Showing 45001 words to 48000 words out of 80635 words

Chapter 16 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

ƙaryata Asabe.


Dafe kansa da yake sarawa ya yi cikin ransa yana karanto hasbunallahu wa ni'imal wakil.Tabbas yana cikin tsaka mai wuya zuciyarsa ta kasa aminta da cewar Aishansa za ta iya cutar dashi ta wannan hanyar. Amma sai dai ya san babu wani dalilin da zai sanya Amma furta masa zancen da bai faru ba.


"Me ye ribarta idan ta aikata hakan a gare ni Amma?".


"Wannan kuma wani ƁOYAYYAR MANUFA ce da ta ɓoye a cikin ranta". Da ƙarfi ya cije leɓensa yana ƙoƙarin miƙewa ta yi saurin dakatar dashi tare da tsiyaya masa ruwar dake ajiye a kan dirowar gefen gadon ta miƙa masa. Tare da umartarsa da ya shanye bai yi mata musu ba ya karɓa ya kafa a bakinsa, sai da ya shanye tas ya ajiye kofin ya yi mata sai da safe sannan ya fice yana jin wani irin nauyin da ƙirjinsa ya yi masa.


Tunda na baro sashi Amma na zauna na kafa tagumi ina tunanin yanda zan yi da ƙulin maganin da ta bani. Na tsayar da matsaya akan gobe da safe yana fita sallar asubahi zan fito na haƙa rami na burne shi. Don ko yanzu da yake cikin ɗakina hankalina ba a kwance yake ba, sai na fitar dashi daga cikin gidan sannan zan sama sallama kuma zuciyata za ta fi gasuwar cewar ba zai cuto ba.


Wanka na yi na shirin cikin shigar bacci na zaunan jiran sa. Asabe ta kawo mini kayan haɗin shayin da yake sha a kowani dare kafin ya kwanta.
Filas ɗin ruwan zafi ne sai gayen shayi da kuma taceccciyar farar zuma. Na ɗauko kofi na ƙaramin cokali na ajiye masa da duk wani abunda zai buƙata, na tisa kayan a gabana ina kallo.


Ina son naga nima ina girkawa mijina abincin da zai ci ko zai sha da hannuna kamar yanda sauran mata suke hidimtawa mazajen su don samun tagomashin lada daga wajen Ubangiji. Sai dai ba ni da wannan damar domin har yanzu babu kayan abinci a sashina ruwa da lemuka ne kawai a cikin firiji.


Jin motsin taɓa ƙofa ya sa ni dawowa cikin hayyacina daga tunanin da na zurma. Yanda ya shigo mini ya sanya gabana yin wani mummunar faɗuwar da zai da na dafe ƙirjina.
Kamar bai gan ni ba ya ɗauki hanyar wucewa ɗakinsa, na yi saurin miƙewa ina shan gabansa.


"Lafiya kuwa?".


Duk da yanayin da yake ciki a hargitse sai da ya yi ƙoƙarin sakar mini da murmushi da ko haƙwaransa basu bayyana ba. Bai iya furta mini komai ya raɓa ta gefe na ya shige ɗakin tare da turo ƙofar ya rufe.


"Na shiga uku!".


Na furta ina ƙara dafe ƙirjina da yake yi mini gudun famfalaƙi. Tunani barkatai suka fara ziyartar kwanyata ni dai a iya sa nina na bar shi za su haura sama da Amma zasu tattaunawa kamar yanda ta ce, daga haka ban san me ya faru ba da ya jefa shi cikin wannan yanayin.
Ko dai wani ne ya rasu ko kuma ɗaya daga cikin su babu lafiya?. Na yi saurin ƙaryata hashashen zuciyata, tare da zabura nima na nufi daƙin.


Yana zaune akan gado ya juya bayansa tare da dafe kansa. Na tako a hankali na iso na tsuguna a gabansa a nutse na furta"Allah ya huci zuciyan sadaukin mazaje, ka sanya ni cikin tsoro ina fatan kowa lafiya daga cikin gidan?". Kansa kawai ya iya yin ƙarfin halin ɗaga mini na ƙara da cewar"ki gaggawa ka sanar da ni menene yake faruw..".
Ban ƙarisa saboda rawar da jikina ya soma da ban san lokacin da na zame na zauna dirshan ba, idan na yi rantsuwa na tabbatar babu kaffara a kaina idan na ce da ya ɗako idonsa ya kalle ni ban da ɗigon baƙi ko kaɗan a cikin ƙwayar idonsa ba.


"La-la-la-lafiya?".


Na furta maganar a rarrabe kamar 'yar koyo. Sai da ya ja lokaci cikin wata iriyar murya ya ce"ki yi haƙuri ki bani lokaci ina son kasancewa ni kaɗai". Yanda ya yi maganar na tabbatar da cewa idan bakina ya yi kuskuren ƙara cewa wani abu babu tantanma zai iya rufe ni da mahaukacin duka. Don haka na nemawa kaina salama na tashi na fito sai dai na kasa barin ƙofar ɗakin nan na zauna na ci kuka har na godewa Allah. Wata zuciyar tana raya mini na je na sanar da Amma halin da yake ciki sai na fasa. Haka na zauna a wajen da tunanin zai neme ni komai dare har bacci ya kwashe ni.


A hankali na soma buɗe idona da ya yi mini nauyin gaske ga ciwon kai da jikin da ya rufe ni, saboda ƙiran sunana da na ji an yi tare da taɓo kafaɗata.


"A nan kika kwana?".


Na yi zumbur na miƙe ina kallonsa kafin na yi magana ya yi saurin taran numfashina da faɗin"ki je ki yi salla idan na dawo daga masallaci zamu yi magana kin ji?". Kaina kawai na ɗaga masa ina matasa na bashi hanya ya wuce na bishi da kallo wasu hawaye masu ɗumi suna gangaro mini.


Ba zan iya jan ƙafana izuwa ɗakina ba don haka na shige ɗakinsa na yi alawala. A zaune na yi sallan asubahin saboda rashin kuzarin da nake ji a jikina. Na ɗauko al'ƙur'ani na fara karanta shafi biyu na yi na rufe don sai zabga kwaɓa nake maimakon samun lada sai na ɗebowa kaina zunubi. Sai ƙarfe bakwai ya shigo kamar yanda yake yi a kwanakin nan da ya taso daga sallan asubahi sashin Amma yake wucewa.
Har ya shigo ɗakin ya ja dirowa ya ɗauki wasu kuɗaɗe ya fita ban ɗago kaina ba. Ina jin sa yana ji wa Al'amin kashegi akan ya rage wasa da kuɗin.
Ya dawo ya zauna ɗan nesa da ni kaɗan ya furta"tashi za mu yi magana".Na tashi daga kwanciyar da na yi akan gardumar ina tattara dukkan nutsuwata gare shi.


"Ba zan gaji da sanar dake cewar kina son ki ba zuciyata ta aminta dake aminta na sosai. Idan ki ka cire Amma ban taɓa yarda da wani mutum kwantankwacin yanda na yarda dake ba. Da ke kaɗai zuciyata ta aminta da na ƙarar da rayuwata tare dake. Na ba ki amanar kaina,dukiyata da kuma duk wasu abubuwan da suka kasance mallakina na kasance tamkar raƙumi da akala a gare ki da kike da ikon jan ragamana zuwa ko wani direction. Idan kin ga dama ki bar ni na mutu idan kuma kin so ki tarairaye ni".


Dam na ji ƙirjina ya buda da matuƙar ƙarfi yana yi mini dakan lugudai. Bayan ya tsuƙa numfashi ya fesar da iska ya ɗaura da"mu maza bamu da wahalar sarrafawa a hannun mata matuƙar suka hano rauninmu babu boka babu malaman zasu mallake mu. Ina yi miki tuni da ki sanya tsoron Ubangijin da baya bacci a cikin dukkan lamuranki, Don Allah matata kar ki yi amfani da son da nake yi miki ki cutar da ni kamar yanda mata suke yi a yanzu".


Haƙwarana suka datse harshena zuffan ya jiƙa mini jikina da yake rawa. Duk yanda na so furta zancen da yake bakina lamarin ya faskara. Na kasa cewa komai illa ƙasa da na yi da idanuna da ya kawo ruwar ƙwalla saboda ɗaurin da ya yi mini da zantukansa da na kasa warwarewa.


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam


________________________________________


Page 2️⃣4️⃣


Ban ɗago kaina ba sai da na ji shi dab da ni har ina iya jiyo bugun da ƙirjinsa yake yi. Ya kai hannunsa ya tallafo haɓana na matsa idona gam ya hura mini iska a fuskata yana yi mini raɗa a kunnena"buɗe idonki ki ganni".


Ban buɗe sai da ya kuma faɗin"kin san bana son gardama ko?". A hankali na buɗe tare da faɗin"tambaya ɗaya zan yi maka don Allah ka sanar dani gaskiyar abinda yake zuciyarka game da hakan".


"Na yi miki alƙawarin sanar dake dukkan gaskiyata akan duk abinda kika tambaye ni matuƙar na sa ni".


"Wani alama ka gani na cewar zan iya cutar da kai?".
Ya juyo fuskana idanunmu cikin na juna kana ya furta"har cikin zuciyata na yi imanin cewar ba za ki taɓa iya cutar da ni ba, shiyasa duk abinda za a sanar da ni game da ke wallahi zuciyata ba zata aminta dashi ba".


Na yi rau-rau da ido "wallahi son da nake yi maka ba zai taɓa barin na cutar da kai ba Abdul-hameed. Ko wani na ga zai cutar da kai sai inda ƙarfina ya ƙare balle kuma ni da kaina ma cutar da kai". Ya sakar mini da laulansan murmushi"na yarda dake matata Allah ya ƙara kare mu daga dukkanin wani abun ƙi".


Jikina a sanyaye na amsa da Amin. Ina ɗaurawa da "jiya ka bani tsoro sosai ban taɓa ganin ka a cikin irin yanayin da ka shigo jiya ba".


"Tuba nake yi ranki ya daɗe, wani labari na ji da ya kiɗima ni na wata matar da ta mallake mijinta ta hanyar sirri ta raba shi da kowa nashi. Labarin ya taɓa min zuciyata sosai shiyasa kika ga na yi miki wannan maganar yanzu don Allah kar ki bari sheɗan ya yi rinjayi akan ki ki faɗa sahun irin waɗannan matan". Jikina ya ƙara yin sanyi lamau"in sha Allah, Allah ya kiyaye mana imaninmu".


"Amin"


Sai da ya yi yanda ya yi ya fitar dani daga halin zulumin da nake ciki. Na ƙara jin so da tausayinsa a lokaci guda yana ƙara shige mini raina. Kamar ko wace safiya na haɗa masa ruwan wanka ya shiga kafin ya fito na gyara ɗakin tare da ciro masa kayan da zai sa na ajiye masa akan gado da duk wasu abubuwan da zai buƙata.


Na koma ɗakina nima na shirya ina zaune gaban madubi na faɗa duniyar tunani maganunsa sun tsaye mini a rai tamkar ƙayar kifi. Ta cikin madubin na ke sa tsaye a ƙofar ɗakin ya naɗe hannayensa a ƙirjinsa na saka ɗan kunnena na juyo ina kallonsa.


Ya kashe mini ido ɗaya yana faɗin"kin yi kyau kamar a sace a gudu".
Na murmusa"kai ma ai haka ne". Hannunsa ya miƙo mini na sanya nawa a ciki muka fita izuwa sashin Amma.


Duk zaune a falon muka iske su suna zaune, sallamar da mu ka shiga da ita ya sanya su zubo mana idonsu har muka zauna. Duk yanda na so ƙwace hannuna daga cikin na sa na kasa saboda riƙon da ya yi mini gam.


Muka haɗe bakin wajen gaishe da Amma ta amsa mana a gajarce sannan Anty Alawiyya. Asabe ta gama jere mana komai na karin kumallo, sai a lokacin ya zare hannunsa daga cikin nawa ya koma kusa da Amma tana zuba musu abincin, take Al'amin ya ce shima tare dasu zai ci, Anty Alawiyya ma kuwa ta ce ba za a barta a baya ba. Ta ƙwala ƙiran Asabe ta kawo musu babban plate suka zuba a ciki.


"Ki zuba abinda za ki ci mana".


Na yi muryar Amma kamar daga sama, na buɗe kular na zuba wainar farar shinkafa da miyar kayan ciki na soma ci. A hankali nake tauna kamar mai ciwon baki yana wucewa ta maƙoshina da ƙyar, babu wanda ya yi magana domin a dokar gidan Amma ba a yin magana yayin da ake cin abinci kowacce magana ce sai an jira an kammala sannan a yi ta.


Sai da muka kammala Asabe tazo ta kwashe kwanukan tare da gyare wajen na bita da kallo a kaina ina jinjina ƙarfin halinta na tsayawa neman halaliyarta don rufawa kanta asiri. Na so tashi na taimaka mata da ɗebe kwanuka gargaɗin da Amma ta yi mini akan na daina shiga harkar da bai shafe ni a cikin gidan ya sanya ni dakatawa.


"Yaya kuka yi da Aminu? Ka san bana juran wulaƙanci".


"Mun yi magana dashi ya ce a bashi lokaci ya yi tunani" Da sauri ta katse shi"wani irin tunani? Ai tunani ɗaya ne shine ya zaɓa ko Alawiyya ko amarya da ya yi. Don matuƙar ina raye ba zan taba barin wani nawa ya zauna da kishiya ba na zan zafin hakan na san irin tarin raɗaɗin da hakan yake haifarwa a cikin zuciya".


Ya yi ƙasa da muryarsa"abun duk bai kai ga haka ba. Amma haƙuri kawai za a yi ta koma ɗakinta ta kula da 'ya'yanta ko don tarbiyarsu a zamanin nan kana kan 'ya'ya ma yaya aka ƙare balle baka kusa dasu. Idan fa ya sake ta dole amaryar ita za ta riƙe yaran kuma duk tarbiyyar da ta zo dashi haka su ma zasu tashi dashi ".


Sai da ta gyara zamanta tana cije leɓanta kana ta ce"ba ka san zafin kishiya ba Abdul-hameed. Ni da ubangijina mu kaɗai muka san irin halin da na faɗa lokacin da dangin mahaifinku suka hura masa wutar sai ya ƙara aure don kawai na haifo 'ya'ya mata har guda biyu ". Daga haka ta yi shuru yana sadda kanta ƙasa na saci kallonta ta gefen idona tabbass akwai abinda yake yi mata ciwo a ranta. Maganar da Anty Alawiyya ta soma yi ya tursasa mini ɗauke idona daga kanta.


"Amma ki yi haƙuri Ni kam kawai a bar ni na koma gidan mijina"


Tana ƙare faɗin hakan ta miƙe ta bar cikin falon. Duk suka raka ta da ido kafin Abdul-hameed ya hau ba wa Amma haƙuri da lallami. Wani takaici ya tokare mini ƙirjina domin na gaza gano haƙurin meye yake ba ta.


Sai da ya ga ta yi murmushi sannan ya sama sallama. Ta ce Al'amin ta je ɗakinta ya ɗauko mata wani leda akan gadonta, babu jimawa ya dawo ya ajiye mata saƙon a gabanta ta turo miki shi tana faɗin"ɗauki waya ce tunda naga shi mijinki nakin har yanzu ba shi da niyyar saya miki".


Kafin na yi magana ya riga ni"ina da niyya daman ina so ƙarshen satin nan na ɗauke ta muje ta zaɓo da kanta".


"Ai yanzu kam na hutar da kai".
Ya sa ki murmushi yana sosa ƙeyarsa. A nutse na furta"mun gode sosai Allah ya ƙara girma".


"Kun gode ke da waye?".


Na yi ƙasa da kaina na ƙara cewa"na gode Allah ya ƙara buɗi".


"Amin zasu iya tafiya na sallame ku".
Na ɗauki ledar wayar muka fita sai da muka isa wajen motarsa ya ce na buɗe wayar na yi kamar yanda ya ce. Sabuwa ce dal launin ruwan toka ga santsi kamar jikin kifi.


"Allah ya sakawa Amma da alkhairi".


"Amin".


Na amsa dashi muka yi sallama dashi na koma sashina. Baccin da ban yi daren jiya bane na fanshe shi yau, ban tashi ba sai lokacin da ake ƙiran sallan zuhr na yi miƙa ina karanto addu'ar tashi daga bacci. Na yi alwala na yi salla na fito falo na ɗauki ruwa a firiji ina tsaye ina sha na ji ana sallama a ƙofar falon na bada iznin shigowa.


"Barka da hutawa ranki ya daɗe, dama uwargijiyata ce ta ce nazo na sanar dake lokacin cin abinci ya yi".


Kaina na jinjina mata na ce "to gani nan fitowa". Ta fice na bi bayanta duk da bana jin yunwa amma ya zama kamar dole a kaina na fita domin rashin fitan zai zama matsala a gare ni.


Sai da muka shiga sashin take sanar dani cewar wai ta ce na fara samun ta a ɗakinta tukunnna. Ƙirjina ya hau dakan lugadai na haura saman ina ɗar ɗar. Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi sallama aka amsa mini tare da bani iznin shigowa na tura ƙofar a hankali na shiga.


Tana zaune akan garduma da alama salla ta iddar. Na zauna ina yi mata sannu. Ba ta amsa mini ba sai da ta zare hijabin kanta ta koma bakin gado tá zauna kana ta ce da ni"kin aiwatar da aikin da na sa ki?".


Na fara inda-inda domin ba zan ta yanda zan fara ba. Ta ƙara maimaita mini muryarta babu alamar sausauci. Na haɗiye wani miyau mai kauri kafin na sama zarafin furta "ban aiwatar ba daman yanzu nake so nazo na same ki game da maganar. Ba zan iya munafurtarki ba gwara na faɗa miki gaskiya daren jiya Abdul-hameed ya shigo cikin wani yanayin da ban gane gan shi ba, ko da na tambaye shi dalili zai ya ce mini wani labari ya ji akan wata mata ta zubawa mijinta maganin mallaka ta raba shi da dukkan danginsa. Na yi tunani mai zurfi yanda ya nuna ƙyamar abun a fili don kawai ya ji labarin wata can da bai sa ni ba to ina ga in ya gano mu?".


Na ƙara sausauta amon muryata"don Allah Amma ki yi haƙuri da wannan abun. Ke uwa duk wani addu'ar da za ki akan sa ba zai taɓa faɗuwa ƙasa banza ba tare da Allah ya amshe ta ba. Ko cigaba da yi masa addu'ar Allah ya sanya tausayi da jin ƙanki a cikin zuciyarki".


Sai da ta ɓata wasu mintoti kafin ta ce"ba za ki iya ba kenan?".


"Ba zan iya kara yarda da amincewar da ya yi da ni bane, ina mai ba ki haƙuri". Yi tayi kamar ba ta ji ni ba ta jawo wayarta da gilashinta ta maƙala a idonta tana latsa wayarta sai da na gaji kana ta furta"ke ji ɗauko min maganin ki kawo min". Zan yi magana ta ɗaga mini hannu alamar ba ta son ji komai daga gare ni. Dole na miƙe na koma sashina sai dai me?.
Magani ya ce ɗauke ni a hankali domin babu shi babu alamarsa, na fito da kayan wajen gabaɗaya amma ban gan shi ba. Na sauƙe wahalallen ajiyar zuciya ina kama ƙuguna da tunanin abin yi.


ƁOYAYYAR MANUFA




©️ Maimuna Tijjani Iyam


___________________________________


Page 2️⃣5️⃣


Dafe goshina da yake tsatstsafo da maiƙon gumi na yi ina cije naman leɓena. Ban daddara ba sai da na ƙara fito da kayan wajen kaf na ƙara dubawa, amma ban yi tozali da abinda nake nema ba.
Babu wanda yake shigo mini ɗaki daga ni sai mijina wanda ko da sakon ɗaya zuciyata ba ta taɓa dasa mini wasi-wasi akan sa.


"Ya Rabbi".


Na furta ina kwasar kayan ba mayar dasu na fito gabana yana tsanata bugu na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login