Showing 48001 words to 51000 words out of 80635 words

Chapter 17 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

nufi sashin Amma. Na haura sama sai da nayi sallama ta amsa mini sannan na kutsa kai cikin ɗakin tare da yiwa kaina mazauni na yi ƙasa da kaina. Domin na rasa ta inda zan fara, na ji muryarta mai cike da taƙama da izza ya bugi kunnuwana.


"Me yasa kika daɗe? Ina maganin?".


Cikina ya bada ƙarar ƙululu, na musguta kana na zama zarafin faɗin"wallahi ban san yanda aka yi ba, da hannuna na ajiye shi amma yanzu babu irin dubawan da ban yi amma ban gan shi ba".


Da mamakina sai naga ta saki dariya mai sauti na ɗauro kaina tare da sauƙe idanuna da ƙwalla ya kwanta a cikin su akanta.
"Aisha kina da yawan rantsuwa". Shuru na yi ina ɗauke idona daga kanta da hakan ya bata damar cigaba da"babu wanda yake shiga sashin ki balle har ya yi miki bincike ta yaya za a ce kin rasa shi?" Zan yi magana ta ɗaga mini hannu dole na haɗiye zancen kare kaina da nake son furtawa.
"Bana buƙatar jin komai daga gare ki tashi ki ba ni waje".


Jikina a sanyaye na tashi ina faɗin"a tashi lafiya". Sai da na fito daga sashin hawayen da suka ciko ƙoramar idona suka kwaranyo, ban yi wani yunƙurin dakatar dasu kamar yanda ban iya samun kuzarin kai hannu na share su ba.
Ina shiga sashina na zauna a falo ina tunanin yanda aka yi na rasa ƙulin maganin nan, wani takaici ya tsaya mini a wuya wataƙil Amma za ta yi tunanin na yi amfani da maganin ne nake ɓoye mata. Ko ma ta yi mini kallo mai fuska biyu.


Ƙiran sallan Asr ya tursasa mini tashi na yi alawa na yi salla, na ɗauko wayar da ta bani na buɗe ina kallonta, har da sabon layin MTN a cikinta. Ina kunnawa ta kawo na fara latsawa ban yi nisa ba na ajiye ta don ban iya komai da ita ba.
Har su Adda Azima suka yi aure basu da waya haka nan ma su Umma. Yayunmu maza da su Baffa su suke da wayoyi. Na yi baya na jingina a jikin kujerar da nake zauna tare da lumshe idona, ina son ganin Ummata ko don na furzar mata da tarin zantukan da suke ƙunshe a cikin raina.
Shin daman haka kowacce suruka take ko kuma ni ce kawai nake da rabon fige kazar wahalar da bani da alhakin yanka ta?.


Jin an banko ƙofar falon an shigo da gudu ya sa ni saurin buɗe idona. Ina kafe kyawawan yara guda biyu ma mace da namiji da suka nufo suka faɗo kan cinyata.
Yanda suke ƙyalƙyala dariya dake bayyanar da zuciyar su wanke take fes da farin ciki, ya hana ni ɗauke idona daga kallon burgewan da nake yi musu. Macen ce ta fara ɗago kanta tana nuna ni da yatsarta ta ce"ke ce ko Anty?".


"Ni ce waye?".

"Ke ce Antyn da Amminmu take faɗa mana".
Na ware idona cike da rashin fahimta"waye Ammin nakun?". Namiji ya yi saurin faɗin"ke ce matar uncle Abdul. Amminmu ta ce muna shigowa sashin nan zamu gan ki, ke ce ko?". Sallamar da aka yi shi ya hani ni yin maganar da na yi niyya, Anty Adama ce cikin shiga ta alfarma leshin ya yi mata ɗas a jikinta sai zabga ƙamshi take yi ta nufo cikin falon.


Fara'ar dake kan fuskantarta ya sanya ni nima ƙawata tawa fuskantar ina yi mata sannu da zuwa. Sai da ta zauna sannan na gaishe ta ta amsa mini tana ɗaura da"Afrin da Aryan sarakan zumuɗi har kun riga ni shigowa" A tare yaran suka saki murmushin da ya ƙara fito da kyawunsu.


"Anty 'ya'yanki ne?".
Ta ɗaga mini kanta na ce"Allah ya raya su bari na kawo muku ruwa". Ina kai aya na miƙe na kawo musu ruwa da lemo da suke cikin firiji na haɗo musu da kofofuna na ajiye musu a gaban su. Muka ƙara sabon gaisuwa da ita, ruwan kawai ta sha kana ta ce"mu kam tun ranar biki kin ji mu shuru ko? Wallahi a daren ɗaurin auren muka yi tafiya sai jiya Allah ya yi dawowar mu. Yau kuwa na ce a gidan amarya zamu wuni".
Kunya gabaɗaya ta yi mini dabaibaya domin ban taɓa ko tambayar ta a wajen Abdul-hameed ba. Na saki murmushi"Ayya sannu da hanya".
"Yauwa mun same ku lafiya, ya fita ko?".


"E ya fita amma zuwa bayan magrib zai dawo". Ta jinjina kanta tana zolaya da cewar"ai dole ya dawo gida tunda yanzu ya ajiye mace". Murmushi kawai na yi mata ina ta biyewa su Aryan da suke ta yi mini shirmen tambayoyi ina masu amsa daidai da fahimtar ƙwaƙwalwa da shekarunsu.


"To ya isa haka. Maza kuje sashin Amma ku gaishe ta kafin na shigo". A guje suka ruga suka fita.Ta sa ki ajiyar zuciyar da sai da na jiyo sautinsa daga inda nake zaune.
"Tun ranar da aka kawo ki gidan nan nazo mu tattauna da ke amma hakan bai yiyuwa ba. Tunda muka je gidanku kai kayan lefe na ga karancin shekarun ki, na tabbatar da cewar za ki fuskanci tarin ƙalubale a zaman ki a cikin gidan nan. Abdul ɗan uwana ne amma na san babu macen da za ta iya jure zama dashi sai mai haƙuri da kuma fahimta, ba shi da halayyar kule-kulen 'yan mata amma duk wata budurwa r da ya yi sai sun ɓata a dalilin Amma yana fifitata akan komai da kowa a rayuwarsa, wanda yin hakan ba laifi bane amma fa kowa yana da matsayinsa. Kullum addu'ata shine Allah ya haɗa shi da mace ta gari wacce za ta fahimce shi, wacce za ta kishin soyayyar da ya ke yiwa Amma ba zai rufe mata ido ba balle har ta cutar da shi, ta hanyar aikata abinda zai raba tsakanin su".


Daga haka ta tsagaita, na gyara zamana ina fuskantar da kyau.
"Amma uwata ce amma ko ni na san ba zan iya jure halinta ba a matsayin suruka, amma son da take yiwa Abdul shi ya kawo haka tun muna ƙanana take nuna kulawa akan sa da sanya ido akan dukkan lamuransa da mutane da yawa suke fassara haka a mizanin cewar tana fifita shi a kan mu. Ta jure abubuwa da yawa kafin ta same shi, ta haɗiye baƙin cikin mai ɗinbun yawa da ba kowacce mace ba ce zata iya yin hakan. Har yau ina tuna irin gori da gugar zanar da ta fuskanta daga dangin mahaifinmu akan ta kasa haifo ɗa namiji. Haihuwar Abdul shi ya wanzar da farin cikin da dishashe a cikin rayuwarta".


Sai da ta sausauta amon muryarta kana ta ɗaura da"haƙuri zan ba ki akan duk abinda zai faru a yanzu, da zaran Amma ta amince dake to babu kamar ki a wajen ta".


A bayyane na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya ina naɗe ƙafafuna waje guda."wallahi Anty har cikin raina ban taɓa kallon abunda Amma take yi da wani fuskan na daban ba. Kuma na san ko zan mutu na dawo ba zan taɓa yaudarar kaina wajen yin tarayya da ita a cikin zuciyar Abdul-hameed ba. Ina da yayu maza abinda ba zan so matansu su aikatawa uwata ba to tabbas ba zan yi shi ga wata uwar ba".
Tabbas na hangi tsantsar farin cikin da kalamaina suka dasa a fuskarta. Godiya ta yi ta jeranta mini kamar za ta yi aron baki. Ta ba ni wasu shawarwarin kana ta shiga sashin Amma don ta ce suna zuwa nan suka fara shigowa.


Na zabga tagumi da hannu bibiyu ina nazarin zancenta daki daki. Kenan duk abubuwan da Amma take aikawata a gare ni son ɗanta ne ya rufe mata ido? Kenan ta mance da cewar nima ɗiyar wasu ce. Ban taɓa samun fuska daga wani a cikin gidan mun yi dogon zance ba sai yau, duk da zuciyata tana yi mini kokonto amma na yi iya ƙoƙarin kana kaina zargin komai da zuciya ɗaya na faɗa mata duk abinda na ce.


Ganin magrib ta fara kawo kai ya sa ni tashi, na maida hulolin kujerun da su Aryan suka faɗar a ƙasa. Sai da na yi salla na karanta wasu ayoyi daga cikin suratul Muminun sannan na tashi na yi wanka na shirya cikin shirgar doguwar rigar kamfala, na yafa mayafi a kaina na fito za ni sashin Amma. Ina fitowa Abdul-hameed yana shigowa da motarsa sai da na tsaya ya gama daidaita fakin sannan na isa gare shi.


Ya kafe da lumshashshun idanunsa da babu komai a cikin su face tarin gajiya da kuma buƙatar hutu.
"Sannu da dawowa ranka da daɗe, da alama ka ɗebo gajiya zai fi kyau ka shiga ka fara yin wanka ka ci abinci. Sannan sauran abubuwan su biyo baya".
Ya saƙalo ƙafarsa ɗaya waje yana kwantar da kansa jikin kujerar motar da ya yi baya da ita ya ce"Amma kawai nake da buƙatar gani yanzu".


"Hakan ma ya kamata".


Ya miƙo mini hannunsa na riƙe sannan ya fito muka shiga sashin muna yi sallama Afrin da Aryan suka rugo da gudu suka rungume shi. Tunin ya sa ki hannuna ya ware musu hannayensa suka faɗa jikinsa.


Na lura yaran akwai surutu ba na wasa ba don tunda muka shigo bakinsu bai huta ba. Tare suka ci abinci da Amma sannan suka fara hirar su na mutanen da ban ma san su ba. Jifa jifa Anty Adama take sako ni a cikin hirar. Da ya tashi zai je ya yi wanka Anty Adama ta matsa mini akan cewar na bi shi, idanun da Amma ta tsura mini suka hana ni sakat ban tashi ba har yaje ya dawo ba, suka cigaba da hirar su.


Na zauna shuru duk zaman ya gundure ni tunanin nawa ahalin ya fara zuwa mini. Nima da yanzu ina cikin 'yan uwana suna hirarmu cike da nishaɗi.


Sai wajajen ƙarfe goma mijin Anty Adama ya ɗauke ta, na rasa abinda zan ba wa su Aryan na cika da kunya. Sai da muka je makwancinmu ya koya mini yanda zan yi amfani da wayar, ya sanya mini lambobin duk wasu wanda zan buƙata. Washe gari bayan ya fita aiki wuni na yi ina waya da Umma in na gama da ita na ce a kaiwa Dada.


Naso na tattauna lamarin Amma da ya ɗaure mini kai da Dada domin ba zan iya maganar da Ummata saboda alkunya irin ta fulani. A tashin farko Dada ta daka mini birki tare da alaƙanta hakan wai da sharrin sheɗan dake son dasa mini wasi-wasi a cikin raina.


Haka na jera kwanaki biyar cif ina ɓuɗuye a cikin kayana amma ban sama ƙulin maganin nan ba. Wata safiyar ranar juma'a bayan Abdul-hameed ya fita aiki Amma ta aiko Asabe ta yi ƙira na, tunda ta sanar dani gabana yake faɗuwa domin ban san me zan tarar ba. Duk lokacin da tayi mini irin wannan aiken sai na faɗa cikin fargaba da zulumi.


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam


________________________________


Page 2️⃣6️⃣


Da mamakina da na isa cikin ɗakin natan na tarar da Abdul-hameed zaune a gabanta, rabuwar da muka yi dashi tun fitar safe da ya yi ya kuma shaida mini zai wuce masallaci kafin ya dawo.


A hankali jikina tamkar wacce aka zarewa laka akan na yi wa kaina matsuguni sannan na yi musu sannu dukkansu. Shuru ya ratsa ɗakin na tsawon wasu daƙiƙai kafin Amma ta yi gyaran murya ta na faɗin"tambaya nake so na yi miki don tabbatar da wani abun da ni na fahimta da kaina". Cikina ya bada ƙarar ƙululu na sauƙe ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na ce"to Hajiya".


"Shin anya kina gamsar da mijinki kuwa ta fuskar shimfiɗa?".


Dam dam ƙirjina ya buda ƙarfi, wani kunya da nauyinta suka ƙara rufe ni. Na kasa cewa komai saboda yanda zancen yazo mini a baranbakau.
"Ke nake sauraro".
Ta ƙara jefa mini tambayar da ya tilasta mini furta"ba zan iya cewa komai akan hakan ba, domin shi ya fi dace ya amsa wannan tambayar".


Ta yi wani ƙasaitaccen murmushi da na gaza gano manufarta kafin ta ce "to kai ka ji abinda matarka ta ce ko?".
"Na ji komai Amma. Haƙiƙa ina samun nutsuwa daga wajenta, ta kowacce fuska tana ƙoƙarin sauƙe haƙƙina da yake kanta".


Basarwa ta yi kamar ba ta ji shi ba. Sai da ta zare gilashin dake kan karan hancinta ta ce"ka dai faɗi son ranka ne kawai, amma kowa ya gan ka ya san babu batun nutsuwa a tare da kai. Na lura matarta bata wadatar da kai don haka ka sa a ranka cewar dole ka ƙaro wani auren. Don ba zai yiyu in zuba ido ina gani wannan dalilin ya sanya ka faɗa harkan banza ba".


Da sauri ya katse ta"wallahi ba ki fahimta bane duk yanda kike tunani ba haka bane. Muna samun farin ciki daga junanmu muna sauƙe haƙƙin juna. Mace ɗaya nake da burin rayuwa da ita kuma Aisha ce". A sanyaye ya ƙare zancen da yake bayyanar da tsantsar gaskiyarsa kenan har cikin ransa.


Zuciyata ta hau tafarfasa wani ɗaci ya gauraye mini dukkan kusurwan bakina. Wani irin cin fuska Amma ke son yi mini na tattauna wannan zancen akan idona? Zancen da ta ɗaura dashi ya dakatar dani daga zancen zucin da nake yi.


"Ba ra'ayinka nake son ji ba, hukuncin da na riga na zartar nake faɗa maka. Watanku biyu da kwana biyu amma ko alamun ɗaukar ciki babu a tare da ita, dole ka yi aure dole ka kawo wata mace cikin gidan nan. Ba cin fuska nake yi miki ba ina son ki kwana da sanin hakan ne tun yanzu, kafin tafiyar ta yi nisa ki ce an yi miki rufa-rufa".


Miƙut na haɗiye miyau ɗin da ya wuce ta maƙoƙarona da ya bushe tamkar ƙasar sahara, kana na yi jaruntar sakin murmushin da ya tsaya iya kan leɓana na ce"babu komai Amma ai addini ya ba shi damar ya auri wasu matan uku bayan ni, ba ni da matsala da aurensa".


"To Allah ya sa abinda kike faɗa har cikin zuciyarki haka yake".


Na cije leɓena"har cikin zuciyata hakan yake". Taɓe baki ta yi"Allah ya yi muku albarka ku tashi na sallame ku".


A zuciyata na amsa ina miƙewa na fice daga ɗakin ba tare da ko kalle inda yake ba. Kaina tsaye ina shiga sashina na ɗauki hanyar ɗakina ya riƙo hannuna na kwafce. Ina shiga na faɗa kan gado ina sakin wani kukan da nake jin ciwonsa har cikin raina.


Ina jin shigowarsa da zaman da ya yi a kusa da ni ya kasa cewa da ni komai, ban motsa daga inda nake ba balle na ce dashi wani abu.
"Ki yi haƙuri, ke kaɗai nake so kuma da ke kaɗai zan rayuwa domin ke kaɗai ce a zuciyata. Ba zan iya haɗa soyayyarki da kowa ba, kar ki sanya maganar Amma a ranki balle har ta dame ki".


Da sauri na ɗago kaina ina kafe shi da idanuna da suke tsiyayar da ruwar ƙwalla na ke faɗin"kar na saka a raina fa ka ce? Da gaske kenan bana wadatar da kai dole sai ka auro wata ka kawo cikin gidanka?".


Yanda nake yi maganar numfashina yan fizge ya sanya shi riƙo ni gam ya manna ni da jikinsa, duk yanda na so ƙwafce kaina na kasa hakan. Kamar mai raɗa yake cewa"ki yi haƙuri shi ne kawai kalmar da zan iya furta miki a yanzu. Dole sai kin taimaka min wajen yiwa Amma biyayya". A wahale na sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi saboda dukan da furucinsa suka yiwa kunnuwana kwatankwacin irin yanda maƙeri yake dukan ƙarfe.


"Shin da gaske baka samun nutsuwa da ni?".
Sai da jijjiga mini kansa kana ya furta"ina samun dukkanin abinda nake buƙata daga gare ki ɗari bisa ɗari". A bayyane na tagwayen ajiyar zuciya ina lumshe idanuna"ina so gobe idan ka yi mini izini na je gida".


"In ce dai ba akan wannan maganar kike son zuwa gida ba?".


"Tun kafin maganar daman ina da niyyar tambayarka".
Sai da ya yi jim kana ya ce"ba zan hana ki ba amma ki bari gobe asabar ba zan daɗe a wajen aiki ba in na dawo sai mu je". Sai a lokacin na buɗe idona daga lumshe su da na yi"inda hali ina so naje na wuni tare dasu".
Sai da ya ƙara motsawa dab da ni kamar zai mayar dani cikinsa, muryarsa ƙasa-ƙasa kuma zancensa a raunane yake faɗin"don Allah alfarmar da zan nema a gare ki kar ki sanar dasu wannan maganar. In sha Allah zan shawo kan Amma har komai ya daidaita".
Wasu hawaye suka ƙara ciko mini idanuna na ɗaga masa kaina alamar na ji. Sai dai har cikin raina nake jin cewar ba lalle na iya yin abinda yake buƙatar na yi ba, dole na sanar da iyayena halin da ake ciki kamar yanda shima dukkan komai yake sanar da tashi uwar.


Sai da aka yi sallan Asr sannan ya fice daga ɗakin bayan ya gama yi mini lallashi da lallamin da basu yi nasarar ɗaɗani da ƙasa ba. Yana fita na kifa kaina a bisa gwiwa ina sakin wani gigitaccen kuka, sosai nake yin kukan da jin cewar gabaɗaya zaman gidan ya gundure ni. Ji nake yi kamar na ruga a guje na fice daga cikinsa.


Shin Indai haka zafin kishi yake to tabbas nawa babba ne kuma ya sha bambam da na sauran matan duniya. Domin jin ƙirjina nake yi tamkar ana sanya tsinin mashi ana sukana. Babu abinda yake yi mini yawon a kwanyata sai zancen Amma.
Da ƙyar na tashi na shiga banɗaki na kwance fuskana tare da ɗauro alwala, na fito na tsaya a gaban madubi ina ƙarewa ƙiran halittar jikina kallo. Ban kasance irin matan da marubutan ƙagaggun labarun hausa suke siffantawa ba, ba ni da hasken fata amma ina da kyawun fata mai laushi. Ba ni da cikar ƙirji sai dai ina da kyawun zubi, tsayi da kuma gashi. Ba za a sako ni a cikin kyawawan mata ba amma ina da kyawu daidai irin nawa.


Na ja ƙafafuna da suka yi sanyi ƙalau na saka hijabi tare da fuskantar alƙibla na tada da kabbara. Na daɗe kan sallayan ina addu'ar neman mafita da samun sauƙin halin da nake ciki, ban saka rai da shigowarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login