Showing 66001 words to 69000 words out of 80635 words

Chapter 23 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

ƁOYAYYAR MANUFA na Ubangiji a cikin aurenki da Abdul-hameed ".


Jikina babu kuzari gabaɗaya na amsa da"in sha Allah Hamma na gode Allah ya bar zumunci".


"Amin amin ".


Da haka muka yi sallama yana ta nanata mini kalmar na dage da kai kukana ga Allah. Na zame wayar daga kunnena zuciyata cike da mamakin wannan abin al'ajabin da ya fi yi mini kama da almara.


*ƁOYAYYAR MANUFA*


©️ Maimuna Tijjani Iyam


_______________________________


Page 3️⃣5️⃣


Na yi iya ƙoƙarin danne komai tare da mance komai, ta hanyar nuna masa cewar komai ya wuce. Sai dai cikin raina na ƙudurce sai na gano abin da yake wakana a cikin ƙasa, ba zan taɓa samun nutsuwa ba kuma ba zan taɓa fita daga zulumi ba sai na gano wanda ya turo mini wannan saƙo da layin Abdul-hameed.


Kwanaki biyu tsakani Asiya ta ƙira ni ta ce an sama yar aiki, za ta taho mini da ita na gan ta idan ta yi mini. Bayan sallan zuhur kuwa sai ga ta ƙira ta ina ɗagawa ta sanar da ni cewar ga ta a bakin gate. Na yafa mayafina na fito na shigo da ita.


"Sannu da zuwa kin ɗebo rana". Na faɗa ina miƙa mata kofin da na tsiyaya mata ruwan sanyi, ta karɓa tana faɗin"wallahi akwai rana kam". Ta kai kofin bakinta ta sha kusan rabin ruwan sannan ta ajiye.
"Ga ta na cika alƙawari na kawo miki ita har gida". Sai a lokacin na bi natashiyar yarinyar dake zaune kusa da ita tana riƙe da Junior"masha Allah ai kuwa muna godiya, in ce dai kin san ta kin kuma san iyayenta?. Don kin san yanzu duniya ta lalace ".


Sai da ta murmusa ta furta"ai sai da na yi bincike sosai, 'yar maƙwabtarmu ce. Ba ta da matsala idan kin zauna da ita za ki ba ni labari".


Na jinjina kaina ina tsayar da ido akan yarinyar"sannu baiwar Allah yaya sunanki?".


"Amira".


Zancen da Asiya ta ɗaura dashi ya katse mini hanzari"ya ce ba kwana za ta yi ba ma ai, zuwa da komawa ne". A bakinta na ji hakan domin bamu tattaunawa dashi akan hakan ba.


Na miƙawa Junior ya maƙe kafaɗa alamar ba zai zo ba. Wasu tambayoyi na yi wa Amira ta amsa mini su tsaf, na lura yarinyar tana da nutsuwa sosai da kuma hankali.


Na tashi na ɗora girki farar shinkafa na yi da miya, na zubo mana muna ci. Ansar suka shigo kallo ɗaya na yi musu na mayar da hankalina ga abincin dake gabana domin ko basu furta ba na san abin da yake tafe dasu.


Umarnin Amma su ka zo aiwatarwa na duba Abdul -hameed yana nan ko ya fita, ba su ce da ni uffan ba haka nan ban ga suna da niyyar gaisar da Asiya ba, sai faman zazzare idanu suke yi tamkar wanda ya yi wa sarki ƙarya.


"Waɗanda fa Aisha? Wani abun suke nema ne?".
Na kora ruwa sannan na amsa mata da faɗin" 'ya'yan yayarsa ce".


"Shine kika bar su suna faɗo miki falo haka? Yo ai ko ɗakin uwarka ne zaka shiga za ka yi alamar a san da shigowarka balle nan, kuma ba su iya gaisuwa ba sai zazzare idanu a mutane". Na yi ƙasa da kaina tare da cewa"kin san kowa da irin yanayin ƙuruciyarsa".


Da sauri ta katse ni"wani irin ƙuruciya? Rashin kwaɓa da tsawatarwa dai". Na ɗago ina kallonta"kin ga don Allah Asiya ki rufa mini asiri, mu bar maganan nan haka nan. Yanzu sai su ɗeba su kaiwa Amma wannan zancen abu ya zama babba".


Cak ta ajiye cokalin dake hannunta fuskarta ɗauke da maɗaukakiyar mamakin ta ce"waɗannan? To ki yarda kawai koya musu haka aka yi babu wani ƙuruciya. Wallahi fuska suka samu shiyasa suka miƙe ƙafafu har da samun damar yin sanya, tun wuri ki taka musu burki me ye haka?".


Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya ina gyara zamana kafin na ce"ba za ki gane bane, amma barin su da nayi ɗin shi ne akwai mafita a gare ni". A bayyane ta tsirtar da tsaki mai dogon zango tana cewa"tun ice yana ɗanye ake lanƙwasa shi idan ya bushe sai dai a karya shi. Ai yanda kika ɗaura su akan hakan zasu ɗaure".


Shuru na yi mata da hakan ya bata lasisin cigaba da faɗin"kin ganni ina da baki da kuma surutu amma sam ba ni da munafurci. Iya gaskiyar abin da ke a cikin raina nake faɗa. Ba na wani ƙunbiya-ƙunbiya. Da Allah ya ƙaddara Azinatu ce a cikin gidan nan a matsayin matar Abdul wallahi da sai mun mayar da Amma kan kashinta". Ban bar ta ta dire zancen ba na yi saurin kai hannuna na rufe mata bakina.


"Kin ga don Allah mu bar maganar nan haka nan. Amma dai kamar uwa take a gare ni, yanda zan yi haƙuri na jure duk wasu halayyar ytawa uwar ita ma haka zan yi haƙuri da na ta".


Wani kallo da na yi mini na ba ki san abin da kike yi kana ta ce"shikenan tunda haka kika ce, amma ina tabbatar miki wataran da kanki za ki ɗaga waya ki ƙira ni ina neman shawarata ". Murmushi kawai na yi mata muka cigaba da cin abincin na tattare kwanukan, lokacin su Ansar suka fice. Alawala suka yi sannan na shimfiɗa musu sallaya suka yi sallan Asr sannan suka fara haramar tafiya.


Fitowarmu ya yi dai-dai da fitowar Amma da Al'amin daga cikin lambun dake kusa da sashin na tan. Muka ƙarisa Asiya ta gaishe ta, ta amsa fuska babu annuri, har bakin gate na yi mata rakiya sannan na koma.


Ko zama ban yi ba Ansar yana faɗin wai Amma na ƙira na, na rasa dalilin da a duk lokacin da aka isar mini da saƙon Amma nake tsintar kaina a cikin matsanancin faɗuwar gaba ba. Yana gaba ina biye dashi har cikin falonta, na yi wa kaina mazauni tare da yi mata sannu.


Kallon da ta tsura mini ya sanya hantar cikina kaɗawa na yi saurin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa. Muryarta a kaurare ya sauƙa a na'urar naɗar sautina.


"Kamar Asiys matar Auwal na ga kun fito tare ko?". Na gyaɗa mata kaina.
"Ciwo bakinki yake yi da ba za ki yi amsa min ba?".


Da rawar jiki na ce"e ita ce".
"Daman tun can kun san juna da ita ne?".


Na jijjiga kaina haɗe da cewa"a'a ranan nan ne muke kai musu ziyara tare dashi". Ta yi shuru babu alamar za ta amsa mini sai da na gaji da zama na ji duk ƙafafuna sun sake kana ta ce da ni"to ki kasa kunne ki saurare ni da kyau daga yau na datse duk wani mu'amalar dake tsakaninku da ita. Da kin san wacece Asiya da ba za ki yi marmarin kusantar inda take ba balle haɗa inuwa ɗaya da ita". Cike da tsoro na ɗago kaina"wani halin take dashi Amma?".


"Ta so haɗa ƙanwarta da Abdul ta hanyar cusa masa ita ta ƙarfi da ya ji. Sai na tashi akan ƙafana sannan na raba su, idan kika sake mata kina nan zaune za ta ɗaura ki a keken ɓeran da zai yi sanadin fitar ki daga cikin gidan nan. Ƙanwarta ta maye gurbinki". Na sauƙe numfashi mai ƙarfi "zan kiyaye in sha Allah na gode".


Hannu kawai ta ɗaga mini da ke alamta mini cewar ta sallame ni. Na koma sashina na kwanta ina bitar zantukanta. Ko da Abdul-hameed ya dawo na sanar dashi zuwan Asiya da abin da ke tafe da ta, ya ce idan yarinyar ta yi mini to babu matsala ko gobe sai ta fara zuwa aikin.


Ni dai kam na yaba da nutsuwar Amira don haka na sanar da Asiya cewar za ta iya fara zuwa aikin. Ta fara aikinta za ta zo ta wuni da yamma ta koma, mun shaƙu sosai da ita domin sam ba ta da wani matsala duk a shekaru zamu iya karawa da ita. Amma ko bisa kuskure ba ta taɓa ƙiran sunana kai tsaye ba tare da ta maƙala mini kalmar Anty ba.


Mun yi zaman wata biyu cur da ita babu wani abun da ya taɓa shiga tsakaninmu. A lokacin aurenmu ya cika watanni goma cur, bana mance wani yammacin da na fito zan shiga sashin Amma, a harabar gidan na hange Anty Alawiyya zaune da wani su na zance.


Kallo ɗaya na yi musu shi ma ya kasance a bisa kuskure ne na ɗauke kaina raina cike da takaici, wai da aurenka kana sauraron wani daban.
Babu kowa a falon sai su Ansar su na guje-gujensu su na tambaye su Amma su ka ce ta shiga ɗaki tana fitowa, waje na nema na zauna ina latsa wayata ina kallon hotunan da muka yi a gidan cin abincin nan.


Ansar ya zo ya ɓoye a bayana yana faɗin"ki cewa Aysar ya bar min abu na".
"Me ye abun?". Na faɗa ina ajiye wayar hannuna ya miƙo mini SIM ya ce"ga shi tsinta na yi wai ya ce na shi ne".


"Idan an tsinta abu ai neman me shi ake yi, ka kai wa Ummanka in ta shigo sai ta nema mai shi ko?".


"A shara fa na samu, ba mai amfani bane". Ya gatsalo mini zancen a kwaɓe, na yi murmushin takaici da tausayin gurɓataccen tarbiyyar da aka ɗora su a kai. Na karɓa na cire SIM ɗina na sanya wanda na karɓan a ciki. Ma'ajiyar lambobi na shiga babu komai sai mu number na latsa, lambobin da suka bayyana ya tursasa mini ƙara ware idona sosai.


Lambar Abdul-hameed ce ta bayyana na fita na ƙara shiga don tabbatar da abin da nake gani. Tabbas shi ɗin ne na fara jeranta lambana zan ƙira na tuna cewar na cire SIM ɗin, wata dabarar turawa kaina saƙo ya faɗo mini na rubuta sallama na tura a layina.


Na cire wannan na mayar da nawa ina kunna saƙon ne ya fara shigowa ga lambar Abdul-hameed ɓaro-ɓaro ya bayyana fau. Na dafe ƙirjina babu shiri ina ji tamkar zai tarwatse na saci kallon su Ansar na ga duk sun zuba mini na jiyamu.


Na saisaita nutsuwata kafin na ce "ka ce a ina ka sama wannan layin?".


"A cikin shara na samu".


"Ka daina ɗaukar abu a cikin shara babu kyau, zan jefa dashi. Na yi maka alƙawarin idan uncle Abdul ya dawo zan ce ya kai ka siyayya ya sayo muku wasu kayan wasan masu yawa" .
Banza duk suka yi da ni kamar basu yi na'am da zancen nawan ba, sai da na ƙara maimaitawa a karo na biyu cikin tashin murya kafin Aysar ya ce"ni kam na yarda".


"Nima na yarda amma na wa zai yi na Aysar yawa ko?". Da sauri na furta "ai ko girma ma ka fi shi dole naka ya fi nashi yawa, amma fa idan kuka faɗawa Amma ko Mommyku cewar kun tsinci SIM a cikin shara zasu yi muku faɗa. Kuma Amma ta ce babu inda za ku je siyayyan".


"Na kulle bakina". Suka furta a tare, na sauƙe wahalallen ajiyar zuciya. Da haka muka rabu dasu suka fice waje. Har Amma ta fito na gaishe ta na baro sashin ban dawo dai-dai ba.


Sai bayan da Abdul-hameed ya dawo muka ci abinci muka nutsa yake sanar da ni yanda suka yi da su Hamma Abubakar. Na hange zallar gaskiyarsa kwance cikin idanunsa sa'ilin da yake ƙara nanata mini cewar ba shi da masaniya game da wannan saƙon.


Na lanƙwashe ƙafafuna wajen guda"ni kam ɗazu ne nake kallo, na ji wani abun mamaki. Daman mutane daban daban su na iya mallakan SIM guda ɗaya?".


"Sosai ma kuwa ana samun irin haka. Don akwai wasu tagwayen da muka yi jami'a tare dasu kamfanin suka je aka yi musu SIM guda biyu amma mai ɗauke da lamba ɗaya kowa ya riƙe guda".
Na jinjina kaina cike da tashin sanin inda zan dafa, shin na sanar dashi ko kuma na bar abin a cikin raina?. Na nuna masa SIM ɗin ko kuwa?. Na fayyace mishi abin da zuciyata take zargi?.


*ƁOYAYYAR MANUFA*


©️ Maimuna Tijjani Iyam


_______________________________


Page 3️⃣6️⃣


Sai da ya taɓo kafaɗata na dawo cikin hayyacina, da ido ya yi mini alama akan lafiya na yi ƙasa da kaina. Ina shawara da zuciyata da take dakan lugudai. Dole na samawa kaina mafita akan abubuwan da suke faruwa kuma ni ɗin dai ni zan tashi na yi yaƙin nemawa kaina 'yanci.


"Daman wani magana nake so mu yi" Na furta bayan na gama sa-toka-sa-katsi da zuciyata. Ya gyara zamansa alamar yana saurara ta, na ciro SIM ɗin da na sanya a bayan wayata na miƙa masa tare da cewa"ɗazu na shiga sashin Amma na tarar da su Ansar suna rigima akan SIM wai tsinta suka yi a cikin shara. Shine na karɓa na gwada a wayata don tabbatar da cewar mai amfani ne ko akasin hakan, babu komai a cikinsa sai lambar layin da ya yi daidai da naka, don tabbatar da hakan har saƙo na turawa kaina ya zo mini da lambarka".


Ya waro idanunsa cike da mamaki ya furta"lambata kuma na ga ni" Na miƙa masa layin da kuma saƙon da na turawa kaina, ya karɓa ya ga ni. Ya sanya layin a cikin wayarsa tare da jera lambata ya ƙira.


Take ƙiran ya shigo wayata da lambarsa, ya sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi da kuma sauti kafin ya ce"tabbas lambata ce take fitowa. Amma yaya aka yi hakan ya faru?". Na daɗe masa kafaɗata alamar ban sa ni ba, ya cigaba da "kwanaki an tura miki saƙo da lambata wanda ba ni da masaniya akan sa yanzu kuma ga bayyanar wannan layin shima. Wai me yake shirin faruwa ne?". Ya ƙare zancen yana dafe goshinsa cike da damuwa.


Na sausauta amon muryarta a nutse nake faɗin"sai fa ka kwantar da hankali tare da haɗe nutsuwarka waje guda sannan mu iya cimma mafita". Na saci kallonsa kana na cigaba da cewa"ya kamata mu faɗawa kanmu gaskiya Abdul-hameed ka yarda ko akasin haka 'yan uwanka ba sa ƙaunar tarayyata da kai, ƙiri ƙiri sun fito sun nuna mini manufarsu. Su zarge ni akan abincin da na girka maka yanzu kuma ga batun wannan layin da ina da tabbacin da shi aka tura mini wancan saƙon".


Da wani irin saurin ya ɗago kansa yana zube idanunsa da suka fara canza launi a bisa fuskata. Duk da ƙirjina yana bugawa fiye da kima ga kuma tsoron da ya yi mini mamaya a cikin zuciyata ban ɗauƙe idona daga kansa ba ban kuma razana da kallon da yake yi mini ba.


"Me kike nufi Aisha? Ki na so ki ce min ɗaya daga cikin 'yan uwana kike zargi da tura wannan saƙon? To a wani dalilin ke nan sannan me ye ribar su idan suka aikata abin da kike zargin su dashi".


Na matse yatsun hannuna waje guda kafin na furta"ba zargin su nake yi yaƙini nake dashi akan abin da na faɗa. Idan ba rami me ya kawo batun rami?. A sashin Amma fa aka sa ma wannan layi....".


Ban gama ba na ji ya ɗauke ni da wani gigitaccen marin da sai da idanuna suka gano mini gilmawan baƙin duhu, hakan ya tursasa mini haɗiye raguwar zancen don dole. Na dafe kuncina na ɗago idanuna da ya cika taf da ƙwalla ina kallonsa zan yi magana ya ɗaga mini hannu alamar na dakata.


"Ki na da damar da za ki iya ɗauka zarginki akan kowa amma kar ki yi kuskuren sako Amma a cikin zancenki". Ya furta cikin ƙanƙace ido dake alamta ya kai ƙarshen gejin fusata da harzuƙa.


Ruwan ƙwallar da suka ciko ƙoramar idanuna suka zubo, cikin kukan da ya kubce mini na ce"mari ni ka mara?. Ba komai na gode". Na kai aya ina ƙoƙarin miƙewa ya yi saurin fizgo hannuna na faɗa jikinsa ya sanya dukkan hannayensa ya riƙe ni gam.
Duk yanda na so raba jikina da na shi na kasa domin riƙon da ya yi mini ba na wasa ba. Har wani zafi nake jin ƙirjina yana yi mini tsabar tashin hankalin da ƙuncin da zuciyata take a ciki. Ya kawo bakinsa dai-dai kunnuwana tare da cewa"ki yi haƙuri ki yi haƙuri matata. Wallahi na kasa jurewa ne da kika ambaci sunan Amma. Na roƙe ki ba don ni ba ko don ɗaurewan zaman lafiya a tsakanin mu, ki san yanda za ki yi magana akan dukkan abin da ya danganci Amma".


Ajiyar zuciya kawai nake sauƙewa akai akai kamar wacce ta yi gudun ceton rai. Ya soma shafa kaina a hankali, ban iya cewa dashi komai saboda wani irin nauyin da nake jin bakina ya yi mini. Na kasa yarda cewar hannunsa ne ya sauƙa a jikina da sunan duka akan abin da bai taka kara ya karya ba.


Washe gari na tashi da wani mungun zazzaɓi ko ɗan yatsata bana iya ɗagawa. Na so ƙiran Hamma Ahmad na sanar dashi abin da ya faru amma zuciyata ta gargaɗe ni da cewar na koya riƙe sirrin aurena na kuma san yanda zan magance matsalata.


Ina kwance akan sallayan da na yi sallan asubahi na kasa motsawa, na ji shigowarsa har ya zauna a gabana ban ɗago kai na kalle shi ba.
"Me yake damunki?". Ya furta muryarsa cike da tausayawa na so na yi banza da shi amma na kasa yin hakan.


"Babu komai".


Ya kai hannunsa saman goshina kafin ya zarce izuwa tudun wuyata. Yana cewa"ba ki da lafiya ne?".


" Lafiyana".


Na faɗa ina ƙoƙarin tashi ba zauna duk da tsananin ciwon kan da yake addaba na. Zai riƙo ni na janye hannuna ina matse jikina waje guda. Ya haɗa hannayensa waje guda alamar roƙo"don Allah ki yi haƙuri ki daina wannan fushin da ni, wallahi ba zan iya jurewa. Sanar da ni damuwar".


"Babu komai kuma Ni lafiyata ƙalau, ka shirya ka tafi wajen aiki kar ka makara".


Ya furzar da iska daga bakinsa"idan akan maganar jiya n....". Da sauri na tare shi ta hanyar faɗin"ka daina dawo da hannun agogo baya ya riga ya wuce har abada".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login