Showing 51001 words to 54000 words out of 80635 words

Chapter 18 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

a wannan lokacin ba domin na san ko ya dawo to sashin Amma zai wuce. Sai bayan sallan magrib zai shigo ya yi wanka mu koma sashin natan tare domin cin abinci.


Ina sallan magrib ya shigo har ya shirya cikin wasu ƙananan kaya marasa nauyi. Sai da ya jira nima na yi wanka sannan muka nufi sashin BASARAKIYA kamar yanda zuciyata ta raɗa mata sunan.
Ba a yi wani dogon zama ba yau ana gama cin abincin ta haura sama. Na yi iya ƙoƙarin sarrafa kaina ta hanyar danne kishin dake ci na, na nunawa Abdul-hameed komai ya wuce.


Daren ranar baccina ragagge ne tunani barkatai sun ƙi barin ƙwaƙwalwata ta sarara. Kafin ƙarfe goma mun gama shirinmu tsaf har mun shiga sashin Amma zamu yi mata sallama, ta tare mu da faɗin"ina zuwa haka?".


"Za ta je gida ne".


Ya amsa yan sosa ƙeyarsa tare da rusunar da kansa ƙasa. Ta jinjina kanta tana ɗauka remote ta canja tashar da take kallo ta ce"kai kuma fa ina zaka je?".
"Zan kai ta ne daga nan mu gaisa da mutanen gidan na kwana biyu ban tsaya ta can ba". Zancen ta yi ya tursasa mini ɗago kaina babu shiri. A karon farko da na yi mata kallon ido cikin ido.


"Direba ya kai ta ko kuma ta hau adaidaita. Kai ɗin ka zauna akwai maganar da zamu yi mai muhimmanci".


*ƁOYAYYAR MANUFA*


©️Maimuna Tijjani Iyam


_________________________________


Page 2️⃣7️⃣


Ƙasa na yi da ido ƙirjina yana bugawa tare da kasa kunnen ina tsimayan amsar da Abdul-hameed zai ba ta.
"Amma bana yin ja-in-ja ko kuma musu akan dukkan maganarki. Zan so ki yi min wannan alfarman na kai sai na dawo mu yi maganar".
"Tashi ka je".


Ƙara sausata amon muryarsa ya yi cikin kwantar da kai da ban baki yake faɗin"ki yi haƙuri Amma ba nufina na ɓata miki rai bane. Bari direba kawai ya kai ta". Su kaɗai suke kiɗansu suke rawarsu domin tunda suka fara zancen ban ce uffan ba.


Ta ƙwala ƙiran Asabe ta ce ta je ɗakinta ta kawo mata jakanta babu jimawa ta dawo. Ta ciro wasu kuɗaɗe sabi fil da ko irga su bata yi ba, ta dire su a gabana tare da faɗin"ɗauki wannan ki yi musu tsaraba".


"An godiya Allah ya ƙara girma".
"Amin".
Ta amsa mini dashi a daƙile muka fito tare dashi, zai fara yi mini magana na dakatar dashi"kar ka damu ba komai". Sosai ya gargaɗi direban da ya yi toƙi cikin nutsuwa.


Sai da motar ta fice daga cikin gidan hawayen da suka kwanta a cikin kurmin idaniyata suka sama damar kwaranya. Ban yi yunƙurin hana su zuba ba, har sai da motar ta faka a ƙofar gidan mu bisa kwatancen da Abdul-hameed ya yi masa muka iso gidan.
Na ɓalle marfin motar na fice na nufi gidanmu tare da sallama ɗauke a bakina. Muryar Anwar ce ya amsa sallama na ƙarisa shigowa cikin gidan.
Yana zaune tare da Umma yana tsince mata zogala na isa da sauri raina cike da murnar ganin uwata na faɗa jikinta.


"Hande min boni. 'Yar nan Allah ya shirye ki". Dariya na ƙyalƙyale dashi ina ɗago kaina daga jikinta"Ina kwana na same ku lafiya?".


"Lafiya ƙalau ya gidan nakin?."
Na amsa mata da lafiya ƙalau ina maida dubana ga Anwar na ce"ɗan saurayi ya kake?".
Harara ya watsa mini"ke kin san dai na fi ki ko?". Na juya masa idona kafin na yi magana ya tari numfashina da faɗin"tare kuke dashi ne?".


Sai da na sadda kaina ƙasa kana na furta"a'a ni kaɗai na zo". Koda da ban ɗago kaina ba amma muryar da ya yi magana da ita ya tabbatar mini da cewar walwalarsa ta daɗu. Hira muka kacame dashi sosai har sai da Umma ta tashi ta koma ɗaki ta bar mu, muka tsince zolayan tsaf na ɗaura a wuta sannan na dawo na zauna.


"Duk da kina ƙoƙarin ƙawata fuskarki da murmushi domin ɓoye damuwar dake ranki. Ni na gano hakan a tattare dake. Shin kina da wata matsala ne?".


A bayyane na sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi ina gyara zamana da kyau. Tabbas Anwar ɗan uwa ne na gari a gare ni amma ta yaya zan fara sanar dashi damuwata?.


"Shurun da kika yi yanzu hakan ya ƙara tabbatar min da hashashen zuciyata, kina da damuwa Boɗɗiam".
Sai da na yi ƙarfin hali wajen danne kukan da yake shirin kubce mini kafin na sama zarafin iya furta"babu abinda ke damuna in ma akwai to addu'arka kawai nake da buƙata".


Sai da ya yi jim kafin ya ce"kullum kina cikin addu'ata a dare da rana, nima ki taya ni da addu'ar Allah ya ƙara min ƙwarin gwiwar iya jure rashin da zuciyata ta yi da ba shi da madadi". Cike da rashin fahimta na watsa masa idanuna ya sakar mini da murmushin da kai tsaye na gane na ƙarfin hali ne.


Har zogalan ya dahu na sauƙe na kwaɗa mana muka ci ina nuna masa sabon wayata, ya yi mini son barka tare da yi mini gargaɗin yin ta-ka-tsantsan game da sharrinta haka nan ma Umma.
Na yi salla snnan muka fita wajen Dada sosai ta cika da murnar ganina. Na waiga ina faɗin"ina Abasiyya fa?".
"Tana can gidan Azima bata ji daɗi ba ita ma". Na jinjina kaina"Allah dai ya raba lafiya".


"Amin".


Suka haɗe baki mun ɗan taɓa hirar da har ta mantar da ni rabin damuwar da na fito daga gida da ita. Bamu sama damar keɓewa da Dada ba sai da na shiga ɗaki zan yi sallan Asr bayan ta shigo ta zauna ta ce dani"ina fatan babu wata matsalar ko?".


Tamkar ta sanya kifiya ta soki zuciyata haka na ji zuciyata ta raunana. Kwalla suka ciko mini idanuna taf suka tsiyayo a bisa kuncina. Cike da kulawa take cewa"subhallahi kuka kuma? Me yake faruwa?".


"Dada ina cikin matsala".


Mamaki ƙarara a bisa fuskarta"matsala tun daga yanzu?". Na jinjina mata kaina"mahaifiyarsa ta ce aure zai ƙara domin ba zai zauna da mace ɗaya tal ba. Tana zargin wai bana samar masa da nutsuwa yanda ya kamata, sannan har yanzu babu wani alamar samun ƙaruwa daga gare ni. Wallahi tun lokacin da ta furta wannan maganar na kasa samun kwanciyar hankali ko murmushi sai dai na yi na yaƙe. Na rasa mafita da abin yi baya taɓa ketare umarninta akan komai".
Na ƙare maganar ina ƙara fashewa da wani sabon kukan tare da kifa kaina akan cinyarta, shuru ya karaɗe ɗakin sai sautin kukana da yake tashi a hankali.


"Yin biyayya ga iyaye mussamman uwa wajibi ne, don ya fifita uwarsa akan komai da kuma kowa akan ba laifi bane. Maganar ƙarin aure kuma ki cire shi a ranki tabbas da akwai ciwo amma idan kika miƙa lamuranki ga Allah mabuwayi haƙiƙa sauƙi zai zo miki ta inda ba ki taɓa zato ba balle tsammani. Ki yi biyayya ga mijinki ki kuma kyautata masa ta hanyar sauƙe dukkanin haƙƙinsa dake kanki. Kar ki damu da duk abinda 'yan uwansa za su yi miki ko kuma su ce da ke. Ke dai kawai ki kyautata musu domin ita kyautata ta na juya tsana zuwa soyayya".


Gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalau tamkar wacce aka zarewa laka. Muryata har ta fara dishashewa na furta"a lokuta da yawa sai in ta tunanin kamar ɓatawa su Baffa da na yi ne, hakan yake faruwa da ni". Sai da sauri ta kwaɓe ne"kul kar na ƙara jin kin furta haka. Babu wanda yake auren matar wani ba ki ji ana cewa matar mutum kabarinsa ba?". Kaina na ɗaga mata na ce"ba sa hira da ni har yanzu bare nake a tsakanin su. Na rasa da waye zan yarda a cikin su". Sai da ta ɗago kaina tana goge mini hawayen da ya ɓata mini fuskana kana ta ce"ki yi haƙuri wasun su na da wahalar sabo kafin su sa ki jiki da mutum ba da wuri ba. Amma inda kika yi haƙuri komai zai wuce ke dai kawai ki tsarkake zuciyarki kuma kar ki nufi kowa da komai face alkhairi.".
Sai da ta numfasa ta ɗaura da"dole ki koyi warware matsalolin aurenki da kanki cikin siyasa da dabara".
Haka ta yi ta aikin lallashina gami da kwantar mini da hankali. Na ji wani rauni a cikin zuciyata na tabbatar da na sama Dada a matsayin suruka da na dace a gidan duniya. Ina da yaƙinin da ba ni da wata damuwa domin za ta nuna mini tsantsar soyayyar da babu algus a cikinta. Zancen da ta ɗaura dashi shi ya fizgo ni na dawo hayyacina daga duniyar tunanin da na lula.


"Amma na yi mamaki da kika ce mahaifiyarss ce ta ce zai ƙara aure, matar nan tana da kirki matuƙar domin ta sha yin aike a gidan nan. Duk juma'ar duniya kuwa sai direban gidan ya kawo abin sadaka".


Zantukanta suka shayar da ni ruwan mamakin da ya hana ni yin ƙwaƙwƙwaran motsi balle iya raba tsakanin haƙwarana da suka haɗe da juna. Meye nufin Amma a gare ni kenan? A gaban iyayena da mijina za ta nuna tamkar ta fi kowa sona alhalin fuskar da take nuna mini ya sha bambam. Na so sanar da Daada zancen ƙulin maganin nan amma jin abinda ta faɗa yanzu akan Amma da irin tarin yabon da ta ɗaura da yi mata, sai suka sake mini gwiwa na kasa taɓuka komai.


Na so zuwa gidan Adda Azima na gano ta amma Daada ta hana ni a cewar ta wai ban tambayi izni daga gare shi, na zamo mai tsaya a inda aka umarce ni dole na haƙura ba don raina ya so ba.
Na numfasa kafin na ce"ni kuwa ya maganar tafiyar Anwar?".


Ita ma sai da ta sauƙe numfashi kana ta furta"ba ni da ta cewa akan hakan sai dai kawai na dage da yi masa addu'a". Na tsinci kaina cikin wani irin yanayi"don Allah Daada a hana shi wannan tafiyar". Na ƙare zancen ina marairaice murya kanta kawai ta ɗaga mini tana sakar mini murmushi.


Muna cikin haka Anwar da Hamma Ahmad suka yi sallama, muka haɗe baki ni da Daada muka amsa musu. Hamma Ahmad ya kafe ni da ido"yaushe a gari in ji maƙi baƙi?". Ya furta yayin da yake yi wa kansa matsuguni, na saki murmushi"ɗazu na zo".
Muka hau gaisawa da juna kafin Daada ta amshe zancen da faɗin"ki yi masa faɗa ko zai ji har yanzu ya ƙi ya fito da wacce zai aura, kullum Babanku a kaina yake juya laifin wai ni nake goye masa baya".


"Ya kamata kam izuwa yanzu ka bar mana gida, mun gaji da ciyar da ƙato". Anwar ya furta cikin sigar zolaya da ya sanya Hamma Ahmad saurin kai masa dundun a bayansa yana haɗe fuska tamau.
Cikin sanyin jiki da na murya na soma faɗin"gaskiya kam yanzu ya dace ace kai ma ka ajiye iyali. Sai darajarkaya ƙara cika na zama babban mutum".Ya zubo mini idanu sai da na ji wani yar a jikina.


"Hmm! In dai ba zaɓa min za ku yi da kanku a ɗaura auren a kawo min ita ba. To ni kam babu wata macen da idanuna za su iya kalle balle saƙon ya kai ga ƙwaƙwalwata har sonta ya yi tasiri a cikinsa. Ki yi haƙuri Daada ni kam ina ga kamar ba ni da rabon yin aure a duniya ne".


Duk muka yi tsit tamkar ruwa ya cinye mu. Saboda kashe mana jiki da ya yi da kalamansa da yana kai aya ya miƙe ya fice daga ɗakin. Duk da kallo muka tara shi kafin Daada ta furta"Allah ya kyauta".


Da zancen Hamma Ahmad na wuni a cikin raina har lokacin da direba ya zo ɗauka na. Lokacin da Anwar ya shigo yake sanar da ni na fito an zo ɗauka na. Na yi tunanin Abdul-hameed ne domin har a Daada cewa na yi shi zai zo ya ɗauke ni har fura ta ce na dama mishi.


Kuɗin da Amma ta ba ni na raba biyu na ba wa Ummata da Daada, sai da na jira dawowar su Baffa muka gaisa. Sannan muka tafi ina jin tamkar an sauƙe mini wani abu mai nauyi daga ƙirjina. Tattaunawar da muka da Daada ya samar mini da nutsuwa haka nan na ƙudurce aiki da dukkan shawaran da ta ba ni domin ina da yaƙinin ba za ta taɓa cutar da ni, ko ɗaura ni a hanyar da ba ta dace ba.


*ƁOYAYYAR MANUFA*


©️ Maimuna Tijjani Iyam


______________________________________


Page 2️⃣8️⃣


Ina isa sashina ana ƙiran sallan magrib na faɗa banɗaki na ɗauro alwala sannan na zo na tada kabbara, ban tashi daga kan sallayan ba sai da na yi sallan isha'i.


Sannan na shiga wanka na fito na shirya cikin shigar abayar da ta sauƙa mini har ƙasa. Ina ƙulle igiyar rigar na tuna cewar lalle Abdul-hameed yana sashin Amma, nasihar Daada ya fara dawo mini cikin kwanyata. Da sauri na ɗaure na ɗaura mayafin rigar a kaina tare da ɗaukar wayata na fita sashin.


Dole nima na dunga kutsa kaina cikin su ba zan ƙara jiran sai an zo an ƙira ni kafin na je ba. Al'amin tsaye nake hangowa a cikin inda ake ajiye motoci da waya saƙale a kunnensa da dukkan alamo waya ya ke yi. Na zo dai dai ta wajen zan wuce kunnuwana suka jiyo mini abinda ya hautsina hanjin cikina.


"Ku tabbatar da cewar kun aiwatar da aikin nan yanda ya kamata. Yana cikin garin har yanzu".


Haka nan kawai jikina ya ba ni cewar ba lafiya ba, kamar yanda zancen suka sama matsuguni a cikin curin ƙaramar ƙwaƙwalwar dake cikin ƙoƙon kaina. Da saurin na ja ƙafafuna na bar wajen ina maimaita kalmar auziya a cikin raina. A hankali na yi sallamar da ya sama amsawar Anty Alawiyya a daƙile tamkar an yi mata dole, sai da na zauna kana na yi wa Hajiya Amma sannu da kuma ita Anty Alawiyyan suka amsa mini ba yabo babu fallasa. Sai dai na lura da cewar kamar wata maganar suke tattaunawa a tsakanin su da shigowata ya sanya su dakatawa.


"Kin sama dawowa kenan?".


"E wallahi na dawo, kuma sun ce a gaishe ku gabaɗaya". Kanta kawai ta jinjina mini tare da kawar da kanta gefe. Rashin ganin Abdul-hameed a wajen ya sanya zuciyata faɗawa cikin wasi-wasin anya lafiya kuwa?. A duk irin wannan lokacin to tabbas za a same shi tare da Amma. Kuma ko wucewata yanzu na ga motarshi a cikin gidan. Ta gefen idona nake ƙarewa girman falon kallo ko zan gano shi amma ban kai ga cimma hakan ba. Domin da yana cikin falon to haƙiƙa da na gan shi.


Bayan na gama sa-toka-sa-katsi da zuciyata da take ingiza ni akan na tambaye inda yake a wajen Anty Alawiyya na ɗago kaina da hakan ya yi daidai da shigowar Al'amin cikin falon. Ya haɗe fuskarta tamau kamar magriban ɗinya, da kallo Amma da Anty Alawiyya suka bi shi dashi har ya zauna da dukkan alamo akwai tarin zancen a bakin su.
Da ido Amma ta yi masa alama akan lafiya ya jijjiga mata kansa yana ƙara ɗaure fuska.


Tsakin da Anty Alawiyya ta tsirka ya ja hankalin izuwa gare ta sai dai ba su bar mini wani alama ɗaya da zan iya gano ƁOYAYYIYAR MANUFAr da suke ɓoyewa ba. A zabure na dawo cikin hayyacina saboda sallamar Asabe ya na ji shi tamkar a tsakar kaina ta ƙwala shi. Ta zube gaban Amma"uwargijiyata girki ya kammala".
Kanta kawai ta ɗaga mata da hakan ya ba ta damar miƙewa ta fara ɗebo kulolin abincin tana jere su a gaban mu.


Kowa shi ya zuba abinda zai ci ni kam na kasa kai koda cokali ɗaya na abincin cikin bakina. Babu irin nau'in tunanin da bai zo raina ba a wannan lokacin har izuwa lokacin da na ji muryar Amma sun bugi kunnuwana.


"Kin yi magana da mijinki ne yau?".


"A'a". Na furta a sanyaye ina ajiye cokalin hannuna.
"Meye amfanin wayar hannunki kenan idan ba za ki ƙira mijinki ki ji lafiyarsa ba?".


Na yi ƙasa da kaina"na sha'afa da wayar ne ma don tunda na fita tana cikin jakata". Sai da ta ja lokaci mai tsawo kafin ta ce"to mijinki ya yi tafiya na aike shi can wani ƙauye, wataƙila gobe ki jibi ya iya dawowa". Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na sauƙe muryata ƙasa ƙasa na furta"Allah ya dawo dashi lafiya".


"Amin"


Ta amsa dashi tana mai cigaba da cin abincinta, gudun kar ta ƙara yi mini wani zancen ya sanya ni ɗaukar cokalin ina tura abincin da ƙyar ba don son raina ko don ina jin danɗanon abincin a bisa harshena ba.


Muna gamawa Asabe ta zo ta ɗebe kwanuka tare da gyare wajen. Al'amin ya buga mini wani hararar da babu shiri na rusunar da idanuna ƙasa.
"Malama ki tashi ki bamu waje zan tattauna da mahaifiyata da 'yar uwata".


"Bana son rashin hankali Al'amin ka dunga bin komai a hankali". A karon farko da Amma ta yi mini magana cikin sanyayyiyar murya mai cike da taushi ta ce da ni"Aisha tashi ki je ki kwanta na sallame ki".


"Na gode, a tashi lafiya". Cikin su babu wanda ya ce dani ko kanzil har na miƙe na fice. Ban san inda nake cilla ƙafata ba har na isa cikin sashina na zube akan kujera a falo ina mayar da numfashi tamkar wacce ta yi gudun ceton rai.
Ina Abdul-hameed ya je? Me yasa bai sanar da ni ba? Wannan dalilin ne ya hana shi zuwa ɗauka na kenan daga gida?.
Da sauri na dafe goshina saboda matsanancin sarawan da kaina yake yi mini, halin da yake ciki kawai shi nake son sa ni. Don haka na tashi zaune ina lalumar wayata. Sai da na dubo har ƙasar kujerar babu ita babu alamarta. Babu shakka a falon Amma na baro ta. Na fito tare da nufar sashinta har na ɗaura hannu a jikin ƙofar tare da yunƙurin furta sallama zancen da suka yi wa kunnewana dirar mikiya suka sanya ni yin mutuwar tsaye, babu shiri na jingina da bango saboda rawar da ƙafafuna suka yi mini da nuna bijirewarsu ga jimirin ɗaukar nauyin gangar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login