Showing 18001 words to 21000 words out of 80635 words

Chapter 7 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

Hamma Ahmad hawaye domin kuwa ya cancanta ta ko wacce fuska. Sai dai ba ni da wannan ikon domin Sarkin da ke da iko da mu ya riga ya tsara komai.


[9/13, 20:07] Maimunatu Iyam: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IPa4qxjMSC6Ke1K7zC3R0t


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam


_____________________________________


Page 1️⃣0️⃣


Tun bayan faruwar lamarin na daina ganin fara'a akan fuskar Umma, idan ina zaune a waje kuwa komai zan yi ba za ta ɗago kai ta kalle ni ba balle ta ce da ni ci kanki. Na zage damtse duk wani aikin gidan kafin hantsi ya fito na kammala shi duk a ƙoƙarin farantawa Umma. Amma a banza tamkar ana ƙwalawa bebe ƙira babu abinda ya sauya zani.


Ranar ina zaune na zabga tagumi bayan sallan magrib ni ɗaya Umma ta shiga wajen Dada. Domin tun bayan faruwar abun ba ta je ba a cewar ta wai kunyarta take ji da nauyin haɗa ido da ita. Hamma Abubakar ya shigo ina jin ya yi sallama na zabura ina ƙoƙarin miƙewa na shige ɗaki ya dakatar da ni.


"Ina za ki je? Koma ki zauna".


Na koma inda na tashi na zauna na sunkuyar da kai ina sauraronsa." Aishatu kin kyautawa kanki kenan?. Ban taɓa sanin ba ki da hankali ba sai yanzu ga inda za ki sama kwanciyan hankali ana nuna miki gabas kina nausawa kudu, me ye aibun Ahmad wani halinsa ne ba ki sani ba? Ba ya shaye shaye, ba ya nema matan banza sannan bai taɓa kusantar zina ba da duk wani abinda Allah ya hane mu da aikata shi, kema shaida ce yana da ƙoƙarin ibada da kuma hidimtawa addini da ƙarfinsa da kuma aljihunsa. Shin bai da siffofin da duk wata macen ƙwarai take buƙata daga wajen ɗa na miji ne ko meye kin faɗa min?".


Da sauri na girgiza masa kaina alamar a'a, hawaye suna gangarowa daga idanuna. Ya yi taku uku ya iso inda nake zaune ya nuna ni da 'yar manuniyar yatsarsa"to wallahi duk wanda za ki aura saɓanin Ahmad ba za mu taɓa farin ciki da aurenki ba".
Muryata a shaƙe na furta"ku yi haƙuri Hamma Abubakar wallahi ba laifina bane". Kafin na rufe bakina na ji ya ɗauke ni da wani gigitaccen marin da tsabar azabar da na ji ya ratsa ni ko kuka na kasa yi, ina dafe kuncina da yake yi mini zogi.


Ya ɗaga hannu da niyyar ƙara zabga mini Hamma Ahmad da Adnan suka shigo. Hamma Adnan ya yi saurin janye ni gefe ya riƙe ni, na kwantar da kaina a jikinsa na kasa kukan sai ajiyar zuciyar da nake sauƙe a kai a kai.


"Me ye haka me ye haka Abubakar? Me ta yi maka da zaka yi mata wannan marin?. Baka tunanin nasiha da nusarwa za su fi yin aiki ga masu shekaru irin nata fiye da duka?".


"Ta cancanci komai wannan yarinyar ba ta san halacci ba". Hamma Abubakar shi ma ya furta a zafafe, a lokuta da yawa idan ya hau dokin fushi da zuciya Hamma Ahmad sausatawa yake yi har sai ya sauƙo. Amma a wannan karon ɗaga masa murya shima ya yi.


"Me ye laifinta don ta faɗa abinda yake ranta? ko kuma ku za ku zauna mata da ni bayan auren?. Kai auren dole aka yi maka ko kuma sai da aka nema amincewar ka?. Me yasa haka Abubakar me yasa kuka ƙasa fahimtar cewar tabbas akwai wata ƁOYAYYIYAR MANUFA na Ubangiji shiyasa duk haka ya faru". Sai da ya tsagaita kana ya cigaba da faɗin"in dai a kaina ake yi mata wannan musgutawan ba zan taɓa yafewa kaina ba har abada, kuma na gwammace na yi nisan zangon da garin nan akan kullum ina shigowa idanuna suna yi min tozali da wannan cin zalin da kuke yi mata babu gaira babu dalili. Idan tsoron lalacewar zumunci kuke gudu to abinda ta yi shine daidai kuma shi ne zai ɗaurar da zumuncin dake tsakani. Ka yi tunanin da ace sai bayan auren ta fara nuna alamomin ba ta sona me zai faru?".


Har ya yunƙura zai ƙara yin wani maganar kamar wanda aka riƙewa baki sai kuma ya yi shuru, yana jijjiga kansa.


"Kin ga abinda kika jawo ko?".


Hamma Abubakar ya furta mini cikin daka mini tsawar da ta sanya Hamma Ahmad zabura ya isa gare shi tare da cin kwalarsa ya riƙe tamau. Idanunsa sun sauya launi yake faɗin"ka san yawan rantsuwa ba halayyata bane, amma na rantse da Sarkin da ba shi da abokin tarayya idan ka ƙara ɗaga mata murya ko ka kai hannunka jikinta da sunan duka sai na yi maka lakani Abubakar".


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Don Allah ku yi haƙuri ya isa haka nan".


Hamma Adnan ya furta cike da damuwa a tattare da muryarsa. Babu abinda nake yi sai kuka na zube ƙasa akan gwiwoyinta tare da haɗe hannayen waje guda alamar roƙo. So na ke na ce da su suyi haƙuri amma sam na gaza samun haɗin kai daga wajen bakina domin na rasa yawun da zan sarrafa a cikin bakina har na iya furzo zancen wajen.




"Innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Me zan gani haka me yake faru?".


Muryar Umma ta yi wa kofofin kunnuwana sallama, duk tambayar lafiyar da take musu ba su bata wani gamshashshen amsa ba sai ce mata su ke ba komai. Shi ma Hamma Adnan kawai yake iya ƙarfin halin furta mata hakan.


A matuƙar fusace Hamma Ahmad ya fice yana dafe goshinsa duk muka raka shi da kallo. Hamma Abubakar ya nema waje ya zauna dafe da kansa.
"Wai me yake faruwa ne? Kun bar ni a cikin duhu?".


"Umma ki kwantar da hankalinki zamu yi maganar daga baya don Allah ".


Hamma Adnan ya furta ya na ɗago ni na miƙe tsaye daga durƙushewar da na yi akan gwiwoyina. Da ido ya yi mini alamar akan na shige ɗaki jiri yana kwasata idanuna suna gani mini gilmawar baƙin duhu na shige ɗakin tare da faɗawa kan katifar kwanciyarmu.


So nake yi na yi koda hawaye ne amma sam hakan ya garare ni, ji nake yi tamkar zuciyata za ta ɓallo allon ƙirjina ta fito waje tsabar damuwar da ya yi yawa a cikinta. Da na rasa samun ta inda zan warware shi.
Filin gidan tsit bana iya jiyo motsin komai, har aka yi ƙiran sallan magrib ban iya tashi domin na je na yi alwala ba. Saboda nauyin da dukkan gaɓoɓin jikina ya yi mini ko yatsar hannuna bana iya motsawa shi.


Ji nake yi tamkar na fita a gude na yi hauka ko zan ji sausaucin raɗaɗin da nake ya na ƙartar zuciyata. Ban ƙara tabbatarwa kaina cewar ina cikin tsaka mai wuya ba sai yau da wannan rikicin ya afku. Tun da na yi wayo na iya bambamce tsakanin fari da baƙi, nake iya rabewa tsakanin hagu da damana. Na san so, ƙauna da kuma shaƙuwar dake tsakanin waɗannan 'yan uwan biyun duk da Hamma Abubakar yana da zafi da zuciya Hamma Ahmad ya kasance tamkar ruwar ƙanƙara mai iya kashe duk wani wutar zafin zuciyar Hamma Abubakar.


Ba su taɓa sa'in sa da junansu ba balle har ya kai su ga matakin ɗagawa juna murya ko bayarwa juna martani da zafafan kalamai. Sai gashi yau a ta dalilina sun yi abinda a tarihin bai taɓa faruwa a tsakanin su.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'u!".


Na furta ina mirginawa tare da dafe ƙirjina da nake jin tamkar ana soka mini tsinin mashi, juyi kawai na cigaba da yi da tunanin samun ɗauki amma babu ko alama. Tun daga lokacin na daina fahimtar komai sai sauƙar ruwar sanyi na ji ya na ratsa jikina. Na yi figigi na tashi a zabure ina sauƙe numfashi a wahale.


Na damƙe hannun Dada da idanuna suke gano mini dishi dishi"Dada ki taimaka mini zuciyata zata fashe".
Tofin wasu addu'o'in da take yi mini a bayyane ta cigaba da yi, hakan ya sanya ni komar da kaina kan cinyarta ina sauƙe numfashi.
"Ki na ji na.


Na tsayar da ƙwayar idona akan fuskarta tare da ɗaga mata kaina alamar e. Ta gyara mini zaman kaina dake jikinta"me ya same ki? Me ya yi zafi haka Aishatu ke kuwa?".


"Zuciyata zafi take yi mini".


"Ki yi haƙuri za ki iya tashi ki zauna?".


Kaina na ɗaga mata ina cije leɓena na tashi na zauna na jingina kaina a jikin bango tare da lumshe idona, wasu hawayen masu ɗumi suna gudun famfalaƙi a bisa kuncina.
"Ki cire komai a ranki, kamar yanda na sha faɗa miki a baya cewar komai zai wuce".


Na kasa cewa komai na gyaɗa mata kaina ta umarce ni da na fito na yi alwala. Umma ta na zaune kan tabarma na yi mata sannu da ba ta amsa ba. Kamar zan kife haka na ɗauki buta na shiga banɗaki. Waje na nema na zauna na ci kuka har na godewa Rabbana sannan na wanke fuskana na fito.


"Yaya kuke son yarinyar nan ta yi ne? Ko so kuke ku ɗaura mata wani ciwon na daban da ba a san dashi ba?. Duk kun juya mata baya babu mai kula ta balle sauraron damuwarta a fahimce ta har ayi mata uzuri. Dubi fa halin da na shigo na tarar da ita a sume ba ta san inda kanta yake ba, in ba don Allah ya rufa asiri na shiga ba yaya kenan lamarin zai kasance?".


Zantukan Dada kenan da na fara cin karo dasu yayin da nake fitowa daga banɗakin. Har na iddar da alwalan ba ta tsagaita ba kamar yanda Umma ba ta ce da ita komai ba. A zaune na haɗe sallolin magrib da isha'in na yi su domin ba ni da kuzarin iya tsayawa akan ƙafafuna da suke tangal tangal. Sosai na yi addu'ar neman sauƙi kana na shafa a sanyaye.


Sanda Dada za ta tafi ta ce da ni na fito na bi ta domin ba zan zauna ni ƙadai wani abun ya kuma faruwa babu mai damuwa da duba lafiyata ba. Ko da muka je gidan Adda Abida da Abasiyya babu wanda ya yi mini kallo arziki balle yi mini yaya jiki duk da yanda Dada take ƙara kambama ciwon da yanayin da ta tarar da ni.


Anwar ne kawai ke ta jeranta mini kalmar sannu kamar zai yi ƙwalla. A nan na kwana cike da kulawar Dada da Anwar, kafin na tashi ya saka mini ruwan zafi har ya kai mini banɗaki ya sanar da ni na fito na tarar da mutum a banɗakin.


Abasiyya ce ta fito sanye da hijabin da take shiga wanka dashi, ya bi ta da wani kallo"da wani ruwa kika yi wankan?".


"Ruwan da yake cikin banɗakin".


"Sai ki wuce ki je ki dafa wani ruwan domin a Aishatu na ajiye wannan". Ta zaro ido waje"da wannan ɗanyar itacen zan dafa ruwan wanka?, sai dai zuwa anjima in an kawo bushashshen itac...".


"Ki wuce ki yi abinda na sa ki".


Ya faɗa a tsawace dai dai sanda Hamma Ahmad yake kutso kai cikin gidan, ya tambayi me ke faru Abasiyya da ta ɓarke da kuka na sanar dashi. Bai goyi bayanta ba shi ma ya ce ta je ta dafa wani ruwan zafin ta kai banɗaki.
Na yi ƙasa da kaina domin bani da ƙarfin halin iya haɗa ido dashi bayan duk abubuwan da suka faru, na tsinkayo muryarsa yana faɗin"idan kin gama ina neman ki". Kaina kawai na ɗaga masa ya fice ya bar ni da sauƙe tagwayen ajiyar zuciya.


Ɗakin Dada na nufo da na iske ta tana faɗa a Abasiyya tare da bata rashin gaskiya, sai da na yiwa kaina mazauni domin ba zan iya jure tsayiwarwa. Kana na sausauta muryata na ce"ki yi haƙuri Dada tsakanin mu da Abasiyya ai ya wuce haka. Nima sau nawa nake zuwa gidan nan ya ɗauki kayanta ba yi amfani dashi, kuma babu yanda ta iya sani dole da ta yi haƙuri da ni don yau kawai ta aikawata aikata wannan a bisa kuskure don Allah ku yi haƙuri".


Kanta ta jinjina"shikenan Allah ya yi muku albarka". Na amsa da kalmar Amin sannan ta ɗaura da tambayar yaya jikin nawan, na ce da ita alhamdulillah. Sai da na ɗaura wani ruwan na yi wanka na sha kunun tsamiyar da Abba Abida ta dosara mini a gabana, sannan na nufi ɗakin zaure domin amsa ƙiran da Hamma Ahmad ya yi mini.


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam


_____________________________________


Page 1️⃣1️⃣


Kamar ko yaushe sai da na yi sallama ya amsa mini sannan na kutsa kai cikin ɗakin. Na zauna tare da gaishe shi cikin sanyin murya, sai ya ja ɗau lokaci sannan ya amsa mini yana ɗaura da"yaya jikin nakin?"


"Da sauƙi alhamdulillah".


Ina iya jiyo numfashin da ya fesar da ƙarfi"na kasa riƙe kaina ne, ina kasa sarrafa fushina matuƙar maganarki ake yi Aishatu. Ban san ina da rauni ba sai yanzu ban san zuciyata a kusa take ba sai bayan faruwar wannan lamarin".
"Ku yi haƙuri Hamma duk laifina ne ni ce silar faruwar komai". Ya yi saurin katse ni"babu laifinki ko kaɗan in ma da mai laifi to bai wuce ni ba, da na kasa danne fushina a lokacin har abinda ya faru ya afku".


Shuru ya biyo bayan zancensa na ƙarshe, sannan ya cigaba da faɗin"ɗazu mun yi magana da Baba akan cewar wanda ya zo da maganar neman iznin fara zancen da ke zai zo yau. Za su tattauna da su Baffa sannan su bashi damar ganawa da ke, don haka ki zama cikin shiri sannan ki kasance mai nutsuwa, ban da rawar kai da rashin kunyar 'ya'yan zamani".
Sai da ya sausata amon muryarsa"Aishatu ke ce ta farkon da zata fara tsayiwa da wani saurayi a wannan ahalin. Don haka dole za ki fuskanci wasu ƙananun ƙalubale da ba za a rasa ba, shawarata gare ki shi ne ki riƙe mutuncinki kar ki bari wani ya yaudare ki da wasu kalamai ko wani ƙale-ƙalen duniya, duk da ba a yabon ɗan yau amma zan iya bugan ƙirji a gaban ko waye na san ba za ki zubds mutuncinki akan abun duniya ko kuma ki wofantar da tarbiyyar da iyayenmu suka ɗaura ki a kai ba".


Sunkuyar da kaina ƙasa na yi hawaye suna gangarowa daga idanuna"Hamma Ahmad ni fa babu wanda ya taɓa cewa yana sona, balle ya zo wajen su Baba".


"To ai hakan da ya yi shine daidai kuma hakan ne ke nuna cewar daga babban gida ya fito kuma yake bayyanar da cewar ya san abinda ya kamata. Ba mutunci bane ga duk wanda ya san mutuncin kansa ya tari mace a hanya ya furta mata kamar so, ba tare da ya tuntuɓi magabatanta ba. Tabbas ko daga haka ya nuna cewar shi na daban ne".


Zazzafan iska na fesar daga bakina ina musgutawa tare da gyara zamana. Tabbas Hamma Ahmad ya cika cikakken ɗan uwa kuma masoyi na haƙiƙa, firgici nake ciki sosai domin ban san wanda zan gani ba. Bana kula kowa a cikin samarin unguwan domin ko su Hamma Abubakar ne ba su cika shigowa da abokansu gidan ba, balle na ce ɗaya daga ciki ne ya ganni har ya gurfana a gaban Baba.


Kwantar mini da hankali ya yi ta yi, har na ɗan ji nutsuwa ya ziyarci sashin ruhina. Ya shaida mini cewar yau da wuri zasu dawo daga kasuwa don haka na zama cikin shiri. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na shiga cikin gidan kaina tsaye na wuce ɗakin Dada, na sanar da ita komai itama kwantar mini da hankali ta yi sosai da kalamai masu daɗi da kyawawan misalai. Ta ƙarƙare da yi mini addu'ar Allah ya yi mini zaɓi mafi zama alkhairi a gare ni da kuma fatan alkhairi.


Haka na wuni da zazzaɓi ina kwance lilif fargaba da tsoro sun gama yi mini mamaya. Ko sallama na ji an yi sai na ji faɗuwar gaba. Ina iddar da sallan magrib kuwa na kifa kai da gwiwa, Dada ta ƙwalo mini ƙira na miƙe ina jin hajijiya yana kwasa ta na je na durƙusa a gabanta.
"Yau za ki yi baƙo kin sa ni?". Na ɗaga mata kaina jikina duk ya yi sanyi ƙalau.


"To ki nutsu ban da rawar kai inda kin fita, ki saurare shi sannan ki kama kanki da kuma mutuncinki kin ji ni?". Take na ji hawaye sun ciki mini koramar idanuna"to in sha Allah". Ta sanya mini albarka tare da umarta na tashi. Har muka gama cin abinci da Abasiyya babu wanda ya cewa wani abu har Baba Alhaji ya shigo. Duk muka yi masa sannu da zuwa ya amsa mana fuskarsa a washe.


Na tashi na wanke hannuna zan shige ɗaki ya ce na dawo na zauna, kamar yanda faɗa hakan na yi na koma na zauna.
"Ki ɗauko mayafinki kina da baƙo a waje".


Ƙirjina ya buda da ƙarfi na miƙe a sanyaye, ban taɓa tsayiwa da wani saurayi ba da sunan zance haka nan ban taso na buɗe ido na ga su Adda Azima na yi ba, don haka abun sai ya zamo mini sabon al'amari a gare ni.


Cikin matsanancin faɗuwar gaba na isa inda aka shimfiɗa tabarma. Muryar da ya sauƙa a masarrafar jina suka sanya ni ƙara gwalo idanuna wajen.


"Kai ne?". Na furta ina nuna shi da yatsata ya ɗago idonsa ya sauƙe akan fuskarta da firgici, tsoro da ruɗu suka bayyana akan ta"ƙwarai ni ne ki zauna mana".


"Me ya kawo ka gidanmu?. Me yasa ba zaka daina bi na ba?. Ko lokacin baya sai da aka yi mini faɗa akab tare ni da ka yi don Allah ka yi haƙuri ka bar ni".


Na ƙare zancen ina haɗe hannayena waje guda alamar roƙo, tare da yunƙurin juyawa da nufin barin wajen. Zancen da ya furta suka tursasa mini tsayiwa cak tamkar dasasshen itace na kasa gaba balle baya.


"Yau da iznin iyayenki zan yi magana dake, domin sai da na nema izninsu kafin na yi wannan zuwan. Don Allah ki ba ni lokaci daga cikin lokacinki domin ki ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login