Showing 60001 words to 63000 words out of 80635 words

Chapter 21 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

kallabina a cikin bakina a ƙoƙarin hana sautin kukan da nake yi fita, sai da na yi mai isa ta sannan na tashi na nufi wajen ajiye kayansa.


Inda yake ajiye t-shirt da wandunan jeans na nufa, ya kwana biyu bai sanya su ba na fara ciro su ina duddubawa. Ina ɗago wani wando na ji wani abu ya faɗi, ban jiyo ba sai da na ajiye shi akan gado sannan na waigo.


Gabana ya yi wani mummunar faɗuwa sakamakon abinda idanuna suka yi mini tozali dashi, jikina yana rawa tamkar ana jona mini wutar lantarki na sunkuya na ɗauki ƙulin maganin ina jujjuya shi a hannuna. Babu ko shakka wannan shi ne ƙulin maganin da Amma ta bani ta umarce ni na sanya masa a cikin ruwan wanka wanda na neme shi ko sama ko ƙasa na rasa shi. Abinda na alkince shi a cikin ɗakina cikin kayana me ya kawo shi ɗakin Abdul-hameed?.



*ƁOYAYYAR MANUFA*


©️ Maimuna Tijjani Iyam


_________________________________


Page 3️⃣2️⃣


Jin kamar zai buɗo ƙofar ya fito ya sa ni saurin sanya ƙulin cikin aljihun rigar atamfar dake jikina. Na juya da sauri zan fice na je falo na jira shi ya dakatar da ni ta hanyar faɗin"ina koma za ki je?".


"Zan je falo na jira ka ne".


Ya tako ya sanya hannunsa ya riƙo ni ta baya yana yi mini raɗa a kunne"ki dawo ki shirya ni". Na juyo idanunmu suka haɗe waje guda wata zuciyar ta ayyana mini na ciro ƙulin maganin na nuna masa tare da tambayarsa inda ya samo ta, sai na yi wani tunanin yanda ya nuna mini komai ya wuce na haɗiye kawai.


Sai a lokacin na hango ashe ko rufe wajen kayan ban yi ba. Na shirya shi tsaf sai zabga ƙamshi yake yi. Na ɗage masa ido ɗaya alamar ya yi bala'in kyau, ya kai hannu zai riƙo ni na yi saurin gaucewa ina sakin murmushi domin na san manufarsa.
Ƙirar wayarsa da aka yi ya bani damar zillewa na koma ɗakina, kai tsaye banɗaki na wuce na je ƙulin maganin a cikin toilet na kunna ruwa ya raka shi. A bayyane na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya ina jin tamkar an sauƙe mini wani dutsi mai nauyi da aka ɗaura mini a tsakar kai.


Fuskana na gyara da kukan da na yi ya ɓata, na yafa mayafina na fito a falo na bar wayata na ɗauka muka fito. Na yi tunanin zai ce mu fara leƙa sashin Amma sai na ga saɓanin tunanina kai tsaye muka bar cikin unguwar, ya kunna ƙira'ar sheik Sudais a cikin rediyon motar. Wani gidan cin abinci muka je wajen shuru babu wani hayaniyar ɗaga hankali, wani teburin da aka tsara shi da wasu wutar kyandir muka zauna aka jere mana na'u'in kalolin abinci da abin sha a gaban mu.


Cike da farin ciki muka ciyar da kanmu cike da tsantsar ƙaunar junarmu.
"Har yanzu abin nan yana damunki ko?".


Na jinjina kaina"ya riga da ya wuce ai tun kafin mu fito daga gida na riga da na mance shi".
Kafin na ankara na ji hannunsa a bisa nawa na ɗago idona na sauƙe a fuskarsa, ya zame daga kan kujerar da yake ya tsuguna akan gwiwarsa a gabana.


Cikin sanyin murya mai cike da taushi ya ce"Aisha ina son ki wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba don Allah ki kasance da ni har izuwa ƙarshen numfashina". Jikina gabana ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri.


"Na yarda da duk wani abunda zai fito daga bakinka. Ina sha Allah babu wani abinda zai raba mu sai dai ikon Allah". Ya kafe ni da ido na turo baki"don Allah ka tashi kaga mutane fa sai kallonmu suke yi".


"To ni ina ruwana domin ni bana ganin kowa sai ke a idanuna". Na haɗe hannayena waje guda alamar roƙo ya tashi ya koma kujerar da ya tashi.


Mun yi hira sosai da hotuna a wajen babu adadi sannan muka baro waje, na jingina bayana a jikin kujerar motar ina faɗin"wash duk jikina ciwo yake yi mini".


"Lalle kuwa! Gwara ma ki zage domin ba gida muka nufa ba". Da sauri na wartsake na buɗe idona tar a bisa titin tabbas ba hanyar gida ya nufa ba, na kallo shi"ina zamu je?".
Sai da ya karya kwana sannan ya ce"ziyara". Ban ƙara cewa komai ba na ɗauki wayarsa dake kan cinyarsa na fara ganin hotunan da muka yi, ban ɗago kaina ba har sai da na ji ya faka motar ya fita ya zagayo ya buɗe mini na ƙi ɗago kaina na kalle shi.


"Za ki fito ko in fito dake?". Da sauri na zaro ƙafata na fito ina cuno baki, ya wuce gaba ina biye dashi a baya. Muna shiga gidan wani mutum ya fito fuskarsa kamar gonar auduga suka gaisa da shi nima na gaishe ya amsa mini yana tafawa da Abdul-hameed ya ce"wato Madam ta ɓoye ka ko a office baka ganuwa".


"Kai bari kawai Auwal".


Ina biye dasu har cikin falon muka zauna yana faɗin bari ya yi wa matarsa magana, jim kaɗan suka fito na matar ta tsaya tana riƙe haɓa"uncle Abdul lalle kuwa wata sabon gani. Yau kai ne a gidanmu amarya ta ɓoye ka".


"Haba Mamana ke ma shaidar da za ki yi min ke nan?". Ta nema waje kusa da mijinta ta zauna kana ta ce"to ai gaskiya ne shurun ya yi yawa jiya nake cikiyarka a wajen Daddyn Junior". Murmushi ya yi ya ce"tuba nake Mamana yanzu dai na wanke laifina don ga amarya na kawo miki".


"Masha Allah Allahumma barik. Sannu da zuwa amarya". Na yi ƙasa da kaina ina faɗin"yauwa". Ruwa da abin taɓawa ta jere mana a gaban mu cikinmu a cike yake amma yanda ta nuna damuwa da matsawar cewar lalle sai mun ci ko kaɗan ne ya sanya mu san ruwan. Hirar wajen aiki Abdul-hameed suka ɓarke dashi da ya sanya ta miƙewa ta kamo hannuna tana cewa"ba ru mu ba ku waje su yi hirarku don ba fahimtar wannan yaren muke yi ba. Amarya tashi mu shiga daga ciki".


Duk dariya suka saka kafin Abdul-hameed ya furta"ni kuwa ina Jinior na ji gidan shuru".


"Yana can wajen Umma". Ta faɗa yayin da muke barin cikin falon muka shiga wani ɗaki muka zauna muka ƙara gaisawa kana ta cigaba da faɗin "abin mamaki wai yau uncle Abdul ne har da mata". Na rusunar da kaina ƙasa"kin san ikon Allah babu abinda ya bari kuma komai in lokacinsa ya yi dole za a yi sa". Ta gyara zamanta muna fuskantar juna"haka ne domin iko Allah ne kaɗai ya isa juya wannan lamarin". Na ɗago kaina fuskana ɗauke da mamakin furcin da ta na ce"ban gane inda kika dosa ba?". Ta numfasa kana ta ce"wallahi ba ni da wani mummunan nufi amma kin ga daga ni har mai gida da ragowar abokansu babu wanda ya yi tsammanin Abdul-hameed zai yi aure nan kusa. Abokansu babu wanda bai ajiye 'ya'ya ba, haihuwata na fari bai zo da raina ba na biyu kuwa sunan Abdul-hameed aka sanya muna ƙiran sa da Jinior".




Na jinjina kaina"daman an ce aure da mutuwa lokaci gare su matuƙar ya yi babu makawa sai an yi su " Ta taɓe baki tare da cewa"haka ne, ki yi haƙuri da abinda zan faɗa miki yanzu Abdul-hameed har da ƙanwata uwa ɗaya uba ɗaya sun yi soyayya, Amma ta kafa musu ƙahon zuƙa sai da ta raba su yanzu haka tana gidan mijinta da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe. Shiyasa duk matan abokansu muka sha mamakin jin cewar ba 'yar uwarsa ya aura ba bamu yi tunanin Amma za ta bar shi ya auri wata daban ba".


Duk da maganganunta sun yi mini nauyi a ƙirjina amma na yi ƙarfin halin ƙirƙiran murmushi na dasa a fuskata, cikin sanyi na furta"dama duk lalume muke yi a cikin duhu, Allah ya riga ya tsara komai ".




"Tabbas haka ne gashi kin zama mai sa'ar samun uncle Abdul". Yanda ta yi zancen cikin zolaya ya tursasa mini sakin wani taƙaitaccen murmushin ina yin ƙasa da kaina. Daga haka ta canja zancen muka koma wani daban mun sha hira kamar mun san juna har album ɗin hotunan bikinsu da na sunan Junior ta nuna mini, sun yi bala'in kyau tufarkalla.


Bamu baro gidan ba sai ƙarfe goman dare saura, Asiya matar Auwal ta cika mini leda shaƙe da kayan shafe shafe na mata mijinta ya ɗaura mini da naira dubu biyar, na yi godiya sosai da yabawa da karamci da mutuncinsu. Haka muka taho bayan Asiya ta yi miki alƙawarin kawo mini ziyara ta musamman muka yi musayar lambobin juna.


Sanda muka iso gidan dare ta tsala don haka kai tsaye muka shige sashinmu muka ja ƙofa, daren ranar mun farantawa juna sosai na kuma sama yabo na bugawa a jarida daga wajen mijina.


Washe gari koda muka isa sashin Amma muka tarar har sun gama yin karin kumallo. Daga gaisawar da muka yi mata ta amsa a daƙila ko kallon kirki ba ta ƙara yi mana ba har izuwa lokacin da ya ƙwala ƙiran Asabe ta zo da hanzari tare da zubewa a gabansa.


"Ina abin karinmu fa?". Sai da ta saci kallon Amma kafin ta furta"uwargijiyata ba ta bada umarnin ɗaura girkin yau da ku ba".


"Subhallahi!". Ya furta a razane yana cigaba da"me ya faru haka Amma?".
"Hukunci ne na riga da na yanke tunda ka fi yarda da matarka fiye da kowa kana girka maka kawai kana ci hankalin kowa a kwance".


"Wallahi ba haka nake nufi ba don Allah ki fahimc..." Da wani irin sauri ta dakatar dashi"babu abinda zaka ce na janye hukuncin da na riga na yanke. Sanin kan ne bana yin magana biyu, don haka zuwa anjima za a kai duk wani abun buƙata sashinka sai tana girka maka". Shuru ya yi tamkar wanda ruwa ya cinye shi ya ɗagawa Asabe hannu alamar ya sallame ta, shuru ya karaɗe girman falon sai can na furta"Allah ya huci zuciyarki Hajiya". Ban iya jin abinda ta furta ba sai dai tabbas na ga leɓanta ya yi motsi. Haka ya tafi wajen aiki kamar wanda aka yi wa mutuwa.


Har fa cikin raina na ji daɗin wannan hukuncin da ta yanke ko babu komai nima zan sama 'yancin girkawa mijina abinda yake so a ko wani lokaci ba sai na jira an shigo mana dashi ba. Bayan ya tafi na ƙira Asiya muka gaisa na lura akwai ta da surutu ba na wasa ba, bayan sallan zuhr direba ya yi sallama na je na buɗe masa ya ce za a shigo da kaya.


Na'u'in kayan abinci kusan komai an kawo sai da suka gama shigarwa na je na duba, ina cikin store ɗin na ji wayata na ruri a falo na fito da sauri. Kafin na iso ƙiran ya katse ban san dalilin tsintar kaina cikin matsanancin faɗuwar gaba ba ganin sunan Abdul-hameed ya fito cikin wayar.


Na bi bayan ƙiran akalla kusan sau uku amma baya tafiya na ajiye wayar zan koma store ɗin, na ji ƙarar shigowar saƙon da ya sanya ni dawowa na buɗe.


Da lambar Abdul-hameed aka turo saƙon da ya sanya ni zaman 'yan bori dirshan ina dafe ƙahon zuciyata tare da karanto saƙon a bayyane.


"Aisha ki je gida sai na neme ki".


*ƁOYAYYAR MANUFA*


©️ Maimuna Tijjani Iyam


_________________________________


Page 3️⃣3️⃣


Take na ji wani zuffa yana tsatstsafowa mini daga dukkan mafitar gashin dake jikina, jikina ya yi lajab da ruwa. Rawar da jikina ya soma yi ya sanya wayar faɗuwa daga hannuna.


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'u!".


Kawai na yi nasarar furtawa ina sauƙe gauruwan ajiyar zuciya mai matuƙar nauyin gaske, me yasa Abdul-hameed zai yi mini haka? Me na aikata masa? . Me ya faru bayan lafiya ƙalau salin ƙalin muka rabu dashi ya fita wajen aiki.
Zumbur na miƙe tamkar wacce aka tsikarawa matsilli na fito a zabure na nufi sashin Amma a riɗime. Anty Alawiyya kawai na iske a falon tana kallo ta bi ni da ido da yi mini alaman lafiya.


Na yi ƙasa da kai na ce"Amma tana ciki ne?".
"Lafiya?". Kamar na kurma ihu saboda Amman kawai nake da buƙatar gani a yanzu na amayar mata da zancen da yake sukan raina.


"Ki haura sama tana ciki" bata gama rufe bakinta ba na bar wajen, a ƙofar ɗakin na tsaya ina ƙwanƙwasawa tun ina yi a hankali har na zage ƙarfina ina dukan ƙofar sai can ta amsa mini sallamar da nake kwaɗawa.


Na shiga ɗakin kamar wacce aka jefo daga sama muka haɗa ido, da alama daga wanka ta fito don mai take murzawa a jikinta tana zaune a bakin gadonta. Na ƙariso na zauna na fara inda-inda, ta riga ni furta"Lafiya? Na gan ki duk a birkice?".


Idanuna ya kawo ruwan ƙwalla muryata yana sarƙewa na ce"wani saƙo na ga ni da ya tada mini da hankali".
"Wani kalan saƙo ne?".


"Saƙo ne aka turo mini da lambar Abdul-hameed cewar wai na je gida sai ya neme ni. Na ƙira layinsa don ji daga gare shi wayarsa ba ta tafiya, na san baya aiwatar da komai ba tare da sanin ki ba shiyasa na zo na tambaye ki sahihacin saƙon". Ban tsinci komai a fuskantar ta hasalima biris da yi da ni duk da muhimmancin zancen da na zo mata dashi, sai can a gajarce ta furta mini"na ga saƙon".


Na laluma jikina babu waya sai a lokacin na tuna tsabar rikicewar da na yi na mance wayar a falo ban fito da ita ba. A hankali na furta"na bar wayar a falo bari na je na ɗauko". Ban ɓatawa kaina lokaci wajen jiran amsarta ba domin ban yi tunanin samun sa daga gare ta ba, na miƙe har na kai ƙofar fita na ji ta furta"Aisha ki sama mai nutsuwa" kaina kawai na ɗaga mata na fito ina yi kiciɓus da Anty Alawiyya tana shigowa, da gudu-gudu na isa sashina na ɗauko wayar na fito. Jikina har rawa yake yi na miƙa mata wayar ta sanya hannu ta amsa tana karanta saƙon a bayyane.


Ban ankara ba na ji wasu hawaye masu zafi su na gudun famfalaƙi a bisa dandamalin kuncina, sai da ta _kammala tsaf ta sauƙe numfashi kana ta ce"to yanzu me kike so daga gare ni?".
Na kai hannu na share hawayen fuskana kafin na sama damar faɗin"na ƙira wayansa ba ya tafiya ne ko za ki ƙira shi".


"Babu abinda zan iya yi akan wannan lamarin Aisha, na yanke hukuncin zare hannuna daga lamarin aurenku. Abdul-hameed mijinki ne kuma yana da ikon zartar da duk wani hukunci game da lamarin gidansa. Indai za ki ji shawaran da zan ba ki to kawai ki tafi tunda ya shi ya nema hakan, ko dan jan mutunci da darajarki".


Ban san sanda wani gigitaccen kuka ya kubce mini ba na kai hannuna na toshe bakina. Babu wanda ya ce dani ci kanki a cikin su har na yi mai isa ta na tsagaita don kaina na miƙe ina jin wani jiri yana ƙoƙarin maida ni ƙasa.


"Na gode, idan na aikata miki wani abu da ya ɓata miki a tsawon zaman da muka yi. Ina neman yafiyarki". Ta ɗago idanunta ta kalle"babu abinda kika yi min". Ta ƙare zancen tana miƙo mini wayata dake hannunta na karɓa na fice, ina isa sashina na zube a ƙasa ina jin wani irin zafi a cikin zuciyata. Kamar mahaukaciya haka na dunga ƙiran layin Abdul-hameed amma baya shiga dole na haƙura na ajiye wayar.


Na shiga ɗakina ina bin ɗakin da kallo da tunanin yanda zan tunkari iyaye da wannan lamarin mai girman gaske, zancen Baffa ya faɗo mini a rai tamkar faɗuwar aradu na dafe ƙirjina hawaye suna zubowa daga idona.
Hamma Ahmad shi ya fara faɗo mini a rai na zabura na ɗauki wayata na danna masa ƙira. Har ƙiran ya katse mai ɗauka ba ina shirin danna masa ƙiran a karo na biyu ƙiransa ya shigo wayata da sauri na ɗauka ina jin muryarsa na fara kuka.


"Subhallahi! Aishatu lafiya? Me ya faru?".


Na kasa cewa komai jin hanyar wuyata nake yi kamar an sanya igiyar kirtani an zarge mini wuyata, sai da na fizgo numfashina kafin na sama zarafin faɗin"kana gida ki kasuwa?".


"Ina kasuwa amma lafiya?".


"Su Baffa fa?". Muryarsa fal da damuwa ya ce da ni"daga ni sai Adnan".
"Ga ni nan zuwa". Na faɗa wani kukan yana ƙara yunƙuro mini dole ba kashe wayar na ci kuka har na godewa Allahna, har aka fara ƙiran sallan Asr ina durƙushe a wajen. Na ƙyar na iya miƙewa akan ƙafata na sauƙo da ƙaramin akwatin laifena na zuba kayana, dubu biyar da jiya mijin Asiya ya ba ni da su na yi amfani na hau abin hawa na isa kasuwa. Na nufi shagon su Hamma Ahmad ban iske kowa a shagon ba na yi sallama a wani dake kusa da wajen na tambaye shi ya ce sun tafi masallaci sun ce idan na iso na shiga na jira su. Na yi masa godiya na shiga na zauna.


Jin ana ƙwala ƙiran sunana da ƙarfi shi ya dawo da ni izuwa duniyar zahiri daga na tunanin da na lula, na sauƙe sakekken ajiyar zuciya ina ɗauke idona daga kallo ɗaya da na yiwa fuskar Hamma Adnan.
Sai da suka zauna Hamma Ahmad ya ce"lafiya me ya faru? Tunda kika ƙira ni hankalina ya kasa kwanciya sai saƙe-saƙe nake yi". Ya ƙare zancen yana tsayar da idonsa akan akwatin kayana dake kusa da ni.


"Magana fa ake yi miki". Hamma Adnan ya furta da hakan ya sanya ni yi ƙasa da kaina ina faɗin"cewa ya yi wai na taho gida".


"A wani dalilin? Me kika aikata masa? Wani laifi kika yi masa da zai ce ki taho gida?. Ko takardarki ya ba ki?". Ya jere ya watsa mini tambayoyin na girgiza masa kaina ina ɗaurawa da" saƙo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login