Showing 42001 words to 45000 words out of 80635 words
Chapter 15 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt
kallon da na gaza gano ma'anar sa, zuciyata ta buga da ƙarfi me bawan Allahn nan yake nufi da ni ne?.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimuna Tijjani Iyam
__________________________________
Page 2️⃣2️⃣
Kwana biyu a tsakani ina juyayin lamarin na Al'amin duk da dama can babu maganar da take haɗa mu. Amma yanzu ko a bisa kuskure muka haɗa ido dashi sai kallon banza sai harara.
Kaina ya ɗaure da kaina na ƙara birkita kayan ɗakina kaf da nufin gano abinda Al'amin yake nema amma ban gan komai ba. Na kasa yin maganar da Abdul-hameed domin ban san ta inda za fara ba.
Da sallama na shigo falon ina dire kofin ruwan da na kawo masa a gaban sa, na yi masa sannu ya amsa mini fuskarsa tamkar gonar auduga. Cike da sha'awa nake kallon zanen foundation ɗin gidan da yake zanawa.
"Gaskiya kuna ƙoƙari sosai". Na faɗa ina ƙara kallon zanen, ya murmusa kana ya ce"bashi da wani wahala ai".
"Haka dai ka ke gani don ka iya". Ya miƙa mini alƙalamin"karɓi ki yi kema za ki tabbatar da rashin wuyarsa da nake faɗa".
Na waro idanuna waje"tab ai sai dai na ɓata maka". Ya saki dariya mai sauti yana ɗaukar kofin ruwan da na ajiye masa ya kafa a bakinsa. Sai ya shanye tas ya ajiye ya turo mini zanen gabana yana faɗin"kin ga wannan structure ɗin gida ne mai hawa biyu ako wani hawa akwai ɗakuna huɗu, falo ɗaya, banɗaki biyu da kitchen sai kuma filin tsakar gidan. Yanzu idan na kai wannan zanen ma'aikata zasu duba shi kafin a miƙawa magina su kuma samar dashi kamar yanda na nuna miki".
Na jinjina kaina cike da gamsuwa da maganar nasan na ce"wani aikin sai mai shi, ban taɓa tunanin idan za a yi gini sai an zana shi a fefa ba kafin a tsara shi".
"E to kin san kullum ƙara samun cigaba ake yi technology yana shigowa. Shiyasa yanzu idan kin lura akwai bambamcin tazara mai yawa tsakanin gine-ginen da da kuma yanzu".
Ya ƙare zancen yana jawo ni jikinsa na tuno baki gaba zan yi magana ya ɗaura mini yatsarsa akan leɓena yana faɗin"shit". Dole na yi shuru domin na lura a duniya kaf babu abinda ya fi tsana kamar gardama tunda na fahimci hakan na yi wa kaina alƙawarin ba zan taɓa yin musu dashi ba.
Yawon da yake yi da hannunsa akan fuskata yana zarcewa izuwa tudun wuyata ya hana ni cewa ko kanzil. Sallamar Asabe ya sanya mu dawowa cikin hankalin mu na yi saurin janye jikina ina matsawa gefe guda, har ta riga ta shigo cikin falon kanta yana ƙasa ta gaishe shi. Bai amsa ba ya fara faɗin"lafiya za ki shigo kan mu haka? Akwai wata matsalar ne?".
"Afuwan ranka ya daɗe, Uwargijiyata ce ta zo na ƙira mata Aisha"
A bayyane ya tsirtar da siririyar tsaki"je ki zata biyo bayanki". Kanta har yanzu yana ƙasa ta fice.
Ya juyo ya kalle ni"ki je ƙiran Amma bari nima na tashi na shiga wanka na fita wajen aiki".
Kaina kawai na ɗaga masa zan miƙe ya yi saurin riƙe mini hannayen yana lumshe idanunsa ya ce"ki dawo da wuri".
Na yi fari da idanuna na miƙe na fita tare da nufar sashin Amma, babu kowa a falon sai Anty Alawiyya da na iske ta na waya. Na yi mata sannu ta zare wayar daga kunnenta ta amsa mini a gajarce ce ta ce da cewa da ni na haura sama Amma na jira na a ɗakinta.
Gabana ya faɗi ya yi ras tun da aka kawo ni gidan ƙafafuna basu taɓa wuce cikin wannan falon ba a sashin natan. Haka nan kawai na tsinci kaina cikin matuƙar fargaba na haura benin ɗakuna uku ne ɗaya a tsakiya biyun kuma daga gefe, na tsakiyan da yake kallona na nufi na tsaya daga ƙofar ina yin sallama.
Sai da na yi baki huɗu har zan juya na koma kasa na sanar da Anty Alawiyya cewar ban gano ɗakin ba, sai na ji an amsa mini tare da bani izinin shigowa. Na turo ƙofar a hankali tana zaune a bakin tankamemen gadon da ya ji bargonan alfarma tana kallon hotuna.
Na zauna akan kafet na yi ƙasa da murya na ce"sannu da hutawa". Kanta kawai ta ɗaga mini na kuma cewa"Baaba Asabe ta sanar da ni saƙon ki shiyasa na yi hanzarin zuwa".
Duk da kaina yana ƙasa amma jikina ya bani cewar tabbas ni take kallo, sai da ta ja dogon lokacin kana ta ce"ina mijinki?".
"Na bar shi zai shirya ya fita wajen aiki".
Ta jinjina kanta tana ajiye hotun dake hannunta akan dirowar dake kusa da gadon"wani aiki zan saka ki".Na gyara zamana ina sauraronta da kyau.
"Ɗauki wancan ledar garin magani ne da nake son ki zuba mishi a cikin ruwan wanka".
Ƙirjina ya buga da ƙarfi tamkar zai fito waje. Na ɗago kaina ina kallon ta ita ɗin ni take kallo na ce"magani kuma? Na menene?".
Kai tsaye ta furta mini"ki kwantar da hankalinki ba na cutarwa bane, ina da damar da zan iya aiwatar da hakan ba tare da sanin ki ba amma na zaɓi na sanar dake domin kema zuwa gaba za ki haifa kuwa za ki zama uwa. Za ki so 'ya'yan da za ka haifa su yi miki biyayya to wannan ƙulin maganin yana daga cikin abubuwan da zasu taimaka wajen samun cikakken biyayya daga 'ya'ya".
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Ki yi haƙuri Amma kamar asiri ne fa wannan. Abdul-hameed ya kasance mai tsananin biyayya a gare ki akan dukkan komai, wallahi ko yaushe cikin labarta mini yanda yake son faranta miki yake duk tashin daren da zai yi sai ya yi addu'ar Allah ya ba shi abinda zai kula dake. Don Allah Amma kar ki aikata haka a gare shi gwara ki yi masa addu'ar Allah ya sanya tausayinki a cikin zuciyarsa ya bashi ikon sauƙe haƙkinki dake kan sa".
Tunda na fara maganar ta ɗauƙe kanta daga kaina har na kai aya bata ce da ni uffan ba. Kwantattun hawayen da suka ciko idanuna suka zubo na yi saurin kai bayan hannuna na share su. Har na cire rai da samun amsarta na ji ta furta" ban ƙira ki na sanar dake sirrina don ki karanto min wannan zantukan nakin ba, yaushe kika haɗu shi da zai nuna min cewar kin fi ni son sa?. Ni na ɗauki cikin Abdul-hameed na yi naƙudarsa na shayar dashi na yi ɗawainiyya dashi har ya kai munzalin iya bambamce tsakanin hagu da damarsa. Babu wanda zai nuna masa soyayya fiye da wanda nake yi masa".
Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau sai ko meye zata faɗa mini bana jin zan iya aikata abinda take so na yi. Zancenta ya katse mini hanzari"zan iya aiwatar da hakan ko da sanin ki ko akasin hakan, amma tunda kin bijire tashi ki bani waje zan nema wani hanyar".
Wata zuciyar ta ya mini cewar idan ma ban amshi wannan tayin da ta yi mini ba, to tabbas zata bi ta wani hanyar kamar yanda ta faɗa don ganin ta cimma ƙudurinta. Haƙiƙi na yi imanin cewar babu wata uwar da zata so ganin ana cutar da ɗan da ya rayu a cikin cikinta ya tsaga naman jikinta ya fito balle a ce ita da kanta ta iya cutar dashi.
Na sauƙe bayyanannen ajiyar zuciya kafin na zama zarafin faɗin"shikenan zan yi duk abinda kika sa ni in sha Allah".
"Da kin kyautawa kanki. Yanzu ba za ki gane duk abinda zan faɗa miki ba sai lokacin da kika haifa kika ajiye 'ya'ya a gaban ki". Ban ce da ita komai ba na kai hannu na ɗauki ƙulin maganin, ta ƙara jaddada mini cewar a ruwar wanka zan zuba masa. Na fito na tsaya ina juya ƙulin maganin a hannuna zuciyata cike fal da wasi-wasi.
Tuna cewar Abdul-hameed yana jira na ya sa ni ɓoye maganin a cikin aljihun doguwar rigar dake jikina na sauƙa ƙasa da sauri.
Murmushin da ya bayyanar da fararen haƙwaranta Amma ta saka a bayyane ta furta"da alama wannan ba za ta yi wahalar kamuwa ba".
Lokacin da na sauƙo Anty Alawiyya ta tashi daga falon. Jin na yi karo da mutum ya sa ni saurin ja da baya.
"Ke ba ki da hankali ne?". Al'amin ya furta a zafafe yana watsa mini wani kallon tsana tare da karkaɗe inda na jikina ya taɓa shi.
"Ka yi haƙuri ban lura bane". Na faɗa ina ficewa daga falon da sauri ina jin kalmar bagidajiyar da ya jefa mini amma ban waigo ba na nufi sashina.
Sai da na fara shiga ɗakina na ɓoye ƙulin maganin a cikin kayana sannan na wuce ɗakinsa. Yana tsaye yana kallo cikin harshen turanci na iske shi, na haɗe hannayena waje guda alamar ban haƙuri sannan na nufi wajen kayansa na ciro masa komai.
Daidai sanda ya gama wayar yana ajiye ta na isa gare shi ya zauna ina murza masa mai a fatarsa. Ya riƙe hannuna hakan ya sa ni ɗago idanuna na yi masa kallon ido cikin ido.
"Me kuka tattauna da Amma?".
Na yi ƙasa da idona ina cigaba da shafa masa man na ce"tattaunawa ce irin ta uwa 'yarta, sai kuma shawarwarin da ta ba ni da zasu amfane mu gabaɗaya wajen tafiyar da zamantakewar mu".
"Allah Sarki Amma tana son duk wani abunda nake so. Shiyasa kullum nake addu'ar Allah ya bani ikon faranta mata". Jikina a sanyaye na ce"Amin". Sai da ya shirya tsaf na rako shi har jikin motarsa muka yi sallama kamar kullum na na yi masa tarin addu'o'i.
Sai da na ga ficewar motarsa sannan na koma ciki kaina tsaye na wuce ɗaki. Na kasa zama sai safa da marwa nake na yi, na kai mafi na kai bango kamar yanda na gaza gano manufar Amma na son aikata hakan.
Shirif na zube akan gado ina mayar da numfashi Indai ba so take yi ya fara yi mata sujjada ba dukkan wani biyayya yana yi mata, zan iya rantsuwa da ban taɓa ganin ɗan dake yi wa mahaifiyarsa irin biyayyar da Abdul-hameed yake yi wa Amma ba.
A kwanakin nan hatta abinci ya koma ci tare da ita a cewar sa daman can tare suke ci, duk da tana da direbanta amma idan zata fita ko ina yaje sai ya dawo ya kai ta kuma ya jira ta kammala dukkan uzurinta kafin ya dawo da ita. Shi yake yanke mata kumba duk sati.
"Rabbi inni lima anzalta alaihi min khairin faƙir".
Na furta ina dafe kaina, daidai lokacin da na ji sallamar Asabe na tashi da sauri na fito. Ganin wacce take bayanta ya tursasa mini murtsike idona ina faɗin"Abasiyya".
Na isa na rungume ta sai da muka zauna Asabe ta ce"daman uwargijiyata ce ta ce na yi mata jagoranci, sannan idan akwai abinda za a dafa mata sai ki sanar".
"Ki dafa mata abunda da ba zai ba ki wahala ba kuma wanda ba zai ɗau lokaci ba".
"An gama ranki ya daɗe".
Ta furta yayin da take ɗaukar hanyar ficewa bayan mun gaisa na kawo mata ruwa ta sha. Fuskarta ɗauke da murmushi ta ce" 'yar uwa kin yi sa'ar uwar miji ke kam, duk yanda muke tsammani ba haka bane. Ban taɓa tunanin har yanzu akwai irin uwayen masu ɗaukar matar ɗansu tamkar 'ya'yan su ba".
Cike da tashin fahimta na ce"kin haɗu da ita ne?".
"Sosai ma kuwa da Hamma Ahmad ya ƙira mijinki ya sanar dashi zuwa na aiko har gida aka zo aka ɗauke ni. To da muka iso sashinta aka fara shiga da ni. Mun yi hira sosai da ita babu ruwan ta kamar dama can mun san juna da ita, ni kam har cikin raina sai na ji ta burge ki kuma kina ji a jikina ke za ki zama ɗaya daga cikin misalin da zai karya alƙanin da ake yiwa uwayen miji domin ke kam kin yi dace".
Fuskata ɗauke da maɗaukakiyar mamaki na ce"Da Amma kuka yi dogon hira?".
Ta gyaɗa mini kanta"ƙwarai kuwa". Na sauƙe numfashi ba don na yarda da maganarta ba na zako wani zance. Domin ni kam tun ranar da aka kawo ni cikin gidan ban da yau da buƙartarta kanta ya sa ta ƙira ni ba ta taɓa yi mini maganar cikakken mintin biyu ba.
Mun sha hira sosai da Abasiyya har take labarta mini kowacce rana da yammaci idan Abdul-hameed ya dawo daga wajen aiki sai ya tsaya a gida ya duba jikin Hamma Ahmad. Na ji wani daɗin sanyi yana mamaye mini raina.
Asabe ta shigo da soyayyiyar dankali da ƙwai ɗin da ta dafa mata, na yi mata sannu. Mun wuni tsum da ita a bakinta nake jin Adda Azima tana jiki kuma bata da lafiya na yi murna sosai.
Bayan mun yi sallan Asr Asabe ta shigo ta ce yallaɓai ya ƙira waya ya ce za a mayar da Abasiyya gida ga direba yana jiran ta.
Babu irin dagewan da ban yi ba amma ta ƙi karɓar kayan kwalliyan da na ɗeba mata daga cikin kayan lefena. Na rako ta sashin Amma domin ta yi mata sallama. Ta bata turamen zannuwa har biyu da mayukan shafawa a cewar ta tunda ni ban bata komai ba.
Haka muka yi sallama ta tafi bayan na gama bata saƙon gaisuwar ta gaishe mini da kowa, sashina na koma na cigaba da tunani daga inda na tsaya.
Sai bayan sallan isha'i Abdul-hameed ya shigo wanka kawai ya yi muka tafi sashin Amma muka ci abinci. Na lura da wani kallo na daban da take bi na dashi tun shigowar mu da na kasa gano manufarsa. Sai da ta miƙe za ta shige ɗakinta duk muka yi mata a kwana lafiya ta amsa tana ɗaurawa da"Abdul ka same ni a ɗaki ina so magana da kai".
Har ta yi gaba ta juyo"kar ki jira shi a nan, ki je ki fara tanadin karɓan da za ki yi masa". A kunyace na ce"To a tashi lafiya". Ta amsa a gajarce ya miƙe ya bi bayanta, ganin daga sai Anty Alawiyya da Al'amin a falon ya ni tashi na yi musu sai da safen da basu amsa mini ba na fice izuwa sashina raina cike da fargaba.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_________________________________
Page 2️⃣3️⃣
Idanu ta zuba mishi kusan mintuna biyar ba ta ce dashi komai ba. Tayi imanin cewar ko zai kwana a zaune a wajen ba ta ce dashi komai ba, ba zai taɓa gusawa ba sai ta bashi umarnin haka nan ba zai tambaye ta dalilin ajiye shi da ta yi ba.
Sai da ta gama ƙasaitarta ta furta"me ka sani game da halayyar matarka Aishatu?".
"Na santa da kyawawan hali da kuma tarbiyya game da girmama duk wanda yake gaba da ita, tana da ilmin addini. Waɗanda halayyan natan su suka ja hankalina zuwa gare ta, kuma zuciyata ta kwaɗaitu da son mallakar ta a matsayin abokiyar rayuwata ta har abada".
Ta sa ki taƙaitaccen murmushin gefen baki"wannan iya halayyan da ta bayyana ka gani kake faɗa, na ga alama baka da masaniya akan zahirin halayyarta na ɓoye". Da sauri ya ɗago idanunsa da ya yi ƙasa da su"ɓoyayyan hali kuma Amma? Shin wani abun aka ce miki ta aikata ko kuma kika gani da idonki?".
"Ya zama dole a gare ni na zama mai sanya ido akan duk wani abunda yake kusantanka. Ka san da cewar yau matarka ta yi baƙuwa?". Kansa ya jinjina ya ce"ƙwarai kuwa da sani na ta zo, amma wannan ba baƙuwa ba ce domin 'yar uwarta ce. Ki sanar da ni inda akwai wata matsalar zuciyata bugawa take yi da ƙarfi".
Dariya mai sauti ta saka tana ƙara fuskantarsa ta furta "yaro yaro ne. Abdul-hameed har yanzu kai yaro ne. To ka kasa kunne ka saurari abunda zan faɗa maka da kunnen basira, 'yar uwar matarka da tazo yau ta zo mata da wani ƙulin magani domin mallake ka. Lokacin da Asabe ta shiga domin kai mata abin taɓawa ta ji tana zayyana mata yanda zata barbaɗa maka maganin a cikin ruwan wanka, kuma ka san adadin shekarun da na ɗauka tare da Asabe tun kafin kazo duniya take yi min hidima kuma ba ta taɓa yi min ƙarya ko faɗin abin da bashi kenan ba".
"Aishan?".
Ya furta muryarsa yana shaƙewa waje guda. Cike da tabbaci ta ɗaga masa kanta tana daurawa da"na san dole za ka yi mamaki domin ni ma da farko zancen ya sa ni cikin kaɗuwa. Amma ka sanya mata ido sosai za ka tabbatar da gaskiyar zancena, sannan in da hali ka sanya dokar hana kowa kawo mata ziyara saboda gudun afluwar matsala a cikin auren ku. Gidanka ne matarka ce kana da damar yin komai ba tare da kowa ya ce da kai komai ba".
Sai da ya share maiƙon zuffan da yake tsatstsafowa daga goshinsa kana ya sama damar raba tsakanin haƙwaransa da suke karo da juna. Kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri yake faɗin"na yarda da Aisha matuƙar yarda na aminta da ita, irin amintar da ko a cikin mafarki zuciyata ba ta taɓa kawo min tunanin za ta iya cutar da ni ba. Wallahi Amma ba don ke kika sanar da ni wannan maganar ba ko duk jikina kunnuwana babu wanda zai sanar dani hakan na yarda".
Cike da jin daɗi ta ce"ai idan mutum ne ƙafafu biyu ne zai aikata fiye da haka ma. Na sanar da kai ne don ka ƙara sanya ido sosai ba wai don na lalata maka aure ba sai ka nutsu ka san abin yi".
Musgutawa ya yi yana naɗe dukkan ƙafafunsa wajen guda tare da sakin sakekken ajiyar zuciya.
"Na gode da kulawar ki a gare ni. In sha Allah zan sanya ido amma wallahi bana tunanin Aisha za ta iya cutar dani ko da kuwa a cikin rashin sani ne. Anya Baaba Asabe ba wani maganar daban ta ji suna yi ba?". Harara ta watsawa masa"so me sanya idanu su makance, na baka damar ka yi bincike idan ka tabbatar da saɓanin abinda na faɗa maka. Sai ka sama bakin