Showing 3001 words to 6000 words out of 80635 words

Chapter 2 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

kasa yarda da cewar ya mutu gani nake yi kamar da zarar na fita daga nan zan same shi cikin ƙoshin lafiya.


"Ke taso kina da baƙi".


Na ji a furta da muryar da sai da kaina ya sara, jikina babu ƙwari na miƙe domin tun bayan faruwar lamarin nan ban sanya koda ƙwayar abinci a cikin cikina ba illa ruwan da nake kurɓa inda zan yi alwala. Kamar bugaggiya haka na fito ina haɗa kaya izuwa wani ɗaki mai ɗauke da kujerun zama guda huɗu, Hamma Abubakar da Hamma Ahmad da wani mutum sai kuma ɗan sandan dake zaune su kenan a cikin ɗakin na ƙarisa na zauna.


Hawaye yana gudu a fuskana na furta" ina Umma?". Ina ina jiyo sakekken ajiyar zuciyar da ya saka a ƙoƙarin ɓoye damuwar dake kan fuskarsa ya ce"tana gida kuma ta ce a gaishe ki". Idanu na ƙura masa don fuskarsa ta bayyanar da gaskiyar da ya ɓoye cikin furcinsa, ya gyara zamansa yana fuskanto ni sosai"wannan abokina ne barrister ne sunansa Aliyu, shine wanda zai taimaka mana akan case ɗinki kar ki ɓoye masa komai ki sanar dashi iya gaskiyarki kin ji?". Kaina na ɗaga masa" da gaske ne Abdul-hameed ya mutu da gaske ne? Wai ni na kashe shi?.


Idanunsa taf da ƙwalla sai dai juriya da taurin rai irin nashi ya hana su tsiyaya, cikin sigar son kwantar mini da hankali ya ce"ai kowa jiran lokaci yake yi, duk wanda lokacinsa ya yi dole zai mutu". Yana gama faɗin haka ya tashi da sauri ya fice daga ɗakin Hamma Ahmad yana rufa masa baya, da kallo na bi shi har ya maido da ƙofar ya rufe.


"Aishatu".


Na ji barristern ya furta da hakan ya sanya ni kai dubana gare shi sannan na rusunar da idanuna. Me ya hana Umma zuwa kotu?, Abdul-hameed yana raye ko kuma da gaske na kashe shi?, meye dalilin ƙwallar idanun Hamma Abubakar?. Menene yake ɓoye wanda ban sa ni ba?. Jerin gwanon tambayoyin da na jefa wa kai kenan da na gaza cimma amsoshin su.
Har izuwa lokacin da barristern ya katse mini hanzari ta hanyar faɗin"Abubakar ya sanar da ni wasu abubuwa game dake, amma zan so ki in ji daga bakinki wani yaya auren ku da Abdul-hameed ya kasance?"..


Zazzafan iska na furzar daga bakina kana na sama zarafin cewa "an ce ni na kashe shi kuma nima kashe ni za'a yi". Da sauri ya tari numfashina"bincike ne zai tabbatar da ke ce ko kuma saɓanin hakan, hakan zai yiyuwa ne kawai idan kin bani haɗin kai wajen amsa tambayoyin da zan miki kin ji?". Kaina na ɗaga masa alamar na ji sannan ya ƙara maimaita mini tambayar a karo na biyu.
Dogon numfashi na ja na fesar ina jin dukkan abubuwan da suka wakana cikin rayuwata, ya na dawo mini sabo bil a idanuna.


Alhaji Ahmadu Sanda shine cikakken sunan mahaifinmu, asalinmu fulani ne usul da aka san su da kara da kuma alkunya, kafin kasuwanci ya sanya iyayenmu baro mahaifarsu. Mahaifinmu da muke ƙira da Baffa mutum me tsananin zafi da kuma tsayawa akan ra'ayinsa komai wuya komai runtsi. Su biyu iyayen su suka haifa shi da ƙaninsa Baba Alhaji, tun kafin samuwar mu 'ya'yansu suka ƙudurce a ransu cewar aure haɗi zasu yiwa 'ya'yansu, domin ɗaurewar zumunci koda bayan ransu.
Hamma Abubakar ne babban gidanmu da ya gado zafi da tsananin Baffa, sannan Hamma Adnan da yake da sauƙin hali da yawan mutane sun fi tsammanin ɗan Baba Alhaji ne. Saboda yanda ku san dukkanin halayya da ɗabi'unsu yake kwaf da kwaf, fiye ma da 'ya'yan da ya haifa a cikinsa ga son tsokala. A cikin 'ya'yansa Hamma Ahmad ne kawai suke kamanceceniyar ɗabi'u dashi. Ni ce auta kuma mace ɗaya tal a tsakanin 'yan uwana, na ci sunan kakata ta wajen Umma. Hakan ya sanya bata taɓa ƙiran sunana kai tsaye ba tare da ta sakaya ba, saboda zallar jinin fulanin dake gudana a cikin jikinta. Hamma Abubakar shi yake ƙiran ta da Umma sanda yake ƙarami saboda yaran makwabtan mu da suke wasa tare haka suke ƙiran iyayensu mata. Ya bi bakin su har muma muka zo muna ƙiran ta da sunan


'Ya'yan Baba Alhaji biyar mata uku maza biyu, Hamma Ahmad, Adda Azima, Adda Abida. Sannan Anwar da yake tsara na, da tsakanimu 'yan watanni ne, sai kuma auta Abasiyya. Muna da rufin asiri dai dai gwargwado da kuma wadatar zucin da muke gudanar da rayuwarmu dai dai ruwa dai dai tsaki. Akwai tsantsar ƙaunar juna a tsakaninmu, mun tashi da tarbiyyar da ya zama abin sha'awa ga mutanen unguwanmu. Unguwa ɗaya muke zaune sai dai kowa da gidan shi, a gidan su Abasiyya na taso domin daga yaye na koma can bacci ne kawai ke dawo dani gida.


Mun shaƙu sosai da Anwar fiye da sauran 'yan uwana domin shine muka taso tare. Tare aka samu a makaranta haka nan tare muke zuwa. Sana'ar gidan mu shine kasuwanci don su Hamma Abubakar suna ƙare makarantar sakandiri suka koma kasuwa. Tare muka yi sauƙa da Anwar a lokacin muka kammala ƙaramar sakandiri ya soma bin su Hamma Abubakar kasuwa.


Zaune nake na tisa kwanukan wanke wanke dake gabana ina shaɓar kuka har da shiɗewa, Allah ya sa ni a aiki gida gabaɗaya babu wanda na ƙi jini fiye da wanke wanke. Sau tari in an sa ni Abasiyya nake lallaɓawa ta yi mini, ni kuwa na goya ta na zagaye filin gidan tsaf da ita.
Ban ji shigowar sa ba illa jin ƙarar kujerar da ya jawo ya zauna a kai, na yi saurin ɗago idona ina kallon Anwar ɗin da shi ma ya kafe ni da ido. Ruwan wanke wanke na ɗeba a hannuna na watsa masa a fuska ina faɗin "me kai kuma ka tsura mini ido kamar wani maye".@


Dariya ya yi yana goge ruwar da na watsa masa ya ce"in da ni maye ne ai da tunin na gama dake yarinya, waya taɓa ki kike wannan kukan?".


"Umma ce ta sa ni wanke wanke".


"Umma ce ta sa ni wanke wanke ". Ya faɗa yana kwaikwayon muryata da hakan ya ƙara ƙular dani matuƙa. Na ɗauka kwanon samira da nufin jefa masa ya yi saurin kama kunnesa yana faɗin"afuwan Boɗɗiam(kyakkyawata) bari na taya ki".


"Da ka wanke kanka". Na faɗa ina goge hawayen da ya ɓata mini fuska, muna hira har ya gama wanke kwanukan tsaf, ya kai madafa ni kuma na soma share wajen. Dai dai sanda Umma take fitowa daga ɗaki ta saki salati tana cewar"oh! Hande min boni 'yar nan ba ki yi wanke wanken nan ba?. Wacce irin malalaciya ce haka?". Ajiye tsuntsiyar hannuna na yi na ɗaga hannuna zan fara rantse rantse akan ni na yi, ta dakatar da ni"kar ki ce min komai duk abinda zai fito daga bakinki ƙarya ne, ina ɗaki na ji sallamar Anwar kuma na tabbatar shi ya wanke kwanukan nan".


"Umma ita ta yi na dai taya ta mun ƙarisa ne".


Anwar ya furta yana fitowa daga madafan, jijjiga kanta kawai Umma ta yi ta ɗauki bota ta shiga banɗaki. Na sa ki dariya har da ƙyalƙyallewa har Umma ta fito daga banɗakin ban tsagaita ba ta rufe ni da faɗan, wai na dunga sausauta muryata duk gidan ya ɗauki dariyata ba. Ban ce komai na cigaba da sharan ta juya ga Anwar"ya kasuwan?".


"Kasuwa alhamdulillah, Baffa ne ya aiko ni daman na kawo cefane". Ya ƙare zancen yana mata nuni da baƙar ledar da take bisa tabarmar dake shinfiɗe a ƙofar ɗaki, da sai yanzu na lura da ita.
"To Allah ya amfana, ka kama hanya ka koma kar ka biyewa yarinyar nan da shiriritarta".


Dariya na kuma saka don ni sam bana ganin wuyar yin ta na ce"ai yanzu ma ina gama wajen Abasiyya za ni".
"Allah ya shirye ki". Ta faɗa tana komawa ɗaki, Anwar ya katse mini hanzari da faɗin"Boɗɗi zan koma zan taho miki da abin daɗi". Kaina kawai na ɗaga masa ya fice yana sakar mini da murmushi, ina gama sharan na zagi hijabina na nufi gidan su Anwar. Ina shiga na hangi Adda Azima tana shaya kayan da ta wanke gefe guda kuwa Adda Abida na hura wuta sai mahaifiyarsu Dada ake zaune Abasiyya tana mata tsifa.


Da gudu na isa wajen Abasiyya na wafce kifiyan dake hannunta ina faɗin"matsa ki bani wuri ni zan mata".
Dada sai faman faɗin"ku yi hankali" take yi amma kamar bada mu take yi ba, sai ture ture muke yi. Sai da Adda Azima ta daka mana tsawa sannan muka nutsu, na ji tamkar na saki fitsari a wandona domin ba kaɗan ba tsawa yake firgita ni.


"Ba kya ji ne ana yi muku magana?, kar ku nutsu a wajen nan ku gani".


Zunɓuro baki na yi ƙasa ƙasa ina cewa" halin su ɗaya da Hamma Abubakar shiyasa su Baffa suke son haɗa su aure, su je can su ƙarisa da masifa".


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________


Page 0️⃣3️⃣


Dole Abasiyya ta saduda ta bar mini na yi wa Dada tsifar, sannan muka koma gidanmu tare bisa umarnin Dada. Da ta ce mu koma muje mu taya Umma aiki mun baro ta ita ɗaya.


Sai bayan sallan isha'i su Baffa suke dawowa gida, tabbas iyayenmu maza sun yi katari da samun iyalai masu tsananin biyayya a gare su. Domin ko tsinke suka ajiye babu mai ƙetarewa. Zaune duk muke akan ƙatuwar tabarmar da Umma ta baje mana a filin tsakar gidan, mun kunna fitilar ƙwai da ya haske wajen.
Abasiyya, Adda Abida da Anwar duk muna zaune tare dasu. Baffa da Baba Alhaji kuwa suna zaure suna cin abincin. Ranƙwashin da na ji a kaina ya sanya ni saurin haɗiye raguwar dariyar da nake yi babu ƙwau-ƙwautawa. Ina dafe wajen na ɗago kaina da nufin tsala ihu, ganin Hamma Abubakar tsaye a kaina ya haɗe rai tamkar magribar ɗinya ya tursasa mini cinye kukan da nake shirin saka.


Cikin ƙanƙace idon da ya zamo ɗabi'arsa a duk lokacin da zai yi faɗa, ya nuno ni da 'yar manuniyar tsayarsa yana cewa" wai ke sai yaushe za ki yi hankali ne? ba ki san cewar muryar mace shima al'aurarta bane?. Sam ba ki iya zance cikin hankali ba sai faman ƙyalƙyala dariya kike".
Tsif wajen babu wanda ya tanka masa illa riƙe hannuna da Abasiyya ta yi dam a cikin nata. Ƙwafa ya yi ya fice yana faɗin"Umma na wuce gidan Baba".


Sai da na tabbatar da cewar ya fice na saki wani uban ƙara kai ka ce yankar nama jikinsa ake yi, Anwar, Abasiyya da Adda Abida suke ta faman lallashina, Umma kam ko kallona ba ta yi ba. Tsananta kukan da na yi ya sanya Hamma Adnan da Hamma Ahmad da suke cikin ɗakin fito a tare suna tambayar meke faruwa. Cikin tsantsar ɓacin rai tattare da furucinsa Anwar ya ce"Hamma Abubakar ne ya ranƙwashe ta wai don kawai tana dariya da ƙarfi".


Su ma lallashina suka yi, ban yi shuru ba har Baffa ya ƙwala ƙirar Anwar ya je ya shigo da kwanukan abincin da suka gama ci cikin gidan. Sannan su ma suka shigo Baba Alhaji ya ce"to jiniya waye kuma ya taɓo ki?".
Muryana har yana shaƙewa"Hamma Abubakar ne". Na fashe da wani kukan sai Abasiyya ce ta ƙarisa musu. Baba Alhaji ya fara faɗa akan ba ya son ana ranƙwashi gwara a kama ni a zane ni.


Da kyar na yi shuru ina sauƙe ajiyar zuciya a kai a kai. Baffa ya ce"ina kuka baro Azima kuwa?". Umma ta yi murmushi tana faɗin" ai tunda Abubakar ya nuna yana sonta shikenan ta ya ye shigowa gidan nan, ko za ta shigo bata yarda mu haɗu". Murmushi Baffa da Baba Alhaji suka yi suna haɗe baki wajen furta"Allah dai ya tabbatar mana da alkhairi cikin wannan lamarin". Duk muka amsa da amin.


"Kai kuma meye sai wani haɗe fuska ka ke yi, me aka yi maka?". Hamma Adnan ya jefawa Anwar da ya ke ta cika yana batsewa tambaya, Umma ta amshe zancen da faɗin"to har sai an masa wani abu, ai tunda aka taɓa 'yar gaban goshinsa daman yau babu zaman lafiya".
Kamar jira yake yi ya fara furzo da zancen dake cikinsa, idanunsa taf da kwantattun ƙwalla"fisabillahi Umma ko me tayi sai ya yi mata irin wannan ranƙwashin idan ya juyar mata da ƙwaƙwalwa fa". Sai da ya yi ƙwafa ya cigaba da"tashi Aishatu mu tafi a gidanmu za ki kwana".


Da sauri na tashi riƙe da hannun Abasiyya ina yi wa Umma a kwana lafiya, har mu kai ƙofar fita Adda Abida ta dakatar damu ta hanyar faɗin"to Anwar wannan fusata haka ko za ka rama mata ne?". Harara ya juyo ya watsa mata"ai don ya fi ƙarfina ne, amma wallahi da wani daban ne sai ya sha mamaki". Dariya suka tuntsure dashi Hamma Adnan ya ce"ashe ma duk ƙarya ce". Hamma Ahmad dai murmushi kawai yake yi don shi bai cika yawan magana ba, in ya zauna a waje har ya tashi ba za ka ji bakinsa ba.


Ko da muka je muka iske Hamma Abubakar da Adda Azima, zaune a bisa tabarma a filin tsakar gidan su na zancen. Tun a zaure daman Anwar ya ce damu in mun shiga kar mu kula su, mu wuce ɗakin Dada. Yanda ya kitsa mana haka muka aiwatar ni da Abasiyya kai tsaye muka wuce ɗakin Dada da muka tarar tana kishingiɗe bacci ya fara ɗaukarta.


"Kai lafiyarku?".


Ta furta tana tashi zaune daga kishingiɗewar da ta yi tare da mirtsike idanunta. Sai ƙunƙuni nake yi sai Abasiyya ce ta yi mata bayani ita ma tayi mini faɗa ta sigar lumana akan na dunga sausauta amon muryata yayin magana. Wai mace ƙwarai da kamewa aka san ta a ko yaushe. Ba mu fita daga ɗakin ba sai da muka tabbatar da Hamma Abubakar ya tafi.
Kwana biyu a jere Anwar ya ɗauka yana fushi laifin Hamma Abubakar har Adda Azima da ba ta san hau ba balle sauƙe ya shafa. Sai da ya ƙira shi ya nusar dashi illar abunda nake yi sannan ya ɗan sauƙa. Don mutum ne mai tsananin ƙaunar gudan jikinsa a ko'ina kuma a ko yaushe, matuƙar ka taɓa ɗan uwansa sai ka ga ɓacin rai a fuskarsa.


Ranar na tashi da matuƙar zazzaɓi ko kaina bana iya ɗagawa, ranar a gidanmu muka kwana. Kafin su Baffa su tafi kasuwa suka shigo suka duba ni dukkansu, Anwar kam an kaɗa an rawa ya ƙi fita kasuwa dole su Baffa suka bar shi. Ranar a kusa da ni ya wuni ko motsi nayi sai ya tambaye ni ko jikin ne, kwanana uku cikin wannan yanayin a wunin na huɗun na ji ɗan dama-dama.
Muna tilawar al-qur'ani tare Anwar a barandar ƙofar ɗakin Hamma Abubakar da Hamma Ahmad da ya komo gidan mu da zama gabaɗaya, duk ɗago idon da zan yi sai naga idanunsa a kaina.


"Lafiya? ni fa bana son kallon nan, da idanunka manya abun tsoro".


Murmusawa ya yi ya ce"ai kin fi ni manyan ido Boɗɗi". Taɓe baki na yi ina rufe ƙur'anin hannuna na ce"faɗa kawai ka ke yi, ai ko a makaranta in an gan mu tare cewa ake yi kamar ba gidan mu ɗaya ba. Su na ce mini 'yar baƙa".


"To ai farin fata bashi yake nuna mai shi kyakkyawa bane, hasken kawai muka fi ki amma kowa cewa yake yi ai kin fi mu kyau Boɗɗiam".
Yatsina fuskana na yi domin a tsakanin su gabaɗaya ni ce baƙar fata, farare ne tas hatta su Baffa da gwagwarmayar rayuwa ta sanya fatar su dafewa sun fi ni haske. Daren ranar bayan dawowar su Baffa daga kasuwa suka tattauna batun auren Hamma Abubakar da Adda Azima, mu na laɓe muna leƙo su daga cikin gida. Yayin da Dada take basu tabbacin Adda Azima ta amince da wannan haɗin. Tsabar murna ni da Abasiyya muka rungume juna tare da rugawa da gudu muka nufi ɗakin mu muka faɗa kan katifarmu muna sakin dariya. Raina fes zan rabu da masifa da ranƙwashin Hamma Abubakar.


A bakin su Hamma Adnan muke jin cewar an sanya bikin nan da mako biyar, babu jan wani dogon lokacin domin tuwana maina za'a. Dakan ɗaka shiƙan ɗaka.
Tunin aka fara shirye shirye na tanadin abincin da za'a ci a hidimar bikin. Su Baffa suka ware mishi jari na shi na daban suka bashi saɓanin da da duk suke tare a rumfa ɗaya.
Duk da kan ahalin a haɗe yake amma su Baffa ba su lamince da zama tare da suruka a gida ɗaya ba. A cewar su haka ne mabuɗi kowacce fitina dake tasowa tsakani iyali, idan ba ayi dace da surukar ƙwarai ba. Wani ƙaramin gidan dake layin gabanmu da aka sanya a kasuwa su Baffa suka saya a can zasu tare da zaran an ɗaura auren.


Shirye shirye ake yi gadan gadan, kafin lokacin komai da za'a buƙata a yayin bikin sai da su Baffa suka samar dashi. Lefe kuwa Hamma Abubakar ne ya haɗe abinsa tsaf babu sisin kowa a ciki da kuɗin da yake ajiyewa. Na sallamar da su Baffa suke musu a kasuwa.


Tunda aka sanya bikin na koma gidan su Anwar da kwana har lokacin ya matsu. A 'yan kwanakin nan za ka fahimci yanda Baffa da Baba Alhaji suke cikin tsantsar murna da annushuwa da ya bayyana a fuskarsu ɓaro ɓaro. Duk wayewar gari sai su sawa Hamma Abubakar da Adda Azima albarka tare da addu'ar samun dawamammen zaman lafiya a tsakanin su.


Tun ana sauran kwanaki goma bikin dangi suka fara zuwa, tsabar murna na rasa inda zan tsoma kaina balle samun matsuguni ɗaya. Ina son ganin jama'a haka domin ba'a taɓa yin wani taro a gidan mu da aka yi irin wannan cikar ba. Sai dai yanda kowa yake faɗin cewar tamkar ba daga tsantson Umma na fito ba, saboda duhun fatata ya sanya ni suƙurewa.
Ana gobe ɗaurin auren aka yi kiɗan kwarya a kofar gida, daren ranar bamu runtsa ba ni da Abasiyya tsabar murnar ganin wayewar garin gobe. Mu saka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login