Showing 27001 words to 30000 words out of 80635 words
Chapter 10 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt
suka tsorita da yawan kayan. Da ya zo nake sanar dashi kayan ya yi yawa har iyayena suna magana akai, ya nuni mini cewar yana da shi ne shiyasa ya yi mini, da bashi da shi ai dole ya haƙura.
Ya gyara zamansa yana fuskanto ni sosai ya ce"da su Abba zasu amince ma da har kayan ɗaki zan miki, ke kaɗai nake buƙata a kawo min gidana".
Na yi saurin dakatar dashi da faɗin"tab ai kuwa dai ba zasu taɓa amincewa ba, ko yaya ne sai sun yi mini daidai ƙarfinsu wanda bai wuce zarafi ba. Ka yi haƙuri kawai".
"To shikenan amma idan an kai ki gidana ai ina da damar saya miki komai". Na ɗaga masa kaina ina faɗin"ƙwarai kuwa".
"Ina so na je na gaisar da su Umma".
Sai da na murmusa kana na ce"tab Umma da kunya ai ba za ta taɓa bari ku haɗu ba, wataƙil sai bayan an ɗaura". Shima murmushin ya yi tare da sauya akalan zancen. Mun yi zance sosai har Anwar ya shigo ya iske mu suka gaisa sannan ya shiga ciki ya bar mu.
"'Yan uwana suna ta yabon ki da suka kawo lefe, cewar kunyarki ta burge su".
"Na fito na gaishe su amma ban gane su ba".
Ya yi ɗan dariya kana ya ce"Anty Adama da Anty Alawiyya duk sun zo kuma sun ganki, bari ki ga hotunan su". Ya ƙare zancen yana zaro wayarsa daga aljihunsa ya soma latsa kana ya miƙo mini hotunan mata biyu ne a tsaye sai wata babbar macen da nake kyautata zaton cewar mahaifiyarsu ce a zaune, yana daga gefen hagunta sannan wani wanda suke tsananin kama dashi yana zaune daga gefen dama. Fuskokinsu gaɓadaya washe da ƙayataccen murmushin dake bayyanar da cewar zuƙatansu wanke yake tas da farin ciki. Shiga iri ɗaya suka yi na shadda ruwar ƙasa da ya amshi jikinsu hatta aikin dake jikin shadda iri ɗaya ce.
Na kasa janye idona daga kan su na ce"masha Allah wannan dai na ganta ranar". Na ƙare zancen ina nuni da Anty Adama.
"Ita ce babbarmu sannan Anty Alawiyya ni sai kuma auta Al'amin".
Na miƙa masa wayar ina faɗin"Allah ya ƙara haɗa kawunanku waje guda". Ya amsa da amin cike da jin daɗin addu'ar. Haka muka yi sallama cike da kewar juna.
Ana saura sati ɗaya bikin na koma gidan Adda Azima a cewar ta so take ta yi mini gyara sosai, saboda ta lura da wani gani ganin da dangin Abdul-hameed suke yi mini.
Kafin a rufa kwanaki biyar na yi fes da ni fatata ta yi kyau har wani ƙyalli nake yi. Sau ɗaya Abdul-hameed ya zo gidan muka yi magana akan kuɗin da zai ba ni na gyaran jiki da kuma abincin ƙawaye.
Na nuna masa cewar ban san komai game da hakan ba, don haka na ƙira masa Adda Azima suka yi zancen da ita. Dangi na nesa da na kusa tunin suka fara cika gidan don ba na wasa ba Dada ta yi gayyata, takanas ta ɗauki ƙafa taje har garin su ta kai gorona da na Adda Abida.
Baba da kansa ya saya mana leshi da turmin atamfa guda ɗaiɗaya ya ce mu yi fitar biki dashi, a cewar sa kar a taɓawa kowacce kayan lefenta musamman ni da nake da dangin miji dole zasu sanya ido akan kayan da suka kawo.
Adda Azima ta ba da aka yi mana ɗinkin kayan iri ɗaya, ranar juma'a da karfe biyun rana bayan an sauƙo daga sallar juma'a ya kasance dai-dai lokacin da aka ɗaura auren.
Bamu san me ya faru ba sai ji muka yi wai an wuce da Anwar da asibiti ya yanke jiki ya faɗi a masallacin. Hankali gabaɗaya ya tashi amma an hana kowacce zuwa Hamma Abubakar ya ce da sauƙi ruwa kawai aka ƙara masa kuma yana tunanin ma zuwa yamma za a iya sallamarsa.
Aka kai mu wajen Umma da Dada suka yi mana nasiha sosai sannan aka wuce damu wajen Baffa da Baba su ma nasihar suka ƙara yi mana. Baffa yana kan bakansa na cewar ko meye Abdul-hameed ya yi mini har na tako gidansa da sunan kawo ƙara ko zuwa yaji ba zai laminta ba.
Hakan ya ƙara dagula mini lissafina na ƙara tsananta kukan da nake yi kamar zan shiɗe. Na ƙamƙame Umma ƙam a jikina da ƙyar aka raba mu. 'Yan uwanta su suka je yiwa Adda Abida jere 'yan uwan Dada kuwa suka je mini jere. Komai iri ɗaya aka yi mana mun sha kukan mu kafin aka raba mu aka wuce da kowa gidanta.
Ba ni da ƙawa ko ɗaya don haka da ni sai dangina da abokan arziki. Har motar ta ja burki ban tsagaita da kukan da nake yi ba tabbas na ƙara gaskatawa cewar aure yaƙin mata, in ban da hakan mai zai raba ni da uwata aka kawo ni nan cikin mutanen da ban san so ba.
Haka aka fito da ni sanye cikin laffaya da alkabba a kai da Baba ya sanya mana ni da Adda Abida. Za a shiga da ni a wuce dani izuwa sashina aka ce sai an fara kai ni wajen Amma mahaifiyarsa.
Aka wuce da ni can kaina a ƙasa yake amma ina iya hango mutanen da suke cike a falon da ya ƙawatu da abubuwan alfarma da more rayuwa tun kafin na zauna wani daddaɗan ƙamshi ya bugu hancina. Aka zaunar da ni a ƙasa sannan suka gaishe da kowa.
Kafin na gaishe su wata murya ta daki kunnuwana, cikin isa da izza aka furzo zancen a dake.
"Wannan ce amaryar abu kamar an roƙo?".
Shuru ya ratsa wajen na tsawon daƙiƙu kafin wata ƙanwar Baffanmu ta furta"ita ce ranki ya daɗe". Ta taɓe baki"madalla ɗauke ta ku kai ta sashinta".
"To ranki ya daɗe ga amana nan sai an haɗa da haƙuri yarinya ce. Don Allah idan ta yi ba daidai ba a nusar da ita, dole sai da kwaɓa wani lokacin".
Ba ta amsa ba sai wata dake kusa da ita ne ta amsa cikin faɗin"in sha Allah, Allah ya basu zaman lafiya ya kawo ƙazantar ɗaki". Duk suka amsa da amin kafin aka ɗauke ni aka wuce da ni sashina.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 1️⃣5️⃣
Kaina yana ƙasa muka shiga sashin dangina suka rangaɗa guɗa. Aka kai ni har cikin uwar ɗaka. Adda Azima ce ke ta kwaɓar waɗanda suke girmama zancen da Amma ta yi. Sai da ango da abokan suka shigo sannan suka tsagaita, suka damƙa amanar amarya a hannun angonta tare da ƙara yi mana nasiha da nusar da mu cewar shi aure ɗan haƙuri ne dole sai mun kai zuciya nisa kuma mu kasance masu yiwa juna uzuri a ko yaushe.
Sai da suka biya kuɗin sayan baki sannan aka buɗe musu fuskata, aka yi addu'a abokansa suka ce mutane su fito su fara mayar dasu. Duk sallama suka soma yi mini domin Bana ya ce babu kwana a gidan amarya ana kai ta cikin ɗakinta kowa ya dawo gida alabashi gobe aje a gano ta.
Na yi kuka tamkar raina zai fita har sai da na ji idanuna sun yi mini wani nauyin gaske da ko buɗe su bana ƙaunar yi balle kallon haske. Tabbas Abdul-hameed ya cika cikakken masoyi domin ya bani duk wani kulawan da ta dace, duk da ya fahimci ina cike da tsoro, fargaba da kuma rashin sabo amma ya yi dabara wajen tafiyar da ni akan yanda nake.
Da safe kafin ya shigo ɗakin kasancewar ba a nan ya kwana ba, na yi wanka na shirya cikin sigar riga da zanin atamfa na ɗaura hijabina a kai. Na zauna na yi shuru duk kewar 'yan uwana ya ishe ni kwana ɗayan da na yi ban gan su ji nake kamar na shekara ban sanya ta a cikin idona ba. A haka ya shigo ya same, ban ji shigowar sa ba illa zaman da ya yi a kusa dani tare da tafa hannunsa.
"Lafiya tunanin me kike haka?".
Na rusunar da kaina ƙasa"babu komai ina kwana an tashi lafiya".
"Lafiya ƙalau ya kwanan baƙuta". A sanyaye na amsa da"alhamdulillah".
"Ya kuma kuka?". Na yi shuru ban amsa masa ba ya yi gyaran muryar sannan ya cigaba da faɗin"a tsarin wannan gidan Amma ta tsani ta yiwa mutum magana ya yi mata shuru tabbas aikata hakan yana jawo tsananin ɓacin ranta. Don Allah kar ki aikata hakan a gare ta". Take naji gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalau na gyaɗa masa kaina alamar na ji sai kuma na tuna da zancen nasan na yi saurin ɗaugo kaina ina faɗin"to in sha Allah zan kiyaye".
"Allah ya bada iko". Na amsa cikin faɗin amin ya miƙe ya ce da ni na fito falo kafin ya yi wanka ya shirya mu je mu gaida Amma. Yanda ya umarce ni hakan na aikata na zauna zaman jiran sa a falon. Kujerun da aka yi mini sun zama abun tausayi a cikin falon saboda girmansa da kuma ƙawatuwarsa. Ga wakeken filin da ya yi saura.
Ƙamshin turaren da na ji ya bugi hancina shi ya sanya ni ɗaga kaina caraf idanunmu suka haɗe cikin na juna, na yi saurin ɗauke nawa. A hankali ya tako ya iso har gabana tare da sa hannunsa ya tallafo fuskana ya ɗago ta. Tsam na matse idanuna na ƙi yarda na buɗe na kalle shi.
Shafo goshina zuwa kuncina ya yi tare da hura mini iska a idanuna. Ya riƙo hannuna ya miƙar da ni tsaye ya na faɗin"mu je". A hankali nake takawa har muka fito daga cikin sashin. Babban gida ne mai ɗauƙe da part uku na Amma ya fi kowanne girma sannan namu da wani a gefensa.
A tare muka yi sallama yayin kutsa kai cikin falonta aka amsa sallamar ciki ciki. Muka zauna a ƙasa sannan muka haɗe baki wajen gaishe ta. Sai da ta ja dogon lokacin kafin ta amsa mana tana kafe ni da ido"Abdallah yaya naga aamryar takan duk ta yaƙwane haka, jiya da aka shigo da ita nan ta fi haka daɗin gani da kuma hasken fata".
"Amma wataƙil dai kallon tsoro kika yi mata a daren jiyan shiyasa, amma ba wani canjawan da tayi. Ta ma kwana da zazzaɓi ne saboda kukan da ta yi". Sai a lokacin na yi nasarar zame hannuna daga riƙon da ya yi mini ina ɗan janye jikina gefe kaɗan.
"Kuka kuma na meye?".
"Kukan rashin sabo da kuma rabuwa da gida". Ya bata amsar kansa tsaye da hakan ya sanya ta sakin dariya mai matuƙar sauti kana ta furta" ai yanzu ko yarinya 'yar shekara goma aka yi wa aure zaunawa take yi lafiya lafiya babu wani tashin hankali, balle wannan da zata iya haura goma sha shida".
"Haka ne amma ko wa da irin halittansa ". Ba ta ce kuma ba illa jinjina kanta da ta yi tana ɗaukar wayarta ta fara latsawa tare da karawa a kunnenta.
"A fito da abin karin kumallo ga ango da amarya har sun fito". Yana gama faɗin haka kit ta katse wayar.
"Kin yi karatun zamani kuwa?". Tambayar ta ya katse mini zancen zucin da nake yi. Cike da girmamawa na ce"na yi amma ban yi nisa ba".
"Yanayinki kuwa bai yi kama da na wacce ta taɓa zaman aji ba. Kin yi girki?".
"Na iya dai-dai gwargwado". Ina rufe bakina aka yi sallama ta amsa sannan aka shigo ta dire kulolin abincin da ta jere a cikin wani kwando sannan ta gaishe da Abdul-hameed nima na gaishe ta ta amsa mini har da yi mini taken amarya mai maganar zuma.
Ta koma sannan ta dawo da wasu kayan ta jere. Ta durƙusa har ƙasa ta ce "ranki ya daɗe komai ya kammala".
"Ki je ki ƙira Al'amin da Alawiyya".
"To ranki ya daɗe, me za a ɗauro da rana saboda baƙin da zasu iya zuwa?". Sai da ta ɗau lokacin kana ta furta"bana son gaggawa Asabe ki bari ranar ta yi tukunna sai a fara tunanin abinda za a yi". Kamar za ta yi mata sujjada ta ce"tuba nake uwargijiyata".
Ba ta kul ta ta miƙe ta fice jim kaɗan Anty Alawiyya da Al'amin ɗin suka shigo. Suka gaisa da Abdul-hameed ni kuwa suka yi banza da ni. Hakan ya tabbatar mini da cewar jira suke na fara gaishe su. Don haka na sausauta muryata na gaishe da Anty Alawiyya sannan Al'amin kafin ya amsa Abdul-hameed ya yi saurin faɗin"kai yanzu sai ka amsa don baka da kunya?".
"To meye abin rashin kunya don ta gaishe dashi ya amsa. Ai girman bishiyar kuka kawai ake gani amma gabaruwa ita ce babba, ko a ido ai Al'amin ya fi wannan yarinyar". Amma ta tsara zancen daki daki, kowa shi yake ɗibar abunda yake son ci ni kam ko motsawa daga inda nake na kasa yi, shi ya zuba mini ya kuma yi mini bismilla.
A hankali nake kai abincin bakina, tunda muka fara cin abincin babu wanda ya ce ko kanzil har muka kammala. Asabe ta dawo ta tattare kwanukan tare da gyara wajen.
"Alawiyya ki je sashin Abdallah ki ɗauko min hotunan kayan da iyayen matarsa suka yi mata". Wani irin yanayi na ji ya baƙunce ni shin tozarta ni Amma take son ta yi ko kuma nata salon ne haka shine abinda na gaza fahimta. Bai ce komai ba shima har Anty Alawiyyan ta miƙe ta fita ta dawo tare da nunawa Amma hotunan kayan da ta ɗauko.
Ta kalla sosai sannan ta ajiye wayar tana taɓe baki"waɗanda kayan ba su yi ba dole za a mayar musu da abun su, don ba zan ji kunya ba sanin kanka ne yau ƙawayena a sauran dangi zasu zo ganin amarya da kuma ganin ɗakinta. Ai ga irin bajintar da iyayenta suka yi mata, idan aka zo aka tarar da wannan kayan ai na ji kunya. A fitar dasu maza a mayar musu zan sanya a zuba wasu da suka dace".
Ƙirjina ya harba da ƙarfi idanuna yana hasko mini hotun ƙatuwar saniyarsa da Baba ya sayar domin yi mana waɗanda kayan. Gabaɗaya sai na ji zaman wajen ya gundure ni babu abunda na fi buƙata kamar na ga na bar wajen na keɓe ni ɗaya.
"Iyayenta sun yi ƙoƙari wajen yi mata wannan kayan, maimakon a mayar musu dashi mai zai hana a sanya su a ɗaki guda har da kujerun tunda ɗakin zai ɗauko. Amma kowa fa zai so yaga yana amfani da wani abu dai da zai dunga tunawa da wani nasa musamman iyaye".
Duk da a cikin lumana da kuma tsantsar biyayya da kwantar da murya ya yi mata zancen, sai na ji ta ɗaga murya sama tana faɗin"na gama yanke hukunci wannan kayan mayar musu da abun su za a yi, idan kuma kana so ka nuna min cewar ban isa na zartar da hukunci akan lamarin gidanka bane to bismilla".
Cikin sanyin jiki da na murya ya ce"kin isa, ba na faɗi haka da nufin ɓata miki rai bane Allah ya huci zuciyarki". A gajarce ta amsa da"Amin".
A take a wajen ta umarce Al'amin da yaje ya yi wa masu gadi jagoranci izuwa sashin sun fitar da komai, a deɓo kayan dake cikin sashin dake kallon namu a mayar dasu cikin namu. Sannan haka ya miƙe ya fice ina jin zuciyata tana yi mini wani irin azabban zogi. Ƙwalla suka ciko mini koramar idanuna na yi saurin mayar dasu.
Muna nan zaune a wajen Al'amin ya dawo yana shaida mata an cire komai, ta jinjina kanta tare da cewar"za ku iya tafiya, bayan sallan zuhr ki zama cikin shiri domin za a baƙi kuma zasu ganki".
"To in sha Allah a tashi lafiya".
Na amsa mata sannan muka tashi muka fito ban san sanda hawayen da nake dannewa suka kwaranyo ba lokacin da na yi tozali da dukkan kayan da iyayena suka yi mini an fake su a gefe waje guda. Hatta kayan katakon basu tsira ba duk da jajircewar da Hamma Ahmad ya yi wajen ganin an zaɓo mini mai ƙarko kuma na ke ce raini.
Ka kallon kayan da aka sauya a cikin falon ban yi ba na wuce ɗaki da sauri, ya rufa mini baya. Na zauna na zabga tagumi ina hawaye. A kusa dani ya zauna tare da naɗe dukkan ƙafafunsa wajen guda ya ce"ki yi haƙuri Aisha zama da Amma tabbas sai ma haƙuri mai haƙuri ma sai mai tsananin haƙuri. Don Allah ki taimaka mini wajen yi mata biyayya domin a yanzu ita kaɗai ta rage mana mahaifin mu ya rasu. Duk bana iya ƙetare umarninta ko kuma na yi mata musu akan komai amma ba hakan bane yake nuni da cewar zan bari ki tozarta a cikin gidan nan. Wallahi ina son ki kuma ba zan taɓa jure ana wulaƙanta ki akan idona ba".
Cike da ƙarfin hali na ɗago idona da har yanzu yake tsiyayar da ruwar ƙwalla na sauƙe akan fuskarsa ina faɗin"abu ne mai kyau yin biyayya ga iyaye musamman uwa domin babu wani abinda za ka yi ka biya ta kwantankwancin rabin ɗawainiyar da ta yi da kai".
"Ba za a mayar da kayan ba, za a sanya su a cikin ɗayan sashin tunda baƙi kawai ake sauƙa a cikin sa". Kaina kawai na jinjina masa ya ƙara matsowa dab da ni har muna jin fitar numfashin juna, ya kai bayan hannunsa yana share mini hawyen da suke fareti a bisa kuncina.
Na lula duniyar tunani shin wani irin zama zan yi a cikin gidan nan da tsarin mutanen cikinsa ya sha bambam da na sauran gidaje. Shin ta yaya zan saba da halin Amma da ragowar 'yan uwansa?.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 1️⃣6️⃣
Sosai ya yi ta aikin lallashi na, ganin yanda ya ke nuna damuwarsa a fili ya sanya ni danne zuciyata da nake jin tana tafasa na nuna masa babu komai. Ko da wasa ban ƙara bari ya fahimci cewar abin yana damuna ba.
Ya shirya ya ce dani zai je wajen abokansa da suka kwana yau duk za su wuce su