Showing 72001 words to 75000 words out of 80635 words

Chapter 25 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

sai dai ya gaza cewa uffan.


Ya fizgo hannunsa kamar zai tsinke shi daga gangar jikina ya fara ja na ina turjewa ina kuka ina faɗin"don Allah Anwar ka tsaya, ka yi haƙuri a gyara komai a nan".


Amma kamar ana ƙwalawa bebe ƙira ki waigowa bai yi ba balle ta saurare ni, muna fita muka sama adaidaita muka hau. Na fashe da wani irin matsanancin kuka har jikina rawa yake yi, bai ce da ni ki kanzil ba har adaidaitan ya tsaya a cikin layinmu. Ya zaro kuɗi daga aljihunsa ya miƙa masa sai da ya fita ya ce"fito".
Na ɗago idanuna da naji sun yi mini nauyi sosai zan yi magana ya ɗaga mini hannu, ya sanya hannunsa ɗaya ya jawo ni na fito.


Dai-dai lokacin da aka sallame sallan Asr a masallacin dake kusa da gidanmu mutane suka fara fitowa, ya cigaba da jan hannu da sauri sau dai abin da muke gudu muke ƙoƙarin kauce masa ne ya faru. Muna isowa ƙofar gidan muka yi kiciɓus daBaffa da Baba Alhaji su na dawowa.


*********************


Dai-dai nan Barrister Adam ya dakatar da ni ya juya yana kallon mai shari'ar da ya tallafi ƙuncinsa ya na kallona da hawaye su ka gama jiƙa mini fuska.
Cike da ƙwarin gwiwa ya maido da kallonsa gare ni ya nafaɗin"kin guji auren ɗan uwanki ki auri Abdul-hameed yayin da kika tarar da abin da ba ki yi zato ba a cikin gidansa. 'Yan uwanki sun ba ki shawarar kar ki juri irin abubuwan da mahaifiyarsa da 'yan uwansa suke yi miki ta hanyar nuna miki ki zama robar wando ta yanda za ki iya kama ƙudun kowa. Sai kika yi amfani da hakan kika kashe shi, ki ka mayar da mahaifiya da 'yan uwansa marayun dole domin shi ya maye musu madadin uba. Ki ka ɗauki wannan mataki wajen rama abin da suka yi miki haka ne?".


Tsabar cin ƙarfina da kukan ya yi na kasa cewa komai, ƙafafuna suka fara rawa ina jin kaina yana juyawa tamkar sitiyarin mota a hannun ɗan koyo.


*ƁOYAYYAR MANUFA*


©️ Maimuna Tijjani Iyam


_______________________________


Page 3️⃣8️⃣


Kotun ya kaure da hayaniya kamar cin kasuwa, kowa ya na tufa albarkacin bakinsa. Sai da mai shari'ar ya dakatar da surutun tare da ba wa Barinsa Adam damar ci gaba da tambayoyinsa.


"Zan so ki amsa min wannan tambayar. Me yasa kika yi amfani da son da marigayi ya ke yi miki ki ka cutar dashi?". Da hanzari Barrister Aliyu ya miƙe haɗe da faɗin"objective my Lord! Lauyan gwamnati ya na ƙoƙarin tsorita wacce ake tuhuma ta hanyar jefa mata tsauraran tambayoyin da zai iya kiɗimata ta furta abin da ba shi ke nan ba".


"Lauyan gwamnati ka kiyaye".


Ɗan ranƙwafar da kansa Barrister Adam ya yi alamar girmamawa sannan ya cigaba da faɗin"zan so Alawiyya ya ga marigayi ta bayyana a gaban kotu". Sai a lokacin na yi ƙarfin halin cira kaina na bi ta da kallo zuciyata ta na yi mini ƙuna da raɗaɗi na ba wasa ba. Ya tako ya isa gabanta ya na gyara zaman baƙar rigar dake jikinsa ya furta" me ki ka sa ni game da Aisha da marigayi, ina nufin ko akwai wani abun da ya haɗa su kafin faruwar lamarin?". Ta yi sama da kanta alamar ta na nazari kafin ta ce"tabbas akwai, domin a lokacin ana shirye-shiryen kai kuɗin aurensa".


"Wani irin shirye-shirye?".


"Zai ƙara aure to lokacin ana shirin kai kuɗi gidan su yarinyar da zai aura".


Ya jinjina kansa da alama ya gama samun abin da yake so jin daga gare ta, ya cigaba da maganan ba bana jiya jin abin da yake furtawa illa ganin bakinsa ya na motsawa da nake yi. Ya gabatar da godiya ya koma ya zauna.
Mai shari'ar ya yi jefawa Barrister Aliyu tambayar ko yana da tambayar da zai yi wa Anty Alawiyya.


Ya miƙe a nutse ya iso gabanta yana ƙare mata kallo"a labarin da yar aikin gidan marigayi da wanda matarsa da ake zargi da kashe shi ta gabatar a gaban kotu. Ya nuna cewar tabbas akwai ƙauna mai ƙarfi a tsakanin su, sannan akwai kulawa na musamman da suke gwadawa junansu. Me ya sanya Abdul-hameed bijirowa da zancen ƙarin aure?".


"Ai kyautatawa ba ta hana magidanci ƙarin aure, lokaci ne ya yi shi yasa zai ƙara". Ya yi wani murmushin gefen bakin kafin ya ce"kina da aure?".


"Ba ni dashi".


"Me ya fito dake daga gidan mijinki?".


"Fifita kishiyata ya yi sama da ni".


Ya zube idonsa akan ta"tunda ya bijiro da zancen ƙarin aure shin matarsa ta taɓa nuna rashin hankalinta game da hakan?".


"A'a".


Murmushi ya kuma yi tare da faɗin"lokacin da aka yi kisan ki na cikin gidan". Ta gyaɗa kanta da hakan ya ba shi damar ɗaurawa da"kun haɗu dashi ranar da lamarin ya faru?".


"E ya shigo gaishe da mahaifiyarmu, bayan ya koma sashinsa muka fara jiyo ihunsa".


"Da ku ka ji ihun me kuka yi?".


Ya gyara mayafinta da yake zamowa kafin ta amsa masa da"garzaya muka yi izuwa sashinsa muka tarar dashi a kwance jikin jini, ita kuma ta na gefe da wuƙar
da sallamarta ta koma mazauninta. Ya ɗaura da faɗin"ya mai girma mai shari'a ƙarin auren da marigayi ya bijiro dashi ba shi zai sanya Aisha hallaka shi, tunda kamar yanda yayarsa ta batyana a gaban kotu cewar ba ta taɓa nuna tashin hankalinta game da auren ba. Ba zan gaji da faɗin cewar haƙiƙa akwai wata ƁOYAYYAR MANUFA a cikin wannan kisan ba".


Wasu ƙananun magana suka fara tashi tsakanin yan zaman sauraron shari'ar da suka yi ka kotun. Ina hangen su Hamma Ahmad ji nake yi kamar na ruga a guje na isa gare su na tuntsire da kuka ko zan ji sausaucin zogin dake sukar ƙahon zuciyata.


"Kotu ta ɗaga wannan ƙara zuwa ranar goma sha bakwai ga watan Mayun shekarar dubu biyu da ashirin da huɗu. A sannan duk ɓangarori biyun su taho da gamshashshiyar hujjar da za ta gamsar da kotu, har izuwa lokacin da za a dawo za a cigaba da tsare Aisha a gidan ajiye ɗaurarru, ba tare da beli ba".


Ya na ƙare zancen ya buga ƙaramar dake bisa teburinsa ya miƙe ya fice ta wata ƙofa. Sai da ya fita sannan ragowar jama'a suka fara ficewa. Aka mayar mini da ankwan da aka cire mini da za a shigo da ni cikin kotun.


Aka fito da ni jama'a suka fara kawo mini hari na duka da jifa jami'an 'yan sandan su na kare ni. Kamar sassaƙeƙƙen gunki haka na kafu a wajen tamkar an dasa ni idanuna ƙar akan dukkanin yayuna mazan da kuma Ummata da take yarce hawayen da suka yi mata lijif a fuska.


Na sauƙe wani gigitacciyar ajiyar zuciyar da ta tafiyar da kukan zucin da nake yi. Ban yi aune ba na ji wata jami'a mace ta fizgo ni da ƙarfin rabbussamawati na kaucewa jifan da wasu fusatattun matasa suka ke yi mini da manyan duwatsu. Cikin kumfar baki su ke faɗin"sai mu kashe ta tunda an ƙi barin doka ya hau kanta, tun zaman farko ya makata an yanke mata hukunci kisa ta hanya mafi muni da tozarci. Amma an bar ta har yanzu ta na cigaba da shaƙar iskar numfashi sai bayan wani lokaci a fito a cewa jama'a ta na matsalar ƙwaƙwalwa an sake ta".


Su na zancen su na ƙoƙarin ƙara kusanta da tare da kawo mini duka ta ko ina. Hamma Ahmad da Umma suka ratso su na kare ni, Hamma Abubakar ya na tsaye ya kasa komai illa hawayen da yake sake. A farin sanin da na yi masa mutum ne mai dauriya da juriya komai girman abu ya na iya danne shi a cikin ransa. Ba ƙaramin abu bane yake sanya hawayen idanunsa tsiyaya, sai gashi yau a dalilina ya na zubar da ƙwalla cikin ƙonar zuci.


Duka da goran da wa ni ya kawo mini Umma ta yi saurin tarewa, ya sauƙar a goshinta take jini ya ce sallama alaikum. Jami'an su ka ƙara ƙaimi wajen ba ni kariya sai dai lamarin ya ci tura sai da suka tarwatsa tarin jama'ar ta hanyar jefa borkonon tsohuwa sannan aka sama sararin jefa ni a cikin mota. Aka fige ta da karfin gaske muka bar cikin harabar kotun.


Sai da aka mayar da ni cikin ɗakin da aka ɗauko ni na sama ƙarfin sakin kukan da yake nuƙurƙusan rai da ruhina. Na rasa abin da zan yi na ji daɗi a halin da nake ciki, babu abin da nake yi wa kaina sai fatan mutuwa. Idanuna sai hasko mini yanda jini yake zuba daga goshin Ummata a lokacin da aka jefa ni cikin motar. Tabbas ɗan kuka shi ke jawa uwarsa jifa.




Da saurin Hamma Ahmad ya riƙe Umma saboda ƙoƙarin zubewan da take yi tana tangal-tangal. Borkonon tsohuwar da aka jefa a wajen ya tarwatsa dandazon jama'ar kowa ya fara yin ta kansa.


Da ƙyar suka fito da ita daga cikin harabar kotun suka tsaya neman adaidaita. Ba su samu ba ga zubar da jinin da take yi har yanzu, faka motarsa Barrister Aliyu ya yi a dai-dai gabansu tare da zuge gilashin motar.


"Ku shigo mu je asibiti". Ya furta yana kallon gefen da Umma take. Shigar da ita suka yi kai tsaye suka wuce asibiti mafi kusa, sai da aka yi mata ɗinkin a wajen tare da wasu allurai sannan ta sama bacci.


Hamma Abubakar ya sauƙe numfashi ya na kallon Barrister Aliyu da tunda ya kawo su bai tafiya ya ce "Barrister anya Shari'ar nan akwai alamun za mu yi nasara kuwa? Wallahi duk na sare".


"Ai ka san ita Shari'a saɓanin hankali ne. Kamar mai cike ne babu wanda ya san abin da ke cikinta sai wanda yake da ikon akan komai da kowa. Amma na yi muku alƙawarin matuƙar Aisha ta na gaskiya sai iya inda ƙarfina ya ƙare akan wannan case ɗin, ku kwantar da hankalinku sannan ku cigaba da yi mata addu'a".


Duk shuru suka yi kamar ruwa ya cinye su sai Barrister Aliyu ne ya cigaba da kwantar musu da hankali. Bai tafi ba sai da Umma ta tashi ya sauƙe su a gida, Baffa ya na zaune a cikin ɗakin zaure kasancewar tun bayan faruwar lamarin fita ko nan da can ya gagare shi, ya na sauraron rediyon da ya kunna sai dai daga kallo ɗaya za ka fahimci cewar hankalinsa a nan yake ba.


Sannu su Hamma suka yi masa amma ko waigowa bai yi ba balle amsawa musu. Da ido Hamma ya yi wa Anwar da Hamma Adnan alama akan su shiga gida tare da Umma. Shi da Hamma Ahmad su ka zauna nan wajen Baffa za su yi magana.


Da hanzari Adda Azima da Adda Abida suka miƙe ganin yanda suka shigo. Suka nufo su cikin tashin hankali kasancewar duk Baffa ya hana su zuwa gabaɗayansu.


"Tun ɗazu muke zaune muna jiran dawowarku, hankalinmu gabaɗaya ya tashi ganin abin da ya faru a kotu da muka gani a waya".


"Shigar da Umma ciki ta kwanta, ina Dadar?".


"Yanzu ta fita zuwa gida, don tun bayan tafiyanku jama'a suka cika ƙofar gidan nan su na hayaniya".


Adda Abida ta furta ta na kama hannun Umma ta shigar da ita ɗaki ta kwanta. Ta fito ta iske Hamma Adnan da Anwar zaune.


"Wallahi tsabar tashin hankalin da na shiga na ma kasa cigaba da ganin Shari'ar da ke haskawa. Zuciyata ta karaya sosai ganin yanda lauyan gwamnati yake ragargaza duk hujjojin da aka bayar domin kare ta".


Zantukan Adda Azima suke da tsantsar damuwa da ya sanya Anwar miƙewa tsam ya tashi ya bar wajen yana riƙe kansa duk suka bi shi da kallo. Don baya Umma da ta kasance mahaifiya a gare ni babu wanda ya kai shi shiga tashin hankali da damuwar abin da ya afku.


Sun daɗe su na tattauna har Dada ta shigo ta shiga ta duba jikin Umma da take kwance lilif.
Sannu ta yi mata cike da kulawa kana ta furta"shi yasa tun farko na ba ki haƙuri akan ki ƙara yin haƙuri tunda Baffansu ya ce kar ki je ki yi haƙuri kawai. Ki cigaba da yi mata addu'a".


Ba ta ce da ita komai ba illa jinjina kanta da ta yi cikin ƙarfin hali"wallahi ba zan iya ba ne, babu ta yanda za a yi zuciyata ta sama nutsuwa ina zaune a nan alhalin ita kuma ta na can".


"Ina tunanin abin da zai je ya dawo ne shi yasa tun farko na hane ki". Ta na rufe bakinta muryar Baffa ta na sauƙa a ƙofofin kunnuwansu yana ƙwaal ƙiran Umma.


Dada ta riƙo ta su ka fito su Hamma da su Adda Azima da Abids duk su na zaune a wajen.
Sai da ya ajiye butar da ya iddar da alwalan sallan magrib da ita sannan ya ce"ya jikin nakin?".


"Da sauƙi". Ta furta cikin ƙarfin halin nuna cewar babu komai. A yarfe ruwan dake bisa goshinsa kana ya furta"zan faɗa a gaban kowa don su zama shaida. Na sanar dake cewar duk ranar da ki ka sanya ƙafa ki ka fita daga cikin gidan nan da sunan zuwa wajen Aishatu to a bakin aurenki. Sai gashi kin aikata hakan don haka zama ya ƙare tsakaninmu, na sauwaƙe miki sai dai ki yi zaman 'ya'yank......".


Da wani irin azama Hamma Abubakar ya yunƙuro Baffa ya ɗaga masa hannu"na riga na furta". Ya na ƙare faɗin hakan ya juya zai fice Anwar da yake zaune a ƙofar ɗaki ya jawo jikinsa
Ya zo ya riƙe ƙafarsa ya na faɗin"don girman Allah Baffa kar ka yi mana haka. Umma ta kasance mai biyayya a gare ka akan komai kuma a ko yaushe a wannan karon zaɓin da ka bata ya yi tsauri da yawa ne da har ta kasa jure shi".


Adda Azima da Abida suka fashe da kuka mai ƙarfi. Umma ta ƙara tako uku ta iso gabansa, numfashinta ya na fizgo da ƙarfi ta ce"tunda lokacin da na yanke hukuncin halaltar zaman kotun da za ayi. Na sa a raina cewar na gama zama da kai, ban taɓa tunanin hakan daga gare ka ban taɓa tunanin za ka aikata hakan ga 'yar da ta fito daga tsatsonka ba".


"Don Allah ku yi haƙuri".


Zancen Dada ke nan da ya sanya Umma cigaba da faɗin"ki bar ni ki bar ni yau na sanar dashi abin da ke ƙunshe cikin raina. Wallahi ba zan iya cigaba da zama dashi ba, ko Aishatu ta kuɓuta ko akasin hakan".


Tana gama faɗin haka ta juya za ta koma ɗaki ta yanke jiki ta faɗi jirif. A ruɗe duk suka rufo a kanta su na faman ƙwala ƙiran sunanta amma shuru babu wata gaɓar dake motsawa a jikinta babu alamar numfashi a tare da ita.


*ƁOYAYYAR MANUFA*


©️ Maimuna Tijjani Iyam


__________________________________


Page 3️⃣9️⃣


Da ƙyar su Adda Azima suka ɗaga ta saboda sakewan da jikinta ya yi, suka mayar da ita kan tabarman da suke zaune. Dada ta ce Hamma Adnan ya deɓo ruwa ya kawo mata a cikin ƙwarya ta shafa mata a fuskarta sai da ta shafa masa sau biyu kafin ta ja dogon numfashi mai ƙarfin gaske da ya ba wa ƙwallar da suka ciko mata idaniya damar kwaranya a bisa kuncinta.


Sannu duk suka hau jeranta mata wani na bin wani. Kafin Hamma Abubakar ya ce"Azima ku fito da ita mu tafi asibiti".


"Ba sai mun je ko ina ba, ku haɗa min kayana kawai ƙauye zan je".


"Don girman Allah Umma ki yi haƙuri. Ki zauna har a sasanta komai, idan kin je ƙauyen wajen waye za ki je a ina za ki zauna? Babu wasu ba dangin kusa da suka rage a cikin ƙauyen, kuma idan kin je ki ce dasu me ye".


Furucin Hamma Ahmad ke nan cike da damuwa. Dada ta amshe zancen da faɗin"gaskiya kam babu inda za ki je, ko da aure ko babu ai yanzu an ruga da an zama ɗaya. Ki yi zamanki a cikin gidan nan domin babu inda za ki je da ya fi nan".


"Ɗaga ni na tashi Abida". Umma ta furta tana cije leɓanta alamar ta na cikin ciwon matuƙa. A hankali ta soma faɗin"don Allah Umma ki yi haƙuri in kika bar gidan nan ina za ki je? Na tabbatar ko akwai to hankalinki ba zai taɓa kwanciya ba matuƙar ki ka yi nisa da nan, ki bari Baba ya dawo a sasanta komai".


"Dukkanku babu wanda bai mallaki hankalin kansa ba a cikinku. Don haka duk inda naje ba ni da fargaba akan ku mussamman idan na tuna cewar ko da ni ko babu ni ba za ku yi kukan rashina ba domin ga Dadarku nan".


Duk shuru suka yi saboda kashe musu jiki da zancen na Umma ya yi. Anwar dai ya gaza cewa komai har yanzu ya na durƙushe inda Baffa ya zame ƙafarsa daga riƙon da ya yi masa ya fice, ya kasa motsawa wani irin zafi ƙirjinsa yake yi masa da ya wuce kima.


Hasbunallahu wa ni'imal wakil kawai yake ta maimaitawa cikin ransa. Ko a cikin mafarki babu wanda ya taɓa kawo irin wannan ranar za ta zo cikin rayuwarsu, ranar da Baffa zai furta wannan furcin ga Umma da ta kasance mai matuƙar biyayya a gare shi. Ahalin da suke rayuwa cikin tsantsar farin ciki, walwala, son juna da kuma nunawa juna kulawa yau su ne ƙaddarar ƁOYAYYAR MANUFA ta share duk waɗannan ababen.


Babu irin magiya, roƙo, ban baki, lallashi gami da lallamin da ba su yi wa Umma ba amma fir ta nuna ba za ta iya cigaba da zama a cikin gidan ba. Da ƙyar ta yarda za ta koma gidan Hamma Abubakar da zama domin a son ranta ƙauyen dai ta so komawa ko jiran dawowar Baba Alhajin da Hamma Adnan yake ta ƙiran wayansa ba ta shiga ba su yi suka tafi tare da Adda Azima da Anwar.


Figigi na zabura tamkar wacce aka tsigarawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login