Showing 33001 words to 36000 words out of 80635 words
Chapter 12 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt
bayan zancen nawan na ƙarshe, har sai da na fara zargin ko na faɗi wani abun da bai dace bane. Sai can ta ta ce dani"iyayenki sun so haɗa ki aure da ɗan uwanki amma kika bijire kika auri zaɓinki. Me yasa kika zaɓi Abdul akan wanda ya kasance jininki?".
Take na ji wani maiƙon zuffa ya kwanta a goshina cikina ya bada ƙarar ƙululu. Ta saki taƙaitaccen murmushi "kina mamaki inda na zama wannan bayanan ko?".
Na jijjiga kaina alamar a'a kana na aro jarumta na yafawa kaina na soma faɗin"ban yi mamaki ba domin duk wasu iyaye idan ɗan su zai yi aure sukan gudanar da nasu binciken, kamar yanda dangin amarya ma suke yi nasu".
Na tsura mini ido tamkar ɗan sandan dake titsiye ɗan fashi cikin sigar son gano gaskiya.
"Bani amsar tambayata".
Na ja dogon numfashi na fesar"ban zaɓi Abdul-hameed akan Hamma Ahmad face dama can Allah ya rubuta cewar Abdul-hameed shi ne mijina a duniya tun kafin samuwar ruhina a bayan ƙasa. Na yi imani da cewar babu wanda yake aurar matar wani domin da Hamma Ahmad mijina ne babu wata ƙaddarar da zata haɗa ni da Abdul-hameed".
Shuru ta yi ba tare da ta ce da ni ko kanzil ba illa ɗauke kanta da ta yi ta zuba idanunsa ga tvn dake aiki a cikin falon. Yanda ta basar da ni tamkar bata saurara na ko kuma bata san da wanzuwa na a wajen ba.
Sai da na cire rai da samun amsa daga gare ta kana ta furta"haka ne maganarki, zan sanar dake wani abu da na ƙudurci faɗawa duk wata matar da Abdul zai aura ya yi zaman aure da ita".
Gabana ya yi ras na dake ina gyara zamana da hakan ya bata lasisin ɗaurawa da"Abdul-hameed a cikin 'ya'ya shi na daban don haka nake ɗaukar duk wani abun da ya shafe shi azimun. Ina bashi dukkanin wata kulawa fiye ma da yanda mata zata kula da mijinta, ki riƙe shi hannu bibiyu domin samun irin sa a cikin wannan zamani abu ne mai wahalar gaske. Abin da nake son sanar dake shine Abdul-hameed ba zai zauna da mace ɗaya tal tamkar rai duk lokacin da na ga wacce ta yi min kuma hankalina ya nutsu da ita zai ƙara aure ya kawo matar cikin gidan nan".
Tsabar harbawan da ƙirjina ya yi ban san lokacin da na runtse idona da ƙarfe ina cije leɓena ba tare da kokuwa da numfashina da yake maƙale mini a ƙirji.
"Lafiya dai?".
Sai da na yi ƙoƙarin dai dai nutsuwata na furta"lafiya".
"To ina fatan kin ji abinda na faɗa?". Na ɗaga mata kaina"na ji kuma ina addu'ar Allah ya bashi ta kirki wacce zata kula miki dashi kamar yanda kike yi".
A daƙile ta amsa mini"Amin". Tana rufe bakinta Al'amin ya shigo falon tare da zubewa akan kujera ya toshe dukkan kunnuwansa da earpiece yana bin waƙar.
"Tashi ki ji ki fara shirin tarban mijinki".
"To Hajiya a tashi lafiya". Hannu kawai ta ɗaga mini na tashi na fice daga falon. Har na isa sashin ina saƙa da warwara cikin raina yayin da maganganun natan suke yi mini amsa-kuwwa a nau'rar naɗar sautina.
Shifit na zube akan gadona ina mayar da numfashi a hankali idanuna zube akan rufin ɗakin da ya zamo shamaki tsakanina da sararin samaniya.
Na daɗe kwance a wajen har sai da na ji an yi ƙiran sallan asr sannan na tashi na yi alwala nazo na gabatar da sallan. Al-ƙur'anin dake ajiye saman dirowar dake gefen gadon na ɗauka na fara karantawa ban tashi ba har aka yi ƙiran sallan magrib na sallan.
Ina naɗe sallan na hange shigowar motar Abdul-hameed cikin gidan, na tsaya ta jikin tagar ina kallonsa ya fito daga cikin motar da waya maƙale a kunnensa bakinsa yana motsi da hakan ya tabbatar mini da magana yake yi sai dai bana iya jiyo abinda yake faɗa.
Sai da ya gama wayar ya juyo na yi saurin ja da baya, a tunanin nan zai shigo amma ina leƙawa sai naga ya nufi sashin Amma. Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina tausar zuciyata da take cike da mararin son ganin sa.
Tuna furucin Amma na ɗazu ya sanya dukkan gaɓoɓin jikina yin sanyi, wata zuciyar ta ce dani gwara ma ki saba tun yanzu domin idan ya yi auren kina gani sashin wata zai shiga su kwana tare gwara nan wajen mahaifiyarsa ya je.
Na danne zuciyata na tashi na shiga banɗaki na yi wanka tare da ɗauro alwala na fito, na sha mai kaɗan a jikina sannan na saka kayana na ɗaura hijabi a kai na yi sallan isha'i. Na gyara fuskata duk da baƙin fatata amma na yi fayau da ni na ɗaura kallabi tare da shafa humrar da Dada ta ba ni, na buɗe ƙofar ɗaki zan fita muka yi kiciɓus dashi zai shigo .
Na yi saurin ja da baya ina bashi hanya ya shigo, ina ɗago idona muka haɗa dashi ya kashe mini ido ɗaya. Tare da miƙa mini hannunsa na yi ƙasa da kaina don na fahimci abinda yake nuni.
Ya ranƙwafo daidai kunnena ya yi mini raɗa"kin yi kyau kamar a sace a gudu".
"Na gode".
Na furta a hankali ya riƙo hannuna muka zauna a bakin gado ya kafe ni da ido da har sai da na fara tsorita da irin kallon da yake yi mini. Na ɗage masa idona ɗaya alamar lafiya, ya sa ki murmushi yana cewa"na kwaso gajiya sosai a wajen aiki".
"To bari na haɗa maka ruwa ka yi wanka ka ɗan huta". Ban jira amsar sa ba na miƙe na shiga banɗaki na haɗa masa ruwan wanka tare da ajiye masa komai na buƙata. Kafin ya fito na ciro masa wasu kayan na ajiye masa akan gado na fita na koma falo ina jiransa.
Jim kaɗan ya fito yana waya abu ɗaya na tsinta a cikin zancen kafin ya katse wayar shine"ka san yanda zaka gyara gidanka tun kafin abubuwa su fi ƙarfinka".
Ya katse wayar sannan ya ƙira Asabe"a shigo mana da abinci". Har ya zauna ina bin shi da kallo bai ce da ni uffan ba ya jingina kansa jikin kujerar tare da lumshe idanunsa yana furzar da iska daga bakinsa.
Na ɗan matso kusa dashi na ce"lafiya kuwa?". Ya ɗaga mini kansa haka nan kawai na ji ban gamsu ba na ƙara faɗin"don Allah ka sanar dani me ke faruwa, idan kuma bani da hurumin jin abinda yake damun ka ne sai na taya ka da addu'a. Allah ya warware maka matsalar".
Nan ma shuru ya yi ya jawo ni jikinsa na kwantar da kaina akan ƙafarsa, jin ana buga ƙofar falon ya sa ni tashi naje na buɗe Asabe ce riƙe da kwandon da ta jerin kuloli a ciki ba karva tare da yi mata sannu na shigo dashi.
Har na zuzzuba abincin yana nan zaune inda na bar shi bai motsa. Na jawo hannunsa ya sauƙa ba tura masa plate ɗin gabansa don tare na saka mana, a hankali yake ci kamar wanda aka yi masa dole.
"Ban san da waye ka yi waya ba, amma na tabbatar yin wayar ne ya jefa ka cikin wannan yanayin".
Ya ajiye cokalin hannunsa yana fuskanto ni"mijin Anty Alawiyya ne wallahi ina jin kunya da nauyinsa sosai amma Amma ta dage akan sai zai na ce masa ya aikowa Anty Alawiyya takardarta ko kuma ya zaɓa tsakanin ita da amaryar da ya yi".
Muƙut na ci abincin ya wuce da ƙyar ta maƙoshina, lalle Amma tana son nata da kuma kishin su. Nata 'yar ba zata zauna da kishiya ba akan hakan ta gwammace a sake ta, amma shi ne ni take ambata mini cewar ko ba daɗe ko ba jima Abdul-hameed sai ya ƙara aure ba zai zauna da mace ɗaya ba.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimuna Tijjani Iyam
________________________________
Page 1️⃣8️⃣
Sai na cika satikai biyu cif a cikin gidan sau ɗaya na yi waya da Umma da wayarsa na tambayi jikin Hamma Ahmad ta ce mini da sauƙi. Ban taɓa ɗaura girki ba kullum Asabe ce ke kawo mana daga sashin Amma, ban taɓa nuna damuwata akan hakan ba balle na nuna masa ina son na yi girkina da kaina. Kamar yanda shima bai taɓa cewa da ni komai akan hakan ba.
Na fahimci cewar duk cikin 'yan uwansa babu wanda yake son Amma da tausayinta kamar sa, baya taɓa tsallake kara idan ta ajiye. Sannan ba ya yi musu da ita akan dukkan abinda ta ce dashi idan ta kalli balbela ta ce baƙa ce bin ta yake yi a haka ya ce babu abinda ya kai ta baƙi.
Bayan gaisawa har yanzu babu wani zancen da ya taɓa shiga tsakanina da Anty Alawiyya balle kuma Al'amin. Basa zama inda nake balle hira da ni tun da nazo gidan basu taɓa shigowa sashina ba.
Ranar wata juma'a ya ce mini na shirya zai dawo da wuri zamu je wani waje, haka na wuni da tunanin idan zamu je. Sai da na yi sallan zuhur sannan na yi wanka na shirya cikin shigar doguwar rigar atamfar da ta sauƙa mini har ƙasa, na ɗaura kallabi ina zauna ina jiran sa.
Na daɗe zaune sai can na ji ƙaran shigowar motarsa na miƙe da sauri na naje jikin taga na tsaya ina leƙansa, kamar yanda na yi tunani sashin Amma ya fara shiga sai dai bai daɗe ba ya fito.
Na saki labulen tagar na fito falon domin tarban sa, muka sakarwa juna murmushi yana ware mini hannayensa na gane nufinsa bai wuce naje gare shi ne, don haka na kauce na wuce na kawo masa ruwa na tsiyaya masa a kofi na miƙa masa ina yi masa sannu da zuwa.
"Afuwan matar kirki na bar ki kina ta jira ko?". Ya faɗa yana zame kofin daga bakinsa, na ƙara ƙawata fuskata da annuri "a'a ban ma daɗe da yin shirin ba nima".
"To shikenan nima bari na je na shiryo". Ya miƙe tsaye tare da miƙa mini hannunsa na riƙe muka wuce ɗakinsa, kafin ya rage kayan jikinsa na haɗa masa ruwan wanka na fito ya shiga. Na ciro masa wani shadda kalar sararin samaniya na ajiye masa akan gado sai ya yi daidai da irin zanen dake cikin atamfar dake jikina.
Na ciro masa hula, agogo da maɓallin hannun rigar na ajiye masa kana na koma falo na zauna. Babu jimawa ya fito yana gyara zaman hular akan sa na yi masa murmushi ina ɗaga masa yatsan hannuna alamar ya yi kyau.
"Mu je ke ma na ciro miki kayan da za ki saka, kamar yanda kema kika ciro min".
Na waro ido ina duban kayan jikina"ai ni na gama shiri na ni kam".
"Wannan bai yi mini ba". Kafin na ce wani abu har ya shige ɗakin na bi bayan sa, yana tsaye a gaban wadrobe ɗin kayan yana dubawa.
Ya zaro wata abaya da mayafinta irin kalar shaddar dake jikinsa sai shi ya yi ɗan duhu haka.
"Yauwa wannan nake so ki saka".
Babu musu naa karɓa na shiga banɗaki na saka na fito, ya bi ni da kallo sannan ya ce na zauna a gaban madubi da kansa ya shafa mini hoda ya saka mini kwalli sannan ya shafa mini man leɓe.
Yana ƙoƙarin ɗaura mini mayafin rigar a kaina na kauce"yanzu duk gyara fuskana da na yi kafin ka dawo bai yi ba kenan?".
Ya lakace mini karan hanci yana faɗin"ya yi sosai ma, kawai ina so yau na hutar dake ne ni zan shirya ki gabaɗaya tunda na dawo da wuri".
Ban ce dashi komai ba har ya gama ɗaura mini mayafin, ya ɗauko wani mayafin mai girma da kauri ya naɗa mini a kaina. Sosai shigar ya yi mini kyau na fito na yi ɗas da ni. Hatta jaka da takalmin da zan saka shi ya zaɓa mini ya riƙo hannuna muka fito falo ya ce sai mun yi hoto.
Sai da muka gama yi muka nufi sashin Amma tana zaune kamar kullum a inda take zama, muka yi mata sannu ta amsa Al'amin yana gefenta yana latsa waya.
"Fita zaku yi na gan ku da wannan shirin?".
Ya ɗan shafa goshinsa"e zamu fita amma ba daɗewa zamu yi ba".
Sai da ta taɓe baki ta furta"kuma muna shirin cin abinci yanzu". Ya yi saurin faɗin"ku ci kawai ba komai zamu tsaya a gidan abinci mu ci".
Sosai ta tsura masa idanun da ya sanya shi rusunar da kansa ƙasa.
"Bana son ina magana ana katse ni kafi kowa sanin hakan".
"Afuwan tuba nake Amma".
Ta yi banza da shi sai can ta ce"ku tashi ku bani waje". Tabbas na san matsayin uwa darajar ta da kuma kimarta daban yake, kuma tana haƙƙi babba akan 'ya'yanta amma na yi mamakin yanda ya maraice tamkar zai fashe da kuka yana bata haƙuri cikin roƙo da magiya, furucin da ya yi a ƙarshen zancen sa ya sanya ni ɗago idona na yi masa kallo ɗaya na maida kaina ƙasa.
"Ba katse ki na yi ba domin bana fatan ganin ranar da zan katse miki zance a rayuwata. Idan ba ki amince ba sai mu fasa fitan mu bari sai wani lokaci".
"Ba zan hana ku aiwatar da abinda kuka shirya ba, amma ka kiyaye katse ni idan ina zance gaba".
Da rawar jiki ya amsa"in sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba".
Sai da zamu fita na ce"a tashi lafiya". Ko kallon kirki ban ishe Al'amin va domin tun zaman mu har muka miƙe bai ce mana ƙala ba.
A motarsa muka fita yana toƙin a hankali kamar wanda aka sanarwa da saƙon mutuwa. Na kallo shi game da faɗin"ka yi haƙuri ka daina saka damuwa a cikin ranka".
Ina iya jiyo yanda ya furzar da iska daga bakinsa, kana ya sama zarafin cewa"a rayuwata babu abinda na ƙi jininsa, nake gudunsa da kuma kiyaye faruwarsa kamar ɓacin ran Amma. Bana iya jurewa ko kaɗan".
"Ba ta yi fushi da kai ba. Ta dai nusar da kai ne a lokacin da kake ƙoƙarin kauce hanya. Kuma na lura a cikin yan uwanka kafi kowa kiyaye ɓacin ranta da ƙoƙarin son faranta mata".
Bai amsa mini ba sai da ya karya kwana kana ya ce"na kasance irin mutanen da ba basa iya ɓoye soyayyar su akan duk abinda suke so ne".
Na jinjina kaina"na ga alama". Mun ɗan taɓa hira kafin muka isa gidan cin abincin muka cika cikinmu. Mu ka ƙara ɗaukar hanya sai a lokacin Allah ya bani ikon tambayar sa inda zamu je.
"In har kin yarda da ni to kawai ki zauna ki yi shuru. Idanunki zasu gane miki inda zamu je".
Yanda ya faɗan hakan na yi na zauna na yi shuru. Ya tsaya ya sayi bandir ɗin lemukan gora da abaya da kankana aka saka masa a bayan motar, muka cigaba da tafiya. Ina ganin ya shiga layin mu na ɗago na kalle shi, ya ƙi yarda ya kalli ni. Har ya faka motar a ƙofar gidan Baba bai kalla inda nake ba.
Ya riga ni fita ya zagayo ya buɗe mini ƙofar ban fito ba na ce "daman nan zamu zo?".
"E ko baka so mu zo ne?".
Na jijjiga masa kaina na fito ya ce na shiga idan na yi masa iso sai ya shigo. Ina sanya ƙafata a cikin zauren muka yi kiciɓus da Anwar zai fita.
"Anwar".
Na faɗa muryata yana rawa saboda wani mummunan ramar da ya yi marar daɗin faɗa da baki. Shi ya fara ɗauke idonsa daga kaina yana cewa"yanzu kika zo?". Na gyaɗa masa kaina.
"To ki ƙariso mana". Yana gaba ina bin sa a baya muka ƙarisa shiga cikin gidan. Dada tana zaune akan tabarma tana sauraron rediyo, Abasiyya na gefe tana wanki.
Da tsantsar murnar da ya kasa ɓoyiwa akan fuskarta Dada ta tarbe ni tamkar za ta maida ni ciki don soyayya, sai nan da nan take yi dani. Bayan na gaishe ta ta amsa mini fuskarta kamar gonar auduga ta ɗaura da"yaya mijinki nakin"?.
"Lafiya ƙalau, tare dashi muka ke yana waje".
Salati ta saka kamar wacce nayi wani zunubi.
"Aishatu Allah ya nuna min ranar da za ki yi wayo, yanzu ku zo tare da mutum amma ki bar shi a waje a tsaye. Anwar je ka shigo dashi".
"Shi fa ya ce na fara shigowa Dada". Ta yi mini daƙuwar tare da sanya Abasiyya ta miƙo mata hijabinta daga ɗaki ta sanya. Aka shimfiɗa masa sallaya akan tabarman da muke zaune.
Duk yanda Anwar ya dage masa akan ya zauna akan sallayan, ƙi ya wa ya yi ya zauna akan tabarman ya gaishe da Dada cike da girmamawa.
Ta amsa tana tambayar "Allah ya sa dai ba ita ta ɗaga maka hankali sai kun zo ba?".
Ya yi murmushi tare da faɗin "A'a mun yi waya da Adnan ne yake shaida min har yanzu Hamma Ahmad yana kwance jikinsa ya ƙi daɗi. Shine na ɗauko ta muka zo duba shi".
"Wallahi Ahmad kam yana jin jiki sai dai addu'a, abu ya ci ya ƙi ƙarewa. Yau ne ma ya ɗan ɗaga don tunda ya fita masallacin juma'a har yanzu bai dawo ba".
Ni da shi muka haɗe baki wajen faɗin"Allah ya bashi lafiya".
"Amin".
Ta amsa dashi kafin ya furta"bari na je masallaci ana ƙiran salla kafin ya dawo". Tare da Anwar suka fita, jim ƙadan yara suka fara shigowa da kayan da ya saya aka zuba masa a mota. Dada ta rufe ni da faɗa na hau yi mata rantsuwa akan ni ba ni ce ya saya ba hasalima ban san nan zamu zo ba.
Salla nima na yi na fito na zauna na kwantar da murya na ce"ni kam Anwar shi ma jinyar ya yi ne naga duk ya rame?". Sai da ta saki sakakkiyar ajiyar zuciya ta ce"babu jinya akwai damuwa ya ɗauka ya ƙwallafa a cikin ransa. Babu irin tambayar da Baffanku da Babanku ba su yi masa ba amma ya ƙi faɗan abinda ke damun sa. Daga ƙarshe ma cewa ya yi wai karatu yake so ya cigaba dashi baya son zaman garin".
Ƙirjina ya duba da ƙarfi"don Allah Dada ki sanya baki a hana shi".
"Nima zan so hakan ya faru. Amma sai na fahimci kamar ba zai sama kwanciya ba matuƙar yana nan ɗin, gwara kawai a