Showing 36001 words to 39000 words out of 80635 words

Chapter 13 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

bar shi ya tafi mu cigaba da yi masa addu'ar. Allah ya yaye masa duk wani damuwar da yake damun sa".


Na kasa cewa komai illa tagumin da na zabga ta janye hannuna ta riƙe"ki kwantar da hankalinki ki yi masa addu'a kawai, Allah ya kawo masa mafita". Kaina kawai na iya ɗaga mata domin jikina gabaɗaya ya mutu murus ta kuma cewa"ki tashi ki je ɗayan gidan kafin su dawo. Abasiyya ta raka ki".


Tare da Abasiyya muka fito da tunda nazo ban ji muryarta ba illa gaisuwar da ta yiwa Abdul-hameed.
"Har yanzu fushi kike yi da ni Abasiyya?".


"Me kika yi min da zan yi fushi dake?".


Na taune leɓena"shi ne nima abinda ban sa ni ba, amma don Allah ina mai ba ki haƙuri ki yafe mini idan na yi miki wani laifin cikin rashin sani ne". Ganin ba ta da niyyar kula ni ya sanya ni cigaba da"na yi kewar ki sosai wani lokacin sai na yi tunanin ki. Ko meye kike yi oho. Don Allah ki daina fushi da ni".
Na ƙarishe zancen ƙarshen cikin maraice murya, ta kallo ni dai dai sanda muka iso ƙofar gidan.


"Nima nan kullum cikin kewarki nake yi 'yar uwata".
Fuskarta ɗauke da annurin da ya sanya na ji zuciyata ta yi fari ƙal ban sa lokacin da na rungume ta ba akan layin ina yi zayyana mata irin kewar ta da nayi da kasancewa tare da ita.


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam


_________________________


Page 1️⃣9️⃣


Umma ta na zaune muka iske ta tana dama fura, na tafi da guda na cike da murnar na rungume ta.


"Ash ash!. Sai kin yi miki ɓari ne?".


Na sake ta ina zaunawa a kusa da ita, ji nake yi tamkar na shafe wasu shekaru masu tsawo ban sanya ta a cikin idona. Na gaishe ta a amsa mini fuskarta ɗauke da annurin da ya sanya zuciyata samun nutsuwa.


"Ina Baffa da su Hamma Adnan?".


"Tunda suka fita masallaci har yanzu ba su dawo ba".


Na jinjina kaina ta katse miki hanzari ta hanyar faɗin "lafiya kuwa 'yar nan?".


"Lafiya ƙalau, mun zo duba jikin Hamma Ahmad ne tare dashi muke zo". Na ƙare zancen ina karɓan ƙwaryan na cigaba da dama mata furan"na daɗe ban sha fura ba, gabaɗaya kwaɗayinta nake yi".


Abasiyya ta yi caraf ta cafke zancen"ai kuwa sai dai ki ci kan ki. Domin wannan furar na su Baffa ne". Na galla mata harara "wannan ɗin kuma shi ya burge ni, kuma ko kin ƙi kin so sai na sha".


Ina gamawa na ɗauko kofi na zuba na fara sha ina yi mata gwalo. Sai da na shanye tas na siɗe bakina, muka yi alwala muka yi sallan asr. Ina zaune akan sallaya Umma ta shigo ta zauna a bakin gadonta mai rumfa"yaya gidan na kin komai lafiya ko?".


Na yi ƙasa da kaina"lafiya ƙalau babu wani matsala".


"To madalla ki nutsu ki ƙara riƙe kanki ki san inda kike. Duk abinda za ki yi tarbiyan gidanku za ki nuna don haka ki san abinda kike yi, kuma ki riƙe gaskiya akan komai".


"In sha Allah, mun gode Allah ya ƙara girma".


"Amin".


Ta amsa mini dashi tana sanya mini albarka, mun ɗan zanta kafin su Baffa suka shigo Abasiyya ta shinfiɗa musu tabarma.
Ina daga ɗakin nake jiyo muryar Abdul-hameed yana gaishe da Baffa da Baba Alhaji, Umma ta sanya hijabi ta fita suka gaisa.


Na miƙe na bi bayanta na zauna a kan dakalin ƙofar ɗakin ina gaishe da Baffa da Baba Alhaji. Suka haɗe baki suka amsa mini suna tambayata ko da wani matsalar na ce da su babu komai.


Da zamu tafi tamkar na tsala ihu Umma sai ƙara nanata mini kalmar haƙuri take yi, da nusar da ni cewar ibadar Ubangiji nake yi don haka dole sai na yi haƙuri wajen neman aljannata.


Kuɗin da Abdul-hameed ya ajiye su Baffa fir sun ƙi karɓa dole ya ɗauke abin sa, muka koma wajen Dada duk muka tarar da su Hamma Abubakar a nan.


Muka gaisa sannan na kallo Hamma Ahmad da gabaɗaya ya canza ko maƙiyi ya yi ido biyu dashi dole ya tausaya masa, idan kuwa mai saurin hawayena sai ya yi masa ƙwalla.


"Sannu Hamma Ahmad".


Ya yi ƙaƙalo murmushin ƙarfin ya dasa a fuskarsa ya ce"sannun ki ƙanwata".


"Ya jikin?".


"Da sauƙi alhamdulillah ". Jikina gabaɗaya ya yi sanyi saboda ganin yanayin da yake ciki na kuma faɗin"Allah ya ƙara sauƙi". Duk suka haɗe baki wajen amsawa da kalmar amin.


Tabbas Hamma Ahmad bai kasance mutum mai yawan zance da shiga cikin jama'a ba amma fuskarsa baya taɓa rabuwa da annuri. Duk da yana cikin jinya wannan dabi'ar bai yasar da ita ba. Ban san lokacin da na fara hawaye ba sai da naji Dada na faɗin"kai ɗan nan kaga ɗauki matarta ku yi tafiyar ku, kafin ta fara wannan kukan natan da bata jin lallashi".


Bai amsa mata ba illa murmushin da ya yi yana satar kallo na, na ƙi yarda mu haɗa ido.


"Haba! Ke fa yanzu babba ce ko dai ba ki sa ni bane?. Ki daina kuka akan komai kin ji?" Hamma Adnan ya furta cike da kulawa a tattare a cikin kalamansa, kaina kawai na ɗaga masa.

Dada ta kawowa Abdul-hameed dammiyar fura sai da su Hamma Abubakar suka saka baki sannan ya sha ya yi hamdala. Ya ce zai jira ni a waje na shirya na fito mu wuce magrib tana kawo kai. Suka yi sallama da Dada, su Hamma Abubakar dukkan su suka miƙe zasu raka shi.


Na yi saurin faɗin"Anwar ba ri mu yi magana mana".


Na tashi na yi bayan sa muka tsaya a zaure, sai da na sauƙe numfashin da nake jin tamkar wani abu aka sanya aka yi tokare mini ƙirjina kana na sama zarafin faɗin"don Allah ka sanar da ni abinda yake damun Hamma Ahmad na san kai kaɗai zaka iya yi mini wannan".


Ya yi ɗan jima kafin ya ce"a asibiti an ce ciwon zuciya ne da kuma yawan tunanin da yake yi, amma tunda aka ɗaura shi akan wasu magungunan abin da sauƙi".


Na dafe ƙirjina"na shiga uku ciwon zuciya?". Na ɗaga mini kansa yana ɗaurawa da"ƙwarai kuwa amma fa ki kwantar da hankalinki. Ai yanzu ma da sauƙi sosai".


Na jingina bayana a jikina gini ina jin wani zogi a cikin zuciyata. Duk tausasan kalaman da ya ke yin amfani dasu wajen kwantar mini da hankali basu yi tasiri wajen tsirkar mini da sanyi a sashin ruhina ba.


"Me yasa kake son yin nisa da garin nan?". Na faɗa idanuna ɗauke da kwantattun ƙwallar da suke jiran ƙiris su kwaranyo.


"Saboda na sama kwanciyar hankali Aishatu".


"Don Allah ka yi haƙuri ka zauna a nan na roƙe ka" ya yi mini kallon ido cikin ido kafin ya ce"me yasa zan zauna?".
Na yi ƙasa da kaina da hakan ya bashi damar cigaba da faɗin"in na zauna hakan zai sanya ki cikin farin ciki?". Da hanzari na ɗaga masa kaina alamar e. Ya sa ki taƙaitaccen murmushi"to shikenan zan duba na gani".


Sai a lokacin hawayen da nake matsewa suka zubo na ce"na gode sosai bari mu yi sallama da Dada". Na koma cikin gidan muka yi sallama da Dada da kuma Abasiyya da nake jin kamar kar mu rabu da ita. Ina ta tambayar ta yaushe zata kawo mun ziyara ta ce dani kwana kusa.


Kafin mu tafi sai da Hamma Ahmad ya ja ni gefe yana tambaya ta ko ina da wani matsala na shaida masa babu komai. Haka muka tafi raina cike da kewar 'yan uwana.


Muna isa gida ko ciki bai shiga ba ya fita masallaci saboda ƙiran sallan magrib ɗin da aka fara yi. Tsam na tsaya babu shiri na saki jakar hannuna ƙasa ina ware idona akan Al'amin da ya yi ɗaɗɗaya da kayan wadrobe ɗin yana yi mini bincike........


"Time up Barrister lokacin ka ya cika".


Furucin da jami'in ɗan sanda da yake zaune cikin ɗakin ya yi kenan, da tilasta mini dakatawa dole.
Na zame daga kan kujerar da nake zaune ina sakin wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro saboda tuno rayuwata ta baya da nayi. Kafin na yi arangama da wannan mummunar ƙaddarar da ta datse mini duk wasu igiyoyin sadar da farin ciki a cikin rayuwata. Ta ɗaiɗaita jin daɗina tare da yin fatali da kwanciyar hankalina da nutsuwata.


"Ki yi haƙuri ki cigaba da addu'a, sai mun haɗu a kotu a zama na gaba".


Ƙirjina yana harbawa da matuƙar ƙarfi, tamkar mai lalurar numfashi haka numfashina yake ja. Muryata ta dushashe na kasa cigaba da yin hawayen.


A hakan idona ya fice na kasa cewa komai aka mayar da ni cikin ɗakin da aka ɗauko ni.
Na yi imanin cewar izuwa yanzu kam ruwan hawayena sun ƙare domin sam na gaza yin kuka da hawaye. Addu'a kawai nake yi Allahu ya ɗauki rayuwata ko zan sama salama don a wannan yanayin mutuwar ce kaɗai hutu a gare ni.


'Ya'yana su kaɗai nake da tsananin buƙatar gani da kuma sanin halin da suke ciki, ko yanzu suna ina oho. Haka na wuni na kwana cikin wannan halin bana iya cin komai balle wani abu ya iya wucewa ta maƙoshina.


Ko rufe idona na yi hotun Abdul-hameed ɗauke da ƙayataccen murmushi a fuskarsa kawai nake gani . Idona biyu nake kwana yanda naga rana haka nan nake ganin dare bana runtsawa.


Bana bambamce wuni da dare domin ba na fita ko ina, na yi imanin cewa da mutane sun irin yawan son da nake yiwa mijina da ba zasu zarge ni da zan iya cutar dashi ba balle raba gangar jikinsa da numfashinsa.


Ban san adadin kwanakin da na ɗauka a haka ba, sai da aka zo aka fitar da ni ɗakin da ake ganawa da mutane. Dishi dishi idanuna suke iya gano mini Hamma Ahmad da yake zaune, ba kasa zama akan kujerar na durƙushe akan gwiwata.


"Aishatu".


Ya ƙira sunana cikin muryar dake bayyanar da tsantsar tashin hankalin da yake ciki.
"Kar ki yi kuka addu'a za ki yi".


Na ɗago rinannun idanuna na zube su akan fuskarsa"Ina Umma? Ina su Ashraf?".


"Duk suna nan lafiya ki kwantar da hankalinki. Muna zo sau huɗu tare da Baba ana hana mu ganin ki, sai yau aka bani mintuna ashirin na gana dake kafin gobe a koma kotu. Don Allah na roƙe ki ƙanwata ki faɗi dukkan gaskiyar ki akan lamarin nan kar ki ɓoye komai, Barrister Aliyu ya tabbatar mana da cewar zai taimaka miki".


Na ji wani ɗaci ya gauraye mini dukkan kusurwan bakina"Hamma bana buƙatar wani taimakon da ya wuce addu'ar ku a halin yanzu. Gwara nima a kashe ni na huta domin na tabbatar ko an bar ni ba zan yi tsawon rai ba zan mutu".


"Kar ki ce haka in sha Allah Indai da gaskiyar ki babu abinda zai sa a kashe ki".


Sai a lokacin na sama damar sakin wani gigitaccen kuka mai sauti bil haƙƙin nake kukan, ina nadamar kasancewata a cikin wannan duniyar haka ina ji ina gani aka fitar da ni daga ɗakin.


Haka na kwana idona biyu washe gari aka zo aka sanya mini ankwa aka fitar da ni, babu masaka tsinke a harabar kotun ko ina ka wulga mutane ne cike maƙil.


Aka fito da ni daga motar kafin na ankara na ji ruwan duwatsu a jikina, jami'an tsaron suka kewaye ni tare da umartan mutanen su ja baya.


Da ƙyar nake ɗaga ƙafata da nake jin cewar tamkar baya jikin gangar jikina. Na ƙarisa inda aka nuna mini domin tsayiwa.
Na hangi Anty Adama da Al'amin a cikin 'yan zaman kuton suna gefen 'yan uwana da kallon banza, ina jin kaina yana juyawa na ɗauke idona daga kan su.


Magatakardar kotun ya gabatar da shari'ar da za a saurara sannan ya miƙawa Alkalin takardan.
"Lauyan wacce ake zargi ya gabatar da kansa".


"Sunana Aliyu Sanusi lauyan wacce ake zargi. Na gode ya mai girma mai shari'a". Ya yi wasu rubuce rubuce sannan ya ce"lauyan gwamnati ko kana hujjan da zaka gabatarwa kuto?".


Da karsashi ya miƙe"ƙwarai kuwa ya mai girma mai shari'a, zan so inspectorn da aka sanar da su kisan da Aisha ta yi ya bayyana a gaban kuto".


Wannan jami'in ɗan sandan ya taso ya fito gaban kuto, sai da Barrister Adam ya tako ya matso gabansa kafin ya ce"zan zo ka sanarwa kuto yanda kuka tarar da faruwar lamarin bayan da aka ƙira ku".


"Misalin ƙarfe ukun yamma aka ƙira mu aka sanar damu cewar an yi ƙisan kai a wannan unguwar, muka je tare da sauran ma'aikatan mu muka tarar da mamacin kwance cikin jini da kuma wannan baiwar Allahn a gefe cikin yanayi da ɗimuwa, mun miƙa gawar sashin bincike yayin da ita kuma kuma ajiye ta a wajen mu kafin muka miƙa ta kuto".


Kuton ya ɗauki hayaniya mai shari'ar da ya dakatar da suturun tare da umartan Barrister Adam ya cigaba da tambayoyinsa.


"Za ka iya komawa ka zauna mun gode, yanzu kuma zan so likitan da ya yi bincike akan gawar marigayi Abdul-hameed ya bayyana a gaban kuto".


Wani farin mutum mai diri ya fito gaban kuton, Barrister Adam ya soma faɗin" a irin ƙwarewar aikin ku na likitoci, meye bincikenku ya nuna muku shi ya yi musabbabin rasuwar marigayi Abdul-hameed?".


"A binciken da muka gudanar ya nuna mana cewar caka masa wani ƙarfe mai kafi aka yi dangin su wuƙa da dai sauran su. An caka masa a ƙahon zuciyarsa har sau biyu, sannan a jikin wuƙar da aka yi kisan da ita tambarin hannun wajen ake zargi muka sama".


Kan ka ce kwabo kotun ya rikice da suturu, kaina ya soma juyawa ina ganin abubuwa yana rabuwa bibiyu a idanuna. Bisa furucin da wani dattijo ya guntso ya furzar, tsabar takaicin dake karzan ransa har ƙwalla ya yi.


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Me yasa masifa da bala'i ba zasu addabe mu ba?. Mata babu tausayi a cikin zukatansu ko na misƙala zarratin, ki ɗauki wuƙa ki daɓawa mijinki don tsabar zalunci. Allah wadaran ki da haihuwar irin ki gwada mutum ya ƙare rayuwar sa babu 'ya'ya babu jika".


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam


_________________________


Page 2️⃣0️⃣


Ɗif ji da ganina suka ɗauke na wucen gadi. Na dafe katagon da ya kewaye inda nake tsaye. Saboda jirin da yake neman kwaɗa ni da ƙasa.
Ina kokuwa da numfashina da yake maƙalewa a ƙirjina da yake yi mini matuƙar zafi da zogi.


"Barrister ci gaba da tambayoyinka".


Alkalin ya furta bayan da dakatar da surutun da ya ɓarke ta hanyar buga ƙaramar gudumar dake hannunsa.


"Da waɗannan hujjojin na sakamakon binciken ƙwararrun likitoci da ya nuna tambarin hannun Aisha ɓaro ɓaro a jikin wuƙar da aka yi kisan Abdul-hameed dashi. Nake roƙon wannan kotu mai alfarma da ta gaggauta yanke mata hukunci domin ya zama izni ga raguwar mata masu irin halinta".


Zance Barrister Adam kenan cike da ƙwarin gwiwa, kafin ya gabatar da godiya ya koma ya zauna. Sai da Alkalin ya ba wa Barrister Aliyu damar yin tambayoyi ga likitan da jami'in ɗan sandan idan yana dashi sannan ya tashi yana gyara rigar aikin sa dake jikinsa.


Jami'in ɗan sandan ne ya fara fitowa domin shi ya buƙaci fara gani.
"Zan so ka sanarwa kotu yanayin da kuka iske Aisha a lokacin da kuka isa gidan?".


"Mun same ta cikin yanayi na riɗimuwa da karaɗuwa, domin har kwanciya a gadon asibiti ta yi kafin a kawo ta nan".


"Da wannan kalmar na riɗimuwa da kaɗuwa nake son na yi amfani na fahimtar da kotu cewar tabbas akwai wani ƁOYAYYIYAR MANUFA a cikin wannan lamarin. Duk wanda yake da ƙwarin gwiwar iya ɗaukar wuƙa ya daɓawa mutum a ƙahon zuciyarsa har sau biyu, bana tunanin bayan ya aikata hakan za a tsinci shi cikin irin wannan yanayin har da zai haifar masa jinyar da za ta kwantar dashi a gadon asibiti, ina roƙon wannan kotu mai alfarma da ta ƙara mana lokacin wajen samo tarin hujjojin da zan gabatar a gaban ta".


Shuru ya karaɗe ilahin wajen tamkar babu wani halitta mai numfashi a cikinsa, har izuwa lokacin da Alkalin ya soma faɗin"bisa rashin hujja daga ɓangaren lauya mai kare wacce ake zargi, zamu ɗaga wanna shari'ar zuwa ranar uku ga watan mayun wannan shekarar da muke ciki. Za a cigaba da tsare ta a gidan ajiye ɗaurarru har ranar da za a dawo kotu".


Kowa ya miƙe tsaye akan ƙafafunsa har sai da ya fita sannan aka fara ficewa. Kowa yana tufa albarkacin bakinsa game da lamarin, 'yan jaridu suka yi miki rubgudu da ƙyar aka sama hanyar da aka sanya ni cikin motar aka komar da ni inda aka ɗauko ni.


Na shiga cikin matsanancin tashin hankali fiye da wanda nake cikinsa a yanzu, furucin Barrister Adam yana yi mini yawo a cikin kwanyata. Shin da gaske ne kenan na kashe mijina na kasha Abdul-hameed?. Da hannuna na daɓa masa wuƙar da ta yi sanadin rayuwarsa?.


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'u". Shi kaɗai kawai na iya furtawa ina dafe kaina da yake juya mini.


Kwance take jikinta ya ɗaukoi zafi tamkar garwashi, Dada da Adda Azima zaune kusa da ita.
"Sun dawo daga kotun ne?". Ta tambaya cikin muryarta da ba ta fita sosai.


"Ki yi haƙuri ba su dawo ba ki kwantar da hankalinki".


A bayyane ta sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya"ina son naje na gan ta. Wallahi a yanzu babu abinda idanuna suka fi buƙata gani kamar Aishatu". Cike da kulawa gami da tausayawa Dada ta riƙo hannunsa tare da taimaka mata ta tashi ta zauna ta jingina kanta jikin matashin da ta sanya mata a bayan ta.


"Tabbas na san kin yi haƙuri amma ki ƙara haƙuri, addu'ar ki ta fi buƙata yanzu fiye da komai kuma ko a ina kika yi mata sai Allah ya kawo mata mafita. Domin alƙawarin Allah ne addu'ar uwa baya taɓa faɗuwa ƙasa banza".


Lumshe idanunta ta yi tana cije leɓanta"ina ji a jikina zamana da Baffan yaran nan ya zo ƙarshe. Tunda ranar da aka kawo ni cikin gidansa da jajayen sawu nake bin umarnin sa, ban taɓa ƙerata kara idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login