da nima sai da na ji sa"tabbas da mata sun kasance masu irin tunani da kaifin basira irin na ki da an zauna lafiya a ko wani ahali. Tabbas na cika mai sa'a da na same ki".
"Amma har yanzu ban gane manufar yi mini tambayar ba". Na faɗa ina matsa hannuna waje guda. Ya sausauta muryarsa ya ce"saboda tare zamu zauna da mahaifiyata, ni nake kula da ita tun bayan rasuwar mahaifinmu. Hankalina ba zai taɓa kwanciya ba matuƙar na yi nisa da ita. Zan so ki taimaka min wajen tabbatar da wannan abun".
Gabaɗaya na ji jikina ya mutu murus a irin labaran da su Umma suke yi na kan suna faɗin irin ƙalubalen da ke tattare da zama gida ɗaya da suruka. Wannan dalilin ne ya sanya Baffa warewa Hamma Abubakar matsuguninsa daban tun bayan aurensa.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 1️⃣4️⃣
Ƙiran sunana da ya yi shi ya dawo da ni cikin hayyacina daga tunanin da na yi nisan kiwo a cikinsa.
"Lafiya kuwa?".
"Lafiya ƙalau".
Ya yi nisa kafin ya furta"na san mata da yawa suna gudun zama da uwar miji. Amma ba kowacce ba ce take zama matsala. Mafi akasari an fi samun matsala daga mijin ta hanyar nuna bambamci a tsakanin su. Da a ce kowa zai tsaya a matsayinsa in sha Allah babu wani ƙalubalen da zai bijiro".
Na yi ƙasa da kaina a hankali na furta"haka ne kam, ni kam daga gare ni bani da matsala game da hakan".
Ya yi hamdala tare da faɗin"na gode matuƙa Allah ya tabbatar mana da alkhairi". A sanyaye na amsa da"Amin". Har muka yi sallama na koma cikin gida zancensa suna yi mini yawo a cikin kwanyata.
Bayan mun gama cin abincin dare na iske Dada a ɗakinta tare da Adda Abida. Na sanar da ita komai ta jinjina kanta kafin ta furta"zama da uwar miji tabbas yana da nashi tarin ƙalubalen dole kuma sai kin kasance mai takatsan-tsan. Wasu iyayen mijin su kan kasance masu katsalandan a cikin harkokin gidan 'ya'yansu, wani matsala kuma daga wajen matayen take tasowa, domin su kan nuna cewar su ne akan gaba fiye da kowa. Suna mance irin wahalhalun da uwarsa ta yi dashi ya girma har ya taka matsayin da suka gan shi a kai har ya aure su".
Sai da ta tsagaita kana ta cigaba da faɗin"ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu wani abun da zai faru. Ki kasance mai biyayya da kuma alkunya, ki so 'yan uwansa ki kuma ɗauki mahaifiyarsa tamkar wacce ta tsuguna ta yi naƙudarki ta haifo ki. Idan kika sanya haka a ranki ba za ki taɓa yi mata ba daidai ba, dole wataran ta yi abinda zai sosa miki rai domin duk ɗan adam aziji ne tara yake bai cika goma ba. Ki zama mai kiyaye dukiyar mijinki kar kina yin almubazaranci, ki na ƙoƙarin ɗaura shi akan hanya sannan ki nuna masa cewar 'yan uwansa suma suna da haƙƙi akan sa. Ki rungumi 'yan uwansa tamkar waɗanda kuka fito ciki ɗaya dasu domin su zasu zame miki maɓoya a yayin da kuka sama saɓani da shi, ki zama mai kyau kuma kar ki bari abin hannunki ya rufe miki ido. Matuƙar kika riƙe waɗanda abubuwan da na lissafo miki za ki zauna da ko waye lafiya ƙalau babu wani tashin hankali".
Na kasa cewa komai jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwar gishiri. Ban ɗago kaina ba har izuwa lokacin da Adda Abida ta furzo zancen da ya sanya ni kallon ta, ta gefen idona da ya kawo ruwar ƙwalla.
"Tabɗijam lalle mutumin daga yin auren kenan zai haɗa ki da uwarsa?. Kina yarinya ƙarama ina za ki iya da wannan ɗawainiyar bayan na shi ga kuma na uwarsa".
Dada ta yi saurin kwaɓar ta"haramun ne zama gida ɗaga da suruka Abida?. Kar na ƙara jin yin makamancin wannan maganar". Ba ta kuma cewa komai ba ta ja bakinta ta tsuke, Dada ta cigaba da faɗin"kar ki ji komai Aishatu ki sanar dashi kin amince da hakan, ki hidimta mata dai-dai gwargwado sai ki ga kimarki da darajarki ta ƙara yaɗuwa a idanun mijinki".
"In sha Allah na gode sosai Allah ya ƙara girma". Na furta muryata ƙasa ƙasa bata fita da kyau, ta amsa tare da sanar da ni cewar zata faɗawa Umma.
Hamma Ahmad ya ƙira ni muka zanta ya ce duk abinda nake buƙata na sanar dashi, kar na ji nauyin sa duk wani abunda na gani ina so na faɗa masa zai saya mini ko menene kuma ko nawa ne.
Cikin sati biyu muka yi sabo da Abdul-hameed sosai ban san meye so ba sai a kansa, tabbas ya iya kulawa ya kuma san matakan sace zuciya tare da narkar da ita.
Kullum cikin takatsan-tsan nake dashi amma ko da wasa bai taɓa yi mini maganar banza ba, bai taɓa yunƙurin kai hannunsa jikina ba. Kullum burinsa bai wuce a ɗaura aure a kai masa ni gidansa ba.
Ko yaushe cikin faɗa mini yanda yake ƙaunar mahaifiyarsa da yanda yake burin kyautatawa da hidimta mata.
Gadan gadan bikin ya matso Hamma Ahmad kullum cikin nan da nan yake yi da ni, Anwar kuwa kwana biyun nan kullum cikin jinya yake da aka kasa gane kansa.
Hamma Adnan ya haɗe lefensa tsaf sai son barka, a unguwar Hamma Abubakar ya yi gininsa.
Ranar da hantsi dangin Abdul-hameed suka kawo lefen gidanmu. A gidan Baba aka sauƙe su wata da na ji ana ƙiran ta da Anty Adama ta dage akan sai dai a ƙira ni su ganni. Na sanyi hijabina na fito filin tsakar gidan na tsuguna na gaishe su gabaɗayan su. Suka amsa suna bi na da kallo kafin Anty Adaman ta furta"ke ce amaryar Abdallah nan?. Ikon Allah sai kallo wannan mitsitsiyar yarinyar ya tashi hankalinsa a kanta kamar zai zauce, kullum cikin zancenta Aishata kasa Aishata kaza Allah ya kyauta".
Na sunkuyar da kaina na kasa cewa komai, Adda Azima ta riƙo hannuna ta ce na koma ciki. Ko da na zare hijabin kaina neman waje na yi na zauna tare da zabga tagumi da hannu bibbiyu. Sai da suka tafi da yamma Umma ta zo ganin kayan.
Ya yi ƙoƙari sosai da kuma bajinta na gani na faɗa, a karon farko sai da su Dada