Showing 78001 words to 80635 words out of 80635 words
Chapter 27 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt
shiga zuwa marasa nauyi ya zauna ya na nazarin labarin da na ƙarishe masa ɗazu, daki-daki ya ke breaking ko wani jumla. A zabure ya furta"i get it". Ya ƙare zancen ya na jawo wayarsa ya shiga latsa lambar Asma'u.
Tunda Umma ta dawo gidan Hamma Abubakar duk dare ba ta iya runtsawa da wani azababben ciwon kan da yake ta'azzaranta. Sawun Baba sau huɗu gidan ya na bata haƙurin ta koma ko zaman 'ya'yanta ta yi kafin lamarin ya dai-dai. Amma ta nuna cewar tun da ya furta zama ya ƙare tsakaninsu to ita ma kuwa babu abin da zai ƙara haɗa ta zama inuwa ɗaya dashi. Sai a lokacin Abasiyya ta zo don farko Hamma Adnan ne daman ya hana ta zuwa saboda tsohon cikin da take ɗauke dashi haihuwa ko yau ko gobe.
Ba don ransa ya so ba dole ya haƙura ya bar ta, ya bata lokacin har zuwa lokacin da za ta huce. Ko kaɗan bai ga laifinta akan hakan ba.
Da Yamma Barrister Aliyu ya zo duba jikin Umma. Ba don ya ƙara musu wani tashin hankalin akan wanda suke ciki ya sanar dasu barazanar da ake masa ba sai ya zama dole su sa ni.
Cike da damuwa Umma ta furta"ɗan nan ka yi matuƙar ƙoƙari da halacci a gare mu wanda ba za mu iya biyanka ba hasalima bamu da abin da zamu iya saka maka dashi. Kar ka saka iyalinka cikin matsala a dalilinmu gwada kawai ka ajiye case ɗin kamar yanda suka buƙata ka yi, na yi imanin idan Aishatu ta na gaskiya Allah ba sai taɓa bari ta wulaƙanta ba, ko kashe ta aka yi sai gaskiya ta yi halinta sai kuma an gane cewar tabbas an cutar da ita". Ta ƙarishe zancen wasu hawaye su na gudun famfalaƙi a bisa kumburarriyar fuskarta da ta yi him tamkar kwaɓin famken da ya ji sinadarin yis.
"Umma ba zan taɓa ajiye wannan case ɗin ba har sai na tabbatar da gaskiya ta yi halinta. Kar ki damu da duk irin matsalan da zan shiga domin hakan aikinmu ya gada, addu'arki kawai muke buƙata".
Shuru Umma ta yi don ta gaza samun kalaman da za ta yi amfani dasu wajen saka masa irin alkhairin da ya yi musu. Maganar da ya cigaba da ya yi ya dawo da ita duniyar zahiri da ga kogin tunanin da ta faɗa.
"Gobe ina son na je na gana da dangin marigaya. Domin samun amsoshin wasu tambayoyin daga gare su"
Jinjina kanta kawai ta yi daga haka ba ta ƙara cewa uffan, su ka cigaba da tattaunawa da Hamma Ahmad da Abubakar game da lamarin ƙiran sallan magrib ne ya sanya su fice.
Washe gari tun safe Barrister Aliyu ya yi dirar mikiya a ƙofar gidan marigayi Abdul-hameed. A waje ya ajiye motarsa ya fito ya na ƙarewa zubin gidan kallo, ya tako ya iso bakin gate ɗin a hankali ya fara ƙwanƙwasawa daga ciki aka ce waye ne.
"Ɓako ne".
Sai da aka yi ɗan jim kafin aka buɗe suka gaisa da mai gadin, ya nuna masa ID card ɗin sa tare da yi masa bayanin wanene shi da kuma abun da yake tafe dashi.
"Allah sarki Hajiya! Wallahi kullum ta na cikin addu'ata Allah ya fitar da ita wannan sarƙarƙiyar da ta faɗa ciki ".
Sosai Barrister Aliyu ya ke ƙare masa kallo kana ya ce"Amin, a yi min iso wajen Hajiyar".
Gaba ya wuce ya na bin sa a baya har bakin sashin Amma, kana ya dakata shi kuma ya shiga. Ya zura dukkan hannayensa a aljihunsa ya na ƙara kallon farfajiyar gidan a ransa yake ayyana cewar tabbas wancan sashin dake kallon na Amman shi ne wanda A'isha da Abdul-hameed suka rayu a cikin sa.
"Waye ne yake son ganin Amman?". Ya ji an furta da ya sanya shi saurin waigowa ya na ƙarewa matashin da ya furto zancen a gantsale ya na harare- harare.
Hannu Barrister Aliyu ya miƙa masa su yi musabaha ya ɗauke kansa, janye hannunsa ya yi yana faɗin"Hajiyar ta na ciki ne? Ina son ganawa da ita".
"Ta na ciki lafiya?".
ID card ɗinsa ya yi masa nuni dashi daga haka bai ƙara cewa komai ba. Da sauri mai gadin ya bar wajen saboda kallon da Al'amin yake jifarsa dashi.
Ya na doso ƙofar falon sautin tsala ihu ya fara sauƙa a ƙofofin kunnuwansa. Akan yaran da suke yashe a falon idanunsa suka fara sauƙa, alamar ihun da suka yi dole cikin biyu akwai ɗaya ko faɗuwa suka yi ko kuma ɗauke su aka yi da gigitaccen mari.
Zama ya yi har yanzun ya kasa ɗauke idonsu akan su. Ƙarar sauƙowar mutum daga matakalan benin shi ya tursasa shi kawar da idonsa daga kan yaran.
"Me ya sama waɗannan yaran suka cikawa mutane kunne kamar jiniya?". Al'amin ya furta a tsawace, take cikin 'yar aikin dake tsaye ta na share abin da ya fashe a wajen ya fara rawa. Cike da tsoro ta ɗago ta furta"lallashin su nake ta yi tun ɗazu, madarar ma sun ƙi sha".
Tsaki ya saka dai-dai sanda Amma da Anty Alawiyya suka ƙariso suka zauna a kujerar dake kallon wanda Barrister Aliyu yake zaune. Sosai yake nazarin yanayin yaran da kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci cewar lalle su na cikin takura da tashin sakewa.
"Kai ne kake so magana da ni?".
Furucin Amma ke nan da ya sanya shi dawowa hayyacinsa daga shagala da kallon su Ashraf da ya yi da har yanzu su ke kukan. Da ido Amma ta yi wa 'yar aikin alama akan ta ɗebe su ta fice daga falon, da rawar jiki ta aiwatar da umarninta.
Sai da ya yi gyaran murya ya ce"ƙwarai ni ne Hajiya lauyan dake kare Aishatu a kotu".
"Mun gane ka ai". Anty Alawiyya ta furta ta na musgutawa cike da son jin abin da ke tafe dashi.
Murmushi ya yi kafin ya ce"ya ƙarin haƙuri kuma? Allah ya jiƙansa". Suka haɗe baki wajen amsawa da kalmar Amin, kafin ya ɗaura da"wasu tambayoyi ne ke tafe da ni". Jinjina kanta Amma ta yi alamar ta na ji da sauraronsa.
"Tun da aka fara zaman wannan shari'ar Hajiya ba ki halalci zaman kotu ba, ko me ye dalili? Shin daman akwai wani uzurin da hana ki halaltar zaman shari'ar kisan ɗanki?".
Cike da ta-ka-tsantsan ta furta"tun ranar da Abdul-hameed ya bar duniya ban ƙara kwana ɗaya da lafiya ba, saboda kaɗuwa da kuma zafin rashin da har yanzu bai bar ni ba wannan dalilin shi ya hana ni zuwa kotu.
Sai da ya ƙare mata kallo kana ya ce"Allah ya ba ki lafiya, 'yar aikinki Asabe zan iya ganinta?".
Tabbas ya lura da yanayin firgicin da ya sauƙa a fuskokin Al'amin da kuma Anty Alawiyya. Sai dai tsabar iya taku irin na Amma sam ta ƙi barin kaɗuwar da ke zuciyarta ya bayyana a bisa fuskarsa.
Cikin tsantsar iya takunta ta soma faɗin"ta je gida ganin 'ya'yanta".
"Tun yaushe?". Ya katse ta da hanzari.
"Tun washe garin ranar da aka yi sadakan uku".
"Ko zan iya sanin garin da take ɗin".
Cikin nuna ko a jikinta ta ɗage kafaɗarta"me zai hana, nan ne babu nisa garin abuwa gidan tsohon sarkin noma". Ta na ƙare faɗin hakan ta fashe da kuka mai ƙarfi har da shashsheƙa.
"Aisha ta cuce ni, ta raba ni da Abdul. Ta bar min wani babban giɓi a cikin zuciyata da babu wanda zai iya cike min shi. Tsakanina da ita Allah ya isa yanda ta sanya zuciyata ƙunci ina addu'ar Allah ya ninka maka sau dubu".
Rarrashinta Anty Alawiyya ta soma yi"ki yi haƙuri Amma in sha Allah sai ta girbi abun da shuka, ai kowa ya san hukuncin wanda ya kashe rai a kashe shi ne".
Taƙaitaccen murmushi Barrister Aliyu ya yi ya na yin ƙasa da kanta ta gefen idonsa yake ƙare wa girman kallo ya ce" Hajiya shi fata na gari na lamiri ne".
"Malam ko don irin hakan bai taɓa faruwa da wani na ka bane shi yasa kake faɗin haka?. Anya ka san raɗaɗin da zuƙatanmu suke a ciki kuwa?".
A fusace Al'amin ya yi zancen da kumfar baki
Shafa fuskarsa Barrister Aliyu ya yi kana ya ce"ko bai taɓa faruwa a kaina ba zan iya fahimtar hakan. Anywhere na gode da lokacin da ki da kika ba ni, ni zan tafi".
Kanta kawai ta ɗaga masa ya miƙe har ya yi gaba, Al'amin ya furta"to mu ma mun gode".
Da hanzari ya waigo haɗi da cewar"kamar na taɓa jin muryar nan a wani waje".
"Ni-ni-ni-ni? Ba ni ba ne malam".
Murmushi kawai Barrister Aliyu ya kuma saka a nutse ya furta"sai mun haɗu a kotu, na bar ku lafiya".
Miƙewa Anty Alawiyya ta yi ta leƙa ta tabbatar da ya fice kafin ta dawo ta zauna cikin tashin hankali ta furta"me kike ƙoƙarin aikatawa Amma?. Anya kin san me kika aikata kuwa?. Sanar da shi inda zai sama Asabe fa ki ka yi, bayan kin san akwai sirrinmu da yake ɓoye a wajenta mai muhimmancin gaske".
Murmushi mai sautin gaske Amma ta saka ta na gyra zamanta ta ɗan zamo daga kan kujerar da take zaune kana ta ce"yarinya ce ke har yansu Alawiyya shi yasa kika kasa gano ƁOYAYYAR MANUFAta ta sanar dashi hakan. Idan muka ɓoye masa zai nemo to gwada mu sanar dashi da bakinmu domin gujewa matsala". Ta dafa kafaɗarta ta mai cigaba da cewar"ki kwantar da hankalinki na yi muku alƙawarin yanda wanda ya mutu ba ya taɓa dawowa haka sirrin da muka ɓoye ba zai taɓa tashi duniya ta ji ba".
"Afuwan na katse muku zancen da kuke yi, makullin motana na mance na dawo ɗauka".
A tsorice duk suka waigo jin furucin Barrister Aliyun a bazata. Ya tako ya iso wajen kujeran da ya zauna ya ɗauki makullin tare da ƙara yi musu sallama, har ya fice babu wanda ya ce da shi uffan a cikinsa illa kallon da suke bin sa dashi.
Iska Al'amin ya kai wa naushi ya na miƙewa a fusace yake nuna Amma da manuniyar yatsarsa"Amma kin ga ni ko wallahi mutumin nan zai zame mana babban matsala. Shi ne fa wanda kwanaki biyu da suka wuce na sanya masa bindiga a kai na ja masa warning, kin ga gashi yanzu ya gane ni".
Ita miƙewar ta yi"shi yasa na hane ka da aikata komai ba tare da sa ni na ba. Ina so kafin ya kai ga garin abuwa a tabbatar da cewar Asabe ta bar cikin wannan duniyar, sannan kar a bar wata alamar da zai karkato da zargi kanmu ".
"Dama umarninki kawai nake jira amma da na daɗe da kawar da matar nan. Don duk lokacin da na tuna cewar ta san sirrinmu hankalina ba ya kwanciya. Hatta 'ya'yana su Ashraf ni fa ƙaunar ganin su nake yi b...".
Marin da Amma ta ɗauke shi da shi cikin ƙankance ido ta ke faɗin" ka yi iya abin da na faɗa maka, ka bar min sauran komai a hannuna". Kansa ya ɗaga mata ya na dafe ƙuncinsa cikin tafasar zuciya.
Cikin kwanakin nan babu abun da nake yi wa kaina fata face mutuwa tun kafin a gurfanar da ni a gaban kotu. Wataƙila a yanke mini hukuncin da zai sanya zuciyar Ummata buga, ta jefa 'yan uwana cikin wani yanayi. A na gobe sauran kwanaki biyu Barrister Aliyu ya zo ganawa da ni, nan ya sanar da ni wani BIYAYYAR MANUFAR da ya ƙara hautsina mini tunanina. Ya ƙara jefa ni cikin wani mungun yanayi.
Ban dawo dai-dai ba har ranar da aka komar da ni kotu, da ƙyar aka sama hanyar da aka shigar da ni cikin kotun Saboda yawan mutanen ya zarce na ko wani lokaci.
Umma da duk yayyuna maza sun hallara a cikin kotun har da Baba Alhaji. A wannan zaman bayan Anty Alawiyya, Anty Adama da Al'amin hatta Amma ta halaccin zaman.
Har Alkalin ya shigo Barrister Aliyu bai zo ba. Ina jin tashin zance daga cikin 'yan zaman kotun su na faɗin Barrister Aliyu karaya ya yi shi yasa bai zo ya na gudun a kayar dashi a case ɗin. Barrister Adam da magoya bayansa su ka fara farin cikin ganin alamar nasara ta na gare su.
Hankalin kowa ya na kaina na kasa ɗago kaina zuciyata ta harbawa a raunane. Na gama cire buri game da cigaba da zama a cikin wannan duniyar, zuciyata ta na raya mini cewar daga nan nima kashe ni za a yi .
Jin wani hayaniyar ya na tashi ya tursasa mini haɗo kaina da nake kunyar haɗa ido da Umma da kuma sauran yayuna.
"Alhamdulillah ga shi nan ya ƙariso".
Na ji an furta daga ɓangaren da kunnuwana suke ji yo mini. A gaggauce ya ƙariso gaban kotun ya na ɗingisa ƙafarsa"afuwan ya mai girma mai shari'a ina mai ba ta haƙuri akan rashin zuwa na akan lokaci. Saboda wasu abubuwan da su ka taso da suka tursasa faruwar hakan".
"Hakan ya na faruwa ba ka da matsala Barrister Aliyu, kai kotu take saurara ka gabatar da hujjojinka". Rusunar da kansa ya yi alamar girmamawa"tabbas yau ina tafe da hujjan da zai warware duk wani ƁOYAYYAR MANUFA. Na fayyace abin da kowa ya daɗe ya na dakonsa. Zan so kotu ta ba ni damar shigo da Asabe da take waje tare da jami'an tsaro".
Hatta ni kaina sai na razana da jin sunan wacce ya ambata. Mai shari'ar ya ba shi dama kamar yanda ya buƙata. Aka shigo da ita ta na tafiya da ƙyar da bangejin da aka kewaye kanta da shi, an naɗe hannunta a ƙasan ƙirjinta alamar karaya.
Ta tsaya a gaban kowa, shuru ya ɗauki wajen. Har zuwa lokacin da Barrister Aliyu ya soma faɗin"kotu za ta so jin abin da kika sani game da wannan case ɗin domin warware mana zare da abawa".
Maimakon ta ba shi amsa sai ma fashewa ta yi da kuka tare da cewar"tabbas ina ɗauke da sirrin da zai warware duk wani ƙulli". Ta dakata a nan ta share fuskarta da ɗayan hannunta mai lafiyar kana ta nuno ni"Aishatu ita ce ta yi kisan Abdul-hameed, sai dai ba ta cikin hayyacinta domin sai da ana gusar mata da hankalin ta hanyar sanya mata wani sinadari cikin madarar da ta sha. Ya fitar da ita daga hayyacinta ta yanda a lokacin duk abun da aka umarce ta ta yi shi za ta aikata ko menene saboda ba ta cikin hayyacinta".
Shuru ya ƙara karaɗe wajen, Barrister Aliyu ya gyara tsayiwarsa"su waye su ka gusar mata da hankalin? Sannan me ye faru bayan shan madarar da ta yi?. Me ye manufarsu ta aikata hakan?".
Shuru ta yi ta na zazzare idanu alamar tsoro da firgici ƙarara a bisa fuskata. Ta kasa cewa komai har sai da ya ƙara cewa"kar ki ji tsoron komai domin ki na ƙarƙashin kulawar hukuma". Sai da ta ja lokaci kafin ta fara yunƙurin buɗe bakinta za ta yi magana ba ta kai ga furta abin da yake cikinta ba ta faɗi a wajen sumammiya.
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!
A nan na kawo ƙarshen liffafi na farko, sai mun haɗu a littafi na biyu wanda yake ɗauke da amsoshin tarin tambayoyin da suka tsaya muku a rai.
Shin Abdul-hameed ya mutu? Me ya faru bayan shan madarar da Aishatu ta yi? Ta ya ya zai kasance cewar ita ta kashe shi?. Menene sirrin da su Amma su ke tsoron Asabe ta tona shi ga duniya?, Anya Amma ita ce mahaifiyarsa?. Me dalilin bambamcin da take gwadawa tsakaninsa da Al'amin?, dukiyar da ya ke juyawa wanene mamallakinta?.
Menene makomar rayuwar Aishatu? A wani irin rayuwa 'ya'ya da maraicin uba ya faɗa musu da ƙarancin watanni za su taso? Tsakanin Hamma da Anwar wa ye zai ƙara da Aisha? Idan ta tabbatar A'isha ta kuɓuta daga wannan sarƙarƙiyar da wani ido Baffa zai kalli Umma?.
Duk za ku sama amsoshin waɗanda tambayoyin cikin littafi na biyu akan N500 kacal. Da a fara posting ɗin a ranar goma sha biyar ga watan Nuwamba.
Domin ƙarin bayani, shawara, ko kuma neman littafi na biyu za ku iya tuntuɓa ta akan wannan lambar kamar haka 07038908713.