Showing 6001 words to 9000 words out of 80635 words
Chapter 3 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt
ankon atamfar da Hamma Ahmad ya yi mana har da su Umma da Dada.
An yi bikin sosai yayin da dangi da abokan arziki suka yi mana kara, gidan babu masaka tsinke ko'ina jama'a ne. Bayan isha'i aka ce a fito da amarya za a kai ta gidanta duk yanda nake faɗin cewar ba zan yi kukan rabuwa da Hamma Abubakar da Adda Azima ba. Tsintar kaina na yi da zubda ƙwallar da ban san su na zuba ba, sai da Adda Abida ta ankarar da ni. Haka aka kai amarya ɗakinta ango ya tare su Baffa suka ce babu kwanan gidan amarya, ana kai ta kowa ya juyo aka bar ta da nasihohin da su Dada da Baffa suka yi mata.
Washe gari tun farar safiya muka fara shirin zuwa gidan ba don sauƙar ruwan sama da ya yi mana cikas ba, a tsarin mu hantsi a can zai iske mu. Ina tsaye ina ɗaura zanina na buɗe ƙafafu. Na soma dariya ina faɗin" kai wallahi Adda Azima kam za ta ga masifa da bala'i. Hamma Abubakar mungu ne na ƙarshe da tayi laifi zai hau zuba mata ranƙwashi". Dariya muka kuma tuntsirewa dashi ni da Abasiyya, muka gama shiri muka fito. Zamu tafi Umma ta ce dole sai mun tafi tare da wasu 'yan mata biyu da suka zo daga gumel, ba su sama zuwa gidan amarya ba jiya.
Ba don raina ya so ba muka haɗa tafiya dasu, basu iya hausa sosai don fullanci yafi zama a harsunansu. Cikin yaren fullancin na ji su na cewar"wannan 'yar kam akwai duhun fata, kamar ba tsantson fulani ba". Ɗayar ta kwashe da dariya"ni fa farkon ganinta na tsorita, domin kwaryar idon ne kawai fari a jikinta sai kuma hakwaranta".
Duk da bada yaren muke magana a gida ba, amma sau tari Baffa da Baba Alhaji dashi suke zance musamman in muna zaune a wajen ba sa son mu fahimci abinda suke faɗa. Su kan sauya harshe, a haka muke tsintar ɗaya da biyu har muka fara fahimta me suke faɗi sai dai ba ma iya maidawa.
Take na ji raina ya tukunzuma zuciyata har wani tafasa take yi. Muka haɗa ido da Abasiyya da ita ma ta fahimci me suke faɗa, idanuna cike da hawayen da nake ɓoyewa na takaici na yi sauri na yi gaba na bar su a baya.
Abasiyya ta biyo bayana tana cewa"meye haka kuma?, kin yi gaba kin bar mu".
"Ku yi tafiyarku na yi tawa". Ina gama faɗin haka na ruga da gudu na miƙe layin, maimakon na karya kwana sai na miƙe na sama wani ɗan lungu na zauna, na kifa kaina da gwiwa ina kuka.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 0️⃣4️⃣
Sai da rana ya iske ni a wajen ya fara dukana sannan na ɗago kaina ina ƙarewa fatar hannuna kallo. Raina cike da takaicin yanda mutane suke sukar halittar da maƙagin rayuwata bai yi shawara da ni, yayin ƙera ni ba.
Goge fuskana na yi duk da ba yau na saba jin an ce dani baƙar fata ba. Amma abin bai taɓa sukar raina irin na yau ba. A zuciyata nake ayyana rashin mutuncin da zan shuka musu, na miƙe na soma tafiya sai na da ƙure lungun da ya ɓullar da ni izuwa wani babban layi.
Na fara waige waige don na rasa inda zan nufa ya kai ni gidan, ware idona nake ko zan gano layin da na fahimta amma babu alamar hakan. Kasancewar ban ko'ina na sani cikin unguwar ba duk yawona bai wuce gidan su Anwar.
Baya na koma da nufin dawowa inda muka rabu da su Abasiyya, ina tafe kaina a ƙasa na ji ƙarar wucewar wata motar da ta wuce ta gefena da matuƙar gudu fiyuuu. Ɗago kan da zan yi ya fancakalo mini ruwar kwatan da ya kwanta a wajen a fuskata.
Na tsaya cak na kasa komai illa hawayen da yake sauƙa daga idanuna. Har cikin bakina ruwan ya shiga na tofar da miyau, ina bin motar da ta faka a gefe da harara. Ji nake yi kamar na je na shaƙo mai motar ko zan huce takaicin da ya tusa mini a raina.
Sai da aka ɗau mintuna kafin aka buɗe ƙofar motar mazaunin driver aka fito, na yi saurin yin ƙasa da kaina cike da kunyar halin da fuskata take ciki. Ganin wasu masu talla da suka tunkaro inda nake tsaye zasu wuce, har suka wuce ban ɗago kaina ba.
"Assalamu alaikum sannu baiwar Allah".
Na ji a furta cikin kammalalliyar murya ma'abociyar nutsuwa, take na ji tsikar jikina ya tashi domin ban taɓa tsayiwa da wani namiji akan hanya ba, bayan 'yan uwana da suka kasance muharramaina. Ban sa ni ko fahimtar hakan ne ya san shi ƙara sausauta murya ya ce"baiwar Allah afuwan ban lura da ke a wajen ba, na ɓata miki jiki da ruwa".
Sai a lokacin na ɗago kaina na sauƙe akan sa, ba za'a sanya shi a layin farare ba kamar yanda ba za'a ƙira shi da baƙi ba. Sajen fuskarsa da kuma farin shaddar dake jikinsa su kaɗai na kalla na rusunar da idanuna ƙasa.
Komawa inda ya ajiye motarsa ya yi ya ɗauko gorar ruwa ya dawo ya miƙe mini, ba tare da na ɗago kaina ba na karɓa na soma wanke fuskata.
Ina gamawa na miƙe masa gorar ruwan na soma tafiya, ƙafufuna har suna harɗewa cikin zanina. Da sauri ya biyo bayana ya sha gabana tare da cewa"baiwar Allah kina ji na?". Hawaye suka zubo daga idanuna ya ƙara sausauta murya ya ce"afuwan baiwar Allah". Kaina kawai na ɗaga masa na raɓe zan wuce ya kuma shan gabana, jikina ya soma rawa ganin yanda mutane suke wucewa ta wajen, rashin sabo ya sanya ni ganin kamar cewar kowa ni yake gani.
"Allah yasa ba ni na yi sanadiyar zubar hawayen nan ba, domin ba zan yafewa kaina ba sanya hawayen wani zuba a dalilina".
Cikin sarƙewar harshe na furta "zan wuce". Ya haɗe hannayensa da yake riƙe da gorar ruwan wajen guda, tare da marairaicewa"ki yi haƙuri". Da sauri na bi gefe na wuce cikin sauri tamkar zan tashi sama.
Ina waige na ga yana tsaye baya biyo bayana na sa ki ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, sai da na ƙure layin ina hango inda muka rabu da su Abasiyya na ji hankalina ya kwanta.
Ban ankara ba naji an danna mini horn ɗin mota a bayana da ya sanya cikina juyawa, na cigaba da tafiya da sauri. Ya zuge gilashin motar muka haɗa ido na kawar da nawa gefe guda, muryarsa suka yi ƙafofin kunnuwana dirar mikiya.
"Ban sa ni ba ko afuwan nawan ya sama karɓuwa".
Izuwa yanzu kam gabaɗaya na gama tsorita ina tina yanda nasihar Dada da take ja mana kunne ni da Abasiyya. Akan cewar kar wani namiji ya yi mana magana a hanya mu tsaya, duk wanda muka gani da babbar mota ɗan yankan kai ne. Ji nake yi kamar na saki fitsari a wando tsabar tsoritar da nayi.
Gudu gudu sauri sauri nake tafiya ba tare da na kuma kallon gefen da yake ba, sai da na iso wajen na gane hanyar gidan Adda Azima.
Ina isa na iske mutane cike a filin gidan kamar an jefo ni haka na faɗo cikin gidan. Muka haɗo ido da Abasiyya da take miƙo abinci a mutane tare da wasu mata biyu. Na galla mata uwar harara na zari buta na shiga banɗaki.
Ina fitowa na saki ajiyar zuciyar samun nutsuwar da na yi, na je kusa da Adda Abida na zauna. Ta kallo ni ta ce"ke kuma ina kika tsaya sai yanzu?".
Turo baki na yi na ce" ɓata mini rai suka yi" ta jijjiga kai ta kuma cewa"za ki je ki haɗu da Hamma Abubakar ne, don ya shigo yana neman ki. Haka nan ma Anwar yanzu ya bar gidan nan". Taɓe baki na yi don yanzu yunwar cikina ce ta dame ni don ko abincin bamu ci ba muka fito. Na miƙe na je na karɓa abinci na soma ci Abasiyya ta zauna a kusa dani, na saki dogon tsaki ina kawar da kaina gefe guda tare da mayar da hankali ga cin abincin da nake yi.
"Ki yi haƙuri mana, Adda Abida ma da ta yi musu faɗa akan abinda suka faɗa miki". Ban kula ta ba ta ɗaura da"kin ji 'yar uwa?". A zafafe na furta"malama kar ki sanya ni na ƙware ki bar ni haka nan". Murmushi tayi don inda sabo ta saba da halina na masifa da rashin barin ta kwana, sai da na cinye abincina tas ba wanke hannuna na shiga ɗakin Adda Azima ita ma ta tsare ni da tambayar inda na tsaya na ce da ita canza hanya na yi nabi tawa hanyar suma suka bi tasu.
Sai bayan sallan asr sannan muka koma gida gidanmu muka wuce, lokaci baƙin nisa duk sun fara watsewa ya rage saura tsirarun mutane ne suka yi saura. Bayan sallan magrib ina zaune a bisa sallayar da na iddar' Anwar ya aiko ƙirana. Da muryana ta na tashi domin yau tun wayewar gari ban sanya shi a cikin idanuna ba, na fita na iske shi a zaure tun kafin na isa na turo baki gaba, ya saki murmushi yana faɗin"waya taɓa mini Boɗɗita?". Na yi ƙwafa na soma sanar dashi duk abinda ya faru a hanyar zuwar mu gidan Adda Azima.
"Duk da kasancewar ki bakar fata ai ke kyakkyawa ce shiyasa nake ƙiran ki Boɗɗiam. Farare dubu nawa ne munanan da baƙaƙen ma suka fi su kyawu?, ke kyakkyawa ce. Ki rubuta ki ajiye wani masoyinki zai tabbatar miki da haƙiƙanin gaskiyar maganar da na furta miki a yanzu".
Dariyar da yau gabaɗaya ban yi kamar ba na saka har da sunkuyawa ƙasa, sosai nake yin ta. Ya dakatar da ni da faɗin"ki nutsu ga Hamma Abubakar shigowa". Babu shiri na miƙe tsam ina rarraba idanu da hakan ya sanya shi sakin dariya.
"Matsoraciyar banza me zai kawo Hamma Abubakar kuma a wannan lokacin, ai yana can tare da amaryarsa". A bayyane na saki ajiyar zuciya ina jefa masa harara ina cewa"tsoritar da musulmi dai haramun ne".
"Tsakanin jiya da yau kin lura da hauhawan annurin su Baffa?". Ya furta yana gyara tsayiwarsa. Na numfasa kana na amsa da "ƙwarai kuwa suna cikin matuƙar farin ciki".
"Allah ya ƙara haɗa kanmu Boɗɗiam".
Na yi fari da idona kana na ce "amin Hamma Anwar" ya yi taƙaitaccen murmushi haɗi da faɗin"ina kika tsaya yau da kuka fita?, don naje gidan Hamma Abubakar aka ce ba ki ƙariso ba". Ban san dalilin faɗuwar da gabana ya yi ba idanuna ya kawo ruwar ƙwalla, na sanar dashi komai game da wannan mai motar da ya fancakala mini ruwan kwata a fuskana.
"Kar ki ƙara sauraran irin mutanen nan. Ko gaba irin haka ya faru ki yi tafiyarki kawai".
Ban amsa masa ba illa kafe sa da idon da na yi, don ganin yanayin da ya yi maganar da gabaɗaya annurin fuskarsa ya gusa. Idanunsa har sun koma launin ja, cikin sanyin jiki na soma faɗin"ni fa ban kula shi ba, ko da ya bani haƙuri ma ban tanka masa ba. Shi ne ya yi ta bina a baya".
"Naji ki shiga gida sai da safe".
Yana ƙare faɗin haka ya fice daga zauren ya bar ni tsaye sororo kamar sokuwa. Haka na koma ciki jikina gabaɗaya babu ƙwari tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, ko da na kwanta na kasa bacci ina ta tunanin ko na faɗa wani abu ba dai dai bane, duk da Anwar yana da saurin ɗaukar zafi da kuma zuciya amma baya taɓa nuna shi a kan 'yan uwansa musamman ni. Da na zama tamkar Hussaina a gare shi.
Washe gari 'yan biki kowa ya watse gidan ya zama sharau. Na nufi gidan Baba ina sako kai muka yi kiciɓus dashi zai fita na matsa da sauri na bashi hanya ina faɗin "ina kwana an tashi lafiya?".
Ba tare da kalle ni ba ya amsa da"lafiya ƙalau". Na marairaice muryar tamkar mai shirin yin kuka" ban san me na yi maka ba jiya ka tafi ranka a ɓace". Ya zaro ido waje"ni na ce miki raina ya ɓaci?".
"Yanayinka ne ya nuna haka ai". Ya sauƙe ajiyar zuciya kafin ya furta" kawai ji nayi ban ji daɗi ba da kika sanar da ni, yanda ya ɓata miki fuska da ruwan kwata".
"To ai ya bani haƙuri fa".
Na faɗa cikin shagwaɓan da ya tilasta masa sakin dariya duk shan kunun da yake yi. Ya ɗago idonsa ya kalle ni ya ce"to ai ya bani haƙuri fa". Na yi rau rau da ido zan yi magana ya tari numfashina"shikenan ya wuce kin ji?". Cike da jin daɗi na sakin murmushi ina cewa "to na gode yanzu ina zaka je".
"Kasuwa su Hamma Ahmad tunin sun wuce".
Addu'ar dawowa lafiya da cimma abinda aka je nema na yi masa, ya amsa cike da jin daɗin da ya bayyana akan farar fuskarsa. Ya wuce ni kuma na shige ciki ina shiga Abasiyya ta soma yi mini dariya.
Ko tambayar lafiyarta da nake yi bata amsa ba ta cigaba da dariyarta, na watsa mata harara ina tsarkin tsaki. Sai da ta tsagaita ta soma cewa"ai daman yanda Hamma Anwar ya shigo gidan nan a daren jiya, sai da na yi zargin cewar da walakin goro a miya. Ashe ke kika tunzuro shi". Ban kula ta don ba ita ce a gabana na faɗa ɗakin Dada.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_________________________________
Page 0️⃣5️⃣
Tun bayan auren Hamma Abubakar na ƙara sakewa a cikin gidan. Sai dai ko wacce safiya kafin ya wuce kasuwa sai ya zo gidan ya gaishe dasu Baffa haka nan bayan sallan isha'i kafin ya wuce sai ya zo ya yi musu a kwana lafiya.
Kasuwancin su Baffa sai ƙara hafɓaka yake yi domin yanzu tunin likafa ta cigaba. Hamma Ahmad da Hamma Adnan ma an ware musu nasu rumfar daban da suke sayar da atamfofi, Anwar ne kawai yake tare dasu Baffa.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya lokaci yana juya, yayin da kullum muke ƙara kwanakin mu suke ƙarewa ba tare da mun sa ni ba, balle tanadin guzuri. Sai ma burin da ya ke ƙara cika mana rai.
Sai da Adda Azima ta cika watanni uku cur a gidan miji sannan ta zo ganin gida, ranar tsabar murna rasa inda zamu tusa kanmu muka yi inda Abasiyya, mu kawo mata wancan mu kawo mata wancan. Duk abinda ya faru kuwa a gidan ko aka yi duk sai da muka sanar da ita. Ta yi ɓul-ɓul kuma ta ƙars yin wani haske na musamman jikinta kamar ka latsa jini ya fito.
Sai da suka dawo daga kasuwa Hamma Abubakar ya zo ya ɗauke ta. Wayewar garin ranar da muka buga lissafi da Adda Abida na cikar auren su watanni bakwai da 'yan kwanaki. Hamma Abubakar ya ƙira a gigice wai ta yi ɓari har sun wuce asibiti, ta sha wahala matuƙar don har wankin ciki aka yi mata bayan ta sha jinya ta dawo gida ta yi sati biyu sannan ta koma ɗakinta.
A lokacin kowa ya fahimci take taken Hamma Adnan da Adda Abida suna son juna, ya kai matakin da har basa iya ɓoyewa ko zaman 'yan awanni ka yi tare dasu zaka fahimta. Tabbas su Baffa sun yi matuƙar farin cikin jin haka daga iyayenmu mata domin zama na musamman suka haɗa dukkan mu muka bayyana, su na ta sa mana albarka da addu'ar Allah ya ɗaurar da zumunci a tsakanin mu ko bayan ransu.
Umma ta aike ni na sayo mata sugari ta damawa Baffa fura, layin sharau domin an shiga sallar isha'i. Na je na tarar da shagon a kunne na nema waje na zauna ina wasa da 'yan yatsun hannuna. Har aka yi sallama aka fara fitowa tun daga nisa na hango mai shagon da hakan ya sa ni saurin miƙewa ina karkaɗe jikina, na gaishe shi ya amsa sannan na sanar dashi abinda nazo saya ya buɗe shagon ya ɗauko ya bani na karba tare da miƙa masa kuɗinsa.
Sauri sauri nake yi saboda yanda maza suka fara cika layin, ban ankara ba na ji na bangaji mutum. Na yi saurin ja da baya tare da tsugunawa ba ɗauko wayar da ta faɗi ƙasa ba ɗago zan miƙa masa kenan idanunmu suka sarƙafe a cikin na juna.
Take na ji jikina ya ɗauki rawa ganin zan kuma yasar da wayar ya sanya shi karɓa"ke ce?". Ban kula shi ba na fara tafiya ya soma jerawa da ni"tun wancan lokacin nake ta addu'ar Allah ya ƙara haɗa ni dake domin na nema afuwarki. A layin nan kike?".
"Ya riga ya wuce tun lokacin na sanar da kai, don Allah ka daina bi na".
"Me yasa?".
Ya jefa mini tambayar da ya sanya ni ƙara saurin da nake yi tamkar zan kife akan hancina, idanuna rau rau na ce"za a yi mini faɗa a gida idan aka gan ni da ka...". Ban rufe bakina ba na hangi Baffa da Baba Alhaji suna nufo gida suna tafe suna tattaunawa da limamin masallacin. Bayan su kuwa su Hamma Ahmad da Adnan ne sai Anwar da yake daga gefe tare da wani abokinsa na cikin unguwar.
Babu shiri na sa ki ledar sugarin ya faɗi ƙasa, na ɗaura hannuna a ka"shikenan na shiga uku". Na sunkuya na zari ledar da yake yoyo ba ruga gida da gudu domin na tabbatar da cewar duk sun ganni.
Ina shiga na ɓarke da kukan da ya tilasta Umma yanke addu'ar da take yi ba tare da ta kammala ba. "Ke lafiyarki?, ina aiken da na yi miki ko kuɗin kika sayar?". Kafin na kai ga bata amsa su Hamma Ahmad suka shigo.
"Ke meya fitar da ke a wannan lokacin, sannan waye wancan da muka tsaya dashi?".
Cikina ya bada ƙarar ƙululu sai da na haɗiye wani miyau mai ɗaci"Umma ce ta aike ni na sayo mata suga, shi ne na gan shi