Showing 39001 words to 42000 words out of 80635 words

Chapter 14 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

ya ajiye ba, ban taɓa yin musu da shi ba balle aikata abinda zai kai mu ga yin rigima. Tabbas zaman tare dole za a saɓa domin ko harshe da haƙori suna saɓawa amma Allah ne shaida na kiyaye dukkan wani abun da baya so tare da ɗabbaka abunda yake so ko da kuwa ni ɗin zan cuto. Amma akan 'yata ya kasa yi min uzuri ya ƙasa fahimtar raunin dake cikin ƙirjina ya jefa ni a tsaka mai wuya ta hanyar ba ni tsauraran zaɓi".


Ta ƙare zancen hawaye suna rige-rigen zubowa daga idonta. Adda Azima da ta kasa cewa komai ganin Umma na kuka gabaɗaya sai ta kashe mata jiki. Ta miƙe ta fice daga ɗakin tare yarce hawayen da suka zubo mata.


Cikin tausasan kalamai Dada ta soma faɗin"tabbas duk inda ake nemar jajirtacciyar mace wajen farantawa mijinta da nisantan abinda baya so kin kai a buga misali dake cike da alfahari. Tun da ya furta miki cewar idan kika je wajen ta a bakin auren ki ba tare da ya ji nauyi ko duba 'ya'yan dake tsakaninku ba . To babu makawa zai iya aiwatar da abinda ya furta, tunda Babansu ya yi masa magana ya ƙi sauraron sa a wannan karon ya kai maƙurar hawa dokin zuciya, ki yi haƙuri ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki yana sane da ke bai manta dake ba, ita kuma Allah ya kawo mata ɗauki ".


Sallamar su Hamma Ahmad ya katse Umma daga maganar da ta yunƙuro da nufin furtawa, sai suka zauna sannan ɗaya bayan ɗaya suka yi mata sannu.
Bata amsa musu ba ta fara faɗin" kun dawo daga kotun? Ina ita Aishan an sake ta ne?".


"Ki kwantar da hankalinki Umma, ai yanzu aka fara shari'ar sannu a hankali ake bin komai".
Hamma Abubakar ya furta cikin kwantar da murya da zummar kwantar mata da hankali , saboda yanayin jinyar da take ciki da tun faɗuwar da ta yi a ofishin 'yan sanda ta suma ta ba ƙara yin lafiya ba har yanzu.


"Ku sanar da ni gaskiya ko da kuwa munin zancen zai yi silar da za a kai ni kushewa, sai na fi samun nutsuwa fiye da ku ce za ku ɓoye min".


Duk shuru suka yi domin gabaɗaya sun rasa ta inda zasu fara zayyana mata lamarin. Hamma Ahmad ne ya yi ƙarfin halin faɗin"tabbas Aishatu tana buƙatar addu'ar kowa a cikin mu, zaman da aka yi yau ya nuna babu alamun nasara daga ɓangaren mu. Amma Allah baya bacci matuƙar tana da gaskiya ba zai taɓa bari ta tozarta ba. Domin ko da da sakan ɗaya zucuyata bata taɓa aminta cewar za ta iya kashe mutum ba balle Abdul-hameed, mutumin da ta nunawa tsantsar so ".


A wannan karan Dada ce ta furta"innalillahi wa inna ilaihir raji'u!. Allah ya dube yarinyar nan da idon rahama, ya bayyana duk abinda yake ɓoye".


Suka haɗe baki wajen faɗin"Amin". Kafin Hamma Adnan ya ce"mun yi magana game da yiyuwar su bamu yaran su zauna a wajen mu kafin muga abinda Allah zai yi, amma mahaifiyarsa ta hana a cewar ta jikokinta ba za su taso su sama irin tarbiyyar da uwarsu take dashi ba. Ba Baffa kaɗai ba hatta Baba Alhaji ya fusata su ce kar ɗaya daga cikin mu ya ƙara tunkarar su game da yaran mu bar su dasu tunda su ma jikokinsu ne".


"Ashsha! Ai in hankali ya gushe hankali ake sanyawa a nemo shi. Ban da abin su ai hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar".
Cike da takaici Dada ta yi zancen tana jijjiga kanta.


Anwar da tun da suka shigo bayan sannun da ya yiwa Umma bai ce ko kanzil ba. Ya tashi da nufin barin cikin ɗakin ɗaga ƙafan da zai yi bai sauƙe ba ya yanke jiki ya faɗi a wajen sumamme.


A rikice duk suka yi kansa suna ƙiran sunan shi tare da jijjiga shi. Hamma Abubakar ya shafa masa ruwar da Adda Azima ta miƙo a fuskarsa sannan ya saki gigitacciyar ajiyar zuciya mai matuƙar ƙarfi yana ƙare musu kallo.


Sannu duk suka shiga jeranta masa wani na bin wani, kafin suka fara tambayar me ke damun sa. Dagewa ya yi akan babu komai lamarin da ya fusata Dada ta zabga masa mari cike da ƙonar zuciya"ka cigaba da riƙe damuwarka a cikin ranka Anwar. Tunda mu ba mu kai ka sanar da mu abinda yake damun ka ba. Idan kana tunanin ba za mu iya magance maka ita bane ai addu'a ya kore komai, ko shi kaɗai muka duƙufa da yi maka zaka sama sassauci".


Tana dasa aya ta fice daga cikin ɗakin cikin matuƙar ɓacin rai, Adda Azima ta rufa mata baya tana bata haƙuri. Da kallo Hamma Ahmad ya bi Anwar da ya miƙe ya fice daga ɗakin bayan ya gama sauraron nasihar da Umma ta yi masa.


Tun faruwar lamarin Adda Azima da Adda Abida a nan gidan suke wuni sai dare su koma tare da mazajen su, Abasiyya kuwa ta na can garin su Baffanmu inda take aure.


Babu wani dogon maganar da yake shiga tsakanin Baffa da Umma daga gaisuwa sai bin juna da ido.
Tsaye Hamma Ahmad yake a ƙofar ɗakin zauren da Anwar yake ciki ya kafa kan shi da gwiwa tare da lulawa cikin duniyar tunanin da ya yi nisan kiwo a cikinsa.


Har ya ƙarisa cikin ɗakin bai san da wanzuwar sa a wajen ba, sai da kai hannunsa ya taɓo kafaɗarsa sannan ya dawo cikin hayyacinsa.


"Hamma yaushe ka shigo?".


"Na daɗe ina tsaye. Yau ina son ka sanar da ni damuwar da ka ɗauki tsawon shekaru kana ɓoyewa a cikin ranka Anwar".
Gyara zamansa ya yi yana naɗe ƙafafunsa wajen guda kana ya ce"babu abinda ya ke dam...". Tun kafin ya dire zancen ya dakatar dashi "ko yaushe haka kake faɗa, amma ni na san cewa akwai komai. Akwai abinda yake damun ka Anwar. Kar ka ɓoye min domin na san komai".


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam


_________________________


Page 2️⃣1️⃣


Fuskarsa ɗauke da maɗaukakiyar mamaki Anwar ya waro idanunsa ya ce"me ka sa ni Hamma?".


Taƙaitaccen murmushi ya saka"na daɗe da fahimtar cewar son Aishatu kake yi na jima da gano hakan. Shaƙuwar da ke tsakanin ku da kowa yake ɗauka a haka a ɓangarenka rikiɗewa ya yi ya koma soyayyar da take wahalar da zuciyarka, tun kuna ƙanana kake bata kulawa kana iya yin faɗa da kowa a kanta. Hasalima ko Umma ce ta yi mata faɗa sai an ga canji akan fuskarka. Ban tabbatar da cewa kana son ta ba sai bayan auren ta da Abdul-hameed, duk ranar da ka gan su tare sun zo gidan nan sai ka kwana da jinya. Ka kasa haƙurin rashin ta zuciyarka ta gaza karɓa ƙaddara Anwar, shiyasa a wancan lokacin ka nema amincewar iyayenmu da su baka dama ka yi nisa da garin nan".


Kansa ya jijjiga yana faɗin"Allah ya tsari zuciyata da son macen da kake so Hamma. Wallahi na gwammace son ta ya yi ajalina akan na yi tarayya da kai a wannan fagen. Ban taɓa tunanin haka za ta kasance ba, nasha tashi cikin dare na yi kuka a mahaliccina don samun mafitar damuwar da nake ciki. Zan iya sadaukar da komai a gare ka".
Dafa kafaɗarsa Hamma Ahmad ya yi yana kallon fuskarsa yake faɗin"ni ya dace na yi maka wannan sadaukarwa. Ni ya kamata na yi fatali da farin cikina domin ɗaurewar tsawon ran naka, na so a ce zan iya maida hannun agogo baya, na so ace zan iya goge duk abubuwan da suka wakana na yi amfani da tsaftaccen alƙalami wajen rubuta wani. Da sai na tabbatar da cewar ka mallaki Aishatu a matsayi mata".


Dafe kansa da jijiyoyin kan suka fito suka yi ɗara-ɗara Anwar ya yi yana faɗin"wani irin jarabawa ce wannan Allah yake jarabce mu da ita?". Ba zan taɓa iya aurar macen da kake so har cikin zuciyarka ba , ba zan iya yi maka wannan butulcin ba. Kowa kai ya sa ni kan sonta don haka kai ne kafi cancanta ka mallake ta fiye da kowa, Hamma Ahmad ka yafe min na kasa samun ikon sarrafa zuciyata ne. Kar iyayenmu su ji wannan zancen".


Jawo shi jikinsa ya yi tare da kwantar da kansa akan cinyarsa yana shafa sumarsa. Tsawon wasu mintoti cikin su babu wanda ya yi magana. Sai can Hamma Ahmad ya yi ƙarfin halin faɗin"ba ka yi min laifi ba domin kai ma ba yi kanka bane kuma babu wanda zai ji wannan maganar. Na yi maka alƙawarin matuƙar Allah ya yi ikonsa ya kuɓutar da Aishatu da wannan sarƙarƙiyar zan ba ka duk wani guduwama wajen ganin ka mallake ta".


Da saurin Anwar ya ɗago idanunsa da suka sauya kala ya zube su akan fuskar Hamma Ahmad da shi ɗin ma shi yake kallo. Ya ɗaga masa kansa alamar son tabbatar masa da sahihacin zancen da ya yi har cikin zuciyarsa hakan take.


Bai bashi damar cewa komai ba ya miƙe ya fice daga ɗakin, ya bar shi cike da zallar ruwan mamakin da ya shayar dashi. Da ƙarfi ya kaiwa iska naushi yana buga kansa a ƙasa"hande min boni na shiga uku. Me yasa na kasa riƙe kaina? Me yasa zuciyata ta kasa daure rashin ki Aishatu?. Tabbas na ji tsananin kunya, kuma zuciyata ba ki yi min adalci ba, ta rasa wacce za ki faɗa soyayyar ta sai wanda ɗan uwana yake tsananin so kaico na".


Haka ya ƙarar da wuni cikin wani halin da shi ma kansa ba zai iya faɗin abinda ke damunsa cikin kalma ɗaya ba.


Na ƙara shiga cikin tashin hankali, na fita daga hayyacina ina da yaƙinin ko maƙiyana ya gan ni sai ya zubar mini da ƙwalla. Sau ɗaya Barrister Aliyu yazo domin ganawa da ni, na kasa cewa dashi komai dole ya haƙura ya tafi.


Ranar da aka mayar da ni kotu kamar yanda na yi hashashe harabar kotun a cike ya ki maƙil da dandazon jama'a. Da ƙyar aka sama hanyar da aka shigar dani izuwa cikin kotun.
Anty Adama, Anty Alawiyya da Al'amin su na fara hanga, gabana ya yi wani mummunar faɗuwar da ya tursasa mini runtse idanuna da ƙarfi.


Alkalin ya buƙaci Barrister Aliyu da ya fara gabatar da hujjan da ya buƙaci kotun ta bashi lokaci domin haɗo su. Ya miƙe ya gabatar da godiya sannan ya ɗaura da"zan so Amira 'yar aikin gidan marigayi Abdul-hameed ta bayyana a gaban kotu".


Sai a lokacin na buɗe idona ina bin Amira 'yar aikin da Abdul-hameed ya kawo mini da kallo yayin da take fitowa ta tsaya a gaban kotun, Barrister Aliyu yana isa gaban ta sai da ya gyara tsayiwarsa ya ce"kotu za ta so ta ji alaƙar ki da marigayi da kuma wacce ake zargin ita ta kashe shi".


"Ni ma'aikaciya ce a gidan marigayi, ina taya matarsa aikace-aikacen cikin gida".


"Kwana kike yi a gidan ko kuma zuwa kike idan kika gama aikinki ki tafi?".


Ta ɗaga kanta tana kallon shi"farkon zuwa na ba na kwana sai da ta sama ciki ne na dawo gidan da kwana".


"Ko za ki iya bayyanawa kotu yanda zamantakewar aurensu yake?".


Sai da ta ja numfashi mai dogon zango kana ta furta"ban taɓa ganin macen da take tsantsar son mijinta kamar yanda Antyna take son yallaɓai ba. Ban taɓa ganin su na musu ba balle tashin hankali, idan ya furta baya son abu kuwa to ta bar aikata wannan abun har abada. Duk wani abunda zai sanya shi cikin farin ciki tana ƙoƙarin aikata shi, ba ta barin sa cikin damuwa domin idan yana cikin wani hali har tana fin sa shiga damuwa. Na sha ji da kunnena yana faɗin cewar shi kam ya yi dacen mata a gidan duniya da yake fatan su rayu tare har a gidan aljanna, rayuwar auren su abun sha'awa ce kuma abun kwaikwayo da raguwar ma'aurata".


Daga haka ta tsagaita tana yarce hawayen da suka kwaranyo daga idanunta.
Barrister Aliyu ya soma faɗin"ya mai girma mai shari'a tabbas akwai lauje cikin naɗi a labarin da Malama Amira ta zayyana a gaban kotu. Babu wani abun da ya taɓa haɗa su, ba a taɓa jin kansu ba balle ayi musu sulhu tun da suka yi aure, zai yi wuya haka siddan ta ɗauki wuƙa ta ɗaba masa ba tare da wata ƁOYAYYAR MANUFA ba".
Ya ƙare zancen yana komawa mazauninsa.


Shuru ya karaɗe kotun, Alkalin ya furta"ko lauyan gwamnati yana da tambayar da zai yiwa malama Amira?".


"Ƙwarai kuwa ya mai girma mai shari'a".


Barrister Adam ya furta yana miƙewa da takun alfarma ya isa gaban ta Kana ya soma faɗin"ko za ki bayyanawa kotu ranar da lamarin ya faru kina ina?".


"Ranar yallaɓai ya tashi da azumin nafilan da suke yi tare da Anty a duk ranakun litinin da alhamis, ranar bai fita ko ina ba saboda Anty ta tashi bata jin daɗi a gida ya wuni. Ta gama shayar da 'ya'yanta ta bar ni tare da su a ɗaki zan shirya su ta fita wajensa. Bayan wani lokaci na fara jiyo ihun sa".


Ya yi saurin faɗin"me yake cewa a cikin ihun?".


"Faɗi yake yi me na yi miki za ki kashe ni Aisha, na kasa fita domin da farko na zargi kunnena da tashin tace sautin da ya jiyo min. Sai da na jiyo kukan mahaifiyarsa da 'yan uwansa na fito na tarar dashi kwance cikin jini baya motsi. Ban don ina cikin gidan abun ya afku ba, ko mahaifiyata ce ta ce da ni Anty za ta iya ɗaukar makami ta yanki jikin yallaɓai ba zan yarda ba balle har ta daɓa masa wuƙa".


Ta ƙarƙare zancen wasu hawayen suna biyo kuncinta, sallamar ta ya yi ta koma ta zauna kana ya fara cewa"ta tafi wajen sa kuma bayan wani lokaci aka ji ihunsa yana ambata sunanta akan kar ta kashe shi, tabbas Aisha ita ce babbar abar zargi a cikin wannan lamarin. Duk tarin soyayyar da ta nuna masa bashi yake nuna cewar ba zata iya aikata laifin da ake zargin ta da shi ba, zai iya yiyuwa a lokacin da ta je wajensa ta ji yana waya da wata zuciya ta ɗebe ta. Ta aikata wanan aika-aikan".


Da saurin Barrister Aliyu ya miƙe"objective my lord! Lauyan gwamnati yana amfani da tsauraran kalamai wajen son jingina dukkan laifin ga Aisha, bayan har yanzu zargi kawai ake yi ba a tabbatar ba".


"Ka kiyaye Barrister Adam".


"In sha Allah, zan zo kotu ta bani damar yiwa A'isha wasu tambayoyi".


"An baka".


Ya iso gabana ya tsaya tare da furta kalmar sunana , ban amsa ba illa ɗago idona da nayi na sauƙe akan fuskarsa da shi ɗin ma ni yake kallo.


"Wani irin zamantakewa ku ka yi da marigayi?".


Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya, idanuna yana hasko mini dukkan abubuwan da suka gabata ɗaya bayan ɗaya. Take na fara jin tamkar yanzu abubuwan suke faruwa.


*******


Turus na yi ina sakin jakar hannuna ta faɗi izuwa ƙasa, yayin da muka haɗa ido da Al'amin da ya gama birkita gabaɗaya ɗakin.


"Lafiya? Wani abun kake nema?". Na furta cikin rawar jikina da na murya. Ya yi mini wani kallon da ya tsananta rawar da gabaɗaya jikina yake yi.


Ya buda tsaki yana nufo inda nake tsaye"ke har kin isa ki titsiye ni da tambayar me nake nema don na shigo sashin ɗan uwana. Bana son shishshigi a lamura na don haka ki kiyaye kuma bakinki ƙanin ƙafarki kin ji ni?".


Da hanzari na gyaɗa masa kaina alamar na ji tsabar tsoritan da na yi na kasa buɗe idona na kalle shi har ya fice daga ɗakin. Na fi mintuna uku tsaye ban motsa ba kafin na yi nasarar furzar da iska daga bakina.


A hankali na tako cikin ɗakin na zauna a bakin gado ina kallon yanda ya yi kaca kaca da ɗakin. Na jewa kaina tambayar da na gaza cimma amshoshin su.


Shin me ya kawo shi har cikin ɗakin baccina? Me yake nema haka? Me yasa ya gargaɗe ni da cewar bakina ƙanin ƙafata?.


Sai da na ji masallacin dake kusa sun iddar da sallan magrib sannan na zabura na tashi, na shiga banɗaki na yi alwala na zo na gabatar da sallan. Ban yi dogon addu'a ba na shafa na ɗaura hijabina a ƙuguna na fara tattare ɗakin.


Sai da na mayar da komai mazauninsa na zauna ina mayar da numfashi lokacin har an shiga sallan isha'i, na tabbatar ana iddarwa Abdul-hameed zai dawo don haka ina yi sallan isha'i na shiga wanka.


Doguwar rigar material na saka na yafa mayafi na fita sashin Amma, domin ta sanya dokar zama a sashinta a irin wannan lokacin kullum. Har ya riga ni shigowa na iske su suna tattauna game da maganar komawar Anty Alawiyya ɗakin ta, ina sako ƙafata Amma ta canza zancen izuwa wani daban.


Da dama da na koma sai sun gama sannan na shigo amma babu dama domin sun riga da sun ganni. Na tabbatar ganin nawan ne ya sanya ta sauya zancen domin har yanzu basu ɗauke ni ɗaya daga cikin ahalin su ba.


Na yi saurin yin ƙasa da ido ganin Al'amin zaune a cikin falon, na zauna ina yi musu sannu da hutawa suka amsa mini fuskar su babu yabo babu fallasa.


"Sai yanzu kika sama shigowa?".


Amma ta jefa mini tambayar kai tsaye, na rusunar da kaina"na yi wasu gyare-gyare ne shi ya riƙe har ban farga da lokaci ba saboda gajiya".


"Hala da kuka fita da motar a hanya kuka ajiye ta, kuka ƙarisa a ƙafa ko?". Anty Alawiyya ta gwatsalo mini zancen.
Na jijjiga kaina"a'a ba haka nak...".


Amma ta katse ni"yaya kuka baro mutanen gidan nakun?". Na ji daɗi a cikin raina domin ko ba komai yau ɗaya ta tambayi lafiyar wani nawa.


"Suna nan lafiya sun ce a gaishe ku". Ta jinjina kanta tana gyara kishingiɗewa da ta yi ta ce"in ce dai ba haka kuke je musu hannu rabbana ba?".


Wani irin na ji tambayar na yi zargin so take yi ta bugi cikina da kuma auna mizanin tunanina don haka na furta"mun je musu da daidai abunda ƙarfinsa ya kai".


Ta yi mini shuru tamkar ba ta ji abinda na furta ba. Sai can ta ce"madalla". Ina ɗago idona muka haɗa ido da Al'amin ya yi mini wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login