Showing 57001 words to 60000 words out of 80635 words
Chapter 20 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt
cin abincin rana Amma ba ta fito ba haka nan ma na dare haka muka ci babu ita. Sai ƙarfe sha ɗayan dare ya shigo ɗakina don tunda muka gama cin abincin ya ce da ni naje na kwanta sai jira fitowar Amma.
Washe gari ma sai da ya makara wajen fita aiki, tun yana bani tausayi har lamarin ya koma ba ni haushi. Kwana biyun nan gabaɗaya kaɗaici ya dame ni idan ya fita ya bar ni bana yin komai har ya dawo. Daga yin kallo sai danna wayar da wani lokacin ma mancewa nake yi da ita.
A ranar da ya dawo bai shigo ba har sai da lokacin cin ya yi na fito, na tarar dashi zaune a tsakiyar wasu yara biyu duk maza sai suturu suke ta zuba masa. Na yi wa Amma sannan ta amsa mini ba tare da ta ko kalle inda nake ba.
"Afuwan kinga ban shigo ba ko?". Ban ce dashi komai ba ya cigaba da "waɗannan 'ya'yan Anty Alawiyya ne zasu cigaba da zama a nan zuwa wani lokaci". Murmushin dole na ƙaƙalo na dasa a fuskana. Muka ci abinci muka gama na yi mamakin ganin yanda Amma ta zage tana tambayar yaran irin zamantakewar da mahaifinsu yake yi da sabuwar amaryar da ya yi, yaran da babban cikin su bai wuce shekaru shida ba sai fayyace mata zancen yake yi.
Ba su yi wani dogon hira ba ta sallame mu muka yi mata sai da safe, har mun yi shirin kwanciya ina zaune a gefensa yana latsa laptop ɗin dake gabansa ya ce"ina son yara a rayuwata sosai". Na yi taƙaitaccen murmushi"ai yara abin so ne daman kana da na 'yan uwa. Kafin Allah ya baka naka".
"Ai su ba ni da cikakken iko akan su tunda ba mahaifinsu bane ɗan uwana". Na jinjina kaina cike da gamsuwa da maganarsa kafin na ce"ni kuwa me yasa Anty Alawiyya ba za ta yi haƙuri ta mance komai ta koma gidan uban 'ya'yanta ba?". Sai da ya ajiye laptop ɗin akan dirowar dake gefen gadon kana ya furta"matsalar ba daga gare ta bane domin ita ma tana son komawar idan kin lura, sai dai Amma ce ba za ta bari ba a cewar ta 'yarta ba zata zauna da kishiya ba".
Na furzar da iska daga bakina haɗi da faɗin"kana yi wa Amma dukkanin biyayyar da ko wani ɗa na gari zai yi wa Mahaifiyarsa kuma ita ma na san tana alfahari da hakan. Amma fa akwai wai gaɓar da ya dace kana nusar da ita ko kuma jawo hankalinta, yanzu ko rabuwa suka yi tana da yaƙinin cewar za ta sama marar mata wanda zai aure ta kuma ya zauna da ita tal ita kaɗai?" Jim ya yi kamar mai nazari sai can ya ce"haka ne lokuta da yawa ina son aikata hakan amma bana iyawa, ban san me yasa ba". Hannuna na ɗaura a saman nasa ina murzawa a hankali"saita lokacin da nake cikin nishaɗi za ka yi sai ka yi mata zancen cikin kwantar da kai".
"Tsarki ya tabbata da Sarkin da ya sanya mace ta gari ta zama silar samun nutsuwar mijinta". Ya furta yana shafa goshina da gashina ya kwanta ya yi luf.
Haka rayuwa ta cigaba da lafiya lokaci yana juyawa kwanakinmu yana daɗa ƙarewa. Kullum muna ƙara kusantar mutuwa ba tare da mun farga ba balle mu yi tanadin guzuri. Har na cika wata takwas cur ban taɓa yin ɓatan wata ba Adda Abida lokacin cikinta har ya fito ya yi mata ɗas. Adda Azima kuwa tunin ta kuma yin ɓarin da har yanzu Allah bai bata wani rabon ba.
Kullum sabon lamari Amma take fitowa dashi a cikin kwanakin nan komai Abdul-hameed ya yi baya yi mata gwaninta, ta maida shi tamkar bawata biyayyar da yake yi mata kuwa kullum ninkuwa yake kamar zai yi mata sujjada. Dukiyarsu kuwa baya zarar ko sule ba tare da ta tuhume shi dalilin fitar kuɗin ba.
Tausayinsa ya mamaye mini raina mussamman da Amma ta bijiro da zancen dole ya ƙaro aure tunda ni ba zan iya haifo masa 'ya'ya ba.
Kwance nake a falo na yi zurfi sosai cikin duniyar tunanin da na faɗa, na ji tsayiwar mutum a kaina da sauri na tashi. Na zabura ina murtsike idona don tabbatar da abinda idanuna suka gane mini.
Anty Azima, Adda Abida da kuma Abasiyya na rungume su tsam a jikina tsabar murna na ma rasa inda zan tosa su. Na kawo musu ruwa da lemo a dire musu a gaban su sannan muka hau gaisawan yaushe rabo.
"Amarya ba kya laifi ko kin kashe ɗan masu gida". Abasiyya ta faɗa cikin sigar zolaya na wurga mata pillown dake kan kujerar ita ma ta dawo mini dashi, Adda Azima ta yi saurin faɗin"ke ki rufa mana asiri kar ki yi mata asara".
"Asarar meye?".
"Ɗan dake cikinta mana".
Kunya ya tursasa mini yin ƙasa da kaina"ni kam Adda ba ni da komai". Dariya kawai ta yi dake alamta mini cewar ba ta gamsu da zancen nawan ba.
"Ina Hamma Ahmad da Anwar fa?". Na furta a ƙoƙarin kawar musu da zancen. Duk suka yi shuru sai Adda Abida ce ta amsa mini da faɗin"Hamma Ahmad yana nan Anwar kuwa ya tafi can Jigawa wajen Goggo".
Na ɗago kaina ina kallonta"yaushe ya tafi?".
"A ƙalla zai yi wata guda".
"Haba Adda shi ne babu wanda ya gaya mini. Kuma fa muna waya da su Baffa da su Dada amma duk ba su faɗa mini ba". Na ƙare zancen muryata tana rawa.
"Tafiyar ce tazo a gaggauce shiyasa amma ai zai na zuwa gida". Duk sai na ji yanayina ya sauya ban ƙara fahimtar hirar da suke yi ba har sai lokacin da Adda Azima ta ce Abasiyya ta tashi ta taya ni ɗaura girki a mijina.
Na san ta faɗi haka ne don fitar dani daga yanayin da na faɗa. Jikina a sanyaye na ce"ba na yin girki daga sashin mahaifiyarsa ake kawowa".
"Ban gane bakya yin girki ba? Kina nufin har yanzu ba kya girkawa mijinki abincin da zai ci sai an girka an ba ku?. Cabɗijam! Lalle Aishatu ba ki da lissafi".
Furucin Adda Abida ke nan a zafafe tamkar za ta kai mini bugu, na sausauta muryata na ce"tsarin su ne haka kuma shi ma bai taɓa ƙorafi akan hakan ba". Ta yi saurin tarar numfashina"daman ta yaya zai yi miki ƙorafi tunda ya gano cewar ke shashasha ce ba ki san inda yake yi miki ciwo ba. Ki tsaya kallo ruwa kwaɗo ya yi miki ƙafa kina nan kina zaune kin sake baki a ƙwace miki miji a banzan a wofi, tun wuri ki san inda dare ya yi miki kwaci mijinki a hannunki. Yo ni Allah na tuba akwai wacce ta isa ta yi min haka ne ai dama tun lokacin da ya ce gida ɗaya zai haɗa ku da mahaifiyarsa na san cewar za a rina wai an saci zanin mahaukaciya".
Da hanzari Adda Azima ta kwaɓe ta"ke Abida ya isa haka. Yanzu idan wani ya ji fa me kike tunanin zai faru? Ai sai a ce mun zo har gidanta muna zuga ta, don Allah mu bi komai a sannu".
"Adda Azima ai abin ne da ciwo. Wallahi tun wuri kafin abun ya yi nisa ki yawa tufkar hanci. Bijirewa za ki yi ki nuna kina son a damƙa miki ragamar girkin mijinki, idan kuwa ta ƙi sai ki yi gaban kanki". Jijjiga kanta kawai Adda Azima ta yi, mun wuni tsum tare dasu sai da muka yi salla na shigar dasu sashin Amma suka gaisa, ta sanya Asabe ta bi yo mu da abinci da abin sha.
*ƁOYAYYAR MANUFA*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
________________________________
Page 3️⃣1️⃣
Tunda suka tafi nake bitan zantukan Adda Abida a cikin kwanyata. Tabbas nima ina son na ga ina girkawa mijina abinda zai ci da hannuna da kuma amfani da basirata, ƙaruwar ajiyar zuciya na sauƙe tunawa da na yi duk tsawon zamana a cikin gidan har yanzu ban san abincin da ya fi so ki kuma abin shan da yafi burge shi ba.
Banko ƙofa da shigowar 'ya'yan Anty Alawiyya shi ya yi nasarar dawo da ni hayyacina daga tunanin da na yi nutsu a cikinsa. Kai tsaye suka wuce ɗakinsa su na leƙawa, fuskana tamau kamar hadirin gabas na ce"lafiya me kuke nema haka?".
Cike da tsiwa babban Ansar ya furta "Amma ce ta ce mu zo mu duba mata ko uncle Abdul ya dawo". Na taɓe baki"to tunda kun ga baya nan ai sai ku koma ku sanar da ita abinda idanunku ya gane muku ko?". Ina dasa aya na miƙe fuu na shige ɗakina cikin ƙonar zuci. Dole sai na shafawa idanuna toka na koya maida martani akan komai da an ce mini kule na ce cas.
Sai da na yi sallan magrib sannan na ɗaga wayata na ƙira mijina, kai na tsaye na furta"me kake buƙatar ci yau?".
Da mamaki cike fal da furucinsa ya ce"duk abinda kika tanada min". Na yi murmushin jin daɗi"to shikenan Allah ya dawo mini da kai lafiya".
"Amin ya Allah".
Da haka muka yi sallama na fito na nufi sashin Amma, babu kowa a falon sai ƙarar na'urar sanyaya waje. Don haka kaina tsaye na wuce kitchen na tarar da Asabe ta kammala komai tana gyara wajen. Sannu na yi mata ina ɗaura da"Baba Asabe girki nake so na ɗauro, ko za ki taimaka ki nuna mini yanda zan yi amfani da komai?". Sakake ta yi tana bi na da idanu da alama mamakin furucina ne ya hana ta motsawa, na ƙara ware idanuna akan ta ina maimaitawa a karo na biyu.
"Uwargijiyata ta riga da ta faɗi abinda za a girka kuma har na kammala. Dokar gidan nan ne idan aka sauƙe sanwa ba a kuma ɗaura wani". Ko a jikin wai a muntsine kakkaura na taho izuwa tsakiyar kitchen ɗin na fara buɗe dorowowin ina dubawa.
"Mijina ne yake buƙata kin ga kowa ko ita Amman ba zata so na saɓawa umarninsa ba. Dambu nake so na yi akwai zogale?".
"Akwai jiya an kawo".
"Madalla! Yana ina na fara aikin da wuri". Ta nuna mini inda yake na ɗauro na fara figewa, kafin wani lokaci na gama haɗa komai na haɗin dambu. Ta kunna mini gas ɗin kasancewar ban iya amfani dashi ba na ɗaura cikin wata tukunya da aka yi ta musamman don turara dambu. Sai da na tabbatar komai ya kammalu na ce"don Allah ki dunga kula mini dashi zan je na yi wanka".
"To ai ko dan wannan daddaɗan ƙamshin da yake tashi ma, ba zan so na yi nisa dashi ba". Murmushi kawai na yi na fice na koma sashina ina jin wani farin ciki na musamman na mamaye mini raina, a gurguje na yi wanka na ɗauro alawa na gabatar da salla. Na shirya cikin doguwar rigar atamfata mai kalar sararin samaniya na kashe ɗauri tare da feshe jikina da turare.
A wajen ajiye motoci na ga motarsa da hakan yake bani tabbacin cewar ya dawo, tun kafin na ƙarisa shiga falon nake jin yanda suke hirarsu cikin raha da son juna. Na yi musu sannu sannan na zauna ina ankare da wani kallon da Al'amin ya bi ni dashi ta gefen ido yana cire leɓe. Sam na ƙi yarda mu haɗa ido da Abdul-hameed duk ƙoƙarin da yake yi, Asabe ta yi sallama tare da jere mana kulolin abinci a gaban mu da ido ta yi mini nuni da kular da girkina yake cikinsa na ɗaga mata kai alamar na gane.
Kamar kullum ya ɗauro plate zai zuba musu shi da Amma na yi saurin faɗin"ka manta alƙawarin da ka yi mini ne?". Ya ɗage mini ido alamar bai gane ba, na jawo kular gabana tare da buɗe ta kafin na ce"yau ai abinci ka yana hannuna don haka bismillah". Na ƙare zancen ina ɗaukar wani plate na soma zuba masa na tsiyaya masa man ƙuli tare da sanya masa yajin da ya daku ya yi luƙui.
Ya kafe ni da ido kamar yanda sauran ma suka yi, kafin ya yi magana Anty Alawiyya ta riga shi da faɗin"wa ya yi wannan girkin?".
"Ni ce na girkawa mijina nima ina son yau ɗaya dai ya ci girkin hannuna". Za ta ƙara yin wani maganar Amma ta ɗaga mata hannu alamar ta dakata, sannan ta karɓe zancen cikin faɗin"da iznin waye kika yi wannan girkin?". Na yi ƙasa da kaina"da izninsa na yi domin sai da na tambaye sa kuma Amma ban yi zaton aikata hakan zai zama laifi ba domin a ganina kyautatawa ne na yi gare shi. Kuma ina da tabbacin ke ma za ki so duk wani abunda zai faranta masa".
Na ƙarƙare ina ɗago idona domin karantar yanayin fuskarta da ya cika da tsantsar mamaki da ya kasa ɓoyiwa sai da ya bayyana. Sai da ta ɗau lokacin kana a gajarce ta furta"kai ka taba iznin shiga madafa ta yi maka girki?".
Inda-inda ya soma yi ganin hakan ya sanya ni saurin yin caraf na cafke zancen da faɗin"kullum nuna mini hanyar da zan samar masa da farin ciki da kwanciyar hankali ki ke yi. Kuma girki yana ɗaya daga cikin ababen da yake ɗaurar da ƙauna tsakanin ma'aurat...". Tsawar da ta doka mini ya tursasa mini haɗiye raguwar zancen tare da runtse idanuna da ƙarfi saboda bugun da ƙirjina ya yi.
"Ina sauraron ka".
"Ni na ba ta izni".
"Menene dalilinka na yi hakan?. Shin abincin da ake yi ne ba ka so ko kuma ba ayin sa yanda kake so ne?". Da hanzari ya jijjiga kansa"ko kaɗan ba haka bane tabbas ina samun duk abinda nake so. Ganin ba ta taɓa bijirowa da zancen tana son girka wani abu bane sai a wannan karon shiyasa na bada dama".
Ba ta ce dashi ko kanzil ba ta tashi daga kishingiɗewar da tayi ta jawo kular farar shinkafa da miyar da ta sha ganye ta fara zubawa a plate. Har ta fara cin abincin ba ta ce dashi komai ba kamar yanda shi ma ya kasa kai koda loma ɗaya na dambun da na zuba masa.
Na haɗiye wani miyau mai ɗacin gaske daga maƙoshina kana na furta"bismilla ka ci mana". Sai a lokacin Amma ta ce "ban yarda da dambun nan ba, ba ta cokalin ta fara ci tukunna".
Ƙirjina ya yi wani wawan bugun da ya sanya ni watsa mata wani kallo ba tare da sanin da na yi ba. Ta ware mini idanunta cike da son tabbatar mini da zancen ta, na kasa aiwatar da komai sai hawayen da suka fara gudun famfalaƙi a bisa kuncina.
"Idan babu wata ƁOYAYYAR MANUFA to ki fara ci tukunna kafin Abdul-hameed ya ɗanɗana". Anty Alawiyya ta furta cike da gatsali da hakan ya ƙara ƙarfin gudun hawayena. Cikin rawar jiki da na murya na furta"wallahi ba zan taɓa iya cutar da Abdul-hameed ba, ko wani naga zai cutar dashi sai inda ƙarfina ya ƙare balle kuma ni da kaina ". Al'amin ya yi saurin daka mini birki"salla malama ki yi abinda aka umarce ki kawai, daga magana za ki fara wani koke-koke a muta....". Marin da Abdul-hameed ya ɗauke shi ya shi ya hana sa dire zancen da ya ɗauko tiryan-tiryan cike da tijara, idanunsa har wani ƙankancewa suka yi yake faɗin"ka san da wacce kake magana kuma ki ita ba ta kai ka girmama ta ba ai za ta ci darajata. Aisha ta wuce duk wani wulaƙancin daga gare ka, abinci ne domin ni ta yi shi kuma ko meye ta saka a ciki zan ci shi".
Salatin da Amma ta rafka tana tafa hannu gami da riƙe haɓa ya sanya shi yin ƙasa da kansa.
"Ba shakka Abdul-hameed macen za ka fifita akan ɗan uwanka da kuka kwanta a cikin mahaifa ɗaya? To abinci ne na ce ba zaka ci shi ba".
"Duk yanda kika ce haka za a yi ba zan taɓa yi miki musu ba. Amma matuƙar Al'amin bai daina furta mata ki wani irin magana ya zo bakinsa ba za mu sama gagarumar matsala dashi. Kowa ya tsaya a matsayinsa shi ɗan uwanane ita kuma matata cikin su babu wanda zan yarda ɗaya ya ciwa mutunci na kyale". Sai da ya miƙe tsaye ya cigaba da"sai da safe na barku lafiya, tashi mu tafi". Ya faɗa yana maida dubansa gare ni jikina a sanyaye na miƙe na bi bayansa ina tare sabbin ƙwallar dake ƙoƙarin kwaranyo mini. Ina jin Ansar yana faɗawa mahaifiyarsa cewar zai ci dambun tana kwaɓarsa da cewar wai ba abun ci bane.
Kamar jira kukan yake yi ina sanya ƙafa cikin sashinmu ya kufce mini mai matuƙar ƙarfi. Na durƙushe akan gwiwata ina sakin kukan da dukkan ƙarfina, ya tsuguna a gabana tare da jawo ni jikinsa ya ƙanƙame ni gam saboda rawar da jikina yake yi. Ya soma hura min iska a goshina haɗi da faɗin"don girman Allah ki yi haƙuri Aisha in sha Allah haka ba zai ƙara faruwa ba. Kar ki sa wannan abun a ran ki na roƙe ki matata".
"Daman duk zaman nan 'yan uwanka basu yarda da ni ba? Daman duk tsawon wannan lokacin kallon wacce za ta iya cutar da kai suke yi mini?".
"Shit". Ya furta yana ɗaura ɗan yatsansa akan leɓena"kar ki ce haka babu wanda yake zarginki a cikin 'yan uwana. Ko yau da kika hakan ya faru haushin rashin sanar da ita da kika yi ya sanya ta aikata komai, ina mai ba ki haƙuri".
Shuru na yi masa ba don na yarda da zancen nasan ba, na koma sauƙe ajiyar zuciya a kai a kai. Ya tallafo haɓata"ki yi haƙuri na miki alƙawarin ba zan taɓa barin ki wulakanta ba". Kaina kawai na iya ɗaga masa ya kai hannunsa yana share mini hawayen fuskana yana faɗin"bari na yi wanka sai mu je gidan cin abinci mu ci abincin ko?". Bai jira amsata ba ya miƙe tare da ɗauka ta cak ya yi ɗakinsa da ni ya dire ni akan gado. Ya shiga banɗaki ranar ko ruwan wanka ban iya haɗa masa ba na tusa