Showing 21001 words to 24000 words out of 80635 words
Chapter 8 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt
abinda yake tafe da ni".
Na faɗa duniyar tunani da nazari me yake nufi da cewar da iznin iyayena ya zo nan?. Na juyo a birkice"ban gane me ye kake nufi ba?".
"Ki zauna sai na sanar dake za ki fi fahimtana".
Na sauƙe gigitaccen ajiyar zuciya a bayane, na yi ƙasa da kaina "ka ce da iznin iyayena ka zo nan?".
"Ƙwarai kuwa da za ki yi haƙuri da kin ji abinda yake tafe da ni".
A hankali na tako na ɗosana akan tabarmar zuciyata tana dakan lugadai. Ya gyara zamansa kana ya soma faɗin"na san za ki mamakin ganina a gidanku ko?". Na ɗaga masa kaina ya cigaba da"tun lokacin da Allah ya haɗa fuskokinmu na ɓata miki jiki da ruwa a bisa kuskure na ba ki haƙuri kuma ba ki saurare ni. A lokacin na ajiye motata ba bi ki a ƙafa har na ga gidan da kika shiga, da yamma bayan na dawo daga aiki na bi ta layin ko zan ganki amma ban sama ganin ki ba. Tun daga lokacin nake ta addu'ar Allah ya sa na ƙara yin tozali da ke, Allah bai nufa ba sai lokacin da na tsaya na yi sallan a wannan masallacin na gan ki, a lokacin na ga gidan da kika shiga. Bayan na tafi na yi bincike akan gidanku har na sama wasu bayanai na zo na iske mahaifinki ya ce zasu gudanar da bincike a kaina daga baya zasu neme ni".
Ya tsagaita sannan ya ɗaura da"tun daga ranar da ya ce na je sai sun neme ni nake kwana cikin zulumi da fargaba, sai dai na dage da addu'a da kai kukana ga Allah. Kwanaki biyu da suka wuce ya nemi da na zo na yi farin ciki sosai da ya shaida min cewar sun ba ni damar fara zance da ke mu fahimci juna kafin na turo magabatana".
Zuciyata tana ɗillin ɗillin na ce"daman kai ne wanda su Baffa suke faɗa?".
"Ni ne Aishatu kina mamaki har yanzu ko?". Na daga masa kaina. "To ki daina mamaki domin zuciya bata taɓa nisa da abinda take so". Na yi shuru ba tare da na ce dashi komai ba, ya kuma faɗin"ina fatan ban makaro ba wani bai riga ni ba ko?".
Na ƙara yin ƙasa da kaina, ya yi ɗan murmushi"shuru ma magana ne, hakan yana nufin dole na ƙara zage damtse kenan na yi shirin yin yaƙi da gaske".
"Yaƙi kuma?".
"E mana Indai zan mallaki zuciyarki ai abun da ya fi yaƙi ma zan yi shirin yin sa".
Yanda ya yi zancen cikin barkwanci ya sanya ni yin takaitaccen murmushi. Zancensa ya kuma ratso kunnuwana "don Allah ki ɗago kan ki ki kalle ni".
Na ɗago idona caraf muka haɗa ido na yi saurin yin ƙasa da nawa. "Allah ya sa na sama karɓuwa a cikin zuciyarki, domin tun ranar da na ɗaura ido akan ki nake jin cewar na sama abokiyar rayuwa in Allah ya yarda".
Na ɗago kaina da nufin furta abinda yake raina na hango Hamma Ahmad da Hamma Adnan suna nufo wajen, jikina ya soma rawa ban sa ni ba ko lura da hakan ne ya sanya shi jefo mini tambayar lafiya?. Tare da juyawa yana kallon inda na ƙurawa ido.
Miƙewa na ga ya yi tun kafin su ƙariso ya isa gare su, suka fara gaisawa ta hanyar yin musabaha da juna ciki raha da girmama juna tamkar sun san juna. Na kasa ɗago ido na kalli Hamma Ahmad don wani nauyinsa nake ji na musamman.
"Ina ji da wannan ƙanwar tawan fiye komai don haka ka riƙe min ita da amana da kuma gaskiya. Don ina iya jure komai a kaina amma idan aka taɓo ta bana jurewa". Furucin Hamma Ahmad kenan cikin sigar zolaya suka sa ki dariya tare da Hamma Adnan.
"Ina sha Allah za ka same ni fiye da yanda kake zato". Ya faɗa cike da girmamawa. Suka yi masa godiya sannan suka wuce cikin gidan, ya dawo inda ya tashi ya zauna yana faɗin"waɗanda 'yan uwan nakin sun burge ni basu da matsala".
"Dukkansu yayuna ne".
"Na ga kammani ai".
Ina wasa da yatsun hannuna na ce"ai kuwa kama gama dasu ko kaɗan, sai dai kawai jini duk inda yake baya ɓoya".
"Kuna kama mana sosai ma kuwa".
Na kawar da maganar ta hanyar faɗin"zan shiga ciki dare yana yi".
"Haka ne amma gashi har zamu rabu ba ki tambayi ko da sunana bane amma ni na san na ki sunan".
Cike da jin kunya na ce"to yanzu na tambaya".
"Sai da na roƙo". Na yi masa shuru ya katse shurun ta hanyar faɗin"sunana Abdul-hameed".
Kaina na jinjina masa kana na ce "na gode a huta gajiya zan shiga daga ciki". Muka miƙe tare ya sanya takalmarsa sannan ya fara ƙoƙarin naɗe tabarmar na katse shi da faɗin"da ka bar shi ma". Sai da ya naɗe tsaf kana ya ce "ba komai yanzu sai yaushe zan dawo?".
"Sai dai ka tambayi su Hammana duk abinda suka ce haka za ayi".
"To shikenan nan kafin ina son na sama gamshashshiyar amsa daga gare ki". Na saki ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ina gyaɗa masa kaina. Ya miƙa mini tabarmar na karɓa sannan ya yi mini sallama, na wuce gida.
Sai da na tsaya a zaure ina sauƙe numfashi tamkar wacce ta yi gudun ceto rai. Na shafe tsawon mintoti kana na ja ƙafafuna na ƙaria shiga cikin gidan ina shiga Baba Alhaji yana ƙoƙarin fita na yi saurin matsawa na bashi hanya.
Abasiyya da Adda Abida duk suka zubo mini idanuna har na ajiye tabarmar dake hannuna na zauna, tare da sadda kaina ƙasa duk kunya ta ishe ni.
"Baƙon ya tafi kenan?".
Dada ta furta ɗaga mata kaina na yi alamar e, Hamma Adnan ya karɓe zancen da faɗin"amma zama a wannan wajen bai kamata ba domin hanyar wucewar mutane ne. A mutunci bane tsayiwa da saurayi a hanya irin haka, don haka gaba ki shigo dashi zaure".
Kunya ya hana ni amsa masa na tashi na shige ɗaki, har mun kwanta Abasiyya ta tashe ni na murtsike idanuna ina faɗin"lafiya?".
"Ina kuwa lafiya bayan duk abinda kika aikata babu alamar nadama ki kunyar hakan a tare ke. Wallahi kin ba ni mamaki, wai ke ko nauyin Hamma Ahmad ba kya ji akan idonsa ki shigo kin dawo daga zance da wani".
Wani ɗaci na ji a raina na kai hannu zan riƙe hannunta ta yi saurin zamewa. Na ƙura mata idanu tamkar yau na soma ganinta"Abasiyya yaya ki ke so na da raina?. Da kin san yanda nake ji na tabbatar da cewar za ki yi mini uzuri".
"Ƙarya kike yi kawai son zuciyarki kika fifita fiye da komai. Ba ki damu da halin da za ki jefa kowa ba ke dai kawai farin cikinki shi kika sanya a gaba". Ban san sanda wasu hawaye masu zafi suka rige- rigen fitowa daga idanuna suna fareti a bisa kuncina. Shin da wani yaren zan yi amfani dashi wajen fahimtar da ita har ta fahimci ni ta daina jifa na da waɗannan miyagun zantukan?.
ƁOYAYYAR MANUFA
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 1️⃣2️⃣
Haƙuri kawai na bata na koma na kwanta na juya mata baya, na kasa tsayar da ruwan hawayen da yake kwaranya daga idanuna. Zuciyata sai tafasa take yi numfashina yana cunkushewa waje guda. Dole na tashi na zauna tsam saboda tarin da ya sarƙafe ni sosai nake yin tarin kamar zan shiɗe.
Na mirgino daga kan gado zuwa ƙasa na kwanta luf, ina jin wani tsaki mai dogon zangon da Abasiyya ta saka. Kafin asubahi wani zazzaɓi mai zafi ya rufe ni sai rawar ɗari nake yi. Dada da Anwar suka tashi hankalinsu a kaina da Hamma Adnan muka je chemist aka ba ni magani tare da tsira mini wasu allurai.
Wunin ranar gabaɗaya ban iya tsinana komai ba sai kwanciya, washe gari na ɗan ɗaga Dada sai kumbar baki take yi akan rashin zuwan Umma duba ni duk da ta aika a sanar da ita cewar ba ni da lafiya. Sai da na yi sallan zuhr na lallaɓa na je gaida Umma domin jiya ban je ba.
Tsakar gidan wayam babu kowa don haka kaina tsaye na wuce ɗakinta, tana kishingiɗe na iske ta nayi sallama sannan na shiga na zauna. A ladabce na gaishe ta ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa.
"Ya jikin nakin?. Jiya Adnanu ya zo yana sanar da ni cewar kun je chemist".
Na amsa muryata ƙasa ƙasa"da sauƙi alhamdulillah". Ta jinjina mini kanta tare da ɗauke idonta daga kaina, na ja jikina na motsa kusa sosai da ita.
"Umma don girman Allah ki sausata mini wallahi fushinki a gare ni ba ƙaramin tashin hankali yake saka ni ba. Yana hana ni sukuni na gwammace ki yi mini ko wani irin hukuncin ne komai tsauri da tsananin sa zan jure. Idan akan maganar Hamma Ahmad ne wallahi ni na amince ki zaɓo mini ko waye ko yaya yake na amince zan aure sa kuma na yi masa biyayya dai-dai gwargwado matuƙar hakan zai sanya ranki ya yi fari".
Na ƙarƙare zancen ina kifa kaina akan hannayenta da ba riƙe a cikin nawa, sai da ta ɗau lokaci kafin ta furta"ba ni da matsala da duk wanda za ki aure 'yar ba, amma abinda nake hange miki shine a cikin wannan zamanin da gurɓatattu suka yawaita ba lalle ki sama nagartaccen namiji kamar Ahmad ba. Ba lalle ki sama wanda zai so, ya riƙe ki bisa amana kuma ya mutuntaki da mu kanmu ba kamar sa. Ina yi miki sha'awar auren sa ne saboda kyawawan ɗabi'unsa".
Sosai zantukanta suka ratsa kwanyata tare da haifar mini da nutsuwa a dukkan jikina. Wasu hawayen suka kuma zubowa daga idona. Na gagara raba tsakanin harshe da haƙwarana balle na sama damar cewa da ita wani abu, na daɗe kaina a sunkuye kafin ta ɗago ni tana goge mini fuskata.
Murmushin da ta ƙawarta fuskarta dashi da na daɗe ban gan shi ba ta sakar mini, da hakan ya sanya ni jin rangwamen zogin da yake sokar raina. Ta yi mini nasiha mai tsoritarwa da ratsa jiki sosai akan na kula da wanda yake zuwa wajena domin mafi yawan mazan wannan zamanin babu Allah a cikin zuƙatansu.
Duk da ba na jin daɗin jikina amma zage damtse na yi. Na yi duk wasu aikace aikace, sai da na yi sallan magrib na tashi zan tafi sallamar Hamma Abubakar ya sanya ni daburcewa domin tun bayan lokacin da wannan saɓanin ya gifta tsakanin su da Hamma Ahmad ban ƙara yin tozali dashi ba.
Kiana a ƙasa na gaishe shi ya amsa mini a gajarce, na yi sallama a Umma zan fice ya dakatar da ni da faɗin"gobe da yamma ki zo gida ina son ganin ki".
"To".
Na amsa dashi ina jin wani matsanancin faɗuwar gaba, ranar baccina ragagge ne domin duk yanda na so fahimtar da Abasiyya ta kasa fahimtana balle ta yi mini uzuri. Na ci kuka sosai a banɗaki wayewar safiyar ranar da na shiga wanka, sai dai na ƙi bada ƙofar da Dada za ta fahimci wani abu tsakaninmu da Abasiyyan domin ba ta yi mini a gabanta, tsakanina da Adda Abida kuwa yanzu harara ce da kallon banza. Idan na zauna a inuwar da take zaune kuwa za ta tashi ta bar mini wajen.
Da Anwar muka je gidan Hamma Abubakar, tunda muka fito daga gida ban ce komai ba sai faman tunane-tunane nake yi. Ya tafa hannunsa tare da ɗage mini ido ɗaya alamar lafiya. Na sauƙe sakekken ajiyar zuciya"ba komai kawai na kasa samun nutsuwa ne da wannan ƙiran da Hamma Abubakar ya yi mini".
Sai da ya yi ɗan jim kafin ya furta"ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu komai".
"Zan so ya kasance cewar babu komai ɗin, amma na san idan na sakankance akan hakan ma yaudaran kaina zan yi wanda ba shi da wani amfani".
Ya kallo ni tare da faɗin"me yasa kika ce haka?".
"Saboda kowa fushi yake yi da ni".
"Har da ni?". Ya furta cikin salon kwaikwayon muryata. Na san manufarsa bai wuce domin ya sanya ni dariya ba duk ƙoƙarin da na yi murmushi kawai na iya saka gajera da iyakarsa kan fuskata, domin bai kai har zuci ba.
"Ki amsa min mana".
"E to kai ɗin ba zan iya cewa komai ba domin ban ga alama ba. Ko kuma kara kawai kake yi mini ban sa ni ba".
Ya yi turus yana kallona"ashe za ki iya yin wannan tunanin a kaina?. Wallahi ban taɓa jin haushinki don kin ƙi Hamma Ahmad ba. Abinda na yi imani dashi shi ne duk zakaran da Rabbana ya nufa da cara to fa ko ana muzurai ana shaho sai ya yi".
Na ɗan murmusa"haka ne". Muka karya kwanar da zata sada mu da gidan ya soma faɗin"ina ta jira ki ba ni labarin sabon saurayin nakin amma na ga kin tsuke bakinki kin yi shuru, ko dai an canja ni a matsayin mafi kusa dake a cikin yan'uwanmu ne ni nan ban sa ni ba?". Na kallo shi sannan na yi ƙasa da kaina"wallahi ban sama sukunin yin maganar da kowa bane ma".
"Saboda kowa ya canja miki a gidan ko?". Na jijjiga masa kaina da sauri, ya ɗaura da"kar ki yi min musu domin ina lura da duk abinda yake faru ba, kuma daman ina son na ba ki haƙuri ban sama damar zama dake ba sai yanzun".
Na ƙirƙiro murmushi na dasa a fuskata"babu komai ni kam, wataƙil ko ni ce a matsayin su na yi makamancin abinda suke yi ko ma fiye da haka".
"Ba dai wannan Aishatun da na sa ni ba, domin ni a sanin da na yi mata sam hakan baya daga cikin halayyata". Yanda ya lanƙwashe murya wajen furta zancen ban san lokacin da dariya ya suɓece mini ba, sai da na dara sosai har idona yana kawo ruwar ƙwalla.
Ya dakata da tafiyar da yake yi tare da naɗe hannayensa a ƙirjinsa ya ƙura mini idanu"idan ki na wannan walwalan ƙara kyau kike yi akan kyan da kike dashi, don Allah ki cigaba da yi ko wani yanayi za ki shiga kar ki daina kin ji?". Na ɗaga idona na kalle shi har yanzun ni yake kallo na yarfa hannu da hakan ya sanya shi ɗan lumshe idanunsa, muka cigaba da tafiyan.
"Ina jin ki".
Ya katse mini zancen zucin da nake yi, na fesar da iska daga bakina ina hango ƙofar gidan Hamma Abubakar ɗin na ce"ba zan iya cewa komai akan sa ba, domin na yi mamakin ganin sa da kuma abinda yake tafe dashi". Ya yi saurin katse ni"daman kin san shi ne?". Na jijjiga masa kaina"shine wanda nake baka labari ya fancakala mini ruwan kwata da daɗewa, Anwar wai shi ne yazo yana so na na ma rasa yanda zan yi".
"Ki nutsu ki yi shawara da zuciyarki duk abinda kika ji kin fi samun nutsuwa a kansa to bakya buƙatar neman shawarar wani. Matuƙar kin yaba da halayyarsa kuma su Baffa suka gudanar da bincike akan sa aka sake shi da dukkan nagartattun halayya, kin ga ke kam ai kin da ce. Amma kafin ki ba shi ko wacce irin amsa ki tabbatar da cewar ki yi istikata".
Ya ɗan tsagaita yana kallona dai dai sanda muka iso ƙofar gidan." Allah ya ba ki ikon fahimtar masoyinki na gaskiya, wanda tsananin son da yake yi miki ba zai sanya shi ya cutar dake ko da na daƙiƙa ɗaya bane".
Cike da rashin fahimta na watsa masa idanuna, ya sakar mini murmushi domin shi ma ya lura da cewar ban fahimta ba. Yana gaba ina bin sa a baya muka shiga cikin gidan. Muka tarar da Adda Azima tana hura gawayi cike da farin ciki ta tarbe mu kamar wasu baƙin da suka taho daga wata uwa duniya. Haka take ta jeranta masa sannu da kuma dire mana kofin ruwa a gabanmu, ta tsiyaya mana tare da miƙawa kowa.
Sai da na jiƙa maƙoshina da sanyayyen ruwan sannan muka haɗa baki wajen gaishe ta, ta amsa mana fuskarta tamkar gonar auduga. Ta na rufe bakinta sallamar Hamma Abubakar yana ratsa ƙofofin kunnuwanmu.
Muka yi masa sannu da zuwa sannan muka gaishe shi ya amsa mana a gajarce yana shigewa ciki tare da ƙiran matarsa. Muna zaune a wajen ya fito ya yi wanka ya ƙara komawa ciki. Na cigaba da hurawa Adda Azima gawayin har ya ruru na aza mata sanwa. Ta fito tare da faɗin na shiga yana yi mini magana. Ƙirjina ya buga da ƙarfi muka haɗa ido da Anwar. A sanyaye na yi sallama ya amsa mini sannan na kutsa kai ciki na zauna a ƙasa ina ƙara yi masa sannu.
Sai da ya ƙarar da wasu mintoti sannan ya ce"na ƙira ki ne akan maganan wanda yake zuwa wajen ki, Baba ya ce tare da na Adnan da Abida za a haɗa. Tun kafin su ba shi damar ganawa dake aka fara gudanar da bincike akan sa. Cikakken sunan sa shine Abdul-hameed Abba ma'aikacin ne mai rufin asiri da ya kasance mai sana'ar zanen gidaje a ƙarƙashin wata ma'aikata da take aiki da injiniyoyi ƙwararru. Mahaifinsa ya rasu shekaru huɗu da suka gabata, yana da yayye mata biyu da kuma ƙaninsa na miji guda ɗaya jal. Shi yake kula da mahaifiyarsa da kuma ƙaninsa bayan aikinsa kuma shi yake juya dukiyar da mahaifinsu su ya bari. Ya sama kyakkyawan shaida daga mutanen unguwansu, sai dai Ahmad ya yi masa fintinkau da zarra akan kyawawan dabi'u sai kawai shi ya fi shi da abin duniya ne, ban sa ni ba ko hakan kika duba ki ka zaɓe shi akan Ahmad".
Da sauri na ɗago idona da suka kawo ruwar ƙwalla"wallahi tallahi ban zaɓe shi akan Hamma Ahmad ba hasalima ni ban san da cewar ya zo wajen Baba ba. Ban da motar da na ganshi da ita wallahi ban san da duk wani abinda ya mallaka bayan ita ba".
Ya kawar maganar ta hanyar faɗin"yanzu dai kina son sa kuwa?". Na yi shuru sai da ya daka mini tsawar da ya sanya Adda Azima shigo sannan na ce"nima ban sa ni ba sau ɗaya kawai muka yi dogon