Showing 12001 words to 15000 words out of 80635 words
Chapter 5 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt
saƙo ne ta ba ka, shine na zo na sanar da kai".
"To ina maraba da wannan saƙon".
Ya faɗa yana ƙara yalwata annurin fuskarsa, ina fita na saki nauyayyar numfashi. Ɗago idon da zan yi na ga Anwar tsaye a gabana ya kafe ni ido, sosai yake mini kallon da sai ya tsorita ni.
Na yi masa alama da hannuna akan lafiya, bai tanka mini ba illa girgiza kansa da ya yi ya fice. A gidan na kwana washe gari muka je gaida Umma ni da Abasiyya.
Na yi zaton su Baffa sun tafi kasuwa domin ba su taɓa kai wa irin wannan lokacin a gida ba, da mamakina na gan su zaune a filin tsakar gidan kusa da garken tumakai. Umma na zaune daga gefen su akan kujera, sallamar da muka yi ya sanya su zubo mini idanu.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________
Page 0️⃣7️⃣
Muka tsuguna muna gaishe su gabaɗaya cike da tarbiyar da suka ɗora mu a kanta ɗorar, suka amsa mana a tare yayin da Baffa da Baba Alhaji suke miƙewa.
"Ki yi mata bayanin komai".
Umma ta ɗaga kai" in sha Allah a dawo lafiya Allah ya tsare ya bada abinda aka je nema". Tun tasowar mu muka buɗe ido muke ganin yanda Umma da Dada suke zazzagawa Baffa da Baba Alhaji addu'ar, yayin da duk zasu fita neman halali. Ba sai sun furta cikin kalmomin baki cewar suna jin daɗin addu'ar ba domin fuskar su ya riga da ya bayyanar da labarin zuciyoyinsu.
Muna addu'ar a dawo lafiya muka yi musu suka fice, sannan muka koma kan tabarman muka zauna. Umma ta kallo ni ta na sakin ajiyar zuciya"ku share filin gidan, sannan ke kuma ki zo ki same ni a ɗaki in kun gama. Za mu yi magana".
Take na ji ƙirjina ya harba da matuƙar ƙarfi, a sanyaye na amsa da"to". Muka miƙe muka ɗauki tsintsiya muka fara sharan. Muna gamawa na nufin ɗakin Umma da sallamata ba ta amsa mini a zahiri ba illa idanun da ta tsura mini har na yi wa kaina mazauni a ƙasa kusa da ƙafafunta.
"Ga ni".
Sai da ta washe wasu tsawon daƙiƙu kana ta ce" 'yar nan jiya wani bawan Allah yazo wajen Babanku da zancen neman iznin fara tsayiwa dake, a matsayin saurayi da budurwa". Take na ji wani zuffa mai maiƙo ya karyo mini, ban ɗago kaina ba har ta ɗaura"Baffanku ya yi faɗa sosai akan me yasa ma ya saurare sa bayan ya ji abinda yake tafe dashi, ya kuma ce a sanar dake ki ba wa Ahmad dama domin babu fashi haɗawa da na so Adnan da suke so a yi tare".
"Wallahi ni bana kula kowa kema kin sa ni, kuma babu wanda ya ce zai zo gidan mu".
"Na yarda da ke amma dai ki kiyaye sosai don Baffanku ya fusata ainun, ya kuma shaidawa Babanku idan ya dawo ya sanar dashi cewar an yi miki miji kuma auren ba zai ɗau lokaci ba za a ɗaura ".
Na faɗa tunanin to waye wannan mai zarra da ƙarfi halin da ya iya tunkaran iyayena kai tsaye?. A iya tinani ban taɓa tsayiwa da wani ba balle har ya san gidanmu ya zuwa iyayena da wannan maganar. Zancen murya ya katse mini hanzari.
"Ba ki da mijin da ya wuce Ahmad don haka ki karkara dukkan hankalinki gare shi".
Ban iya cewa da ita komai ba sai jinjina kaina da nayi, ta sa mini albarka tare da umarta ta da na tafi. Haka na fito jikina tamkar wacce aka zarewa laka, duk wunin ranar na ƙarar dashi wajen tunanin waye wanda ya zo wajen Baba Alhaji jiya, har zargi na yi kodai wannan matashin da muka tarar dasu jiya tare ni?.
Take zuciyata ta ƙaryata hashashen ƙwaƙwalwata babu ta yanda za a yi wannan matashin da ya murza shadda mai wakilya ya zo neman iznin fara zance da ni, duk da ban ga fuskarsa ba amma ban bari ba yaudari kaina da tunanin mallakan irin sa a matsayi abokin rayuwa ba.
Sai da muka je kwanciya na sanar da Abasiyya ta faɗawa Hamma Ahmad cewar na bashi dama, haƙiƙa farin cikinta ya ƙara ruɓanya babu abinda yake yi mini sai godiya tare da jadadda mini cewar gari na wayewa zata fara yi masa albishir da wannan daddaɗan labarin.
Haka na kwana cikin fargaba da tatardadin da ban san dalilin tsintar kaina a cikin sa ba, muna cin abinci Hamma Ahmad ya shigo ina jin muryarsa gabaɗaya ya yi faɗu da ya haddasa mini runtse idanuna. Na miƙe da sauri na shige daƙi ina jin Adda Abida da Abasiyya suna yi mini dariya. Na sauƙe ajiyar zuciya jin da na yi yana yiwa Dada sallamar ya tafi kasuwa.
Ya ɗago labulen ɗakin ya kare ni da ido na yi saurin rusunar da nawa ƙasa, ina iya jiyo saurin dariya da ya yi taƙaitacciya kana ya furta"sai ki fito cigaba da cin abincinki, tunda dodon da kike gudu ya tafi".
"A'a ni fa ba kai nake gudu ba".Na faɗa cikin inda-inda bai.
"Shikenan in na dawo da dare zamu yi magana kar ki yi bacci da wuri". Kaina kawai na ɗaga masa ya saki labulen ɗakin ta juya dai-dai sanda ruwar ƙwallar da suka wadaci koramar idanuna zubo.
Haka na wuni kamar marar lafiya gabaɗaya na rasa gane kaina, ana ƙiran sallan magrib fargaban da na wuni a ciki ya tsananta. Na zari hijabina zuwa duba jikin Anwar da har yanzu yana kwance, kiciɓusu muka yi dashi Ai shiga gidan yana dawowa daga masallaci.
Muka haɗa ido ya yi saurin ɗauke nashi tare da ƙoƙarin shigewa na yi saurin riga shi shiga, tare da tsayawa a gabansa. Har yanzu idanuna suna kan fuskarsa na ce"wai me ye yake faruwa na kasa gane kanka gabaɗaya, wani laifin na yi maka ne?". Sai da ba cire rai da samun amsarsa kana ya furta"ba komai tun ba yau ba na faɗa miki ba komai".
"Ba gaskiya kake faɗa ba wallahi wannan ba gaskiya bane, bayan ka san ina cikin tsaka mai wuya na taskun da su Baffa suka jefa ni. Shi ne kai ma ka bijiro da wannan halayyar da waye kake so na zauna na sanar dashi damuwata ya fahimce ni?. Bayan da kai kaɗai zuciyata ta aminta da ta ji sirrin dake adane a cikinta".
Na faɗa idanuna suna kawo ruwar ƙwalla, jingina ya yi da bango yana cije leɓansa tare da runtse idanunsa kana ya buɗe su tar a kaina.
"Ki yi haƙuri wallahi ba zan iya sanar dake abinda yake damuwa ba a yanzu, kawai ki taya ni da addu'a Allah ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar". Yana ƙare faɗin hakan ya shige cikin gidan ya bar ni tsaye a wajen, sai da na yi kokawa da numfashina da yake sarƙewa kafin na ja ƙafafuna na ƙarisa cikin gidan. Ban tarar dashi a tsakar gidan ba da nake kyautata zatona cewar ɗakinsa ya wuce.
"Akwai abinda yake damun yaron nan, gabaɗaya ya canja". Dada ta furta cike da kuma Adda Abida ta karɓe zancen da faɗin" nima na lura da kanka dubi fa wani ramar da ya yi kamar wanda ya kwashe watanni yana jinya".
Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ina jin wani ɗaci a raina, sai bayan isha'i Hamma Ahmad ya aiko ƙirana na je. Yake shaida mini ya ji saƙona a wajen Abasiyya kuma ya gode tare da yi mini alƙawarin ba zan taɓa da na sanin bashi damar kasancewa abokin rayuwata ba. Cike da kunya nake amsa masa, ya rako ni har zauren gidanmu ya ce na fara shiga shi zai biya wani waje kafin ya shigo.
Wasa-wasa asaran rai haka aka makonni biyu, babu abunda ya sauya zani na daga matsayin da na ajiye Hamma Ahmad a zuciyata na ɗan uwana. Duk ƙoƙarin kyautata mini da yake yi da bani kulawa bai sanya na ji son sa a cikin zuciyata ba. Gefe guda ga rashin sake mini fuska da wasa da dariyar da Anwar yake mini da ya fi komai jefa ni cikin damuwar da ya haifar mini da yi wata 'yar rama. A lokacin na fara yin sallan istikata na neman zaɓin Allah kamar yanda Dada ta umarce ni na yi, tare da roƙo na da na sanar da ita duk canjin da na ji a raina.
Haka na yi har na tsawon kwanaki bakwai, zuciyata ta kasance tamkar dutsin da ba ya jin shuri da ƙafa balle zunguri domin har yanzu bana jin koda ɗigon soyayyar Hamma Ahmad a cikin zuciyata sai dai na kan yi masa kara ina dannewa saboda alaƙar 'yan uwanta mai ƙarfi da yake tsakani.
Ranar da na yi kwana biyu da gama sallar neman zaɓin Allah Dada ta aiko ƙirana, ban yi ƙasa a gwiwa ba na gurfana a gabanta.
"Na ƙira ki ne na ji shin ko an sama canji, bayan istikatan da kika gudanar?".
Na sunkuyar da kaina ƙasa domin Allah ya sa ni ba zan iya kallon tsabar idon Dada na furta mata cewar bana son ɗanta ba, alhalin ita bata da burin da ya wuce faranta mini da ganina cikin walwala. Ganin na kasa cewa komai ya sanya ta ƙara faɗin"ke nake sauraro kar ki ji nauyin sanar dani komai, domin aure ba abun wasa bane. Dole sai da so da ƙauna a tsakani domin su ne ginshiƙin da yake riƙe aure har ya yi tsawon rai, kar ki yi duba da matsayin Ahmad a gare ni hakan ya sanya ki ɓoye abinda ke zuciyarki".
"Zan iya zama da Hamma Ahmad koda kuwa babu son sa a cikin zuciyata, zan yi wannan sadaukarwa a gare shi domin kuwa ya cancanci fiye da hak..". Tun kafin na ƙarisa ta yi sauri kwaɓa da faɗin"kul kul kar ki soma wannan tunanin, cikin dukkan lamuran zaɓi Allah yana kan gaba shin ki na jin son sa a cikin zuciyarki ko kuma a'a?".
Take na ji wani zuffa yana tsatstsafowa daga jikina na ƙara yin ƙasa da kaina cike da kunyarta. Na ji hannayenta a bisa nawa"Aishatu sanar da ni komai kar ki ji nauyina, yanda na su Azima suke a wajena kema haka na ɗauke ki. Kuma na yi miki alƙawarin cewar ba zan taɓa bari ki auri wanda babu shi a zuciyarki ba. Domin na san ɗacin dake cikin haka tamkar gudanar da rayuwa ce cikin duhun makanci da babu san ran zuwan haske ta wani ƙofa".
Sai da ta sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya mai bayyanar da damuwar dake danƙare cikin ƙalbinta kana ta cigaba da"ban taɓa ganin sa ba sai bayan an ɗaura mana aure, na yi biyayyar iyaye na zauna dashi kuma na yi masa biyayya dai-dai gwargwado tare da ƙoƙarin sauƙe duk haƙƙinsa da Ubangiji ya ɗaura mini. Sai dai har muka haifi Ahmad ban taɓa jin soyayyarsa a cikin zuciyata dai-dai da rana ɗaya ba sai dai hakan bai hana yi bashi girmansa da yin biyayya da dukkanin umarnin sa ba, na kan shiga ɗaki na ci kuka har na godewa Allah. A haka ba rayuwa har muka haifi 'ya'ya biyar dashi har yanzu da nake yi miki wannan maganar da ban taɓa sanar da ko wani mahaluki ba. Ba zan so ki yi irin wannan rayuwar ba".
Sai a lokacin na iya ɗago idona na sauƙe su akan fuskarta da idanunta suka tara ruwan hawaye. Tabbas Dada ta cancanci a ƙira ta da jarumar mace kuma jajirtacciya a cikin jerin matayen wannan nahiyar gabaɗaya.
"Dada zan yi biyayyar iyayen ni ma zan zauna dashi kodan na cigaba da samun albarkan iyayena".
Sai da ta yi jim kana ta furta"yarinya ce ke kuma zuciya bata ƙashi kar ki je garin nemar yarda iyaye ki jefa kanki da rayuwarki cikin garari. Ki bar zuciya akan abinda bata so domin babu irin kyautatawan da bawan Allahn nan baya min amma hakan bai canja komai ba".
Gabaɗaya jikina ya gama yin mutuwa na gama narkewa cikin tsantsar mamakin yanda zaman auren su yake. Na ƙara yarda da sahihacin wannan karin maganar na Hausa "mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo".
Ta ɗago haɓarta"kar ki damu in sha Allah zan san abin yi akan hakan". Kaina kawai na ɗaga mata hawayen da ban shirya musu ba suna zubowa daga idona ta sanya hannu tana share mini su. Lumshe idona na yi cikin raina ina ƙara jinjina ƙarfin soyayyar da Dada take yi mini da babu algus a cikinsa.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 0️⃣8️⃣
Tun bayan da muka zanta da Dada na rage damuwar da na azawa kaina, Anwar ma ya sauƙo ya fara sakar mini fuskata sai dai jikinsa babu cigaba kullum ji-i-yau. Bana taɓa mance safiyar wata asabar da kai tsaye zan iya ƙira da baƙar rana mafi muni a rayuwata.
Kafin su Baffa su fita kasuwa suka ƙira mu gabaɗayanmu muka haɗu a filin tsakar gidanmu akan babban tabarma. Baffa ya yi gyara murya yana cewar" mun taru a nan ne domin tabbatar da wani babban lamari da muke saka ran ya sama alkhairi a gare mu gabaɗaya in sha Allah. Mai babban suna shin kun daidaita tsakanin ku da Aishatu?".
Hamma Ahmad yake nufi domin haka yake ƙiransa a ko yaushe, kasancewar sunansa ya ci. Wajen ya ɗauki shuru kowa yana dakon sauraron abinda zai ce.
"Mun samu daidaito sai dai na ce ta yi istikata har yanzu bata sanar da ni canjin da aka samu bayan gudanar da hakan ba".
"Shin bayan gudanar da istikaran da kika yi kina jin Ahmad a cikin ranki ko kuwa?".
Baffa ya watso mini tambayar da ya sanya hanjin cikina kaɗawa, na kasa cewa komai illa ƙasa da na yi kaina jikina yana rawa. Na ji muryar Dada sun sauƙa a ƙofofin kunnuwana.
"Ta gudanar da istikara da nufin neman zaɓin Allah, amma sai dai har yanzu bata jin Ahmad a cikin ranta. A tunani zai fi kyautuwa a bata zaɓi ta zaɓa wanda take so. Domin zaman aure da wanda babu shi a zuciyarka wallahi abu ne mai wahalar gaske musamman idan aka yi duba da ƙaranci shekarunta. Kar aje garin neman ido a rasa gir.." Baffa ya tari numfashinta" bata son shi daman tun asali na fahimci haka".
Ta buɗe baki da zumar kare ni ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu"ba ta son shi ne kawai, domin na lura tun lokacin da muka ba shi damar yaje ya nema amincewarta. Gabaɗaya ta canza ta daina walwalar da ta saba balle gudanar da lamuranta kamar da. Ba ki da mijin da ya wuce Ahmad matuƙar ni ne haife ki kuma in na isa dake".
Cikin tsananin ɓaci rai ya yi maganar da hakan ya sanya ni ƙasa yin wani ƙwaƙwaran motsi. Baba Alhaji ya ɗaura da faɗin"ash ash asha yaya ban so ka furta hakan ba. Ya kamata a karɓa uzurinta domin uzuri ne mai ƙarfi da ya kamata a saurara. Istikata fa aka ce ta yi sallar neman zaɓin Allah kuma bayan gudanar da hakan ya kasance cewar bata jin sa a cikin ranta. Hakan yana nufin babu alkhairi cikin wannan haɗin koda kuwa an yi shi, kamata ya yi mu yi hamdala mu godewa Allah ya hakan ya bayyana tun gabannin a kai ga ɗaura auren".
"Dama tun can ba son shi take yi ba shiyasa ta yi amfani da wannan hanyar wajen bijirewa zaɓinmu".
"Don Allah Yaya ka sanyawa zuciyarka ruwan sanyi da lumana, a bi komai a sannu idan hankali ya ɓata hankali ake sanyawa a nemo shi. Wallahi ko an ɗaura wannan auren babu abinda za a dunga cin karo dashi sai tarin da-na-sani da nadama a yayin da lokaci ya ƙure mana, kar mu bari ɓaci rai ya sanya mu mance da ilmin addinin da muke dashi . Neman zaɓin Allah akan duk wani abun da kake ƙoƙarin yi abun ne mai matuƙar kyau domin Annabinmu ma ya umarce mu da yin hakan a dukkan lokacin da muke son aikata wani abu. Tunda lamarin ya kasance haka ni ina ganin akwai mu ba wa wancan bawan Allahn da ya taɓa zuwa neman iznin fara zance da ita dama, mu yi bincike a kansa idan an same shi da dukkan nagartattun halayya sai mu bashi damar turo manyansa".
So nake na ɗago kaina amma sam na kasa domin ba zan iya haɗa ido da Baffa a wannan yanayin ba, cikin wani irin yanayin da tunda Umma ta haifo ni na zo duniya ban taɓa kunsa a cikin makamancinsa ya soma ba wa Hamma Ahmad haƙuri.
"ka yi haƙuri mai babban sunan ni nayi maka alƙawarin aura maka Aishatu ba tare da na san hakan zata kasance ba, ta watsa mini ƙasa a ido tare da karyar mini da zuciya. A yau da ina da wata ɗiyar bayan ita da babu abinda zai hana na aura maka ita daren yau ɗin nan ka ɗaure ta ku tafi. Babban burina na aurar da ita ga ɗaya daga cikin 'ya'yan ɗan uwana ɗaya jal da ya rage min a duniya, domin na yi imanin komai runtsi komai wuya da tsanani da yanda rayuwa za ta juya zai riƙe ta bisa amana zai kuma samar mata da rayuwa mai inganci.
Shuru ya biyo bayan zancen na san na ƙarshe, babu shiri na ji wani kuka mai ƙarfi ya kubce mini. Na rarrafo na iso gaban Baffa cikin kuka na ce"ka yafe mini ka yafe mini Baffa, wallahi ba zan taɓa watsa maka ƙasa a ido ba. Ba zan taba baka kunya ba akan ko menene matuƙar ina da damar yin sa in zai saka farin ciki zan yi shi komai wuyarsa".
Da ƙyar na iddar da zancen saboda sarƙewa da numfashi yake yi, da kuma kukan da nake yi da dukkan ƙarfina. Sai da aka kwashi wasu mintuna kafin Baba Alhaji ya furta"tashi ku shiga ciki". Ya ƙare zancen yana nuni da ni da Abasiyya.
Muka miƙe muka shige ɗakin kwanan mu, a cikin labulen na tsaya don ba zan iya samun kwanciyar hankali ba matuƙar ban ji abinda aka yanke ba.
"Don Allah