Showing 9001 words to 12000 words out of 80635 words

Chapter 4 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

a cikin layin daman tun lokacin auren su Hamma Abubakar ne ranar an yi ruwa ya fancakala mini ruwan kwata a jikina shi ne wai yake bina zai ba ni haƙuri".
Hamma Ahmad ya yi ƙwafa yana nuna yi da 'yar manuniyar yatsarsa"shi ne kuma ba ki taɓa faɗawa kowa ba".


"Na faɗawa Anwar tun a lokacin". Na furta ina nuni da Anwar ɗin dake tsaye a bayan su.


"To ki nutsu ki ji ni, wallahi kika kuskura na ƙara ganin ki ki sanya ƙafa kin fita daga cikin gidan nan a irin wannan lokacin sai kin yi mamakin matakin da zan ɗauka. Duk wani aike a ba wa Anwar ya je ya siyo".
Furucin Hamma Adnan kenan yana saka kai ya shige ɗakinsu, Hamma Ahmad ya kallo ni yayin da yake rufa masa baya"ki kiyaye". Na ɗaga masa kaina da sauri.


Umma da tun ɗazun ba ta kuma cewa komai ta zo ta ɗauki ledar sugar tana faɗin"kin kyautawa kan ki". Haka na cigaba da kukana Anwar yana lallashina ina jin gyaran muryan Baffa dake alamata mini zai zo na yi zumbur na shige ɗaki. Sai da aka jera kwanaki biyu muna wasa 'yar ɓoya dashi, faɗawa kuwa na sha shi a wajen Umma tamkar za ta yi aron baki.


Bayan abun ya lafa ina zaune a ɗakin kwananmu ina shafa mai a fatata mai duhu. Na ji sallamar Abasiyya.
Umma ta amsa mata kana ta ɗaura da"ke dai kam Abasiyya tufarkalla, ba kya taɓa shigowa gidan nan ba tare da sallama ba". Na san gugan zana Umma ke son yi mini don haka na ɗago labule na leƙo"ita ma ɗin munafurci ne sai da ta tabbatar kina tsakar gidan, sannan ta ƙirƙiro sallamar ta shigo da ita". Umma ta sa ki dariya tana miƙewa, na gallawa Abasiyya harara na koma na cigaba da sha mai ɗin.


Ta shigo ta zauna tana kallo na har na saka kayana na ɗage mata ido ɗaya alamar lafiya. Ta sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi kafin ta ce"lafiya ƙalau Hamma Ahmad ne ya aiko ni na ƙira ki".


Na taɓe baki "shine kika zo kika wani tsare ni da ido" . Bata ce dani komai ba illa murmushi da ta saka, ta jira ni na sanya hijabina muka sanar da Umma kafin muka fita. Ɗakin dake zauren gidansu Abasiyya ta ce mini yana ciki, na yi sallama sai da aka amsa sannan na ɗaga labulen na shiga.


Yana zaune akan ɗaya daga cikin kujeru biyu da suke ɗakin, na zauna a ƙasa nisa dashi kaɗan na ce"an ce kana nema na". Ina ina jiyo sakakken ajiyar zuciyar da ya sauƙe da matuƙar ƙarfi kana ya soma cewa"haka ne wani magana nake so mu yi dake". Na ɗaga kaina alamar ina sauraron sa.


"Su Baffa ne suka umarce ni da na zo na nema amincewar ki, idan kin amince mun daidaita kanmu. Suna son a haɗa tare da na su Adnan". Babu shiri na ɗago kaina ina yi masa wani kallo cike da son ƙarin bayani game da furcinsa da ya yi mini a dunƙule.


"Amincewata akan meye kenan?".


Ya ɗan yi jim kafin ya furta sunana a kasalance"Aishatu". Na amsa a sanyaye sannan ya cigaba da" na daɗe da fahimtar cewar son da nake miki ya wuce na 'yan uwantaka, ina miki so irin wanda nake fatan yin rayuwa dake har ƙarshen rayuwata idan kin bani dama".


"Ka yi mini afuwa har yanzu ban gane abinda kake son ka faɗa ba".


"Ina son ki Aishatu".


Take tsikar jikina ya tashi na ɗago ido na yi masa kallo ɗaya sannan na kawar da nawa idanun gefe guda. Tsawon ɗakiƙu ashiri cikin mu babu wanda ya ce ko kanzil, kowa da abinda yake saƙawa a cikin ransa. Na ji muryarsa ya katse mini hanzari.


"Ki je ki yi tinani sannan ki yi istikata. Ina son ki sanar dani duk abin da ke ranki game da ni kar ki ɓoye min komai. Babu wanda zai yi miki tilas akan abin da bakya so" Da mutuwar jiki na ɗaga masa kaina sama alamar na ji. Sai da ya bani damar tafiya sannan na tashi na fice daga ɗakin. Ko cikin gidan ban shiga ba na koma gida jikina gabaɗaya babu kuzari tamkar kazar da aka jefa da ruwar gishiri. Ban tarar da Umma a tsakar gida ba don haka kai tsaye na shige ɗakin kwanan mu na zauna na zabga tagumi da hannu biyu.


Allah ya sani ban taɓa koda mafarkin yin soyayya da Hamma Ahmad ba balle har ya kaimu ga yin aure. Bugun zuciyata ya tsananta ba zan iya kallon tsabar idon shi na ce dashi ba zan iya aurensa ba. Sai dai tabbas zan cutar da kaina cutarwa mafi illa domin zan yi rayuwa ne ba tare da farin ciki koda na sakan ɗaya ba.


Ban ankara na ji hawaye yana gudu a bisa fuskata, na kwanta na yi lamau ina ta tinane-tinane. Haka ranar na wuni tamkar marar lafiya ko Umma na kasa faɗawa ba. Sai bayan sallan magrib Anwar ya shigo lokacin muna ci abinci da Abasiyya, ya gaishe da Umma sannan ya zauna akan dakalin ƙofar ɗakin mu.


"Yau lafiyarki kuwa?". Muryarsa ta dawo ni duniyar zahiri daga duniyar tunanin da na faɗa. Kallon shi kawai na yi ba tare da na ce komai ba na tsame hannuna daga kwanon abincin na koma gefe. Ya kuma cewa"Umma ba ta da lafiya ne?". Ta yarfa hannunta alamar bata sa ni ba tana tashi ta shige ɗaki. Ya dawo kusa da ni ya tsuguna akan ƙafafunsa ya ce"Boɗɗiam menene yake damun ki?". Maimakon na bashi amsa sai na tsinci kaina da sakin hawaye.


"Subhallahi kuka kuma Boɗɗiam? Menene yake faruwa?".


"Wata magana nake so yi". Na faɗa tare da ɗago kaina wasu hawayen suna ƙara zubo mini. Ya juya ya ga Abasiyya da tayi shuru tana sauraron mu ya ce"tashi ki ɗauki abinciki ki bamu guri". Ta tashi ta shige ɗaki ta ba mu waje. Ya gyara tsugunan da ya yi ya furta" ina jinki menene?".


Na rasa ta inda zan fara sanar dashi domin na rasa makama, ya sausauta muryarsa ƙasa ƙasa ya ce"ki gaugauta sanar da ni zuciyata bugawa take yi da ƙarfi". Na zuƙe majinar kukan da yazo mini kafin na sama zarafin faɗin"su Baffa ne suka ce Hamma Ahmad ya zo ya nema amincewata, idan mu daidaita kanmu a haɗa tare da na su Hamma Adn...". Ban ƙarisa ba sakamakon firgicin da na ke iya hangowa a fuskarsa.


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam


Page 0️⃣6️⃣


______________________________________


Na kafe shi da ido ina faɗin"lafiya me ya faru?". Bai amsa mini ba ya dafe goshinsa da jijiyoyin kansa suka fito ɗarau ɗarau, kana ya furta"me kika ce?". Na kuma tsare shi da wani kallon da ya fi kama da na rashin fahimta.


"Su Baffa suka ce Hamma Ahmad ya nema amincewata, idan mun daidaita tsakaninmu a haɗa tare da su Hamma Adnan".


Na maimaita cikin sanyin jiki kamar yanda ya buƙata ina sunkuyar da kaina ƙasa. Sai da ya ɗauki wasu mintoti kafin ya furta"to ke kuma meye kika ce masa?". Na ja dogon numfashi na fesar"ban ce masa komai ba amma shi dai ya ce mini na je na yi istikata, sannan kar na ɓoye masa duk abinda na ji a raina game dashi".


"Kina son sa?".


Ya jefa mini tambayar da ya tilasta mini ɗago kaina na yi masa kallo ɗaya kafin na amsa da faɗin"bani da amsar wannan tambayar domin nima kaina ban sa ni ba".


"Ki yi istikatan kamar yanda ya faɗa miki in sha Allah khairan ne". Muryarsa a shaƙe ya ƙarƙare zancen yana miƙewa tsaye na bi shi da kallo"muna magana kuma ka tashi".
"Yau gabaɗaya bana jin daɗi ne, tun ina kasuwa nake jin kaina yana min ciwo. Zan je na nema magani".


"Akwai magani a wajen Umma ai bari na karɓo maka". Da sauri ya dakatar da ni"a'a ki bar shi kawai". Yana ƙare faɗin hakan ya juya da nufin ficewa daga cikin gidan, ɗaga ƙafan da zai yi ya sauƙe ya faɗi.


Na sa ki ƙara a gigice kafin na isa wajensa ina ƙwala ƙiran Umma. A tare suka fito da Abasiyya suka iso wajen tare da tambayar lafiya. Hawaye su na gudu a fuskata na ce"kawai ya tashi zai tafi ne ya faɗi". Umma ta na jera masa sannu Abasiyya kuma tunin ta zare kallabin kanta tana yi masa fiffita dashi.


Ya tashi ya na zaune riƙe da kansa, Umma ta ce na ɗebo ruwa a ƙwarya na kawo mata. Na tashi da sauri na je na ɗebo na kawo mata ta fara tofa wasu addu'o'i a ciki, kafin ta miƙa masa ta ce ya sha akan nasan. Ya karɓa ya yi kamar yanda ta ce, duk sannu suke jera masa wani na bin wani ni kam na kasa cewa komai illa hawaye na ke yi.


"Lafiya kuwa Anwar me ya faru?".


"Jiri ne daman tun a kasuwa ina jin ciwon kai".
"To Allah ya sauwaƙe tashi ka koma ka zauna, sai ka sha magani". Kamar wanda ta watsawa wuta ya zabura da faɗin"a'a zan tafi zan je na sha maganin sai na kwanta". Sai da ta kalle shi sosai kana ta ce"babu inda zaka je a cikin wannan yanayi koma ka nema waje ka zauna". Babu yanda ya iya haka ya koma ya zauna ko sallan isha'i a gida ya yi, ana fitowa daga masallaci Hamma Abubakar, Adnan da Ahmad suka shigo a tare.


Hamma Abubakar shi ya fara tambayar Anwar dalilin da ya bai gan shi a masallaci ba. Abasiyya ta yi caraf ta sanar dasu abinda ya faru ganin ya ƙi faɗa kai tsaye sai hanya hanya yake yi. Duk sannu suka yi masa kafin Hamma Adnan ya shi ɗaki ya ɗauko masa wani magani ya ba shi ya sha.


Tunda suka shigo na kasa ɗago kaina na kalli inda suka zauna, amma jikina yana bani tabbacin cewar idanun Hamma Ahmad yana kaina don haka na kasa samun nutsuwa. Na tashi na koma ɗaki, daren ranar ban iya runtsawa kamar yanda na kasa faɗawa kowa damuwar dake raina.
Na kasa tantancewa shin ina son Hamma Ahmad ko a'a, shin a ɗan uwa na ɗauke shi ko kuma masoyi. Har gari ya waye raina a cunkushe ban fito daga ɗaki ba sai da na ji gyaran muryar Baffa ya fito zai tafi kasuwa su Hamma Ahmad suna gaishe shi, sannan na fito.


Na tsuguna na gaishe shi ya amsa mini fuskarsa da fara'a, kafin ya soma tambayar jikin Anwar a wajen Abasiyya da ta shigo yanzun. Ta ce da sauƙi amma har yanzu ma yana kwance a ɗaki, duk addu'ar samun lafiya muka yi masa suka fita da nufi zuwa duba jikin nasan. Ɗaki na koma na yi kwanciyata duk abin duniya ya ishe ni duk tambayar da Abasiyya take mini ban tanka mata ba, har ta gaji don kanta ta yi shuru. Sai da na ji Umma ta ɗago labulen ɗakin tana shaida mana za ta je dubo jikin Anwar sannan na miƙe ina faɗin"nima zan je".


Tare duk muka fita muka nufi gidan bayan mun gaisa da Dada muka shiga ɗakinsa, yana kwance lulluɓe kirif da bargo. Muka zauna muna yi masa sannu ya ɗago kansa ya dube mu yana ƙoƙari tashi zaune. Idanunmu suka sarƙafe cikin na juna ya yi saurin ɗauke na shi, na cigaba da kallon shi da muraɗi ko zai ƙara ɗago idonsa amma ya ƙi yarda mu haɗa ido.


"Da Umma kuke tare ne?".


Ya katse shurun da ya karaɗe ɗakin, na ɗauke idona daga kan shi ina sauƙe ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.
"Tare muke da ita". Abasiyya ta amsa masa kansa ya jinjina, na yi saurin tare hawayen da suke ƙoƙarin zubo mini.


"Ke kuma lafiyarki? Kukan nan fa?".


Abasiyya da ta ankara da ni ta furta kaina na jijjiga mata alamar ba komai ta taɓe baki tare da ficewa daga ɗakin. Cikin sanyi jiki da na murya na ce"ya jikin?".


"Da sauƙi".


Ya amsa mini a gajarce, na kuma faɗin"ka yi haƙur...". Ya yi saurin katse ni"ba ki yi min komai ba". Hawayen da nake matsewa suka zubo"na kasa sanar da kowa Anwar".
Ina iya jiyo sakakken ajiyar zuciyar da ya sauƙe kana ya soma cewa"ki kwantar da hankalinki domin kowa ya sa ni, ko jiya Dada sun yi zancen da Baba da ya shigo".


"Me yasa jiya ka faɗi bayan na sanar da kai maganar nan?". Cije leɓansa ya yi alamar ya fara gajiya da zancen ya ce"babu na ce miki babu komai". Yanayin yanda ya yi maganar ya sanya ni miƙewa na fice daga ɗakin, Dada da Umma suka bi ni da kallo sa'ilin da nake faɗawa ɗakin kwanan mu.
Ina ji Umma na faɗin ko dai jikin Anwar ne ɗin ya yi tsananin da ya sanya ni kuka. Labulen ɗakin da iska ya ɗage shi ya bani damar hango su yayin da suke tashi suka nufi ɗakinsa.


Sai da muka baro gidan tare da Umma sannan na fito daga ɗakin. Washe gari bayan ba iddar da sallan asubahi ina zaune akan sallayan da al-ƙur'ani ajiye a gabana na kasa buɗewa balle ba karanta. Umma ta shigo ta zauna kusa da ni sai da na daidaita nutsuwata kana na gaishe ta cike da girmama ta amsa mini tana ɗaurawa da"menene yake damun ki cikin kwanakin nan duk kin canza?".


Na jijjiga mata kaina alamar babu, ta kamo hannuna ta sanya cikinta" 'yar nan ni mahaifiyarki ce babu wani abinda za ki ɓoye min. Fuskarki ta daɗe da bayyanar da damuwar da kike ɓoyewa a cikin ranki, shuru ba ya taɓa zama mafita domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa. Zancen haɗin aurenku da Ahmad shi ne yake sanya ki cikin damuwa?". Da sauri na ɗauro idona cike da mamaki na sauƙe a fuskarta.


"Kema kin sa ni kenan Umma?".


Ta sakar mini murmushi kana ta ce"na sa ni Baffanku ya sanar da ni kuma na yi na'am da wannan haɗin. Ahmad ɗan uwanki ne da ko bai aure ki ba shi mai iya tsayawa akan dukkan lamuranki ne, ko muna nan ko a bayan idonmu. Ki amsa masa domin ku ƙara fahimtar juna".


"Ba na jin son sa ne ko kaɗan a raina".


Na furta ina sunkuyar da kaina cike da kunya, ta sanya hannunta ta tallafo fuskata tare da faɗin"idan kika ba shi dama zai koya miki yanda soyayya take, har kema ki fara son sa". Tagwayen ajiyar zuciya na sauƙe mai ƙarfi.


"To".


Na furta can ƙasan maƙoshina ta shafi kuncina tana sami mini albarka cike da jin daɗin amsan da na bata. Tana fita na zabga tagumi wataƙila idan na bi maganarta na bashi daman sannu a hankali son sa nima ya shige ni. Sai da hantsi ya fito sannan na fito waje domin baccin da ban samu na yi shi daren jiya bane, na fashe shi da asubahin ba tare da na sani ba. Sanda na fito har su Baffa sun tafi kasuwa.


Na taya Umma aikace-aikace, kwaɗon zogala musamman ta yi ta ce na kai wa Anwar kafin da yammaci tazo ta ƙara duba jikin nasan. Na iske Dada da Adda Abida a tsakar gida na gaishe su sannan na shiga ɗakin Anwar. Yana zaune idanunsa akan rufin ɗakin ya yi nisa cikin tunanin da ya faɗa, ina sanya ƙafata kunnuwana suka jiyo mini zancen da ya tsaya ni yin mutuwar tsaye jikina gabaɗaya ya fara rawa.


"Ina son ta wallahi ba zan iya jurar ganin ta a gidan wani ba ni ba, ko da kuwa wanene. Allah ka mallaka min wannan baiwar takan domin kai kaɗai ka san irin tsananin son da nake yi mata".


Yana ƙare zancen hawaye suna rige-rigen zubowa daga idanunsa, ganin kwanon zogalen na ƙoƙarin faɗuwa daga hannu ya san ni dosara shi a wajen na ƙarisa shiga ɗakin. Har na zauna bai san da kasantuwa ta a cikin ɗakin ba sai na ƙira sunansa, ya yi figigi ya dawo hayyacinsa yana goge hawayen da suka ɓata masa fuska.


"Wacece ka ke so haka Anwar? Da son ta ya jefa ka cikin wannan halin?".


Tabbas na ga alamar firgici akan fuskarsa da kuma ruɗewa, ya gyara zaman sa da kyau"ni kuma? Babu wacce nake so ko mun taɓa wannan maganar dake?".
Na yi masa kallon gefe ido na ce"baka taɓa ba yanzu dai kunnuwana suka jiye mini kana faɗa".


Kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce"ban ma san na faɗi hakan ba, wataƙil zafin zazzaɓin da nake ji ya sanya ni sumbatu".


Ba don na yarda da furucinsa ba na jinjina kaina ina faɗin"Allah ya sauwaƙe". Na tashi na ɗauko kwanon na ajiye masa a gabansa tare da cewa"ga zogale Umma ta aiko maka, ta na maka sannu kafin anjima ta shigo".


Da hanzari na juya na fice kamar zan kife na faɗa kan cinyar Adda Abida ina rero kukana. Babu tambayar da basu yi mini ba amma na ƙi cewa dasu komai, Dada da ta fusata ta fara balbale Anwar da masifa da tambayar sa ko wani abun ya yi mini ya ce a'a. Na saddaƙar tare da ƙudurin ba wa Hamma Ahmad dama kamar yanda Umma ta ba ni shawara.
Bayan mun yi sallan magrib muka fito tare da Abasiyya, a ƙofar gida muka tarar da Baba Alhaji zaune a bisa tabarma da wani matashi a gabansa ya duƙar da kansa ƙasa yana sanye da fararen kaya tas. Ban tsaya wani ƙare masa kallo ba domin abinda yake gaba na ma kaɗai ya ishe ni, muka tsuguna muka gaishe da Baba sannan muka wuce cikin gidan. Ta wuce ciki ni kuma na tsaya ina sallama a ɗakin dake zaure sai da ya bani iznin shiga sannan na shiga a hankali bakina ɗauke da siririyar sallama.


Bayan na gaishe shi kowa ya yi shuru, ya katse shurun da faɗin"an gama wasan ɓuyan da ake yi da ni kenan, yau an kawo kai?". Na ƙara yin ƙasa da kaina ina wasa da yatsun hannuna. Sautisa ya kuma dira a kunnuwana a karo na biyu"to ina jin ki". Kunya ya hana ni samun ta inda zan fara yi masa bayani, take wani dabaran ta faɗo mini na miƙe na ce"daman zan ba wa Abasiyya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login