Showing 75001 words to 78000 words out of 80635 words

Chapter 26 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

matsilli ina kurma ihu ina faɗin"Umma". Wani jami'in 'yan sandan ya zo wajen da hanzari ya na tambayar me ke faruwa.


Wasu hawayen suka ciki mini idaniya na haɗo na kalle shi hawayen su na zuba na ce"don Allah Ummata nake son gani. Na roƙe ka ƙira mini ita ko a waya ne." Kallon da ya jefa mini ya tursasa ni saurin janye idona daga kan sa.


"Ba hawaye idanunki za su na fitarwa ba, ko jini ne wallahi ni dai kam ba zan ji tausayinki ba. Balle har na nema miki sauƙi, babu wanda zai shigo ya ganki a nan wajen a yanzu sai dai lauyanki. Don haka tun wuri ki cire ran sake ganin kowa idan kun haɗu a kotu bayan an yanke mi ki hukunci ku yafi juna da su".


A wulaƙanci ya yaɓa mini zancen cike da ƙyama da kuma kyara. Ya na gama faɗin hakan ya joya ya fice babu jimawa ya dawo ya buɗe ɗakin ya danƙwafa mini akwanon abinci da ruwa a gabana ya fice.


Na jifa kaina ina ƙara sakin wani kukan marar sauti sai dai haifar da zogi a cikin rai. Tunanin Umma ya ƙara ruru wutar tashin hankalin da nake ciki ina jin zuciyata tamkar za ta fashe.


A bayyane na furta"wallahi ban kashe Abdul -hameed ban kashe ba. Abdul-hameed bai mutu ba". Na ƙara fashewa da wani matsanancin kukan idanuna su na hasko mini hotonsa cikin farar kaya ƙyal ya na baza kyakkyawan murmushin da yake bayyanar da wushiyar dake tsakanin jeranrun fararen haƙwaransa.


Ƙunci ya mamaye mini zuciya izuwa yanzu na daina kuka da hawaye sai dai na zuci mai tsananin ƙuna. Ba na iya runtsawa ba saboda zafin da ƙirjina yake yi mini ga wani tarin da ya turnuƙe mini rai idan ya na yi kaki maimakon miyau jini nake tofarwa.
Kwana biyu tsakani babu wanda ya zo wajena sai a yinin na uku Barrister Aliyu ya zo ganawa da ni har cikin ɗakin da nake ya shigo ya yi zaman dirsham a gabana.


Dishi-dishi idanuna suke iya gane mini shi, kunnuwana da su na jiyo mini sautin muryarsa can ƙasa ya furta kalmar sunana. Na ɗago idona da ƙyar na yi masa kallo ɗaya ina mayar da kaina ƙasa.


"Sati biyu cakal kotu ta ƙara mana a koma zama na gaba, wanda nake hashashen idan a ba yanke miki hukunci a wannan zaman ba to a zama na gaba dole hakan zai faru. Saboda jama'a sun fusata sosai akan case, idan aka cigaba da jan case ɗin za su iya ɗaukar doka a hannunsu su illata ki ko ma su hallaka ki. Hatta ni kaina da an ƙira ni a waya an yi min barazana akan na fita daga cikin case ɗin. Na yi iya ƙokarin ganin na bibiyi diddigin lambar da aka yi ƙiran dashi amma babu wata kafar yin hakan, rayuwar Iyaye, 'yan uwanki da duk wasu makusantarki su na cikin hatsari. Tambayoyi biyar zuwa shida zan yi miki domin tabbatar da wani hashashen zuciyata".

Ban iya cewa dashi komai saboda nauyin da bakina ya yi mini da ya hana ni samun damar cewa ko kanzil. Shurun da na yi ya ba shi damar ɗaurawa da"ki ƙarisa min labarin zaman aurenku da marigaya a taƙaice".


Na ja dogon numfashi na fesar ina haɗiye miyau ɗin da ya taro a bakina kana na zama zarafin faɗin"Lokacin da Anwar ya taho da ni gida Baffa ya daka tsalle ya dire akan ba zan zauna a gidan ba sai dai in saki na ya yi. Da ƙyar da tsiɗin goshi Baba Alhaji ya jawo hankalinsa ya bar ni na zauna, ban koma ba sai da aka yi sunan Adda Abida wanda ta ci sunan Ummanmu Aliyatu. Sosai Hamma Ahmad ya nunawa Anwar ɓacin ransa akan me yasa zai taho da ni gida bayan ya san furcin da Baffa ya yi game da aurena. Ban koma ba sai da alamomin samuwar ciki suka bayyana a gare ni saboda wani rashin lafiyan da na yi na tsawon kwanaki uku , aka kai ni asibiti aka tabbatar da samuwar cikin sati biyar a jikina. Da kansa Baffa ya ƙira Abdul-hameed ya ce ya zo ya ɗauke ni mu tafi ba zan yi renon ciki a gida ba hakan aka yi na koma ɗakina tare da nasihar Umma da kuma Dada. Daga lokacin Baffa ya hana koma zuwa gidana, ko da na koma na tarar da Amira ba ta zuwa aiki da na nema jin dalili bayan na ƙira Asiya na sanar da ita ta shaida mini cewar bayan tafiyata gida Al'amin ya yi ƙoƙarin keta mata haddi shi yasa ta daina zuwa.
Da ƙyar na shawo kan mahaifiyarta har ta dawo aiki, na fuskanci tarin ƙalubale daga wajen Amma da sauran 'yan uwansa a lokacin mijin Anty Alawiyya ya aiko mata da takardar saki kamar yanda ta daɗe ta na buƙatar hakan daga gare shi.


Cikin ya na ɗan watanni biyar laulayi ya sako ni a gaba ba na iya taɓuka komai hakan ya sanya Amira dawowa gidan da kwana, na sama dukkan wani kulawa daga mijina. A lokacin Amma ta bijiro da wani sabon hali sai ta saita lokacin dawowarsa ya yi sai ta ƙira ni sashinta ta ce na zauna ba ta bari na na tafi har sai dare ya tsala. Ranar da naƙuda ya taso mini na sha baƙar wahala tamkar ba zan yi raina ba sai ba yar da wasiƙa nake yi. Sai da aka yi mini aiki aka ciro mini 'yan tagwaye, tsabar farin ciki da nuna godiyarsa ga Allah Abdul-hameed har azumi ya yi. Sai dai haihuwar ta zo da wani abu na daban domin yaran sun kasance dukkan su zabiya ne, Amma ta shafe idonta da toka ta ce sam ba jinin ɗanta bane domin a danginsu kaf ba a taɓa haiho zabiya ba. Sai da aka kai ruwa rana sannan ƙorar ta lafa bayan an gudanar da gwajin ƙwayar halittar da su ka nuna cewar yara dai na ɗanta ne.


Tunda muka dawo daga asibiti ba ta shigo baSai ana gobe suna ta shigo tare da Anty Alawiyya suka zo ɗakina wai sun zo ganin yara da kanta ta sa aka yi musu kuɗuba, washe gari babu wanda ya sanar da mu sunan yaran sai da yammaci muka ji sunan mahaifiyarsa da na mahaifinsa aka sanya bayan mun gama magana dashi akan sai ɗau ɗaya nima na ɗau ɗaya, Adda Azima ita take ta tausa ta akan kar na tada hankalina akan hakan na yi addu'ar Allah ya raya mini su kawai.


Tun su na cikin zanin goyo Al'amin yake gwada musu tsana da ƙiyayya a bayyane, a cewarsa wai ƙyamar ganinsu yake yi balle kuma ɗaukar su idan ya matso kusa dasu kuwa har kakakin amai yake ji. Na sha matuƙa wahala akan 'ya'ya kullum mijina cikin ba ni haƙuri yake tun ina ganin laifinsa idan wani abun ya faru har na dawo jin tausayinsa domin na fahimci ba laifinsa bane. Hamma Ahmad shi yake tsaye akan lamarin aurena duk wani matsala idan ta taso kafin na sanar da kowa shi nake fara ƙira na sanarwa. Mun zama ƙawaye sosai da Asiya lokuta da dama ta na taimaka mini da shawara akan abin da ya shige mini duhu, na yi gwagwarmaya har yarana su kai wata uku Amira ita ke taimaka mini da aikace-aikacen cikin gida, har wannan lokacin Hamma Ahmad bai yi aure ba har maganin aljannu ake karɓo masa da tunanin ko aljana ce ta aure shi ta hana shi aure amma duk a banza. Na yi ƙoƙarin haɗa shi da Amira amma abin zai yiyuwa ba.


Amma ta tsiro da cewar tun bayan haihuwata na dawo ƙazama ko wulgawa na yi sai an ji ƙarnin nono a cikina. Yara kuwa daman ta ce a daina shigowa dasu sashinta. Lokacin da su ka watannin biyar cif a duniya wani iftila'i ya faɗawa Abdul-hameed ya yi asaran wasu maƙudan kuɗin a kasuwancinsu, na ga tashin hankalin da ba na fatan ƙara ganin makamcinsa a cikin rayuwata domin Amma da raguwar 'yan uwansa sun gaza fahimtarsa hasalima shi suke zargi da salwantar da kuɗin. Hatta gaisuwarshi sai da Amma ta daina amsa ta fita daga duk wani abun da ya shafe shi gabaɗaya, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba".


Daga haka na tsagaita ina zuƙe majinar kukan da ya zo mini kana na ɗaura da" na sanar da Hamma Ahmad halin da ake ciki. Ba tare da sanin kowa ba ya sayar da shanayansa biyu da ya mallaka da suke ƙauye suka haɗa baki da mai kula dasu akan ya faɗawa su Baffa cewar sace su aka yi. Ba tare da sanin kowa ba ya damƙa mini kuɗin ya ce na bawa Abdul -hameed, ranar na yi kuka na yi kuka kamar raina zai fita na ƙara tabbatarwa kaina cewar lalle samun ɗan uwa kamar Hamma Ahmad babu dace ne a rayuwar nan ta duniya.


Mamaki sosai na hanga a fuskar Abdul-hameed lokacin da na bashi kuɗin tare da zayyana masa yanda aka same su sai na ga hawaye su na fita daga idonsa.
A take a wajen ya ƙira Hamma ya ce ba zai iya karɓan wannan kuɗin ba amma ya nuna masa cewar babu komai yi wa kaine, da kuɗin ya yi amfani wajen mayar da asaran da aka yi kasuwanci ya cigaba da tafiya. A wannan lokacin Amma ta bijiro da cewar lalle zai ya ƙara aure domin ya sama 'ya'yan da suka amsa sunansa kuma cikakkun ba irin wanda na haifo masa.


Idan na ce ba na kishin mijina wallahi na yi ƙarya amma na yi ina ƙokarin dannewa wajen mayar da komai ba komai ba. Da kanta ta zaɓo masa matar da zai aura aka shirya kai kuɗi gidan su, sai dai hakan bai sai dai-dai da sakon ɗaya ya sauya mini ba illa ma ninka kulawar da ya yi a gare ni".


A nan na ƙarƙare ina cigaba da kukan ya taso mini ina ganin komai a idanuna tamkar yanzu su ke wakana. Ina jiya jiyo sautin ajiyar zuciyar da Barrister Aliyu ya sauƙe kana ya ce" sorry" ya zaro handkerchief a aljihunsa ya miƙo mini na karɓa na goge fuskana.


"Ranar da lamarin ya faru za ki iya tuna wani abu muhimmi da ya faru?".


"Babu wani sabon abu da ya faru, na bar Amira da yara ta na shirya su na fito falo wajensa kasancewar ranar ban ji daɗi ba bai fita ko ina ba gashi kuma ya na azumi".


Ya yi ɗan jim kafin ya cigaba"ki dai ƙara tunawa babu wanda ya ko ya shigo inda kuke je?". Na yi shuru ina nazari sai can na furta"Asabe ta zo ta ce da ni Amma ta na ƙira na".


Da sauri ya tari numfashina"za ki iya tuna abin da ya faru da kika je sashin natan?".


Na gyaɗa masa kaina"damammiyar madarar da aka sanya zuma a cikinta ta saka Asabe kawo mini. Ta umarce ni da na shanye ta tas a gabanta saboda samun wadataccen ruwan maman da zan shayar da yarana da suka fara darawa".


"Daman ta saba ba ki madarar ne ko kuma wannan ne karon farko?".


"Wannan ne karon farko, saboda a lokacin abincin da suke samu daga gare ni ba ya isar su. Sai an haɗa musu da madara".


Ya miƙe tsaye tare da goye dukka hannayensa a bayansa ya na zagaye ɗakin yana faɗin"babu wani abun da ya faru bayan kin sha madarar?".


"Babu komai, na dawo sashina muka cigaba da hirarmu da Abdul-hameed".


Ya yi shuru ya cigaba da zagaye ɗakin da yake yi a zabure ya jefo mini tambayar"wa ya kawo miki madarar kika ce?".


Na ɗaga kaina na kalle shi"Asabe 'yar aikin Amma". Ya jinjina kansa haɗi da haɗe hannayensa waje guda yana faɗin"na sama abin da nake nema. Zan tafi yanzu amma zan dawo kafin a koma kotu".


Kaina kawai na ɗaya masa ya juya ya fara tafiya har ya kusa ficewa ya waigo da faɗin " kin yi dacen ɗan uwan da samun kamarsa sai an tona Hamma mutumin kirki ne". Yana faɗin haka ya fice ta bar ni rusar kuka.


*ƁOYAYYAR MANUFA*


©️ Maimuna Tijjani Iyam


______________________________


Page 4️⃣0️⃣


Motarsa da ya faka ta a waje Barrister Aliyu ya nufa yana tafe ya na nazari a cikin ransa, da tunanin ta yanda zai ɓullowa wannan lamarin mai tsarƙarƙiya.


Ya na shiga motar ya maida ƙofar ya rufe tare da jingina bayansa jikin kujerar dake zaune yana lumshe idanunsa. Jin an saita shi da wani abu a kansa ta baya ya sanya shi saurin buɗe idanunsa a zabure jikinsa ya na rawa.


"Idan ka juyo sai na harba kunaman bingiran nan na fasa kanka. Kashegi na zo na ƙara yi maka a karo na biyu idan ba ka ajiye wannan case ɗin da kake yi na Aishatu ba rayuwarka da ta iyalinta matarka da ta je gidansu haihuwa duk ku na cikin babban hatsari".


Runtse idanunsa ya yi jin ya ambaci matarsa da ta shiga cikin watannin haihuwarta. Zuffa ya na kwanciya a bisa goshinsa ya ce"matsalarku da ni ba da matata ba kar ku sako ta cikin wannan case ɗin". Ƙara danna masa bindigan ya yi cikin kakkauran murya ya furta"kuskuren da kake son yi na ganin ƙarfi da yaji ka wanke ta. Shi ya shafi matarka da kake tsananin so, idan ka ɗauki gargaɗin da na yi maka ka ajiye wannan case to ka yi kyan kai, idan kuwa ka yi kunnen uwar shegu to ka yi kuka da kanka".


Ya na gama faɗin hakan ya buɗe motar da sauri ya fice tare da shigewa wata motar da ta faka a wajen yanzu. Da ƙarfi aka figi motar aka bar wajen, ya fito da sauri ya na bin motar da kallo ko lamba babu a cikin motar da dukkan alamu sabuwa ce ko kuma since lambar aka yi.


Dafe kansa ya yi ransa cike da damuwa a tarihin aikinsa na lauyanci bai taɓa cin karo da case mai sarƙarƙiya kamar wannan ba. Bai taɓa gudanar da shari'ar da ta jefa rayuwarsa da ta iyalinsa cikin hatsari ba sai wannan.


Da hanzari ya koma cikin motar ya ɗauko wayarsa ya fito ya ɗauki hoton bayar motar sannan na ya fara ƙiran layin matarsa Asma'u, sai da ƙiran ya kusa katsewa ta ɗauka cikin sanyin murya ta yi sallama bai amsa ba illa sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi da ya yi. Jin muryarta kaɗai da ya yi ya samar masa da nutsuwa ya kuma goge masa mummunan hashashen da zuciyarsa take yi masa.


Kashe wayar ya yi ba tare da ya ce da ita komai ba ya kifa kansa a bisa sitiyarin motar. Waye wannan da yake yi masa barazana a waya da har ta kai ta kawo ya fito masa yau a zahiri tare da yunƙurin ɗaukar rayuwarsa?, Me yasa yake son ya ajiye wannan case ɗin mai girman gaske? .


"Waye wannan! Waye wannan?". Ya furta a bayyana ya na kaiwa iska naushi, ya daɗe a wajen da tunanin yanda aka yi ya san inda yake da kuma hanyar da ya bi ya shigo cikin motar bayan da hannunsa ya rufe ta kuma yanzu da ya fito sai da ya danna makulli kana ta buɗu.


Da ƙarfi ya figi motar bai tsaya ko ina ba sai ofishin 'yan sanda, bai fito ba ya na zaune cikin motar ya ƙira layin Inspector Ammar wanda case ɗin Aishatu yake a hannunsa kafin a miƙa ta kotu. Mintuna ƙalilan tsakanin ya fito ya buɗe ɓangaren mai zaman banza ya shiga.


"Barrister lafiya kuwa?".
Sai da ya furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakinsa ya na shafa sajen fuskarsa kana ya ce"Ammar akwai matsala bayan wannan lambar da na turo maka an ƙira ni dashi an yi min barazana game da wannan case ɗin. Yau kuma har cikin motata aka shiga aka sanya min bindiga akan ƙara jaddada min na ajiye wannan case ɗin, matuƙar ina ƙaunar zaman lafiyar matata da abin da take ɗauke dashi a cikin cikinta".


"Ya salam! Ina fata dai ba su cutar da kai ba?". Kansa ya ɗaga masa ya na latsa wayarsa ya nuna masa hoton bayan motar da ya ɗauka. Ya karɓa ya na gani a tsanake sai da ya gama kallo tsaf kana ya ce"ka tura min hoton ta what's app za mu yi bincike akan motar da kuma mamallakinta in sha Allah za mu gano ko waye ne ka kwantar da hankalinka, sannan kar ka ɓoyewa matarka komai ka sanar da ita ta yanda da zaran ta ga wani abun da ba ta yarda dashi ba za ta ƙira ta sanar da kai".


Kansa Barrister Aliyu ya jinjina cike da yaba ƙoƙarin Ammar ɗin ya ce"I trust you inspector na yarda da kai".
Murmushi ya yi masa tare da faɗin"ya ya ake ciki game da zaman da za ayi a kotu, akwai alamun nasara kuwa?".


"In sha Allah akwai alamun nasara domin na fara hango wani haske game da lamarin. Gobe ina so na je na gana da mahaifiya da 'yan uwan marigayi".


Gyara zamansa inspector Amma ya yi sosai yana sauƙe ajiyar zuciyar da ya tokare masa ƙirji. A sanyaye yake faɗin"wallahi na daɗe ban ji labarin da ya yi matuƙar ɗaga min hankali ba irin labarin rayuwar yarinyar nan, yarinya ƙarama amma ta haɗu da jarabawar rayuwa".


Cije leɓansa ya yi da ƙarfi kana ya sama damar faɗin" shi yasa nake son tsayiwa tsayin daka wajen ganin na yi duk mai yiyuwa don ganin ta buƙuta, idan ka ga halin da mahaifiyarta take ciki sai ka zubda mata da ƙwalla".


"Allah ya taimaka, in sha Allah za ka sama duk wani gudumawan da kake bukata daga gare ni ". Murmushin ƙarfin halin Barrister Aliyu ya saka ya na miƙa masa hannu su ka yi musabaha, bayan Inspector Ammar ya ba shi wani nau'rar da duk inda yake ya danna ta saƙo zai iso masa.




Daga cikin ofishin gidansa Barrister Aliyu ya wuce ya yi wanka tare da sauya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login