Showing 1 words to 3000 words out of 80635 words

Chapter 1 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

 ƁOYAYYAR MANUFA


©️Maimuna Tijjani Iyam


Bismillahir rahamanir rahim da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, maƙagin rayuwata. Wanda cikin ikonsa, yardarsa, amincewarsa tare da aron numfashin da ya bani na rubuta wannan littafin na ƁOYAYYAR MANUFA. Bayan kammala littafin MATAN AREWA. Ina roƙon Allah da ya tsare mini hannayena, wajen rubuta abinda zai zamu cutar ga al'ummar musulmai tare da tarbiyar su.


Page 0️⃣1️⃣




_______________________________________




Fizgar da aka yi wa hanayena tamkar za'a tsinke su daga gangar jikina, ya sanya hankali da nutsuwata da suka yi ƙaura daga gare ni dawowa. Sai a lokacin na sama zarafin calla wani uban ƙara mai matuƙar sauti, dukan da aka rufe ni dashi ta ko'ina ya sanya sautin kukan nawan dishashewa.
Jefar da aka yi da ni gefe guda ya tilasta mini runtse idanuna da jinin dake zuba daga goshina da na ke jin wani azabar zogi. Yana wanke mini fuskata, jin raɗaɗin da ya ratsa kwanyata shi ya tabbatar mini da cewar haƙata bata cimma ruwa ba. Fatan mutuwar da nayi wa kaina ubangijina dake da ikon sarrafa rayuwata bai amshe ta ba.


"Kin cuce ni Aishatu na yi da-na-sanin auren ku da Abdul-hameed. Ashe ajalinsa ne yake zaune da ita".


Zancen da suka yi dirar mikiya kenan a kunnuwana, da na gaza tantance takamanmen mamallakin muryar. Sai dai tabbas amon ba baƙuwa bane ga kunnuwana. Dishi dishi idanuna suke gane mini 'yan uwan mijina Abdul-hameed da suke tsaye cirko cirko a kaina babu alamar ranƙwafawa, tamkar sun haɗiye taɓarya.
Na gaza kare kaina daga dukan da suka cigaba da yi mini, balle na sama yawun da zan sarrafa wajen furta kalaman kare kaina daga mummunar zargin da suke jifa na dashi. Cushewar da numfashi ya fara yi tare da maƙalewa a ƙirji ya sanya idanuna fara gano mini baƙin duhu yana gilmawa.


Jiniyar motar 'yan sandan da na ji ya yi dai dai da tsananta bugun da ƙirjina yake yi a raunane. Surutai da koke koke suka ƙara karaɗe wajen kafin na ji an ɗago ni cak an dire ni akan ƙafafuna da suke rawa.


Hannayena duka biyu aka sanyawa wani abu, da nake kyautata zatona cewar ma'aikatan tsaro ne suka sanya mini ankwa. Kamar yanda na ji wata murya tana faɗin"ga ta nan ita ce ta kashe shi".
Da ƙarfin rabussamawati aka finciko ni kukan tagwayen 'ya'yana Ashraf da Arfat 'yan watanni takwas a duniya da na same su bayan na shafe shekara cur da watanni a gidan mijin, suka dira a kunnuwana. Da ya tursasa mini wartsakewa nan take. Jin sun ƙammame ni ya sanya ni sakin sakekken ajiyar zuciyar da ya tafiyar da kukan zucin da nake yi. Ina ji ina gani aka ɓanɓare su daga jikina ni kuma aka jawo ni izuwa waje. Maƙil ƙofar gidan yake da mutanen da suke yi mini tofin ala tsine tare da Allah wadarai da halina.


Kukan da ya zo mini da ƙarfin gaske da kuma jan dogon numfashin da nayi, ya yi dai dai da lokacin da na daina fahimtar komai. Saboda daina bugun da ƙirjina ya yi.


Sai buɗe ido na yi na gan ni kwance cikin wani ɗakin da na ƙarewa kallon tsaf. Tabbas asibiti ne ga kuma ƙarin ruwa a maƙale a hannuna. Kuka na fashe dashi mai tsuma zuciya fahimtar da na yi cewar tabbas har yanzu ina raye cikin duniyar da ƙunci da halin ƙaƙayi kayi suke yi mini dabaibayi, yunkurar da na yi da nufin tashi zaune na ji kamar an riƙe mini hannuna ɗaya. Shi ya sa ni kai dubana izuwa ɓangaren, ankwa ne saƙale a hannun a saka a cikin gadon da nake kwance a kai.


Dole na koma na kwanta don izuwa yanzu na rasa ƙarfin tashin, tuna abubuwan da suka wakana da nake jin wanzuwar su tamkar a cikin mafarki ya sanya kaina sarawa.


"Innalillahi wa inna ilaihir".


Shi kaɗai bakina ya yi nasarar furtawa ina cije leɓena, wata irin ƙaddara ce wannan ta gilma a cikin rayuwata?. Tare da rushe duk wani gini da foundation ɗin da na yi, wajen ganin inganta rayuwar aurena da ta 'ya'yana masu tasowa.


Hannuna da aka sanyawa ƙarin ruwan na ƙurawa idanu, raina a jagule wai da wannan hannun na yi amfani wajen daɓawa Abdul-hameed wuƙar da ta yi sanadin rayuwarsa. Kaicona! Tabbas na yi saƙa da mungun zare. Na yi saurin rufe idanuna da yake gano mini Abdul-hameed kwance cikin jini.


Na daɗe cikin wannan yanayin har izuwa lokacin da aka buɗe ƙofar ɗakin aka shigo, maza ne biyu ɗaya sanye da rigar likitoci ɗayan kuma cikin cikakken shirgar 'ya sanda. Duba ni likitan ya yi sannan ya juya haɗe da faɗin"za ku iya tafiya da ita tunda ta farka".


Take na ji kaina ya juya na daina fahimtar komai, har wata ma'aikaciyar 'yan sanda ta shigo. Ta since mini ankwan ta riƙo ni muka fice daga ɗakin. Duk da idanuna suna ƙasa amma tabbas ina ji a jikina irin kallon da jama'ar wajen suke bi na dashi har aka shiga dani motar 'yan sandan muka bar cikin harabar asibitin.


Tunda na shiga cikin motar hawaye suke kwaranya daga idanuna, zuciyata na yi mini wani irin zogi da suya. So na ke na sama ƙwarin gwiwar tabbatarwa kaina cewar a zahiri abubuwan da nake kallon su tamkar mafarki suke faruwa. A ofishin 'yan sandan da ya cika da ma'aikatan gidan jaridu motar ta tsaya aka fito dani, tunin suka yi mini rubdugu tare da jefo mini tambayoyi wani na bin wani.


"Me za ki iya cewa akan zargin kashe mijinki da ake yi miki?".


Tambayar da na ji ta har cikin kwanyata daga bakin ɗaya daga cikin 'yan jaridun kenan. Ma'aikatan tsaron suka hana su ƙarisowa gare ni tare da shigar da ni cikin ofishin. Mahaifiyata tare da yayyena maza biyu Hamma Abubakar da Hamma Adnan idanuna suka yi tozali da su tsaye a cikin ofishin.


Muna haɗa ido na ji wasu hawayen masu ɗumi su na fareti a bisa dandamalin fuskata. Fuskar Ummata ta kumbura tsimtim, ga damuna da firgicin da ya bayyana ɓaro ɓaro a fuskokin su. Da sauri ta iso gare ni tare da tallafo fuskana tana faɗin" me yasa, me yasa?. Me yasa kika aikata wannan ɗanyen aikin?".


"Umma wallahi ban aikata ba, ban kashe Abdul-hameed ba. Ku yarda da ni".


Na faɗa cikin dushashewar muryata da bata fita sosai. Kafin ta kai ga furta mini wani kalmar wani ɗan sanda ya kaɗa ƙeyata izuwa cikin cell. Cikin kuka Umma ta zube akan gwiwoyinta haɗin da cewar"don Allah ku bar ni na yi magana da ita 'yata ce ƙwalli ɗaya jal".


Cikin halin ko in kulawa da rashin tausayi ya furzo mata zancen da ya sanya duk gaɓoɓin jikin sakewa. "To tun wuri ma ki cire ta daga ranki ki manta da cewar kina da wata 'ya mai kamar ta. Domin wannan kam na tabbatar da cewar ana zuwa kotu, hukuncin kisa alkali zai yanke mata. Ku yi ta haihuwar 'ya'ya sakaka kamar fari ku ka sa basu tarbiyyar da ta dace su zo su zama annoba ga al'umma gabaɗaya. Da haihuwar irin wannan ai gwara ɓarin cikinta".


Duk da babu abunda na fi buƙata a yanzu fiye da mutuwata, sai dai ganin yanda zancen nashi ya ƙara sanya Umma da 'yan uwana cikin wani tashin hankali. Na yi takaicin kasancewa ta a raye, nayi nadamar ganin wannan ranar a cikin rayuwata. Ranar da na jefa duk wani makusancina cikin mungun yanayi. Kalman na san ya sanya Umma yanke jiki ta faɗin a wajen sumammiya, ma'aikatan suka dakawa su Hamma Abubakar tsawa tare da umartar su da su ɗauke ta su fice daga wajen.


Dole na zame nayi zaman 'yan bori dirshan a ƙasa. Izuwa yanzu na kasa yin hawayen ma sai kukan zuciya da nake yi. Kaina ya shiga sarawa tamkar zai rabe gidan biyu. Duniyar ta yi mini zafin da komai na cikinta ya gundure ni, jikina ya ɗauki rawa tamkar ana jona mini wutar lantarki.


"Ban kashe Abdul-hameed ba, ban kashe Abdul-hameed ba".


Zancen da nake maimaitawa kenan a cikin zuciyata domin nauyin da bakina ya yi mini. Da nake jin ba zan iya furta ko kalma ɗaya ba, ban san iya tsawon lokacin da na ɗauka ina faɗin wannan kalmar ba. Har izuwa lokacin da aka buɗe cell ɗin, ban ɗago kaina ba sai dai na ji tsayiwar mutum a kaina. Na fita daga hayyacina sam babu nutsuwa a tare da ni tun ina furta cewar ba ni na kashe Abdul-hameed ba a cikin zuciyata har sautina ya fara fita.


"Ki nutsu".


Da sauri na ɗago kaina ina ƙarewa jami'in ɗan sandan dake tsaye a kaina, na ce"ba ni na kashe shi ba wallahi ban kashe shi ba".


Bai ce dani komai ba sai da ya tsuguna akan ƙafafunsa a gabana sannan ya furta"na ji ba ke kika kashe shi ba, meye sunan ki?". Na sauƙe ajiyar zuciya" Abdul-hameed".


Sai da ya ƙare mini kallon tsaf kana ya juya ga ma'aikacin dake bayan sa ya ce"a kai ta ta yi wanka, ta canza kaya sannan a bata abinci ta ci. Kafin nan ta dawo hayyacinta sai da amsa mana tambayoyinmu".


"Ok sir".


Ya furta cikin tsantsar biyayya tare suka fice sannan wata mace ta shigo. Ta kai ni na yi wanka sannan na canza kaya, abinci kam inda ta dosara mini shi ko kallon shi ban yi ba. Hawayena sun kafe ko ina kukan basa zuba, tabbas ina cikin tsaka mai wuya. Halin da mahaifiyata take ciki a yanzu shi ya fi ɗaga mini hankali fiye da makomar tawa rayuwar, domin ni kam na san shan ruwana ya ƙare a cikin wannan duniyar.


Sai da dare ya tsala na ƙara shiga mawuyacin halin, tunanin yarana da abincin su yake zuba daga jikina ya tsaya mini a rai. Ko yanzu su na wani hali oho, ko sun ci ko basu ci ba duk ban da masaniya akan hakan. Sai da gari ya waye wannan ma'aikaciyar ta dawo, sai da ta gama jefa mini kallon tsana kafin ta soma yi mini magana a tsawace"yanda na ajiye abincin haka kika bar shi kenan?, in kin ci ma kanki ki ka yiwa ba wani ba. Munguwa kura da fatar akuya. Allah wadaran ki".


"Ina so na yi salla".


Tabbas na ga tsantsar mamaki a bisa fuskarta ta taɓe tare da faɗin"kin san da wanda za ki yiwa sallan, amma kika manta dashi a lokacin da zuciyarki take yi miki saƙa da mungun zare. Duk wanda ya kashe rai shima hukuncin kisa ne akan sa kin san da hakan?". Ban ce da ita ko kanzil ba har ta gama ta fita bayan ta tsirtar da wani tsaki mai dogon zangon. Waige waige na soma yi ko zan sama ƙasan da zan yi taimama dashi a cikin ɗakin, amma ban ga alamar sa ba dole na miƙe ina jin wani jiri yana ɗeba ta na zo jikin ƙarfe ɗakin da yake bani damar hango inda ma'aikatan suke tsatstsaye.


Sai da na yi baki ya fi a irga sannan wani ya zo inda nake, tare da yi mini gargaɗi kar na ƙara damun su. Dai dai lokacin da wannan ma'aikacin ya shigo wajen duk suka miƙe suna sara masa cikin girmamawa. Ya tambayi dalilin tsayiwata a wajen suka sanar masa, take ya basu umarnin samar mini da ruwan alwala, hijabi da kuma sallaya.


A zaune na yi sallan saboda bana iya miƙewa akan ƙafata jiri yake mayar da ni ƙasa, na kasa furta komai illa rawar da bakina yake yi na ɗaga hannayena duka biyu sama. A hakan wannan ma'aikacin ɗan sandan ya shigo ya iske ni, duk tambayoyin da ya yi mini babu wanda na amsa domin ba na jin ko na yi yunƙurin amsa masa zan sama haɗin kai daga bakina wajen furta zancen dake zuciyata, ko zan rage zogin da nake ji.


Ganin ba zan iya amsawa ba ya tilasta masa ficewa daga ɗakin, haka na cigaba da zama na kwana na wuni a wajen kafin aka zo ka sanya mini ankwa a duka hannayena aka fito da ni izuwa wani ɗaki. Ina shiga na ga Umma da Hamma Adnan zaune, da gudu na isa gare ta na durƙusa a gabanta, tare da ɗaura kaina akan cinyarta.


A hankali take bubbuga bayana hawayen da suke kwaranya daga koramar idanunta, suna sauƙa a bayan wuyana.


"Aishatu".


Ta furta kalmar sunana cikin karayar murya, a karo na farko da taɓa ƙirana da Aishatu kai tsaye babu sakayawar da ta saba. Ban iya amsa mata ba saboda kukan da ya ci ƙarfina. Ta cigaba da cewa"kowa sai faɗin albarkacin bakinsa yake yi akan ki, wasu sun ce kishi ne ya rufe miki ido kika ɗauki wannan hukuncin. Me yasa kika aikata haka?". Kukan na cigaba dashi da dukkan ƙarfina kafin na yi nasarar ɗauko kaina da ya yi mini nauyin gaske, na sauƙe rinannun idanuna akan fuskarta." Ban kashe shi ba ban kashe ba. Umma bai mutu ba fa.


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'u".


Hamma Adnan ya furta yana dafe goshinsa, daga ni har Umma kuka muke babu mai lallashin wani.


"Time up, lokacinku ya yi ku tashi ku fita".


Ma'aikacin ɗan sandan dake tsaye a kan mu ya furta a zafafe tare da ƙirar wacce ta shigo da ni tazo ta maida ni. Da sauri na rarrafa gaban Hamma Adnan na ce" ina Baffa?". Kafin ya amsa mini har ta shigo ta ɗago ni zamu fice. Amsar da ya ba ni ya tsaya Ni tsayawa cak.


"Ki yi haƙuri Baffa ya ce bai zai tako yazo inda kike ba".


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam


Page 0⃣2⃣


____________________________________


Har aka komar dani cikin cell ɗin ban san inda nake cilla ƙafafuna ba, ina shiga jiri ya makani da ƙasa. Na dafe ƙahon ƙirjina da yake bugawa a raunane, zuffa yana tsatstsafowa daga dukkan mafitar gashin dake jikina. Take numfashina ya fara yi sama sama, ina jin ƙirjina tamkar an ɗaura mini dutse tsabar nauyin da ya yi mini.


A hankali na soma buɗe idanuna da suka yi mini nauyi ina motsa jikina da ya sake. Lumshe idanuna nayi hawaye suna bin gefe da gefen fuskana, ƙwaƙwalwata tana tariyo mini amsar da Hamma Adnan ya ba ni. Zuciyata ta ƙara karyewa.
Rayuwar ya ƙara ficewa daga raina gabaɗaya tunda mahaifin da ya haife ni ma ya yanke mini wannan hukuncin ba tare da ya ji daga gare ni ba, to ina ga sauran al'ummar da nake rayuwa a cikin su?. Take zuciyata ta ayyana mini kawai na amshi abunda ake zargina dashi domin shi ne kawai mafita a gare ni.


Sai da nayi kwana biyu a asibiti ƙarƙashin kulawar ma'aikatan lafiya da kuma jami'an tsaro, a rana na uku aka wuce dani kotu. Tun daga sauƙa na daga cikin motar 'yan sandan jama'a suka yi mini ca tamkar zasu cinye ni ɗanye. 'Yan jaridu kowa na san samun abun yaɗawa, sauran jama'a na yi mini tofin ala tsine da jifa na da munanan alkaba'i, sai da 'yan sandan suka kewaye ni daga dukan da mutane suke kawo mini sannan muka shiga cikin kotun.


A tarihin rayuwata kaf ko ƙofar ofishin 'yan bijilanti ban taɓa zuwa ba, amma ƙaddara ya sa ni yau ni ce da kwanan ofishin 'yan sanda har da zuwa kotu.


Maƙil kotun yake da jama'a bayan a nuna mini cikin inda zan tsaya, na soma rarraba idanu ko zan gano wani nawa. Can na gano Hamma Adnan da Hamma Abubakar sai kuma Baba Alhaji ƙanin Abbanmu da 'yansa Hamma Ahmad da Anwar su kenan waɗanda na sa ni cikin dandazon jama'ar da suka yi tururuwa a kotun. Ban hangi ko kare daga dangin Abdul-hameed ba.


Magatakardar kotun ne ya tashi ya gabatar da shari'ar tare da miƙa wasu takardu ga Alkalin, sai da ya gyara zaman farin gilashin dake zaune akan karan hancinsa kana ya ce"lauyan gwamnati ya gabatar da kansa". Ya miƙe yana cewa"sunana barrister Adam Lawan lauyan gwamnati daga chamber na ɗari uku da ashirin da biyu, na gode ya mai girma mai shari'a". Sai da Alkalin ya yi wasu rubuce rubuce kafin ya ɗago ya kuma faɗin"lauyan wacce ake zargi ya gabatar da kan shi".


Babu wanda ya tashi da sunan kare ni hakan ya haifar ƙananun surutai. Sai da Alkalin ya tsawatar ta hanyar buga karamar gudumar dake hannunsa.
"Ina lauyan da zai kare ki?".


Ya jefo mini tambayar da ya sanya ni haɗiye wani miyau mai kauri daga maƙoshina da ya bushe, tamkar tafkin da ƙasa ya tsotse ruwan cikinsa. A sanyaye na furta "ya mai girma mai shari'a ba ni da lauya". Shuru ya biyo bayan zancena na tsawon daƙiƙu kafin ya furta"sakamakon rashin lauya daga ɓangaren wacce ake ƙara, an ɗaga wannan shari'ar zuwa ashirin da takwas ga watan afrilun shekaran dubu biyu da ashirin da huɗu". Yana dasa aya ya buga gudumar kowa ya miƙe, sai da ya fita ta wani ƙofa sannan mutane suka fara fita. Aka sa mini ankwa aka tisa ƙeyata.


Har yanzu harabar kotun a cike yake da jama'a, su Hamma Abubakar suna tsaye suna jiran fitowata. Suka iso gare ni da hanzari.


"Ki yi haƙuri kin ji ki ta addu'a, in sha Allah zamu sama lauya kafin zama na gaba".


Furcin Baba Alhaji ke nan yayin da za'a tusa ni a cikin motar na yi saurin riƙe hannun Anwar gam ina sakin wani kuka marar sauti. Suma kukan suke yi Baba Alhaji yana lallashin mu, haka aka sanya ni cikin motar ina hangen su har suka ɓacewa ganina. Ba'a mayar da ni ofishin 'yan sanda ba aka wuce da ni gidan ajiye ɗaurarru. Na ci kuka tamkar raina zai fita na rasa inda zan sanya raina na ji sanyi, kwana huɗu cur a wajen babu wanda yake zuwa inda nake sai 'yan sandan da suke kawo mini abinci da kuma ruwar yin alwala.


Ina takure a ƙurriyar ɗakin na kifa kaina a bisa gwiwoyina, tunanin lokutan da muka ƙarar tare da Abdul-hameed na nunawa juna so da tattali suna ziyartar kwanyata. Zuciyata ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login