Showing 63001 words to 66000 words out of 80635 words
Chapter 22 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt
ya turo mini ta cikin waya, na ƙira layinsa ya fi a irga baya tafiya. Na sanar da mahaifiyarsa ta ce babu abinda da za iya yi akai kawai na tafi ɗin".
Duk suka yi shuru na tsawon wasu daƙiƙu kafin Hamma Adnan ya furta" da ta ce ki taho kuma da yake ke shashasha ce sai kika ɗauko ƙafa kika kwaso kaya kika taho ko?. Ai tsayawa za ki yi ki jira shi ya dawo cikin gidan ki ji daga bakinsa". Ya ƙarƙare yana fiddo wayarsa daga aljihunsa ya shiga dannawa layin Abdul-hameed ƙira, ya ƙira ya fi sau goma layin ba ta tafiya ya ajiye wayar tare da cewa"na ƙira ba ta tafiya amma zan ƙara gwadawa zuwa anjima. Ahmad yanzu me ye abin yi ka yi shuru baka ce komai ba".
Ina iya jiyo sautin da ajiyar zuciyar da ya sauƙe ya bada kafin ya furta"ai na rasa abinda zan ce ne, amma tabbas kin yi wauta da kika taho ba tare da kin ji ta bakinsa ba. Dole yanzu za ki koma mu zauna dashi sai mu tattaunawa".
Wasu hawayen masu ɗumi suka gangaro daga idona"baya dawowa Sai bayan sallan magrib ko mun je yanzu ba lalle bane mu same shi".
"Shikenan yanzu ki tashi ki je gida wajen Abida inda mun tashi daga kasuwa zamu biyo ta can". Hamma Adnan ya furta cike da taushi cikin kalamansa. Kaina kawai na ɗaga masa ya zaro Naira ɗari biyar ya ajiye mini akan cinyata, a sanyaye na ce"akwai kuɗi a wajena". Bai ce da ni uffan ba amma kallon da ya yi mini kaɗai ya isa na fahimta nufinsa.
Har cikin kasuwar Hamma Ahmad ya sanya yaron shagon ya taro mini adaidaita na hau ya kai ni gidan Adda Abida. Tana wanke shinkafar tuwo na iske ta, fara'ar dake bisa fuskarta da ta juyo dashi ya rikiɗe izuwa mamaki ganina da ta yi da akwatin kaya a hannu.
"Lafiya na gan ki da wannan kayan?".
Ban ce da ita komai ba sai da na nema waje na zauna na ce"zan yi miki bayani amma yanzu bari na fara yin salla". Na tashi na ɗauki bota na yi alwala na shiga ɗakinta na gabatar da sallan Asr na daɗe ina addu'ar samun mafita da makarin warware wannan ƙullin da ya cakuɗe mini kafin na shafa addu'ar, dai dai lokacin da sallamar Adda Abida ya ratso kunnuwana.
Ta zauna tare da kafe ni da ido"me yake faruwa ne? Ina shi Abdul-hameed ɗin?". Na cije leɓena na sanar da ita komai, ta riƙe baki cike da takaici ta soma cewa"lalle wannan lamarin akwai ɗaure kai matuƙa, amma kuwa ita ma uwar tashin ba ta san dattaku ba. Yanzu idan 'yarta ce zata so haka ya kasancewa da ita ne da har za ta ce babu abinda za ta iya yi a kai, yanzu ki zauna ki jira dawowar nasun sai mu ga abinda halin zai yi".
Kaina kawai na gyaɗa mata. Ta fice ta bar ni na kasa taɓuka komai illa tunanin da na yi nisan kiwo a cikinsa. Zuciyata zafi take yi mini tamkar ana watsa mini garwashin wuta na tisa wayata a gaba ina kallon saƙon hawayen suna tsere a idona. Har aka yi sallan magrib ban tashi daga wajen ba Adda Abida ta zo ta iske ni a yanda ta fi ce ta bar ni.
"Aishatu haƙuri za ki yi kar ki je ki ɗaurawa kanki wata damuwar akan namijin da uwarsa ma ba ta damu dake ba. Ake samun mutuwar aure ma kuma a cigaba da rayuwa kamar babu wani abun da ya taɓa faruwa balle kai da gida kawai ya ce ki zo. Ki tashi ki ci abinci sai kin yi wanka kafin su iso".
Na haɗiye miyau da ƙyar ya wuce ta cikin bushashshen maƙoshina "Adda wallahi ni kam ko yunwar ma bana jin ta, zan yi salla kawai na jira isowar su". A fusace ta furta mini"za ki kashe kanki Aishatu za ki ɗaurawa kanki hawan jini a banza da wofi idan akan namiji ne wallahi. Ki tashi ki yi abinda na ce dake tun na saɓa miki". Ba ni da zaɓi face aiwatar da umarninta dole na tashi na ɗeba ruwa na je na yi wanka sai da na ɗauro alwala sannan na shiga ɗaki na yi salla, na caccakala abincin da ta ajiye mini a gabana ina wanko hannuna na dawo ɗakin ko zama ban yi ba na ji sallamar su Hamma Ahmad. Gaba ya yi ras.
Adda Abida ta yi musu sannu da zuwa tare da shimfiɗa musu tabarma ina hangen su daga inda nake laɓe a bayan labulen ɗakin. Suka ce a ƙira ni na yi saurin komawa na zauna Adda Abida ta ɗago labulen ta ce na fito.
Na fito na zauna tare da yi musu sannu da zuwa, Hamma Adnan ya buƙaci da na nuna musu saƙon da na ce ya turo mini ɗin na miƙa musu wayata suka gani.
"Na ƙira wayarsa har shugowarmu cikin gidan nan amma baya ɗauka, ba zamu sako Baffa cikin wannan lamarin ba domin ina da tabbacin cewar ba ki mance yanda kuka yi dashi ba". Take jikina ya mutu murus komai ya fice fit daga raina. Hamma Ahmad ya ɗaura da faɗin"kin tabbatar cewa kuma babu wani abunda kika yi masa?". Na gyaɗa masa kaina ya cigaba da"shikenan ki zauna a nan ki kwana zuwa gobe sai mu je can gidan mu same shi, kafin nan Abubakar ma ya iso. Ina fatan dai babu wata matsalar ko?".
Ni kuwa nake da tarin matsaloli ma ba matsala ba, na furta a cikin raina a zahiri kuwa cewa na yi"babu wata matsala". Da haka suka sallame ni, ko da dare ya tsala na kasa runtsawa ban yi tunanin za a kai har wannan lokacin bai neme ni a waya ba sai gashi abin yana nema zarce tunanina.
Na kasa yin hawayen illa soyar da zuciyata take yi mini furcin Baffa na cewar ko yankan namar jikina Abdul-hameed yake yi kar na kuskura na zo gida da sunan yaji ko kawo ƙara sai yawo suke yi mini a cikin kwanyata
*ƁOYAYYAR MANUFA*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 3️⃣4️⃣
Yanda na ga rana haka na ga dare idanuna ƙas tamkar na soyayyan kifi na kasa runtsawa. Akan sallaya Adda Abida ta zo ta iske ni bayan na iddar da sallan asubahi, na gaishe ta cikin harshen fulanci ta amsa mini cike da kulawa kana ta furta " ba ki yi bacci ba daren jiya ko?". Na sunkuyar da kaina"na kasa yi ne".
Sai da ta yi jim kafin ta ce"ya kamata izuwa yanzu ki nemawa kanki mafita akan waɗannan abubuwan da suke faruwa. Na yarda kina son Abdul-hameed amma fa wani lokacin ki dunga nemawa kanki 'yancin, ƙiyayyar uwar miji da danginsa wallahi ba ƙaramin bala'i yake haifarwa ba ko da kuwa kin yi dacen samun miji mai ƙaunarki".
Ban ce da ita komai ba illa laƙwashe ƙafafuna da na yi waje guda ina sauraron zancen da ta ɗaura dashi.
"Idan kika koma ɗakinki ki yi duk wani mai yiyuwa wajen fito da maƙircin 'yan uwansa a fili ya gani kuma ya shaida".
"Adda ni ba su bane a gabana, tunda na tabbatar da cewar mijina yana sona ai shikenan". Riƙe haɓa ta yi cike da mamaki"haka da yawan mata suke ɗauka amma in har ba ka yi dacen dangin miji ba to wallahi ba kya taɓa jin daɗin zaman aure, ko haihuwa kika yi ƙiyayyar nan sai ta shafi 'ya'yanki"
A bayyane na sauƙe wata shirgegiyar ajiyar zuciya mai nauyin gaske kana na sama damar faɗin"ganin nake yi kamar bijirewa zaɓin su Baffa a gare ni shine musabbabin faruwar waɗannan abubuw..." Da sauri ta kai hannunta ta toshe mini baki tana cewa da ni"har ki ce haka domin wani baya taɓa auran matar wani, kuma ai matar mutum kabarinsa".
Haka ta yi ta lallashina gami da kwantar mini da hankali da daɗaɗan kalamai masu taushi, sai da muka yi karin kumallo sannan Adda Abida ta ce na fito ga Hamma Abubakar ya iso, duk su ukun suna zaune a bisa tabarma na iske su na gaishe da su suka amsa mini a tare.
"Me yake faruwa tsakaninki da mijinki?". Hamma Abubakar ya jefa mini tambayar muryarsa a kaurare. Ban yi ƙwauron baki ba a feɗe masa biri har wutsiyarsa, ya jinjina kansa"ƙira wayarsa yanzu". Na dannawa lambarsa ƙira amma ba ya tafiya har yanzu.
"Ɗauko kayanki ki fito ki tafi, ki jira shi ya dawo ko bangon duniya yaje shi ya dawo. Ya sanar dake dalilin cewa ki zo gida da ya yi. Idan kuma sakinki ya yi sai ya sanar".
Furcin Hamma Abubakar ke nan cikin ƙololuwar ɓacin ran da ya bayyana ɓaro-ɓaro a cikin muryarsa, Hamma Ahmad ne ya amshe zancen da faɗin"ya dai kamata mu jira zuwansa tukunna mu ji ta bakinsa kafin ta koma".
"Ba za ta zauna ba ko ka manta furcin da Baffa ya yi ne akan auransu?. Ta koma idan har sakinta ya yi ya bata takardarta a wannan sa'in sai da ta dawo ". Wasu hawayen da nake jin sauƙar su a bisa fatana tamkar tafashashshen ruwan dalma suka shiga wanke mini fuska , na gaza cewa uffan saboda yanda haƙwarana suka datse harshena.
Na tashi na shiga ɗaki na ɗauko akwatina na yi wa Adda Abida sallama muka tafi. Tare da Hamma Ahmad da Hamma Abubakar muka je gidan, gabana yana tsananta bugu na yi sallama a ƙofar falon Amma. Aka amsa tare da bada iznin shigowa ni na fara shiga duk suka zubo mini idanu tamkar sun ga wani baƙuwar halitta.
Na rusuna na gaishe da Amma ba ta amsa mini illa kallon mamakin da ta cigaba da bi na dashi har izuwa lokacin da na ce "tare nake da yayuna suna son magana dake".
"Su na ina?". Ta faɗa a gadarance, na yi ƙasa da idona kafin na ce"su na waje". Da ido ta yi mini alama akan su shigo na fito na yi musu iso, ta sallame kowa daga mu sai ita. Hamma Abubakar ya musguta tare da cewar"Hajiya mun zo ne mu ji dalilin tura ta gida da Abdul-hameed ya yi, kuma mun neme sa a waya ba ma samun sa shiyasa muka ɗauko ta muka dawo da ita".
Gabana ya tsananta bugu saboda banzan da Amma ta yi masa. Na san Hamma Abubakar da zafin zuciya da saurin fusata. Muka haɗa ido dashi na yi saurin janye nawa. Sai can ta ce"nima bai sanar da ni dalilinsa na yin hakan ba amma za ku iya jiran dawowarsa sai ku tattauna dashi".
A wannan karon Hamma Ahmad ne ya yi magana"zamu je mu dawo, domin dole mun zauna dashi. Ita dai yanzu za ta koma ɗakinta".
Kafaɗarta ta ɗage musu alamar duk yanda suka yi dai-dai ne, sallama suka yi mata domin ko kaɗan ta ƙi basu fuskar tattauna wani zance da ita game da lamarin balle har a sama hanyar da za a ɗinke ɓarakar. Sai da muka fita Hamma Adnan ya sauƙe numfashi kafin ya ce"anya ba zamu tafi da yarinyar nan ba kuwa? Mu jira har sai ya zo don mu ga gudun ruwansa".
"Haka ne amma dole ce za ta samu mu bar ta nan, domin idan har wannan labarin ya iske kunnuwan Baffa to duk ranmu sai ya ɓaci. Ki yi haƙuri ki shiga ki zauna in sha Allah zamu yi magana dashi kin ji?". Jikina a mace na ɗaga masa kaina ina jin wasu hawayen su na ciko mini koramar idanuna.
Nasiha su ka ɗan yi mini kafin suka tafi tare da yi mini gargaɗin duk abinda ya ƙara faruwa nan gaba, kafin na bar gidan na sanar dasu a waya tukunna. Haka suka tafi suka bar ni raina cike da zulumi, na ja saƙararrun ƙafafuna na koma sashina yana nan kamar yanda na bar shi wanka na fara yi na gyara ɗakina tare da mayar da kayan da na zuba cikin akwatin.
Na zauna na zabga tagumi cike da rashin sanin matsayin aurena a halin yanzu. Firgitit na dawo cikin hayyacina saboda rurin da wayata ta soma yi, da azama na ɗauko ta ganin sunan Asiya ya bayyana cikin screen ɗin wayar ya sa ni furzar da iska daga bakina domin na yi zaton Abdul-hameed ne.
A hankali na yi sallama ta amsa mini muka gaisa kana ta ce"ya ke ma na ji muryarki wani kala yanzu mijinki ma ya bar gidan nan shi ma kamar marar lafiya".
"Mijina? Abdul-hameed ke nan fa ?". Na faɗa da wani irin sauri har ina nema zamewa daga kan kujerar da nake zaune.
"E shi fa yanzu suka fita da Auwal. Ya zo ya ce yana buƙata na nema miki 'yar aiki wacce za ta taya ki aikace-aikace".
Na taune leɓena da ƙarfi tamkar ba namar jikina ba, sai da na fizgo numfashina da ƙarfi na sama lasisin faɗin"to fa sai ki samo mana mai nutsuwa". Sai da ta dara sosai ta ce"irin wannan kashedin dai shi ma ya yi ta yi min, in sha Allah zan nema miki ko a cikin yaran maƙota da suke shigo min. Idan an samu zan sanar dake".
"To godiya muke mun haɗa ki da aiki. Ina mai sunan mu fa?".
"Yana can wajen su Umma".
Saƙon gaisuwata na bayar gare sa sosai kafin muka yi sallama. Na manne wayar a ƙirjina na so na tambaye ta ƙarin haske game da yanayin da yake ciki sai na gudun kar ta zargi wani abu.
Wuni na yi ina sarƙa da warwara cikin raina na kasa assala komai har aka yi sallan magrib. Ina ta tsumayin ƙiran su Hamma Abubakar amma su ma shuru kamar an shuka dosa kunya ni kuwa ta hani na ƙira su na tambaye su yaya ake ciki.
Ina zaune kan sallaya bayan na gama iddar da sallan isha'i na ji ƙarar shigowar motarsa kamar zan kife akan hancina na tashi na tsaya ta jikin taga ina leƙansa. Ya yi fakin ɗin motar ya fito sannan ya zagayo ta kujerar mai zaman banzan ya ɗauko jakarsa, na ƙara ware idona akan sa domin kamar tun kayan jiya da fita dashi har yanzu shi ne a jikinsa. Har sai da ya ɓacewa ganina ya shige sashin Amma sannan na bar wajen na koma na zauna.
Ban yi tsammanin shigowarsa nan kusa ba don haka na yi zama na a ɗaki raina duk a jagule. Kamar an ce ɗaga kanki ina ɗagowa idanuna suka sauƙa akan fuskar idanunsa ƙar a kaina ya naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa. Na gyara zamana domin ko kaɗan ban ji ƙarar buɗe ƙofar ba balle motsin shigowarsa.
Duk takun da zai yi yana ƙara matso ni sai bugun zuciyata ya tsananta fiye da kima da tunani.Ya yi wani tsuguno mai ban sha'awa akan ƙafarsa a gabana yana ƙawata fuskarsa da annurin da ya sanya mamaki bayyana a bisa razananniyar fuskata
"Afuwan tafiya ce ta kama ni ta gaggawa a wajen aiki kuma inda muka je babu network ba zan iya ƙira ko amsa ƙira ba".
"Ta-ta-tafiya kuma?".
Na furta kalmar a rarrabe tamkar mai koyan magana. Ya ɗaga mini kansa"ƙwarai kuwa akwai wasu NGO da suka ɗauki nauyin ginawa waɗanda iftila'in ambaliyan ruwa ya rutsa da su a cikin Borno. Sun kawo aikin ofishinmu shi ne aka wakilta ni nake na ga wajen. Motata ta sama matsala sai da Auwal ya ɗauko ni aka gyara sannan na dawo".
Na ji wani sanyin daɗin ya ziyarci sashin ruhina, na saki ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ina jin raina saƙayau. A raunane na ce"na ga saƙon da ka turo mini hankalina gabaɗaya ya tashi na ƙira wayanka kuma ba ya tafiya. Har su Hamma su ma sun jarraba amma ba ya shiga".
Da mamakina sai na ga ya waro idanunsa waje alamar mamakin zancena yake yi ya ce"wani irin saƙo?".
Ma galla masa harara ina ƙarawa da watsa masa kallon uku saura kwata. Na ɗauki wayata dake kusa da ni na shiga wajen saƙon na haska masa a idonsa. Ya karɓa ya karanta bai ce komai sai da ya zame daga tsugunan da ya yi ya zauna dirshan.
Ya ɗago idanunsa da suka sauya launi ya zube su a fuskana"yawan rantsuwa bai kasance daga cikin halayyata ba, amma na rantse miki da Sarkin da bashi da abokin tarayya ba ni da masani game da wannan saƙon. Ban tura ko wani irin saƙo da wayata ba hasalima a mota na bar wayata da wayar wajen aiki nake amfani har na je na dawo".
Na ɗaga masa hannuna alamar ya dakata mini haka nan"lambarka ce fa aka turo saƙon dashi kuma ka ce baka da masaniya akan saƙon".
"Wallahi ban san yaushe aka turo ba ban kuma san waye ya turo ba ki yarda da ni". Na kasa cewa komai don ya gama ɗaure ni da jijiyar jikina, sai da na karɓa wayata na miƙe tsaye idanuna taf da hawaye na ce"ka ƙira Hamma Abubakar dashi za ku yi magana". Ina dasa aya na shige ɗakina fu na ja ƙofar na rufe.
Na jingina a jikin ƙofar ina sauraron bugun da zuciyata yake yi tamkar zai ɓallo allon ƙirjina ya fito waje ya daka rawar disko. Na daɗe a haka kafin na fara sulalewa izuwa ƙasa dai-dai lokacin da wayata ta soma ruri ba tare da na duba mai ƙira na ba ɗaga tare kara wayar a kunnena.
"Aishatu kina ji na?".
Na ji muryar Hamma Abubakar daga ɗayan ɓangaren sun yi dirar mikiya a kunnuwana.
"Ina ji Hamma".
"Yanzu mun yi magana da mijinki abin mamaki ya yi min rantsu da abinda zai kashe shi cewar ba shi ya turo wannan saƙon ba kuma bai san wanda ya turo ba". Hawayen idanuna suka zubo na share su kafin na furta "haka nima yanzu yake shaida mini amma zuciyata ba ta nutsu da hakan ba".
Ya yi shuru kamar mai nazarin wani abu kafin ya ce"kar ki damu tunda ya ce bai aikata ba shikenan a bar shi a hakan. Ki yi haƙuri ki manta komai ki nuna mana kema daga ɓangarenki komai ya wuce, sannan Aishatu ki dade da addu'a tabbas akwai wata