Showing 69001 words to 72000 words out of 80635 words
Chapter 24 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt
Ina dasa aya nan na fice daga ɗakin, na koma ɗakinsa na jingina jikin ƙofar ina sakin wani kuka marar sauti kafin na isa ga wajen ajiye kayansa ba fito masa komai na ajiye masa na fito, muka yi kiciɓus dashi na matsa da hanzari ina ba shi hanya ya wuce.
Na ƙudurce a raina cewar ba zan yi faɗa dashi ko na yi fito na fito dashi ba. Amma dole na nusar dashi kuskuren da ya tafka, ba zaɓa ladabtar dashi ta hanyar janye jikina daga gare shi. Kafin ya fito na haɗa masa ruwan shayi da soyayyan ƙwai na ajiye masa a falon. Dai-dai zan shige ɗakin na ji muryarsa kamar daga sama.
"Don Allah tsaya ki saurare ni".
Na juyo fuskana a haɗe"na tsaya don girman wanda ka ambata". Ya tako ya iso har gabana ya na zura dukkan hannayensa a aljihun jamfar dake jikinsa.
"Ki yi haƙur....".
Na ɗaga masa hannu"ya wuce, ga karin kumallonka ka ci kafin ya huce Allah ya tsare a dawo lafiya". Na ƙare zancen ina ƙoƙarin shigewa ɗaki ya riƙo ni na fizge. Lokacin sallama da shigowar Amira muka ji yo shi a tare, na yi wuf na shige ɗakina na bar shi tsaye a wajen.
Sai da na ji ƙarar fitar motarsa sannan ba fito na iske Amira tana gyara falon, ta gaishe ni na amsa mata ina ƙoƙarin sake fuskana da babu annuri. Har ta gama ta yi mopping wajen ban ce da ita komai ba, ta zo ta durƙusa a gabana.
"Anty lafiya kuwa?".
"Lafiya kawai yau na tashi ba na jin daɗi ne".
"Allah ya sauwaƙe". Na ɗaga mata kaina, ranar wuni na yi ban leƙa ko ƙofar sashina ba ko zuwa gaisar da Amma ban yi ba duk da zuciyata ta ba ƙoƙarin nusar da ni rashin dacewar hakan, amma na yau dai na danne. Ban fita sai da nayi sallan Asr na shiga sashin tare da Amira.
Ta na kishingiɗe a wajen zamanta na kullum kullum. Na rusuna na gaishe ta, ba ta amsa mini ba sai ma tambayar da ta jefo mini.
"Me ya faru tsakanin ki da mijinki".
"Babu abin ya ya faru a iya sa ni na, amma wani abun kika gani ko ya faɗa miki?". Babu shiri ta yi mini wani kallo da alama ba ta yi zaton samun irin wannan amsar daga gare ni ba.
"Na daɗe ban gan shi cikin irin yanayin da ya zo min a safiyar yau ba. Tabbas na san akwai wani abun da ya faru da ya jefa shi cikin wannan yanayin". Sai da ta ƙara kaurara amon muryarta ta ɗaura da"kar ki yi amfani da son da Abdul-hameed ya ke yi miki ki cutar dashi, Allah ya rufa miki asiri da samun miji irin sa don haka kar ki yi wasa da damarki".
Zancenta su da daki ƙwaƙwalwata tare da munana zuciyata. Na gyara zamana"tabbas da ni dashi duk mun yi sa'ar samun juna". Ina ankare da kallon da ta yi mini ta gefen idonta ba tare da ta ce da ni komai ba.
Haka nan kawai na tsinci kaina da faɗin"ina Anty Alawiyya fa da su Ansar?".
Kamar ba za ta amsa ba sai can kuma ta ce"su na ciki". Na miƙe ta yi saurin faɗin"ina za ki je?".
"Zan je mu gaisa ne, don wataƙila sai gobe na kuma shigowa".
"Kar ki damu in ta fito zan sanar da ita zuwanki". Na maida dubana ga Amira ina bada umarnin tashi mu ta fi.
A falo muka zauna Amira ta yi ƙasa da kanta tana cewar"Anty tun da na shigo yau na iske kuna ja-in-ja da yallaɓai da kuma yanayin da ki ke ciki, na ji gaɓadaya jikina ya yi sanyi. Gashi har lokacin tafiyata ya gabato ba ki dawo kamar da ba, don Allah in wani abun na yi miki ina mai neman afuwarki".
Da ƙarfi na furzar da iska daga bakina ina zamewa na jingina bayana jikin kujerar da nake zaune"babu abinda kika yi mini Amira. Kamar yanda na gaya miki kawai yau na tashi ba na jin daɗi ne".
"Shikenan Anty daman ina so na yi miki wata tambaya, amma ina tsoro ki ce na zaƙe da yawa ko saka kaina cikin abin da bai shafe ni ba". Na gyara zamana da kyau ina sauraron ta"tun ranar da na fara zuwa gidan nan aiki kafin na shigo wajenki, mai gadi ya kan ce da ni Hajiya tana nema na idan na ce tambayoyi take yi mini akan yanda kuke zaune da Yallaɓai".
"Ba komai Amira kar wannan ya dame ki, babu abin da zai dawwama komai zai wuce wataran ai sai labari. Shi yasa nake kawar da kai akan abubuwa da dama".
Cike da gamsuwa ta amsa mini da"haka ne kam, Innata ta ce na gaida ki sosai". Na ƙirƙiri murmushin dole na yaɓawa fuskata yayin da nake amsawa.
Ko da ta tafi ta barni na kasa taɓuka komai a wajen na zauna ina tunanin wanda zan ƙira na sanarwa damuwata. Tabbas duk wanda ya fito daga tsantson fulani a san shi da matuƙa kunya musamman akan lamarin da ya shafi aure wannan dalilin shi ya hana ni sanar da Umma abin da yake faru tuntunin. Hamma Ahmad na ƙira na irge masa komai tabbas shi ma ya shiga ruɗu sosai, haƙuri ya yi ta ba ni shawarwarin cewar na dage da kai kukana ga Allah.
*ƁOYAYYAR MANUFA*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
______________________________
Page 3️⃣7️⃣
Sai na jera kwanaki bakwai cur bana shiga shirginsa, duk wani abun da na san zai buƙata tun kafin ya nema nake tanada masa shi. Girki kuwa ina kammalawa zan ajiye masa na shige ɗaki ba zan fito ba sai na ji ƙarar ficewar motarsa daga cikin gidan, ko kuma shigowar Amira.
Fitowata daga wanka ke nan bayan na gama girka masa karin kumallo na dawo ɗaki, na yi saurin isa ga wayata da take faman ruri na yi turus ganin baƙuwar lamba ce, sai da ya kusa katsewa ba kara tare da maƙalawa a kunnena.
"Ki zo sashina ina son ganin ki yanzu". Na ji muryar Amma sun sauƙa a ƙofofin kunnuna, ta na dire faɗin zancen git ta kashe wayar. Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya gabana yana tsananta bugu da tarradin abin da zan tarar.
Sai da na gama shiryawa tsaf na ɗauki wayata na fito, duk su na zaune a falon sallamar da na yi ya sanya su zubo mini idanu har na yi wa kaina mazauni tare da gaishe da Amma. Ba ta amsa mini illa fara faɗin da ta yi"har nan na ƙirawo ki na tambaye ki me ke faruwa tsakaninki da mijinki amma ki ka nuna min cewar ba komai. Sai gashi yanzu da kan sa ya kawo min kukansa cewar ba kya kula shi".
Na gyara zamana sosai "Amma kamar yanda na sanar dake ne babu wani abu a tsakanin mu. Ko yanzu ma mun rabu dashi cikin farin ciki da kewar juna". Na ƙare zancen ina satan kallon Abdul-hameed ta gefen ido da mamakin zancen nawan ya bayyana ɓaro-ɓaro a bisa fuskarsa.
Ta yi masa wani kallo da ya fi kama da na tuhuma kafin ta furta"kai me kazo ka faɗa min?". Ya sunkuyar da kansa ya na sosa ƙeya"kamar yanda ba faɗa miki ne kwana biyun nan ba ta shiga harkata, komai nake da buƙata ajiye min shi take yi ta koma ciki. Shiyasa na kawo kukana gare ki ki taya ni ba ta haƙuri idan wani laifin na aikata a gare ta".
"To kin ji abin da ya ce"
"Na ji dukkan abin da ya ce, manufata na ba shi lokaci na lura kamar kwana biyun nan yana kwaso gajiya daga wajen aiki ne gashi ba ya dawowa da wuri shiyasa na ke basa lokaci ya huta".
Sai da ta ja dogon lokacin kafin a ƙasaitance ta furta"wannan ba huruminki ba ne, ya tabbatar a kanki dole ki samarwa mijinki nutsuwa. Idan kuma kin fara gajiya dashi ne za ki iya fitowa ki faɗa, domin Abdul bai rasa gata ba bai kuma cancanci wulaƙanci ko wata iriyar mace ba balle Aisha".
"Gaya mata dai, ban da so ma da kwashe-kwashe me ye haɗin kifi da kaska?". Furucin da Al'amin ya yi ke nan ya na yatsina fuska duk da na ji zafin zancen amma ban ce komai ba, na sunkuyar da kaina ƙasa ina godewa Ubangijin da ya tsaro mini yin rayuwa a cikin waɗannan mutanen.
Sai da ta ƙare zancenta da suka yi kama da kashedi kafin ta sallame mu, tare muka fito ki kallonsa ban yi ba na ɗauki hanyar komawa sashina ya yi saurin shan gabana.
"Wai don Allah menene? Yaya ki ke na yi da raina ne?. Yanzu fa a gaban Amma kika nuna ba komai yanzu kuma mun fito za ki canja min". Yanda ya ƙare zancen cikin maraice tamkar mai shirin fashewa da kuka ya yi matuƙar taɓa mini zuciya ainun.
Tabbas na shaida irin son da Abdul-hameed yake gwada mini, ba zan iya yin dogon fushi da shi ba na tabbatar ko share shi da na yi na tsawon waɗannan kwanakin ya gano kuskurensa.
"Ai kamar yanda na faɗa a gaban natan ne komai ya wuce". Ya matso gab da ni tare da ranƙwafo da kansa"hukuncin da ki ka yi min ya yi tsauri da yawa, don Allah ki dunga sausauta min. Na gane kuskurena kuma in sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba". Kaina kawai na gyaɗa masa saboda yanda ya matso ni na kasa cewa komai illa ƙamshin turarensa da nake shaƙa.
Ganin alamar yana ƙoƙarin zarcewa ya sa ni saurin zillewa ina ɗaga masa hannu alamar sai ya dawo, ina juyowa na hango Al'amin ya na fitowa sai da muka haɗa ido na juya da saurina na isa ga Abdul-hameed da yake ƙoƙarin shiga mota.
Duk da ya zarce ni sosai a tsayi na yi ɗage na manna masa kyakkyawan sumbata a ƙuncinsa ina kashe masa ido ɗaya, zai kamo ni na kauce da hanzari muna sakarwa juna murmushi. Sai da ya ja motarsa ta jfice daga cikin gidan, na juyo ina watsawa Al'amin da ya yi mutuwar tsaye ya kasa gaba balle baya wani kallo. Na wuce ta gefensa ina baza takuna raina ƙyal kamar farar azurfa, ko banza na bashi amsar zancen da ya yaɓa mini a ciki.
Babu jimawa Amira ta zo tare muka yi karin kumallo da ita sannan ta gyare sashin tsaf, muka zauna mu na hira ina nuna mata hotunan bikinmu. Sai yabawa take da faɗin Masha Allah.
"Anty duk sun fi ki haske amma kin fi su kyau".
Na bushe da dariya mai ƙarfi sai da na tsagaita na ce"kallon tsoro kika yi musu har kyawun ma sun ɗara ni, ba ki ga duk su na kama ba ni ce dai kamar rabe a tsakanin su". Ita ma dariyar ta yi ta ce"kallon ƙurilla fa na yi musu".
Haka muka sha hirar mu sosai kafin muka ɗaura girkin rana. Ina jin daɗin daɗin zama da Amira sosai wani lokacin ganin ta nake yi kamar Abasiyya.
Cikin kwanakin nan mun dawo kamar yanda muke da mijina babu abinda muke yi sai kulawa da tattalin juna. Izuwa kam kan mage ya waye domin ba na ƙwauron baki wajen mayar da martani da ba da amsa dai-dai da tambayar da aka yi mini, sai dai duk furucin da zan yi bana taɓa jefa kalmar rashin girmamawa ko cin fuska ga Amma, domin ko ba komai ita uwa ce kuma in zan yiwa Abdul-hameed adalci dole na ɗauki uwarsa tamkar tawa kamar yanda shi ma yake mutunta tawa kamar ita ta yu naƙudarsa.
Duk safiya bayan fitarsa da zazzaɓi nake wuni ga kasala da kuma rashin ɗanɗanon da bani dashi. Ina kwance a falo na ji sallamar Amira na amsa tare da bata iznin shigowa.
Tana daga bakin ƙofar ta ce"Anty ki na da baƙo a waje". Na ɗago kaina da ƙyar"waye ne? Kuma ni yake nema?".
"Ya ce dai ki leƙo ki ganewa idanunki".
Tsiririin tsakin na saka don Allah ma ya sa ni bana ƙaunar motsa jikina ko kaɗan sai ya zama dole, ina leƙowa idanuna suka yi mini tozali da abun da ya tilasta mini jin wani karsashi a cikin jikina.
"Anwar".
Fuskarsa tamkar gonar auduga ya ce"Boɗɗiam". Hawayen farin ciki suka ciko mini idona na maida duba ga Amira"yaya ne wanda kika hotunan mu rannan". Ta ɗaga mini kanta alamar ta gane, ya shigo ya zauna na dunga jere masa lemuka a gabansa tare da umartar Amira ta ɗaura girki yanzu.
Cike da zumuɗi na ɗaga wayata ya katse ni da faɗin"wa za ƙira kuma?".
"Zan ƙira shi ne na sanar dashi yau muna da babban baƙo". Dariya kawai ya yi ni kuwa na cigaba da dannawa layin Abdul-hameed ƙira sai da na ƙira sau biyu bai ɗauka ba na ajiyewa wayar.
"Na ƙira ma bai ɗauka ba ina ba ya kusa. Yaushe ka zo? Kai kuma tafiya kamar ana koranka babu sanarwa balle a yi sallama".
Murmushin ya ƙara saka haɗe da faɗin"jiya da yamma na zo, wallahi tafiyar ce ta zo min a matsayin zaɓi na ƙarshe babu yanda na iya shiyasa". Na jim ina sunkuyar da kaina ƙasa, lura da canzawar yanayina ya sanya shi ɗaurawa da"wani kyakkyawan albishir na zo miki dashi, wanda idan kika ji shi sai kin yi min kyauta".
"To wani irin albishir ne wannan?".
"Ki canka" Na ɗaga kaina sama ina nazari da ƙarfina na ce"ko dai Hamma Ahmad ne zai yi aure?".
"Hamma Ahmad kam ai sai dai mu taya shi da addu'a, domin ko batun aure ma shi ba ya yi. Ki dai ƙara nazari ko za ki canka dai-dai".
"Ba wani cankan da zan iya kawai ka faɗa mini".
"Adda Abida ta sauƙa lafiya, ta haiho ɗiyarta ta mace". Ban san sanda na zame daga kan kujerar da nake ba ina faɗin"da gaske?". Ya ɗaga mini kansa alamar tabbatar mini da zancensa.
"Shi ne komai babu wanda ya ƙira ni ya gaya mini?".
"Tun jiyan aka so ƙiranki a gaya miki na ce a bari zan zo da kaina na sanar dake". Wani sanyin daɗin ta rufe ni na rasa inda zan tsoma kaina tsabar murna, ji nake yi kamar na yi tsuntsuwa nake na ga Adda Abida da abin da ta haifa, na san Hamma Adnan bakinsa har ƙeya don farin ciki.
Ina ta zuba masa surutu har Amira ta gama girkin ta kawo, na yi na yi dashi amma ya nuna mini ba zai ci komai. Babu yanda ban yi dashi ba amma ya ƙi ruwa da lemon kawai ya sha. Na ɗauki plate na fara zuba mishi abincin na cika taf na miƙa masa.
"A ƙoshe nake Aishatu alhamdulillah". Na harare sa"har kazo gidan da bake ka tafi baka ci komai ba". Ina rufe bakina idanuna suka sauƙa akan Amma da Al'amin da suke tsaye a ƙofar falon ta ciki sun zubo mini idanuna da dukkan alamo sun daɗe tsaye a wajen ba tare da na farga ba.
Bai karɓa ba na ajiye plate ɗin a bisa teburin dake kusa da kujerar, su ka ƙariso tsakiyar falon. Ba zan iya tuna ranar da Amma ta shigo sashin ba tun wayewar ranar da aka rako ni gidan a matsayin amaryan Abdul-hameed da suka zo da ƙawayenta ganin kayan ɗaki.
"Aisha".
"Na'am sannu da shigowa".
Anwar ya zame daga kan kujerar da yake ya ɗan rusuna yana gaishe ta cike da bata cikakken girmanta. Ba ta amsa ba ta soma faɗin"wanene wannan kika shigo dashi har cikin falon mijinki?".
Ƙirjina ya harba da ƙarfin gaske"Amma ɗan uwana ne ya zo sanar da ni Adda Abida ta sauƙa lafiya".
"Duk cikin danginku a rasa mace ƙwara ɗaya jal da za a wakilta ta zo ta sanar dake haihuwar sai wannan jibgegen ƙaton za a turo?. To me ye amfanin wayarki da ba za a ƙira ƙi ba?. Da ya sanar dake shine aka ce ya nema waje ya zauna har kuna ja-in-ja dashi akan ya ci abinci".
Cikin taushin murya Anwar ya ce"Allah ya huci zuciyarki Hajiya, na ga kamar ba ki fahimta ba ne ɗan uwanta ne ni".
"Wani irin ɗan uwa ke nan yi min bayani". Ya ƙara tausasa amon muryarsa"iyayenmu maza wa da ƙani suke".
"Amma ka san cewar akwai aure a tsakanin ku da ita ko? Domin kai ba muharraminta bane. Kun aurar da yarinya amma kin hana ta samun kwanciyar hankali a gidan mijinta sai bibiyar rayuwar gidan aurenta kuke yi. Zuwa ka yi ka hure mata kunne ta cigaba da wulaƙanta mijinta don ɗan uwanka ya rasa ta watau kowa ma ya rasa ko?".
Zan yi magana Al'amin ya daka mini wata gigitacciyar tsawar da ta tilasta mini haɗiye zancen da nake yunƙurin furzowa.
"Dalla ki rufewa mutane baki munafukar banzan munafukar wofi, me ye kuma za ki ce mana bayan abin da idanunmu suka gane mana?".
Da wani irin ƙarfi Anwar ya miƙe daga rusunawar da ya yi yana ƙarewa mini kallo"daman irin wannan zaman ki ke yi Aishatu?". Ban amsa masa ya ɗan matso kusa da Al'amin na riƙo bayan rigarsa ina jijjiga masa kaina alamar kar ya yi amma bai saurare ni ba.
"Waye kai da kake siffanta ta da waɗannan munanan kalmomin?". A gadarance ya ce"ƙanin mai gidan ne ni, ka ga kuwa na fika iko a cikin gidan".
Ya cije gefen bakinsa kafin ya cigaba da faɗin"da kun san irin sadaukarwa da tarin ƙalubalen da Aishatu ta fuskanta akan auren yayan nakan don tabbatar da ɗaurewa farin cikin da kwanciyar hankali a rayuwarsa. Da ta zama abin girmamawa, mutuntawa da karramawa a gare ku. Ni na kawo kaina cikin gidanku don haka dole na jure komai daga gare ku".
Ya juyo gare ni muryarsa har wani ja yake yi tsabar ƙololuwar ɓacin ran da ya kai ya ce"zan tafi". Yana gama faɗin haka wuf ya juya ya fara tafiya.
"Da ka tsaya ai, in ban da ƙaddara me ye yaya Abdul zai yi da wannan. Ya haɗa mu da dangin jaraba dangin da ko riƙon aure ba su iya ba".
Furucin Al'amin ke nan da ya sanya Anwar dawowa da wani irin sauri kamar iska ne ke jan sa, ya shiga nuna shi da 'yar manuniyar yatsarsa yana cije bakinsa