Showing 54001 words to 57000 words out of 80635 words

Chapter 19 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

jikina.


"Wallahi tunanina gabaɗaya ya tsaya cak na rasa ma inda zan dafa. In har ba mu gudanar da wannan aikin a yau ba to tabbas ba zamu ƙara samun wannan damar ba. Dole mun karɓa wannan muhimman takardun daga wajensa".


Tsabar tashin hankalin da na dulmiya a cikinsa, na ma gaza tantance takamanmen mamallakin muryar da aka yi zancen da ita.
"Wasu takardu kenan?".
Na jefawa kaina tambayar da ba ni da amsarta kuma bani da mai amsa mini ita. Na daɗe tsaye a wajen jikina yana karkarwa, jin an dafa kafaɗata ya tursasa mini dawowa hayyacina daga karatun wasiƙar jakin da na faɗa. Asabe ce tsaye a gabana tana bi na da wani irin kallon da ya fi kama da na tuhuma hakan ya sanya ni saurin gyara tsayiwata ina goge fuskana.


"Ke lafiya?".


"La-la-la-lafiya wayata na manta a ciki na zo ɗauka". Sai da ta ƙare mini kallo kafin ta miƙo mini wayata tare da faɗin "ga ta nan yanzu uwargijiyata ta ba ni ta ce na kawo miki". Da hanzari na karɓa"na gode, don Allah zan nema alfarma mana ko za ki zo mu kwana tare wallahi tsoro nake ji ba zan iya kwana ni ɗaya ba".


"Ba zai yiyuwa ba domin uwargijiyata ba za ta bani damar yin hakan ba. Ki yi haƙuri kawai ki je ki yi kwanciyarki. Sannan ki taya mijinki da addu'a domin yana buƙata".
Take jikina ya ƙara yin la'asar kaina kawai na jinjina mata na ɗauki hanyar barin wajen. Na so na tambaye ta ko tana da masaniya akan inda yake amma wata zuciyar ta gargaɗe ni ba da kowa zan yarda ba.


Sai da na murzawa ƙofar falon ɗan makulli na kashe duk ƙwayayen wutar falon kana na wuce cikin ɗaki na zauna. Lambarsa da ya sanya mini da kansa na laluma tare da danna masa ƙira bayan na sanya ƙiran a amsa-kuwwa na tisa wayar a gabana ina kallonsa. Har ƙiran ya katse ba a ɗauka ba na ƙara dannawa a karo na biyu shima babu amsa. Na ƙira ya fi sau goma amma duk ba a ɗagawa dole na haƙura ba don na sama abinda raina yake so ba.


Ban ankara ba na ji ruwan hawaye suna gudu a kuncina. A bayyane na furta"Allah ya kare ka da kariyarsa a duk inda kake mijina". Domin sam zuciyata bata aminta da inda yake ba, haka na kwana ina zabura da mungayen mafarke-mafarke idona biyu yanda na ga rana haka nan na ga dare na kasa runtsawa.
Ƙiran assalatun farko kuwa tamkar a kunnuwana ladanin ya ƙwala shi, ban tashi daga inda na yi sallan ba na ɗaura daga inda na tsaya daga ƙiran wayansa amma har yanzu ba a ɗauka.


Na rasa yanda zan yi har tunanin ƙiran gida na yi na sanar dasu halin da nake ciki. Amma na ji zuciyata bata nutsu da hakan ba. Haka na wuni a ɗaka ban fita ko ina ba sai bayan sallan zuhr na ji ana buga ƙofar falon da sai yanzu na tuna da cewar ban buɗe ta ba. Na tashi jikina babu ƙwari na je na buɗe Asabe ce tsaye a ƙofar.


"Uwargijiyata ce ta ce a zo a duba lafiya ba ki fito ba har yanzu". Na murtsike idona da babu komai a cikinsa face bacci kana na ce"lafiya ƙalau na makare amma yanzu zan fito". A gurguje na yi wanka na shirya na fito duk su na zaune a falon a iske su na gaishe su suka amsa mini.


"Lafiya ba ki fito da wuri ba? Ko duk kaɗaicin rashin mijinki a kusa dake ne?".


Kaina na jijjiga mata ina ɗaurawa da"A'a kawai an sama akasi na makara ne". Ba ta ƙara cewa da ni komai illa mayar da idanunta da ta yi akan TVn dake aiki a cikin falon. Asabe ta ajiye mini abincin karin kumallona a gaba domin har sun yi nasu. Caccakala na yi na ɗebe kwanukan na kai kitchen na ajiye. Tana tare da wasu yan mata biyu suna ta aikin abincin rana, sannu na yi musu sannan na juya na fice ina jin daya daga cikin 'yan matan tana labartawa Asabe cewar tun ranar da ta fara ganina ta ji tana tausayina.


Sashina na wuce na yi kwanciyata na ƙiran layin Hamma Abubakar muka gaisa amma na kasa sanar dashi damuwata. A madadin hakan sai ɓugewa na yi da tambayarsa jikin Adda Azima ya shaida mini da sauƙi. A falon na yi sallan magrib na shafa doguwar addu'ar da na yi da hakan ya yi dai-dai da shigowar mutum cikin falon. Da hanzari na kai dubana izuwa ƙofar shigowa.
Zumbur na miƙe jikina har wani rawa yake yi tamkar mazari take idanuna suka kawo ruwar hawaye na furta"kai ne?". Kafin ya ba ni amsa tunin na isa gare shi tare da kifa kaina a ƙirjinsa ina sakin kuka. Shafa kaina yake yi a hankali kamar mai raɗa ya ce"ki yi haƙuri ki daina wannan kukan ba ga ni dawo ba. Tafiyar ce ta zo min a bazata shiyasa".
Muryata har tana shaƙewa na furta"na ƙira wayanka ya fi a irga amma ba a amsawa, na faɗa tunani da yawa ko bacci na kasa yi".


"Na manta wayata a falon Amma shiyasa idan kika ƙira ba a ɗagawa, sai yanzu da na dawo ta bani ita". Da sauri na raba jikina da nasa ina ƙare masa kallo fuskata da maɗaukakiyar mamaki na ce"ka bar ta a wajen Amma?". Cike da bani tabbacin zancensa ya ɗaga mini kansa da hakan ya yi musabbabin jin miyau ɗin bakina kaf ya tsaya tamkar rijiyar da ta yi shekaru aru-aru da kafewar ruwan cikinta.


Sai da ya taɓo ni na dawo hayyacina ya kuma ɗage mini idonsa ɗaya alamar lafiya?. Ƙasa na yi da kaina na ce"ina kaje?".
" Zan sanar da ke amma yanzu na fi buƙatar na yi wanka tukunna".
Ban ƙara faɗin komai ba na wuce ɗakinsa na haɗa masa ruwan wanka ya shiga. Na ciro masa duk abinda zai buƙata na ajiye masa akan gado na dawo falo na zauna. Ba zan iya yin komai ba sai na sama amshoshin tarin tambayoyin da suka tsaye mini a rai tamkar ƙaryar kifi a maƙoƙwaro daga gare sa.


*ƁOYAYYAR MANUFA*


©️ Maimuna Tijjani Iyam


__________________________________


Page 2️⃣9️⃣


Ban ankara da fitowarsa daga ɗaki ba sai ji nayi ana hura mini iska a fuskata da hakan ya tilasta mini ɗan lumshe idanuna ina buɗe su akan fuskarsa.
Alama ya yi mini da ido akan lafiya, na sauƙe gigitacciyar ajiyar zuciya kafin na kai ga furta abinda ke nuƙurƙusan raina da ruhina sallamar Asabe ya ratsa ƙofofin kunnuwanmu. Ya amsa mata ta shigo ta dire kulolin abincin da ta sako cikin wani ɗan kwadon.


"Yau nan aka kawo mana abincin ke nan?". Tambayar da ya yi mata ya sanya ta dakatawa ta ɗago kanta tare da faɗin"yau uwargijiyata ta ce a kawo muku abincinku nan, don ka sama ishashshen lokacin da matarka. Sannan ta ce a sanar da kai ko ka dawo daga masallaci ka wuce wajen matarka ta sallame ka sai gobe idan Allah ya kaimu mu na cikin rayayyu". Ta gefen idona nake ganinsa na lura da wani murmushin jin daɗin da ya saka yana murza hannunsa. Na san tatsuniyar gizo bata wuce labarin ƙoƙi ko shakka babu na san ganin hakan ya yi a matsayi nuna kulawar Amma a gare shi.


Har ta gama ajiye kulolin ta fice ban ce ko kanzil ba. Ya jawo ni jikinsa idanunmu suna cikin na juna ya ce da ni"menene yake damun matata na gan ta wani kala?".


"Magana nake son mu yi mai muhimmanci". Kansa ya gyaɗa mini alamar yana saurarona da hakan ya bani lasisin ɗaurawa da"ina kaje? Domin na lura tun dawowa ta jiya akwai damuwa da fargaba tare da Amma da kuma su Al'amin game da tafiyar da ka yi".


Sai da ya ɗan janye jikinsa daga nawa kafin ya furta"zan sanar dake komai, amma ba ri na je masallaci na dawo sai mu yi maganar". Kaina kawai na iya yin ƙarfin halin ɗaga masa, ya lakaci kuncina yayin da yake miƙewa, da kallo na bi shi har ya fice kafin na sa ki bayyanannen ajiyar zuciya. Sai da na ji an shiga sallar isha'in sannan na tashi daga falon.


Alwala na ɗauro na yi sallan sannan na yi wanka na shirya cikin wasu kayan marasa nauyi da takura, ina buɗe kulolin abincin ya shigo na tashi da sauri na je na karɓa sallayan hannunsa ina yi masa sannu da zuwa. Tare muka ci abincin a kwano ɗaya abinda da rabona dashi tun kwanakin biyun amarcina.
Sanin ƙa'idarsu na cewar idan ana cin abincin ba a yi ko wacce iriyar magana, ya sanya ni tsuke bakina har sai da muka gama cin abincin na tattare kwanukan na dawo na zauna.


Ya riga ni farawa da faɗin"to yanzu bari na amsa miki tambayarki Gimbiyata. Ƙauyenmu naje can garin mahaifinmu domin ganawa da wasu danginsa akan wani gonarmu dake can". Na yi ƙasa da kaina"amma na ji Al'amin yana maganar karɓo wasu takardu".


"E akwai wani gonarmu da services ɗin kamfanin MTN ya faɗa a ciki suka buƙaci a sayar musu dashi shine takardun da na tafi dashi". Duk da ya sanar da ni iyakacin abinda na tambaya amma zuciyata ta kasa nutsuwa, a sanyaye na ɗago kaina ina faɗin"don Allah idan akwai wani abun da ya dace na sani game da kai ka sanar da ni".


Yanda ya ƙura mini manyan idanunsa ma'abota girma ya tursasa mini janye nawa idanun daga gare sa. Sai da ya yi nisa kafin ya furta"kin san abubuwa da yawa a game da ni amma zan ƙara buɗa miki hanyar saboda yanzu kin zama ma'ajin sirrina".


Daga haka ya dakata tare da furzar da iska daga bakinsa ya cigaba da faɗin"tun muna yara muka fahimci akwai takun saƙa tsakanin mahaifiyarmu da kuma dangin mahaifinmu, a da ba haka Amma take ba macece mai matuƙar haƙuri, kawaici, zurfin ciki, da kuma kara.Yau da gobe ya sa ta canja, ta fuskanci ƙalubale masu yawan gaske saboda haihuwar 'ya'ya matan da take yi. Ta haifa biyu basa zuwa da rai sannan Anty Adama da kuma Anty Alawiyya, a lokacin dangin mahaifinmu suka lashi takobi matuƙar ta ƙara haihuwar ɗiya mace sai sun ba wa ɗan uwansu mata ya aura wacce ta ke da ƙwayayen halittar haifo 'ya'ya maza. Allah ya ƙaddara kasantuwana a cikin Amma har ta haife ni, ta nuna min son da kowa ya shaida har ake ganin kamar tana nuna fifiko a tsakanina da ragowan 'yan uwana. Mun rayu cikin tsangwaman dangin uba saboda Allah ya rufa masa arziki fiye dasu".


Sai da ya gyara zamansa ya cigaba daga inda ya tsaya"jin labarin faɗuwan services ɗin kamfanin MTN cikin gonan ya sanya Amma tura ni ƙauyen babu shiri, domin su sun dage akan ba za a sayar da gonar ba duk da kuwa alkhairi da riban da za a samu, to in ji dalilin fargaban da kika gani a tare dasu game da tafiyata".


Ƙirjina ya yi tsalle ya dawo kwatankwacin yanda gero ke hautsinawa yayin da ake casarsa a cikin turmin. Na yi nisan kiwo cikin tunanin da na faɗa, tabbass idan Amma ta fuskanci dukkan wannan ƙalubalen da ya labarta mini ta cika a ƙira ta jaruma. Sai dai me ye dalilinta na son jefa ni a makamancin halin da bata ji daɗin kasancewa a cikinsa ba?.


Haƙiƙa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne amma mafi yawan mata su suke zamowa matsalar junansu ba tare da sun farga da irin illar da hakan yake yi a rayuwarsu ba. Jin ya ƙira sunana da babban murya ya sanya ni dawowa cikin hayyacina, da ido ya yi mini alama akan lafiya na gyaɗa masa kaina.


"Ki daina sanya kanki a cikin damuwa Amma da sauran 'yan uwana sun yi min tsantsar soyayya. Ba zasu taɓa iya cutar dani ba ki saka haka a ranki".


Ban iya cewa dashi komai ba, ya cigaba da ja na a jikinsa. Daren ranar dai shi ya yi kiɗansa kuma ya yi rawarsa domin na kasa taɓuka komai.
Washe gari kafin ya tashi har na gama duk wani abun da zan yi, na zauna a bakin gadon na zuba masa ido. Yana buɗe idonsa muka sakarwa juna murmushi ya tashi ya zauna na matso gabansa muka gaisar da juna.
Sosai ya yaba da kwalliyata na haɗa masa ruwan wanka tare da ajiye masa duk abun buƙata akan gado na koma falo zaman jiransa. Ina latsa wayata amma sam hankalina ba nan yake ba, so nake yau nima na girkawa mijina abincin da zai ci da hannuna. So nake na ciyar da shi daga abinda na sarrafa amma sai dai babu damar yin hakan don har yanzu babu wani na'u'in kayan abinci ko ƙwayar gero a cikin sashin.


Ganin ya fito ya sanya ni ture wannan tunanin a gefe na tarbe shi tare da yaba kyawun da muka yi. A wayarsa ya ƙira Baffa muka gaisa har da Umma haka nan ma Baba sai zuba mana albarka yake yi. Cikin nishaɗi muka fito muka nufi sashin Amma muka gaisar da ita ta amsa mana fuskarta a sake.


Sai da muka gama cin abincin ta kallo shi haɗin da faɗin"kamar bakinka da magana". Ƙasa ya yi da kansa yana ɗan sosa ƙeyarsa"e daman za mu sama hutun ƙarshen shekara ne a wajen aiki, shine nake son mu yi wani ɗan tafiya tare da Aisha".


"Zuwa ina?".


"Da na ce ko cairo".


"Cairo? Da wannan ɗin za ka je cairon?". Al'amin ya ƙara jinjina zancen yana taɓe baki. Da sauri ya ɗauro kansa da nufin maida masa da amsa Amma ta tari numfashinsa"ku dakata da tafiyar sai wani lokaci. Ka san da har yanzu ba wai an raba gado bane juya su kawai kake yi don haka ka dunga sanin abinda zaka yi hidimar iyalinka dashi".


Kalamanta suka soki ƙahon zuciyata da take azalzala akan na ɗago na galla mata kallo amma na danne. Na maimaita zancen a raina daman ba su yi rabon gado ba kenan?.


"Ina lura da dukkan abinda nake kashewa na daga kuɗi. Hasalima Amma ai account ɗin da riban wancan
kasuwancin yake shiga daban yake kuma in dai ƙudin da zai shiga ko ya fita sai kin sa ni".


Banza ta yi dashi kamar ba ta ji abinda ya faɗa ba, sai can ta ce"yau idan ka taso daga aiki ina so ka je gidan mijin Alawiyya ta kwaso min 'ya'yan nan gabaɗayansu ka kawo min su nan".


"Innalillahi! Haba Amma ai duk abin bai yi zafi har haka ba. Don Allah ki yi haƙuri ko da Anty Alawiyya ba za ta koma ba a bar yaran nan su taso a gidan ubansu, ko mai lalacewar tuwo ba a canja masa suna".


Carab Al'amin ya karɓe zancen"ni fa daman tun can Amma mutumin nan bai taɓa burge ni ba. Kawai dai Yaya Abdul ne ya dage har aka yi auren nan wai don yana yayan abokinsa".
A harzuƙe Abdul-hameed yake faɗin"ka dakata min haka nan Al'amin. Sau nawa zan ja maka layi akan idan ina maganar da Amma wanda bai shafe fa ka daina yi min katsalandan?".


Tsam Amma ta miƙe ta na kakkaɓe hannu"ga ka gashi idan kun ga dama ku cinye kanku. Na tashi na baku guri". Tana dasa aya ta haura sama ɗakinta. Abdul-hameed ya rufa mata baya yana bata baki.


Tagwayen ajiyar zuciya na saka ina kallon Al'ain da ya ɗauke kansa tare da nuna halin ko in kula da fushin da Amma ta yi, sai ma zaro wayarsa da ya yi daga aljihunsa yana latsawa.



*ƁOYAYYAR MANUFA*


©️ Maimuna Tijjani Iyam


________________________________


Page 3️⃣0️⃣


A sanyaye ya sauƙo na bi shi da kallo yayin da ke ƙarisowa cikin falon. Da ido ya yi mini alama akan na taso na miƙe ya figi hannuna da ƙarfi ya fara ja na muka fice daga cikin falon, sai da muka isa tsakiyar falonmu kana ya saki hannuna ya zube akan kujerar zaman mutum uku dafe da goshinsa.


A tsuguna a gaban kujerar tare da ɗaura hannuna akan hannunsa da yake bisa goshinsa. "Ka kwantar da hankalinka ka ji?". Sai da na cire tsammani da samun amsa daga gare shi kana ya furta"hankalina ba zai taɓa kwanciya ba matuƙar Amma tana fushi da ni, ba zan taɓa samun nutsuwa ba".


Na zame daga tsugunan da na yi akan ƙafafuna na yi zaman dirshan akan kafet ɗin"ai baka aikata wani abunda zai sanya ta fushi da kai ba".
Sai da ya ɗaura ɗayan hannunsa a saman nawa kafin ya ce"na aikata mana ba ki ga yanda ta bar cikin falon a fusace ba?".


"Na ga ni, amma idan akwai wanda ya dace ya shiga wannan yanayin to Al'amin ne. Domin da bai tsoma baki a maganar da bai shafe sa ba da duk hakan bai afku ba. Hamma Abdul ya kamata ka daina ɗaurawa kanka laifi akan komai". Ina iya jiyo sautin ajiyar zuciyar da ya sauƙe yana matse hannunsa dake ƙasan nashi bai ce da ni komai ba, ya saki hannuna ya tashi ya zauna yana matse hannayensa da ya haɗe waje guda yayin da yake miƙewa ya nufi ɗakinsa na yi saurin dakatar dashi da faɗin "wajen aikin fa?".


"Babu inda zan iya fita matuƙar Amma ba na fushi da ni, ko nake ba zan iya taɓuka komai ba".


Yana gama faɗin ya shige ɗakinsa na bi bayansa da kallo raina cike taf da tsantsar mamaki . Ni dai ban ga laifin da ya aikata da za ta ɗau fushi dashi ba hasalima Al'amin shi ne mai laifin ba shi ba.


Take zuciyata ta fara harbawa da ƙarfi ina soyayyar da kowa yake faɗa cewar Amma tana yi masa?. Anya akwai uwar da za ta yi wa ɗan da ta haifa irin hakan kuwa?. Tsam na miƙe a ƙoƙarin ƙaryata hashashen zuciyata mai munin gaske.


Ranar wuni na yi ina lallashinsa da ba shi baki. Ko da muka je

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login